← Book details Azal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 117

Sashe 67

Azal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hankali ya bude ya shiga, idannuwansa suka sauka a kanta saman mamakeken gadonta, kanta saman cinyar RAUDA hannayen RAUDA din rike da hannunta idannuwanta lumshe ko barci ya dauketa? Allah masani, shi dai tunda suka yi ido hudu da RAUDAR ya yi tsaye har sai da ta dauke dubanta sannan ya karaso a hankali ya duka ya kawo hannunsa a nutse ya janye na RAUDA wanda hakan sai da ya sa suka kalli junna da sauri RAUDA ta dauke idannuwanta kirjinta na rawa, shi kuwa a hankali ya rike hannun Mah kasa kasa ya ce" Mah, kin yi barci?"

idannuwanta ta bude da suka dan fara cenza kala ta dube shi

a tausashe ya furta" Kar ki daga hankalinki, a kan abinda kike da damar cewa a yi ko kar a yi, bakya so ko?"

Mah ta gyada kanta a hankali tana sake kallonsa

Murmushi ya yi ya ce" Ba zan yi ba"

Mah ta sake dubansa ido cikin ido, ya sake tabatar mata cewar ba zai yi ba, dan haka ta ringa sauke ajiyar zuciya, ama cen kasan zuciyarta cike da mamakin mijinta take, ohk shi mai yar uwa ko? ita ta ki nata saboda ba zata taba iya amincewa da wannan soyayar ta rana tsaka ba shine shi zai amince da nasa? ba zata hanna shi zumunci da Nana ba, yar uwarsa ce , ama ba zata taba amincewa da wannan abin ba! never!

Ya dan jima har sai da ya ga ta fara barci , RAUDA ta sauke kanta saman gadon a hankali ya mike ya dora kaffafuwanta sosai ya gyara mata kwonciya sannan ya dago ya juyo, nan suka sake yin ido hudu da Rauda Wace ta yi saurin sada kanta, shima ya samu damar kare mata kallo kafin ya girgiza kansa ya fice a dakin cike da takaicinta, abu daya ya sani idan har ta yarda ta yi masa gangancin da suke shirin yi jibi ba zai taba yafe mata ba! ba zai taba yafe mata ba!

.................................................

washe gari tunda safe gidan ya ringa cika da baki, jama'a ta ko'ina suna zuwa ana ta shirye shiryen auren MALIK

A cikin part din Mah yan uwanta da mutanenta na arziki ta ko'ina sunne ke kai kawo ana ta hulda irin ta manya
karfe goma na yi Mah ta tashi RAUDA ta saka ta yi wanka wannan ta rakata dakin da ta ware saboda harkar kitson ta da kunshinta, karfe goma da yan mintunna Bara'atu ta karaso gidan da akwatinta domin ta yi iya yinta mijinta ya amince mata ta kwana dan ta fita daga girki yau ita da amsar girki kuma sai ya yi kwana biyu a dakin dayar matar, hakan ya sa hankali kwonce da kansa ya kawo ta yana fada mata zasu hade ne gobe ai saboda daurin auren SIR.

Tunda ta karaso Salima ta samu ta fice dan idasa shirye shiryen kayan RAUDA din, domin harkar kayan lefenta kiri kiri Mah ta nuna ba za'a kawo ba a zuba a dankareren gidan da zata zauna wanda ABDALLAH ya tanfatsa , ta nuna akoy sutura da za'a yi mata a nan , wadinncen yan kai amarya sa karba, ita kuwa ta yi masa haka ne dan sarai ta san bashi da kowa a garin sai irin yan cin arzikin nan, ba zata so a cakula mata lamarin y'a ba, in sha Allah idan an kaita gobe ta tarda kayanta kawai ya kai ajiye, Mah din kuwa tuni ya je ta ga kayan da ita da Salima da gidan da komai, harda dankareriyar motar da aka siya mata a kampanin YUSUF a parker as gift na oyoyo

tunda Atu ta zo take hankalce da yannayin RAUDA , gaba daya kana ganninta zaka gane tunaninta a rarrabe yake, duk irin yadda ta yi dan ta kawo hankalinta kanta gudun kar ta gane halin da take ciki sai da ta ringa tambayarta lafiyarta? me yake damunta? bale zuwa yamma da aka shiga shirye shiryen sakata a lalle kamar yadda tadar garinmu yake idan amarya budurwa ce ana sakata a lalle du sai ta idasa rikicewa ya zamo bata magana bata amsawa har sai da Atu ta sanarwa Mah dake cen cikin baki sai walwali take domin tun daga kan shigarta har fara'ar dake fuskarta zaka gane tana cikin wani hali na farin ciki ne

ko da Mah ta shigo ta sameta an gama wanke kunshin ya yi wani irin kyau ta zauna daf da ita dan mai kunshin ta gama shafa mata turare a tausashe ta kamo hannunta ta ce" Baby, ko dai rikicewar za'a barni ne? to ba gari guda muke ba? idan kina so du safia sai in je in ga yaya kika kwana dan Ni kam har sai an ringa yi da Ni ana cewa wata irin uwa mai zuwa gidan y'arta"

daria mai kumshin da Atu ke yi, Atu na kallonta tana karantarta, kai, ta kasa yarda cewar babu wani abu dake damun RAUDA, ta san RAUDA tun sunna yara, ko da ido ta yi magana zata iya fassara abinda ta ce, sam ta kasa samun sukunin yannayinta , wani abu na damunta, wani abu mai girman gaske, ama kuma ta ki fada, a haka har aka gama shirya sakata a lalle domin gabanin sallar magariba ake sakawar,

