← Book details Azal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 117

Sashe 80

Azal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A dole ta je ta zauna din, ita Kuwa RAUDA a lokacin ta zuba maganin Mah a dan kofinta ta mika mata, bakin nan a cune kamar zata fashe ama ita batama san a cikin yannayin fushi take ba, Mah din dai ke hankalce da ita, shi kuwa tunda Hajia ta fara fada ya yi gaba zuciyarsa da matsanancin mamakin y'ar cen, daga baya kuwa ya yi wuri ya ajiyeta a ransa yana ayyana' Mai hali da wahala ya daina halinsa, idan ka ganta kamar ba zata ciza dan yatsa in aka saka mata ba, bayan duk wani rashin ji a kanta ya kare, Allah shi kyauta, wai matata ta yiwa haka? oh!"

A tausashe Hajia na dubanta ta ce" Bana son idan ina maki magana na ringa yi maki a haka, ko menene halinki wanda kike da a gidanku ya kamata ace kin fahimci yanzu fa dole ko daidaita wasu abubuwan, Amnah ke budurwa ce, auren farko aka yi maki, kuma aure mai darajan gaske, ke ko a idon mijin naki bakya tsoron ki rage daraja ne? yaya za'a yi ki ringa abubuwa kamar ba mace ba? mace fa an santa na da kamun kai da aji, ke ya kamata ya ringa rawar kafa idan ya ganki ko waye shi, ba wai ke ki ringa abubuwan nan ba, namiji fa idan ya rainaka shikenan, kuma kin ga idannuwa fa a kanki, bai dace ace ko wani lokaci aka daga ido ana iya ganninki ba, ina darajarki take? ke da ya dace ace ko Ni sai ta kama zan ga fuskarki? kina bangarenki kina mulki daidai gwargwado? haba dan Allah, yanzun da binshi zaki yi? ki duba fa ki ga jikinki, suturar nan ai ba wace ta dace ace kin bi bayanshi bane shi ya dauki wanka kamar zai je hawan sallah ke kuwa da wannan abin? ki yi anfani da damar ki ki tabatar da kin gyara zamanki da mijinki sannan ki so ahalinsa, ba kamar mahaifiyarsa, idan kika kiyaye abubuwan nan na tabatar maki mijinki zai so ki, zai mutunta ki kin ji?"

A lokacin da Hajia ke yi mata nasiha , irin wace zata fisheta, ita wasu tunani take yi daban na abinda zai fisheta

Kwarai kamar yadda Hajia tace ita din mai daraja ce hakane, kuma tunda ta zo gidan nan suka yi watsi da ita take dauke da haushinsu
Babu ruwanta da wani umarni ya bada ta je bangaren mahaifiyarsa, babu ruwanta da wani rasuwa aka masu, ko menene ya dace ace sun bata kulawa ta daban da ta kowa, ama tsabar son kai suka ki yin hakan kuma yanzu ake son nuna mata fi'ili
Idannuwanta kuwa a kai a kai sai sun sauka kan RAUDA, a bayane take dan dantse lebenta, a zuciyarta tana ayana' Lalle baki san wace Ni ba, dan na yi zaman watannn nan a gidanku ba yana nufin na zama sharar da zaki taka ba, ko Wacece ke zan binciko zan nuna maki Ni din Wacece, na tabata ko waye ubanki ba fin nawq kudi ya yi ba, kuma na tabata du rashin jin ki baki kai Ni ba, zan san dalilin da yasa kika zageni kafin na shake wuyanki har sai kin kusa barin duniya, walahi na amshi tayin masifar da kika min, ko Ni Ko ke!'
(Uhum, a yi dai mu gani, wannan tashin tashina haka)

Hajia a tausashe ta sake fadin" Ki yi zamanki a nan bar dare ya yi a raka ki a mutunce, yanzu zan sa a kwashe kayan ki a kai cen din a kimtsa maki, bai dace ace an ga shigarki da rana haka ba kin ji?"

Kai ta gyada, a lokacin ita kuwa RAUDA ta lumshe nata idannuwan da suka yi mata wani irin nauyi

Kasa kasa ta furta" Mah, zan je na yi girki"

Mah ta sake dubanta, da kula ya ce" Baby zaki iya? Sai na ga kamar baki da lafiya?"

RAUDA ya girgiza kanta a hankali ta dauki jug din maganin Mah ta mike kasa kasan itama ta furta" A'a Mah, i'm fine, sai kin zo"

Daga nan ta juya ta fice a falon , zuciyarta a cinkushe, tana jan carbinta ta karasa bangaren Mah lokaci daya ta je wajen kujeru ta zauna tana dan yatsina fuskarta, hakan ya ba dimple din kusan idannuwanta damar lotsawa

Da dan takaici ta fitar da numfashi kadan daga bakinta a hankali ta furta" Aikin banza marar tarbiyya, ki shigo ki tardo manyan mutane ki kasa gaishe da kowa, ana magana kina kada kafa a gaban iyayenmu, kuma ki ce zaki tafi baki gaishe su ba? Ni bana son rashin da'a waye sa'anta a nan? Sai wani firirita take yi da takamar an san ita Wacece? wace ke banda shara ajebo?, abu daya ya tsallake fuskarki daga hanuna Mah ce!, in ba dan wannan ba da na gwada maki Ni din wace da kika zagar min uba, wace ke kuwa banda mace marar aji, wai gidan aure ne aka kawo ki kina azarbabi haka? shirme wata nawa da auren kina nan kina shirme?, mtssssss auren naku da babu wanda ya dama?...."

