← Book details Azal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 88 OF 117

Sashe 88

Azal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kwonci tashi asarar mai rai
Yau RAUDA ta wayi gari cikin wata sabuwar rayuwar da ta sake sakata a halin tunanin yau da gobe kafin ta dangana ta ajiye gefe saboda mutanen dake zagaye da ita tamkar ana yin wata sabgar ne

Tunda safe Atu ta sauka a gidan, Salima kuwa duk kin da ta yi sai da ta kunsa mata kunshi dan Hausa harda yan yatsunta sannan ta amso dinkunnan da aka yi mata tace a gobe sai ta saka, ko da safiya ta yi da ta yi wanka a dole ta sa ta saka suturar ta yafa mayafi ta zauna tare da bakinta da yan gidan

sun mike a fira, Bah ya yi kira cewar ta zo su yi salama da Uncle dinta, dan a yau yau zai daga zuwa kasar waje dan neman lafiyarsa kamar yadda MALEEK ya sanar masu, kuma kiran da aka yi mata bangaren MALEEK din ne zasu je dan su Bah din sunna cen tare da uncle Umar da likitan da zai yi masa jagora har zuwa ƙasar wajen, kasancewar yau Asabar bai fita ba , sai suka same shi a cen din gaba dayansu

Hijab ta so daukowa, sai Mah ta nuna mata mayafinta bashi da wani laifi, sannan ta nuna ATU da Salima su yi mata rakiya

Har zata fita a dakin Mah, Mah din ta yi kiranta, ta mike ta dauko turare ta karaso ta shiga fesa mata fuskar nan tamau a hade danma kar tace a'a, sai da ta yi mata wanka da shi sannan ta umarce ta kan ta je, ta juya ta fita tana waiwayan Mah din, domin tun jiya da dare ta ga yannayinta wani iri, kuma ta yi ta tambayarta amsar daya ce lafiya kalau , ba komai.

A nutse suke takawa, tana bin gine ginen nan da kallo, dan rabonta da ta karewa wajen kallo tun kaurowarsu da gabanin aurenta, tunda ta shiga takaba kuwa bata tako ta nan baban filin gidan ba, ta dai fita ta cen baya zuwa bangaren Hajia, sai yau da suka fito ta ringa gannin gidan sai karra kyau yake sanadiyar shuke shuken da aka zuba ta ko'ina, flawowi ne da shuke shuken fruits kala kala, du sun fara tasawa gidan ya fara daukan Color na shuka masha ALLAH

tafia suke yi a nutse, a jikinta dinki ne na lesh fari kal mai dan digo digon somon sai dan kyalkyalin da ba za'a rasa ba, an yi mata ɗinkin sket da riga budadiya ama bakin tsayin rigar gwuiwarta dan sam bata sauka kasa ba, hannayen ne a bude sosai sai wuyan da aka yi irin baban wuyan nan da baya yiwa ramamu kyau
ta yi daurin dan kwalin da ya fitar da gashinta sosai ta baya, sai mayafin da ta yafa a saman kanta, mayafin kuwa shara shara ne sosai, hannayenta ba komai dan ko wayarta ta baro a dakinta,, sai takalmin da ta saka plat mai tsadar gaske

Sunna daf da shiga get na farko bayan sun gaisa da sojawan dake kofar baban sojan dake ja gabar masu tsaron wajen ya zuba mata ido da kallon da har sai da su Atu suka ankara da shi,, ama ita ta yi tamkar bata ganshi ba, dan ta riga ta tsarawa kanta soyaya kuma ba dai kwana kusa ba gaskiya, shi yasa ta dauke kai a lokacin da Atu ta ce"

Shi yasa ta dauke kai a lokacin da Atu ta ce" Ama gayen cen ya iya kallon kurula, ji min mutun, ta yiwu kowa idan ya zo sai ya kure shi da kallo haka"

Salima ta sake waigawa da sauri ta dauke kanta dan ita tsoronsa take ji tun ranar da suka zo rakiyar Amnah kiri kiri ya hanna masu busa shiga, kuma yan rakiyarma sai dai da daidaya aka ringa shiga ana fitowa, irin yadda ya tsare gida a ranar harta manyan sai da suka tsorata, yau kuma shine da kallo irin wannan?

"Uhum, wancen? barshi inda kika ganshi, walahi mugun miskili ne, kuma baba ne a harkar soja, kin san shi ke jagorar sojawan gidan nan kaf, Ni tsoro yake bani, Allah ya sa kallon da yake yi din ba na ya koramu bane!"

Jin haka ya sa RAUDA jan birki, itama ta juyo ta dube shi kamar yadda ya dan mike daga tsayuwar da yake gannin ta tsaya kuma har ta dube shi

har ga Allah ya san a aikinsa akoy kiyaye irin abubuwan nan, bale a wajen da yake shi ke hanna yarensa shagalta da komai da gindaya masu sharudan ba su ba bibiyar yan matan gidan koda barori ne bale ya'yan gidan, sai gashi yana ji yana gani kaffafuwansa na sake matso shi har ya samu kansa da tsayawa dan nesa kadan da ita yana sake yi mata kallon da ya wuce ka'ida yana gannin yadda Salima ta sake tabatar masu ta tabata kora su zai yi, ya kasa ce mata ba kora su zai yi ba, karra kallon wannan halita dake gabansa zai yi koda kuwa ya san hakan na iya jaza masa yin nesa da aikin nan mai tarin ni'ima

Murmushi ya yi ya ce" Yan matah....., bakuwa ce ke ko a nan kike?"

