← Book details Azal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 117

Sashe 36

Azal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ko a da idan ana masa irin haka ba baki yake budewa ba bale yau da yake ji kamar an dinke masa bakin ne?
Da idannuwansa ya ringa masu alamun amsawa sannan ya juya ya nufi ciki mai gadin get din ya duka yana gaishe shi har sai da ya bacewa ganninsa sannan ya mike ya rufe get din yana murmushi a bayane ya ce" Yan garina tabas yanzu kuka hadu da daidai da ku, daga manya har yara yanzu zamu san mecece sarauta"

A nutse yake ta takawa har ya karasa kofar dakin Bah

Budewa ya yi ya shiga da salama ciki ciki yana kai dubansa saman doguwar kujerar da ya hangi farare tas din kafafuwa

A nutse ya karasa yana jin sanyi na ratsa zuciyarsa sakamakon gannin Mah na bude idannuwanta jin tafiyar mutun da ta yi a kunnenta

Dubanta ta sauke saman fuskarsa lokaci daya tana sakin murmushi a tausashe ta furta" MALIK"

Idannuwansa ya lumshe yana jin sunnan da daraja a bakinta ya mika hannayensa ya tayata tashi ya zauna gefenta a nutse a hankali ya shiga ware rawanin dake kusa da habarsa sosai yana jin wata iska na ratsa shi ta ac, a tausashe ya ce" Mah, hw Are You?, yaya jikin Bah"

Mah ta sauke ajiyar zuciya itama a tausashen ta mike tana fadin " Da sauki, likita yace wai zai tashi, "

Tana fada ta karasa ta dauko kular abincin da ta tanadar masa ta kawo ta ajiye a baban plate mai dauke da su cokula da sauransu

Yana kallonta tana zubawa har ta gama ta dago plate din tana kallonsa ya fara magana kamar haka" Zan fita da shi, in sha Allah zuwa gobe nake so da yama"

Ido ta zuba masa sosai ta ce" Ka manta yanzu ba da bane?, koda za'a fita da shi sai dai Ni na fita da shi"

"Mah,"
Ya fada yana kallon kafarta mai yi mata ciwon

"Babu mai jinyarsa ne? Ina sauran suke?" Ya fada yana kallonta

Mah ta yi shiru tana bashi abincin ta masa alamun ya ci, dan ko rantsuwa ta yi ba zata yi kafara ba yau bai ci komai ba

Abincin ya ringa tabawa yana ta tunanin abinda ke ransa

Sai da ta ga ya ajiye ta zuba masa ruwa ta mika masa ya sha ya miko mata kofin a tausashe ta ce" Ka yi hakuri da duk wani abu dake iya taba maka zuciya, zan iya jinyarsa tunda ba daukanshi ake yi cikin dare ba, ka yi hakuri bayan adu'ar bakwai sai a fitar da shi din tunda a yanzuma ba wai ciwonsa ne ya hanna shi farkawa ba, alluran da ake masa dan ya samu hutu mai nauyin gaske ne, ina adu'ar Allah ya sa kafin nan ya farka da kansa cikin nutsuwarsa, ka ji?"

Kai kawai ya iya gyada mata, suka dan tattauna, gaba daya firar danarsa ne take yi, da bashi hakuri da nuna masa hukuncin ubangiji kennan, ta sake sanar masa ya bari mahaifinsa ya dawo hayacinsa ta tabata komai zai zo masa da sauki
Karshe dai ita da kanta ta raka shi har dakinsa wanda Salima ce ta yi tsaye aka masifar gyara dakin har aka gama tana tsaye dan fitowar nan da ta yi ta ga jikin mahaifiyarta sai da aka yi gyaran ne ta koma shi yasa ta cika dare

Da kanta ta kunna masa AC harda tunatar da shi addu'a kafin ya kwonta sannan ta tafi

Tana tafiya ya samu ya tube ya shige bayi yana ta tunanin Allah ya sa kayansa dake dakin nan sa shiga jikinsa , a killace dai suke , sai dai a ajiye suke sun jima haka

Tawul ya bude ya ciro cikin wrdrb din dake bayin mai madubi yar madaidaiciya
Bude shi ya yi daga cikin ledarsa sannan ya nufi waje ya rataye ya shiga wanka

Alwallah ya dauro ya fito ya haye salaya

A yanzu YUSUF ya san ya shigo wani fage da barci bai ganshi ba, shi da kansa ya san a yanzu ya zame masa wajibi ya yi sallah ya yi addu'a ya daga hannu ya roki Ubangijinsa kariya da taimako a kan baban abinda yake wuyansa

Ya jima saman salayarsa, kansa a kasa yake, ya sani a yanzu yana gaban wanda ya isa ya kifar da duniyar da yake ciki baki daya a cikin second daya, ya sani ne yana gaban wanda ya cenza masa zanen Kadara cikin yan sekwani, bai taba garajen wasa da ibada ba, dan ya yarda da kalmar LA'ILA HA ILALAH, ya kuma shaida MUHAMMADU RASULULAH SALALAHU ALAIHI WA SALAM MASOYINSA NE, ya san cewa akoy lokacin da rai zai yi halinsa domin ya yarda Kulu nafseen za'ikatul m'aut, kuma ya san akoy kwonciyar kabari bayan fitar rai, akoy ranar tsayuwa gaban Allah, kawai ya zamo cikin bayin nan wa'inda ta yiwu ba zasu samu rabauta ba? A yadda yake tunani kennan dan kuwa ka san zaka je ka fadi me ka yi? A ina ka yi? Saboda me ka yi? Kai da wa ka yi? A wajen wanda ya halicce ka, yake da ikon saka ka a wutar jahannama, ama kuma *KAKE YI DIN*.......( ASTAGFRULLAH WA ATUBU ILAIK)

Yana ganawa ya je saman gadonsa ya dauki babbar wayarsa ya danna yana kallon tarin miss call din da aka jera masa

Kai ya gyada yana tunanin ina shi ina iya amsa wadinnan tarin call din? Yana shirin aikawa ISHAK kira kiran SHAHEED ya shigo wayar

Kwonciyarsa ya gyara ya daga kiran kasa kasa ya ce" Yaya da kiran mutun tsakiyar dare kuma ?"