(Mu dai ya dame mu☹️)

Sosai take fada a zaune har ta cinye lokacin da ita da ganta bata ankara ba sai da ta dago dan ganin time ta mike da sauri ta nufi kicin din tana tunanin abinda zata dafa, domin haka kawai take jin ita kanta ya shafe ma bata san me zata dafa bama!

A cen inda ta baro su Mah,Hajia ta jima tana yiwa Amnah nasiha da nuna mata ya dace ko me ta nado a turminta ta gyara dakanta dan uwar mijinta uwa ce a gare ta kuma bata da wata wace ta fi ta

Mah na zaune ne tana bin su da kallo, ama a ranta tunani ne kala kusan hudu ya hadu ya rarraba mata yannayi

A lokacin da akace ta bi shi, da farko ya so dakatar da hakan, domin a yannayin da ya yiwa fuskarsa ta gane ya so ya hanna hakan, sai dai idannuwanta sun nuna mata wani abu, domin a lokacin ne ta ga ya kuma kallon Baby, bayan kallon da ya mata fiye a irga tunda ta zauna, kallon da ya bambanta da wanda yake yiwa SALIMA, kallon da ta fadawa Bah tun cen baya ya nuna mata ba komai bane kar su ce wani abin ne, tana hankalce da shi a lokacin da ya ga ta dago da sauri sai da ya yi murmushi sannan ya nuna su je!.....Hakan ya matukar daure mata kai

Sai abu na biyu, abinda Baby ta yi!
a zamanta da baby, zata iya cewa yarinya ce mai hankaltuwa da abu komai kankantarsa ko girmansa, ta kasance mai kwontar da hankalinta a kan komai, abu komai kankantarsa baya shige mata, ta yaya Baby zata dube su tace wai bata gane ana nufin Amnah ce matar YUSUF ba? me yake faruwa da Baby ne?, a irin abinda ta ga yau ta yi, zata iya rantsewa bata taɓa gannin ta yiwa ko bawan gidan nan ba, wani yannayi mai tafe da rigima da neman fitina da wani yannayi mai zafin da kuma alamun son fashewa da kuka?......Kar dai duk irin yadda ta ringa bin su da tambayar nan cewar kin amince da auren wane? ka amince da auren wance dan kawai su yi kokarin kwatanta mata da wani abu komai kankantarsa suka yi mursisi dan su raina mata wayo ne?
....
Sai abu na uku, yannayin Hajia!
Hajia uwa ce a wajenta
hakan da ta sakawa ranta ya sa take zaune da ita duk rintsi
a rayuwa ta sha wulakancin Hajia wanda kare ba zai dauka ba
a yanzu yannayin nan da ta samu sabo yana so ya saka ta fito fili ta tambayeta sanyi take son yi a kanta dan ta sakankance ta yarda cewar itama mutun ce sai ta sake da ita ta sake masheta baiwar da bata da ubangida?, da ace Hajia zata dubeta a matsayin y'a da ta dora kanta a saman cinyarta ta yi mata kukan dake kirjinta na tsayin shekaru ko komai ya wuce a ranta, sai dai zuciyarta na cike da matsanancin tsoron kar baya ta dawo gaba a sakata yin faduwar tasar da ba zata iya gyaruwa ba!

dayan abin kuwa yarinyar nan ce dake gabanta zaune
Tun daga kan yarinyar har zuwa dan yatsar kafarta ta gama gane cewar yaronta ya samu daidai da zamaninsa kuma Allah ya hada shi da irin classs dinsa....., haka kawai take cike da kukan zuci, wanda zuciyarta ta fi bata amsa daya tak *ME KIKE TUNANI ANDIYA? KALAR ZAREN KALAR KAYAN, AI DAMA DA WAHALA ALLAH YA HADA ABINDA BA DAIDAI DA JUNNA BA, TA YIWU ITA DIN RAINONSA CE!* , walahi wannan kalamai su ke gigita mata duniya, kuma ta fada ta karra da babar murya domin ba zata iya yin mugun son kai fiye da kima ta yadda zata take abinda ke gabanta ba,
Amnah, tana bata tsoro
yannayin Amnah na firgita tunanin ta, bata san me yasa ba, ta dai san cewa ba bada kama ne ke gabanta ba, zahiri ne!

Sunne abubuwan da suka hadu suka yi mata kwawanya a kwonyarta

"AMEERAH, ki je bangaren ki da ita, dan bata da wani wajen da ya wuce cen, zan sa a kawo mata suturarta da ta dace da kaurarta, zan sa a je a kimtsa mata bangarenta yadda ya dace, idan aka yi sallar isha'i zan saka datijawan mu na arziki da kannen ta su hadu su raka ta, ki yi hakuri da abinda aka yi maki da farko, ina mai tabbatar maki na za'a maimaita ba, " Hajia ta ajiye maganar a nutse, sannan ta sake kallon Amnah dake zaune, kanta a sade, domin duk yadda ta so yi masu kiririta da bin su da ido cikin ido ya gagareta, kai abinda ke kai kawo a cikin zuciyarta ya fi komai yawa, dan haka sai kawai ta sada kanta tana tunanin abinda ke iya fitar da ita
Chapter 80 · 0% Book details