← Book details Azal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 117

Sashe 52

Azal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana murmushi tana kallonta ta ce" Ki fa ci, Mah tace ki ci sosai, tana dakin yaya MALIK ne, kin san da wahala yanzu kuma Mah ta bada Abdul?, bale idan ya nuna ba zai rabu da ke ba, ita kuma fa ta yi y'a, babu mai rabata da y'arta sai mutuwa da aure"

RAUDA ta yi murmushi, a ranta tana tunanin abin ai sai ya yi yawa, ita da kanta da ace namiji ne ya kai shekarunta da tabas ta wuce riko, bale kuma ta karra kawo wani? A'a in sha Allah da zarar ta warware zata je banki ta kwashe duka kaf kudadenta ta gyara gidan inna sosai sannan ta siya masu kayan abinci sosai, kuma ta saka shi makarantar kudi ta daukar masa Aminu mai adaidaita ya ringa kaishi yana dawo da shi, kuma ta saka hukuma ta shiga tsakaninsa da su Mama, kafin ta koma ta rama abinda suka yi mata, domin ta kudurci aniyar ita da su za'a dora ne da kare jinni , biri jinni!

Ta dan taba abincin, barci ya ringa sandarta, ama bata kwonta ba har sai da likitar ta zo ta karra saka mata karin ruwan nan , ta kuma bata magunguna sannan ta tafi, tana tafiya da yan mintuna barci ya yi awon gana da ita, hakan ya sa Salima ta daidaita mata sanyin acn ta kashe mata fitila ta kwashe kayan abincin ta rufo mata dakin ta tafi wajen sauran yan matan dan su fitar da kayan girki, domin kwarai akoy yan aiki ama tunda iyayensu suka nade hannaye suke harkokin gabansu sai Mah ta nuna masu ita fa ba zai taba yiwuwa tanada yan mata kamar su wasu su ringa masu girki ba, a dole sauran da basa so suke haduwa da wa'inda hakan ya masu daidai dan dama sunna son girki suke yi tare

Kusan wuni RAUDA ta yi tana barci, ko Abdul dabara aka yi ta masa, karshe aka kunna masa tv sai kawai ya yi zaune sallah kawai ke tashinsa, shima sai Mah tace idan bai tashi ya yi sallah ba zata dauke TV din abinka da yaro tsaf ya yi wuri ya ajiye RAUDA yake sha'anin sa, cikinsa ba yunwa, jikinsa da sababin kaya, ai sai farin ciki

Sai da yama Mah ta tashi RAUDA da kyar dan abin maganin nan bai barta ba ta saka ta yi wanka ta cenza tufafinta zuwa doguwar riga marar nauyi ta dauki mayafinta ta bude shi ta yafa a kanta sannan ta fita wajen su Salima tana takawa a hankali ko zata ji dadin jikinta sosai dan ta jima a waje guda a kwonce tun jiyan nan, gashi bata saba ba

Sunna nan sunna yar fira a baban falon gidan, har magariba ta kusa shigowa Mah ta fito da sauri, ta dube su ta ce" Yan Matana zamu je asibiti an ce abanku ya farka wai, Please ku kula da kanku sai na dawo, baby ki sha maganinki fa, sai na zo"

Ko iya tsayawa ta ji adu'ar da suke yi bata yi ba ta fice, bayanta su Hajia suka fito summa ko ku ci kanku basu ce masu ba suka ficewarsu, hakan ya sa Salima dake ta murna ta nufi mahaifiyar dawowa jiki a sanyaye ta zauna hadi da dan dafe habarta da yatsarta manuniya tana kallon RAUDA dake mata alamun ta ware ba komai

Murmushi ta yi mata ta sada kanta bata iya sakin jikin nata ba, karshe kiraye kirayen sallah ya saka su mikewa kowace ta nufi hanyar da zata daura alwallah dan yin Sallah, RAUDA kam da Abdul ta tafi dakin Salima dan ta fi sakewa a cen, bale yanzu da Mah ta fita

Tun sunna saka ran dawowar Mah har suka fara cire rai, domin su Hajia tuni suka dawo kuma basu sanarwa kowa yadda jikin marar lafiyan yake ba, hakan ya sa suke cikin damuwa dan sunna son jin yaya jikinsa sosai, bale ita RAUDA ta fi damuwa bata san dalili ba, ko dan ta ga a duniya wannan matar dake nuna mata soyaya tana matukar son wannan bawan Allahn ne? Ita dai tana masa fatan samun lafiya har cikin zuciyarta

Gannin karfe tara tana neman yi ta karɓe wayar Salima da Abdul ke buga game din da ko iyawa bai yi ba ta ce maza ya mike ta masa wanka ya cenza kayansa

Kayan da ta dauko ya kalla, riga da wando ne na barci da pant, pant dai pant na mata aka hado a cikin kayan nasa na barci, ita kuwa bata taɓa Sannin wai ba wandon maza bane dan haka tace ya shige su je

Da yannayinsa ya shiga make kafada yana fadin" Aunty, to sai nawa zan yi wankan? Ni dai a'a, mura zata kamani, a'a aunty, kuma ba zan cire kayan nan ba kar aje wani ya dauke min, ina son su"

Da yannayin rarashi tana rike mayafin rigar jikinta ta ce" Abdul dina, mura ba zata kamaka ba, ka ga a nan sau uku ake yin wanka fa, kuma kayanka babu wanda zai dauke, mu je dan albarka na maka wankan ka ji?"