Murmushi SHAHEED ya yi shi dinma ya ce" kai da baka ajiye NAJEEBA da Nadia ba ai baka da time din da za'a kirayeka"

YUSUF ya yi dan shiru, cikin yannayin maganarsa ya ce" Nine zaka cirewa rawani dan ka rantse sai an nadani ko?"

"MALIK alkawarin Allah ne fa" SHAHEED ya fada a tausashe dan ya sani sarai YUSUF yanzun yana bukatar a tausasa masa

A tausashe ya dora da fadin " kai ka san tana binka, YUSUF saboda ka guje mata ne ka kaura nesa da ita, kai ka san na san wannan ne dalilin da ya sa ka fito daga garin nan , dan ba wani rikici da ya isa ya saka ka yin nesa, ama kuma abinda ka ki yarda shine , ita fa danko ce, du inda ka yi tana biye da kai"

YUSUF ya bude idannuwansa da suka yi ja saboda gajiya da tunani kala kala, kasa kasa ya ce" Kai ka san sarauta ba tawa bace, ba rayuwar da nake iya yi bace"

SHAHEED ya yi murmushi ya ki bashi amsa a kan maganar nan, saima tambayar da ya masa kan awon hular dake masa

YUSUF ya ce" Hula kuma? Me za'a yi?"

SHAHEED ya yi murmushi ya ce" Dinkunnanka ne sun yi nisa sosai, bani da awon hularka ne ranka shi dade"

YUSUF ya dafe kai, hakane fa yanzu sai ya yi dinkunnan nan ko? Da hulunan, tunda ba'a zaman fada da gajeran wando
Firar dai ta dan dauki lokaci kafin su yi salama ya kwonta yana sake yin
addu'a

Washe gari tunda duku duku gidan ya dauki haya haya, wato bangaren Honorable

Tunda gari ya fara haske kadan aka ringa shigo da takardu na neman son gannin MALIK
takardun dake sauka hannun matar Honorable mahaifiyar Salima saboda a lokacin dole baki daya kowa ya fito falo baba dan a karya a kuma jirayi fitowarsa, dan sun sani ba maganar su fara neman fitina a fili bane, koda zasu yin sai dai su samu makami ba dai fito da fito da YUSUF dan BELLO ba!

RAUDA na daya daga cikin wa'inda suka farka da wurin har aka yi yan aikace aikacen kayan kari da ita, a daidai lokacin sunna wajen diner baba, diner din da tabas in har zai karya a nan ne zai karya sunna ci gaba da kimtsa wajen dan Mah ta fito tuni ta kawo mata sutura ta yi wanka ta cenza , sai dai bata zumbula hijabin da Salima ta bata ba, ta dai yafa gyalen mayafin a kanta sunna dan dauki ajiye da Salima da kuma su Musulima wa'inda suka ba Salima mamaki ainun, domin a lokacin da suka shiga kicin yan matan nan uku kowace ta tambaya a bata girkin MALIK ne ta girka, hakan ya ba Salima mamaki dan a tsakaninsu a lokacin suka shiga yiwa junna kallon ke fa? WHO Are You da zaki nemi a baki girkin Malik? Me kike nufi da hakan? ................karshe dai sun zamo iyayen gida ne dan babu wace ta taɓa girkin sai bin su Salima da suke sunna kokarin saka su ko hannasu da son basu order na yadda zasu shirya komai har sai da hakan ya saka RAUDA yin murmushi ta girgiza kai dan kwarai ta gane shirmen yaran nan da abinda suke nufi, hakan sai ya bata dariya da mamakin yan matan zamani, to ita akoy wani girmemen katon da zata gyara dan ta birge? Sam mata basu san abin so bane Bama, uhum wahala!.......

🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔
Azl 21
*Tallah, tallah.....tallah manyan hajiyoyina*

Bismillahi rahamanin rahim

Metaforce online business ne na crypto
Wanda aka tabbatar da halaccin sa ,sannan aka tabbatar da cewa ba irin wannan platform din bane da ake gudu da kudin mutane.....domin Metaforce zaka shiga ne da kadan ka dauki da yawa, da wannan Hajia Ummu Khalil wace ke zaune a kasar Nigeria sananiya ce fitaciya ce mai dauke da numbobin waya kamar wanann 07038708382 ta kawo mana hanya mafi sauki dan samun ci gaba.......ku saurara dai
*METAFORCE*
Yana da level 1_12
Idan Zaki level 1 Zaki Fara da Doller 5,,level 2 Doller 10 ,level 3 Doller 20 Haka dai har 12
YADDA AKE SAMUN ALKAIRI A METAFORCE

💃🏼 Kina Gama register za'a Baki TR coins na adadin level din da kikayi,ko a iya su kin Mai da kudinki fa idan akayi lunching🏃🏻‍♀️🕺😁 .....WASHE BAKI SOSAI HAJIATA....YEAH KO A IYA SHI KIN MAIDA KUDINKI BALE GA WANI DANDANO MAI ZAKI.....

*Refferel bonus duk mutum 1 fa idan Kika kawo za'a Baki adadin abinda yasa yayi level din, banda 2 na farkon level 1 da 2*
Chapter 36 · 0% Book details