← Book details Azal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 117

Sashe 17

Azal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da sauri ya kalli macen da aka ce an dauko yana karkatawa dan lalubar kudin dake aljihunsa gaba daya ya ciro yan jaka goma goma sababi kal kal lokaci daya yana shaƙar kanshin dake jikin mayafinta haka kuma yana dubanta ya samu kansa da jin zai iya fada mata inda zai je ya san zata aminta su yi tafiya tare ko dan furucin da ya ji ta yi a kan *IYAYE*

A tausashensa yana kallonta, sai ya ji nauyin niyar da ya yi na bata kudaden nan duka, bai san dalili ba, a hankali ya ce" Mahaifiyata ce ba lafiya, idan ba takura ki bari a ajiyeni"

Bata taba jin damuwar wani bawan da bata sani ba na neman zama damuwarta sai yau
Bata taba dagawa wani gardi kafa ba komai laushinsa da tsarin halitarsa ba sai yau, bata taɓa ragawa wani dan uzurinsa ta bar nata ba sai yau

A hankali ta dauke dubanta daga saman fuskarsa ta ce" Mu je ka kai shi Aminu" RAUDA ta fada a hankali tana dauke dubanta a kansa

Tuki Aminu yake yi a Nutse ba da garaje ba,
A daidai wajen da zasu yi kwanar Nandu din kwanar da Nandun ke jikinta wani mai mota ya daki gaban adaidaitar ta su adaidaitar ta daku da jikin garu ama bata fadi ba, gabanta dai ya yi ratsa ratsa

Mai motar so ya yi ya gudu, dan a lokacin da ya ga adaidaitar bata fadi ba da sauri ya so juyar da motarsa ya yi tafiyarsa dan wajen yana kusa da police station ne, baya son bata lokaci , yanzu za'a zo a shiga surutun sai an yi aune aune an ga waye marar gaskiya a yi ta BATAWA mutun lokaci

Da karfi ya fito daga adaidaitar ya daga murya yana fadin " SANI ZAKWALAM!?"

Wanda aka kiraya da Sannin sai da ya zarro ido jin Muryar da ta kirayeshi

A rikice ya taka birki ya juyo da dubansa da kyau dan gaskatawa
Ai kam tsaf ya hango biya muradi na masa alamun ya gansa sannan ya juya ya koma wajen adaidaitar Aminu dake kiran SUNNAN RAUDA, dan kusan su mazan direwa suka yi ama ita bata iya dira daga adaidaitar ba, ga dukkan alamu ta bugu dan gefen hannunta jinni yake yi sosai

Da kyar ta ciro kafarta daya, tana shirin ciro dayar gaba daya jikinta ya kwashi rawa idannuwanta suka tafi luuuuuu suka rufe ta nemi dikuwa da kas

Kusan a tare suka tare ta, mayafinta ya fado saman hannunsa hannayensa kuwa suka talabeta dan Aminu sakar masa ya yi domin kamar ya shi kusa da ita sosai

Zuwa lokacin Duda dare ne wajen ya fara cika da mutane ana ta salalami, nan da nan aka fito da abin daukan marar lafiya dan a jikin garun asibitin ne aka maka su

Karbarta suka yi suka yi gagawar dorata lokaci daya sunna danne wajen dake jinnin suka shiga turata cikin clinik din, shi kuwa ya daga kafa a hankali yana rike mayafinta a hannunsa idannuwansa suka sauka cikin na mahaifinsa da ya'yan mahaifinsa wato sarki da kanwarsa HAJIA A'isha, sai kuma Sani ZAKWALAM wanda ya kade sun shima ya fito daga motar yana faman fadin " oga walahi ban san kunne a adaidaitar ba, innalilahi Oga mu je ciki a duba ka dan Allah"

A hankali ya so dauke dubansa daga kansu saboda a cikinsu babu mai binsa da tausashen kallo, sai dai ba dama a tsayen nan da suke idan har bai zo inda suke ba kamar ya wulakantasu ne baki dayansu

Kallo daya ya yiwa Sani kasa kasa ya ce" Ka bari mana baka gannin Ubana ne?, ka je kawai ku karata da police"
Daga haka ya karasa wajensu a Nutse ya furta" Barka da dare, yaya mai jikin?"

Mai martaba ne kaɗai ya iya amsa shi, mahaifinsa gefen hannunsa dake dauke da jinni yake kallo a zuciyarsa yana tunanin ko shima ya ji ciwo ne?, HAJIA A'isha kuwa takaici tamkar zai kasheta, ba wata damuwa ko Dar, ba wani jin nauyi ko gudun a jita ta ce" Asibitinma da mace zaka zo YUSUF?, mahaifiyar taka a kwoncenma sai ka zo da mace dan ka nunawa duniya waye kai?"

A hankali mahaifinsa ya kalleta yana jin kamar bai dace ba daga zuwansa ta hau shi da wannan balakin bayan ta ji ana fadin hatsari suka yi, shi wasu lokutan sai ya ga kamar tana nunawa son kai a lamarin BIYA MURADI, ta cika zakalkalewa da wulakantarwa da nuna tamkar laifinsa ya fi na y'arta da d'anta ne, nan fa suka zo suka raba rikicin auren y'arta, an yiwa yarinyar aure da yan watanni da wani kamilin dattijo ya kawo karar cewa yarinyar na hali na bin maza a cikin gidansa har a saman gadonsa, da aka titsiyeta ta nuna eh hakane kiri kiri dole aka raba auren take zaune daram cikin mutane, dayan kuwa kannin RISLAN ba'a cewa komai, lamarinsa sai addu'a kawai, katon barawo ne mai sata a kasa da kasa, sha ba'a magana, maganar bin mata kuwa a cikin masaraitarma sau nawa yana kawo MACEN da ba ta aurensa ba? Yanzu haka da jikarta daya tasa, ama sai ta ringa irin abubuwan nan haka , bai san me yasa take yin haka ba, a ƴaƴanta ita din da kanta RISLAN ne kawai mai sauki, shine mai dama dama mai kamanta rayuwa da jin tsoron Allah
"Da sauki jikinta, ama tana son ganninka, tana daki na biyu ka je YUSUF" Mahaifinsa ya fada a hankali, da murya a rarrabe yana dubansa tamkar ba shi ba