RAUDA ta lumshe idannuwanta tana jin tamkar ta yi wani mulmulalen ashar, dan har ga Allah sai ta ga ana neman wulakantata ne a wulakanta takabarta, duka duka yau fa ta gama ko? shine har za'a samu wani dan balaja'un da zai tsayar da ita?
Takaici ya sa ta juya bata tare da tace da shi ci kanka ba ta nufi ciki

Da dan sauri ya dubi Salima da mamakinsa ya gama kasheta yana fadin" Kanwata, dan Allah ke ki saurare ni"

Salima ta yi murmushi tana kallon sa

Shima sai ya rasa me zai ce, ta inda zai fara, abu daya ne ya sani yana kallonta ya ji ta gama yi masa dari bisa dari, dan kuwa ya ga halitta gannin idannuwansa

Ajiyar zuciya ya sauke yana hangen ta kama babbar kofar falon ta bude ta shige a raunane ya furta" Ina son ta!"

Salima ta dan zaro ido, ba dan komai ba sai jin muryarsa ta cenza daga yannayin karfi da umarnin jiya, zuwa laushi a yau

Murmushi ta yi, ita kuma hankali kwonce ta ce" Ka tabata da gaske kake?"

Ya yi murmushin shima yana kallonta ya ce" Ta fi karfina ko?"

Salima ta dan baza hannayenta tana sake kallonsa ta ce" Ya danganta, da wani irin mutun ne kai, idan har kai din namiji ne da ya iya son mace , da kuma da mace, to tabas zan iya baka y'ar uwata, ama kafin nan ka fara neman izini wajen Bah baba idan ya baka an gama "

Tana gama fadi ta juya tana murmushi ta yi ciki, shi kuwa ya rasa fargaban maganar ya tambayi uban gidansa maganar nan zai yi ko kwarin gwuiwar tunkarar uban gidan nasa saboda ta cencenta? abinda ya sani daya ne yarinyar nan ta isa a cikin isasu tunda har ta iya dukan zuciyarsa a gannin farko, ashe y'ar gidan ce? ya rab ka sa abin ya zo min da sauki

A lokacin da Salima ta karaso, ATU na tsaye bata shiga ba, hakan ya sa ta kalli hanyar da ta tabata a irin yadda RAUDA ta yi gaba da zafin rai yaci ace ta shige tuni

Idannuwanta suka sauka a kan RAUDAR a tsaye, hannunta rike da fari kal din labulen falon, idannuwanta kuwa a risine tamkar wace ke kallon wani abu ko ke gudun kallon wani abin

Kasa kasa ta ce" Menene? lafiya?"

ATU ta sauke ajiyar zuciya tana jin tamkar ta gudu, sai dai ta san ba damar guduwa

A cikin falon kuwa, tunda Rauda ta bude dakin nan da yannayin garaje a zuwanta na bakuwar wajen wace bata taɓa ziyarta ba, ko a yau din ta bude din ne dan Salima ta tabatar mata cen din shine baban kofar falon baba na bangaren gaba daya, sai ta ji duk irin sanyin wajen yana neman zame mata zafi sakamakon gannin wata rigar alfarma sakale da jikin alfarma daga barin hagu mai dan tazara an dan bude labulen wajen ana tsaye ana kallon baban filin get din na biyu na dogarai, wanda ke tabatar mata duka kaf abinda ya wakana yanzu an gani, hakan ya sa ta kasa karasawa cikin falon take tsaye da burin jin an maidata baya dan ta riga ta sanyo kanta cikin, sai dai aka yi kamar ba'a san da ita a wajen ba, aka yi kamar ba'a gane ta shigo wajen ba aka ci gaba da kallon abinda bata san ko menene ba, har sai da Salimar ta karaso kasancewar bata dauki lokaci mai tsayi ba ta gaza tsayawar kawai ta kama hannun Atu tana fadin" Mu je mana aminiyar mu"

Suka shigo su dinma, sai dai su sunna shigowa Salima ta nemi zubewa saboda wanda RAUDA ke tsaye tana kallo su dinma sun ganshi

A nutse ya juyo da jajayen idannuwansa ya sauke a kan fuskarta
Tun daga sama har kasa ya sake bin suturar jikinta da kallo da mayafin dake jikinta

Kansa ya dauke ya nufi falon da su Bah ke shan fira shi da abokinsa wato uncle Umar, dan alakarsu a yanzu tana da karfin gaske

A hankali ta ringa fitar da numfashi daga hancinta, kasa kasa ta ringa kallon su SALIMA

Idannuwanta ta lumshe ta masu alamun su je

SOSAI Salima ta so juyawa, ama ta kasa saboda rikowar da Atu ta mata ta nuna mata tare fa zasu je din walahi sai dai kowace wace

sunna karasawa Bah ya tarbe su da fara'a yana masu sannu yana kama sunnan daya bayan daya, haka uncle Umar

Zama suka yi a saman kafet su dukansu, a lokacin ne kuma Amnah ta sake zuwa dauke da wani plate din kayan baki ta sake ajiyewa, Bah na yi mata adu'a ta juya, ama idannuwanta sun sauka a kan wace take hako da burin samun yancin da take bukata dan birkita duniyarta!, hakan ya sa ta kasa komawa sai kawai ta labe a kusa dan jin komai a kan wannan karamar y'ar barikin
Chapter 88 · 0% Book details