Shi kam sai ya ga abin wani iri, kuma yau auntynsa ce zata masa wanka bayan a da ba ita ke yi masa ba? Abinka da yaro sai kawai ya juya ya diba a guje yana fadin shi dai a'a ba zata yi masa wanka ba, ba zai cenza kayansa ba!

Ido ta zarro, gannin dare ne fa, kuma ga gida na yan gayu ba hayaniya suka cika so ba, gashi a gidan ta jima da gane ba kowa ke ra'ayinta ba,sai ta dauki sauri tana fadin"
Azl 29
*Tallah, tallah.....tallah manyan hajiyoyina*

Bismillahi rahamanin rahim

Metaforce online business ne na crypto
Wanda aka tabbatar da halaccin sa ,sannan aka tabbatar da cewa ba irin wannan platform din bane da ake gudu da kudin mutane.....domin Metaforce zaka shiga ne da kadan ka dauki da yawa, da wannan Hajia Ummu Khalil wace ke zaune a kasar Nigeria sananiya ce fitaciya ce mai dauke da numbobin waya kamar wanann 07038708382 ta kawo mana hanya mafi sauki dan samun ci gaba.......ku saurara dai
*METAFORCE*
Yana da level 1_12
Idan Zaki level 1 Zaki Fara da Doller 5,,level 2 Doller 10 ,level 3 Doller 20 Haka dai har 12
YADDA AKE SAMUN ALKAIRI A METAFORCE

💃🏼 Kina Gama register za'a Baki TR coins na adadin level din da kikayi,ko a iya su kin Mai da kudinki fa idan akayi lunching🏃🏻‍♀️🕺😁 .....WASHE BAKI SOSAI HAJIATA....YEAH KO A IYA SHI KIN MAIDA KUDINKI BALE GA WANI DANDANO MAI ZAKI.....

*Refferel bonus duk mutum 1 fa idan Kika kawo za'a Baki adadin abinda yasa yayi level din, banda 2 na farkon level 1 da 2*

💃🏼 Ga Kuma garabasa na spillover
Ko kin kawo mutane ko Baki kawo ba kina iya samu 💃🏼💃🏼musamman tunda Ni da Zan Miki register Ina aiki sosai (wauh fantastique)

Spillover shine zakiga ansa Miki mutum a kasanki ,Kuma a biyaki fa ko Kuma a cike Miki biyu ko dayan farkon nan💃🏼 (magnifique)

Da Dollars suke biya idan kinaso Zaki iya siyarwa duk dollers din Kika samu a take a tura Miki kudinki cikin account 💃🏼💃🏼💃🏼 (da wa kika ja Madame?)

Metaforce Babu FADUWA Babu asara a ciki...... Ku zo mu kafta duniyar sananu mu samu yanci, nema sai da nema, ki shigo Mu je, kasuwanci mu babu algus ba cuta, zaki kwashi kudinki koda baki kawo kowa ba😍😍😍 sai kun zo

Da sauri RAUDA ta biyo bayansa tana fadin" Kai, Abdul, zo nan, baka gannin dare ne ba kyau gudu da dare? Zo nan ina wasa da kai ne?"

Tana fada tana karasowa falo ne, hadi da ja ta tsaya ta rike tsatso tana hada gabas da yama irin bata son wasan nan dan ta kula idan ta ce zata tsaya yi masa dariya yana iya janyo mata magana ne

Kai ya dago daga danna wayar da yake yi ya zuba mata ido, irin tsayuwar da ta yi tana tafka harara ta saka shi juyawa dan gannin abinda take yiwa hararar , gannin Abdul na nufarta yana shashekar kuka alamun yana iya fashewa da kuka ya saka shi tabe baki hadi da girgiza kai a ransa ya ayana' dama kema ba fita rainon kika yi ba, kuma sai Allah ba baki wani rainon, bawan Allah, Allah ya sa kar ta rikita yaron nan'

" Kai, yaushe na fara maka magana kana raina Ni? Nace mu je na maka wanka ka cenza kaya ne zaka wani fita a guje? Ya maka kyau wuce mu tafi!" Ta fada tana zazaro masa ido da nuna masa hanya hadi da fitar da pant din dake hannunta dan da shi a hannunta take nunawa tana yin fadan

Idannuwansa ya kankance yana kallon abin da dukkanin son ya gane abinda ke hannun nata, ita kuma tunda ta fito Allah bai kai hankalinta kan babar kujerar falon na, ko dan ba abinda ya fitar da ita ba kennan, duk kuwa da irin yadda hancinta ke jiyo mata kanshin turaransa wanda zuwa yanzu ta gama gane nasa ne, bata saka cewa shi din ne a wajen ba, dan ta gama hardace turaransa koda baya nan kana iya jiyo kanshin a waje, tsabar nacin kanshin turaran ya sa duk inda ya shiga yakan bar kanshin ne na dan lokaci bale wajen da yake rayuwa

"Wandon waye a hannunki kuma?" Ya fada yana asalin ajiye wayar hadi da zuba mata ido

Har ga Allah bata taɓa kawowa zata ji muryarsa a kusa kusa ba, hakan ya sa ta daka tsalle hadi da yin dan ihu tana dafe kirjinta hadi da kallon inda yake zaune

" Haba bawan Allah sai ka saka na kamu da hawan jinni mana!" RAUDA ta fada, kanta tsaye, ba tare da ta ankara da wa take maganar ba, har sai da ta dasa aya sannan ta sake kallonsa a sace, a hankali ta sunne kwayar idannuwanta kasa kasa ta furta" Sorry Please" sannan ta juya da dan sauri da nufin tafiya

"ZO NAN" ya samu harufan bakinsa da fitarwa a wannan yannayin
Chapter 52 · 0% Book details