Yusuffff ya zuba masa ido na yan dakiku da karantar sabon salo, hakama yan uwansa baki daya sai suka zuba masa idon sunna mamakinsa

Murmushi sarki ya yi a hankali ya dan dafa kafadarsa, ba dan komai ba sai dan dama shi yana fada masa ya fa kiyayi bakinsa a kan yaronsa ya ja abinsa a jiki shiriya ta Allah ce, shi dai baya ra'ayin mahaifiyarsa gaskiya, ta yiwu hakan ya samu nasaba da irin yadda mahaifiyarsu ta tsani mahaifiyar YUSUF din

Ajiyar zuciya YUSUF ya sauke ya nufi cikin Asibitin, yana so ya ga yarinyar nan yaya nata jikin, ama ya fi jin sai ya ga mahaifiyarsa koda zai iya tunanin wani abin a irin wannan lokacin

A sanyaye ya karasa gaban gadon Mama a lokacin da ya bude dakin ya zuba mata ido yana kallonta

Murmushi ta sakar masa a hankali ta mika hannu tana masa alamun ya zo, lokaci daya kuma tana bin mayafin dake nade a hannunsa da kuma abin jinnin dake gefen rigarsa wajen damtsensa

A hankali ta riko jinnin fuskarta na nuna alamun damuwa tana riko shi tana so sai ya hayo gadon nata tamkar wani yaro tana tataba jikinsa da hannayensa ta ce" Sajan, jinni ne a jikinka? Me ya same ka?"

Sai yanzun ya ga ashe jinnin da dan yawa, sai ya ji dama ya wanke kafin ya shigo, dan a duniya idan kana so ka ga rikicewar mamansa ya yi koda atishawa ce, yanzu zata nemi fita hayacinta

Da kyau ya zauna yana taba fuskarta dake danshin raba yana duba nata hannun mai dauke da abin karin ruwa ya ce" Rohi ba fa wani abu ya sameni na, hatsari ne muka yi a adaidaita, yarinyar dake cikin adaidaitar ce ta bugu, ama ba sosai bane ba fa"

"Yarinya?, ya Salam, budurwarka ce? Ya Allah, ina take ne? Sajan tana ina ne?, ya Allah ga jinni a jikinka ance yar buguwa, Allah ya sa ba wani abu ya samu y'ar mutane ba, tana ina ne? Kaini in ganta" mamansa ke fada tana alamun son sauka daga gadon ita da karrin ruwa ke jikinta hankalinta tashe

Zuba mata ido ya yi yana jin nutsuwa da tarin kauna marar misaltawa a zuciyarsa, a hankali ya rikota da hannayensa yana son sai ta nutsu ya ce" Mahmah, ba fa abinda ya sameta, buguwa ce a hannu tana wajen likitocin, ba budurwata bace, adaidaita ne kawai muka hada da ita ina gagawar zuwa na Ganki, Please kar ki cire karin ruwan ke da ba ce lafiya gareki ba?"

Sai a lokacin ta kalli karrin ruwan, kai ita fa tunda ya shigo ta ji ta warke daga dukkan wani abu da ya tsaye mata a kirjinta , ko yanzu zuwan su sarki da A'isha Sarkin kawai ta iya amsawa gaisuwar da ya mata, yau shine harda tambayarta jiki? Kwarai ta yi mamaki , A'isha kuwa ta zo din ama bata jin lokacin da ta tambayeta jikinta ba, itama bata bukata, dan ta riga kuma ta rantsewa kanta ba zata kuma daukan wannan wulakancin na A'isha ba!

Sai da ya tabbatar da jikinta da sauki sannan ya barta bayan ya sheda mata lekawa zai yi ya ga jikin yarinyar, ita dinma ji ta yi dama zai yarda ta cire karin ruwan su tafi, sai dai ta san yanzu kuma ya zo ba zai yarda da komai ba , sai ta bi tsarin likitoci koda bata so dan ya zauna ya nemi tayar mata da hankali ba komai bane a wajensa a kan lafiyarta

Aminu ya samu tsaye a kofar catégorie din da aka saka RAUDA

Da sauri ya dan duka yana ba YUSUF din hannu dan a dazu bai san waye ya dauko ba sai yanzu da aka gama komai na lafiyar Rauda aka sheda masa wanda ya dauko din, hakan ya bashi mamaki ainun

Da kula sosai YUSUF ya ce" Tashi mana, yaya jikin ta? Ka santa ne?"

Aminu ya dan dago din ama ya kasa mike kafadarsa da ta Yusuf din dan girmamawa ya ce" Alhamdulilah da sauki sun sakata barci dai, na santa biya muradi yar anguwarmu ce, Ni kuwa Ni ke mata dan sahu kulun"

Yusuf ya bude dakin ya shiga yana sauke idannuwansa a saman kanta, tana kwonce lambak tana barcin da karin ruwan ke sakata, an daure wajen da ta ji raunin an dan sasabto mata rigarta sosai

Dauke dubansa ya yi ya kalli Aminu ya ce" Ka je ka sanar a gidansu, tunda da wahala su barta ta koma gida yau"
Chapter 17 · 0% Book details