Tunda aka fitar da ita baban falo dan saka lalle aka zaunar da ita saman cafet aka cire mata hijabi Sarkin kida ya fara kidan nan mai hawa kai, zabiya nata , makeriya na nata, masu daukan vidio na dauka, masu hawaye na hawaye hankalinta ya idasa tashi a hankali ta kankame Atu aka shiga shafa mata lalle , kanta, hannayenta,kirjinta dai da sauransu ana darzarta har aka gama aka lulubeta luf sannan aka mikar da ita Mah da Atu suka kaita dakin Mah suka nufi bayi da ita dan yin alwallah ta gabatar da Sallah kafin cin abinci a irin lokacin ne kuma RAUDA ta dauki wayarta tana ta amsa kiran Abdallah tana tsokanarsa shima yana ramawa har ya shaida mata abinda yana fadar, kuma a nan zai kwana? ita dai ta ki bashi RAUDA har ta gama sallah ta kwonta ta ki sauraronta, dan ba yadda bata yi da ita kan su yi fira ko zata iya yi mata magana amma fir ta kiya har sai da itama lokacin nata barcin ya yi ta hakura ta kwonta zuciyarta cike da tunanin abinda ke damun aminiyarta

karfe uku na dare message ya shigo wayarta
kasancewar ba barcin ta samu ba sai ta laluba ta duba
message din na dauke da kalamai ne kamar haka
"kin san bakya son sa, me yasa kika cika kafiya ne?"
haka kawai take bin message din da kallo, wani bakin ciki na turnuko mata zuciya, ta ki ta amsa dan a tafiyar nan ta fi so ace ta tafi ba tare da ta nuna ta gane Yaren mai Yaren ba

"ki sani, idan kika yi haka, kin kuntata min, kuma ba zan taba yafe maki ba! RAUDAH tunda na fara gannin ki, na san na hadu da *AZAL DINA!*"
Yanzun kam zaunawa ta yi zuciyarta na kunna ta shiga rubutu kamar haka" kai ne *AZAL DINA* domin kafin ka ban san ciwon nan ba, kai ne AZAL DINA saboda kai ke son hadasa min fitina a duniyata, kana tunanin Ni mai iya raba makiyi ce bale wanda ya zamo tsokana? IDAN KA YARDA KA AURETA SAI NA DAME KU, WALAHI SAI NA DAME KA!" daga nan ta tura sakon a hankali ta kwonta zuciyarta na tabatar mata da lalle wanda take tunani ne,...to ama ita da kanta bata san me ma'anar furucinta ba, abinda ta sani daya ne ba zata taba iya yafe masa idan ya auri wata ba

(tambayeta itace, da kuke cin alwashin nan, shin akoy episode din da muka rasa wace kuka furtawa junna kalmar so?....🤔🤔🤔🤔)

babar rana

Rana bata karya

................lokaci na zuwa sai dai mai rai ya mace
...
........ a yau take babbar rana,

😌😌😌😌😌😌😌😌🥺🥺🥺🥺🥺

Azl 38

*KADA A YI BA KU, BONANZA TA NOVELS DINA A KAN FARASHI MAI SAUKI, WATO 1K SU 22 CIF IN SHA ALLAH.....KU GARWAYO DAN SAMUN NAKU A BISA FARASHI MAI RAHUSA .....KU TUNTUBI NUMBARNA 93811618*

*Tallah, tallah.....tallah manyan hajiyoyina*

Bismillahi rahamanin rahim

Metaforce online business ne na crypto
Wanda aka tabbatar da halaccin sa ,sannan aka tabbatar da cewa ba irin wannan platform din bane da ake gudu da kudin mutane.....domin Metaforce zaka shiga ne da kadan ka dauki da yawa, da wannan Hajia Ummu Khalil wace ke zaune a kasar Nigeria sananiya ce fitaciya ce mai dauke da numbobin waya kamar wanann 07038708382 ta kawo mana hanya mafi sauki dan samun ci gaba.......ku saurara dai
*METAFORCE*
Yana da level 1_12
Idan Zaki level 1 Zaki Fara da Doller 5,,level 2 Doller 10 ,level 3 Doller 20 Haka dai har 12
YADDA AKE SAMUN ALKAIRI A METAFORCE

💃🏼 Kina Gama register za'a Baki TR coins na adadin level din da kikayi,ko a iya su kin Mai da kudinki fa idan akayi lunching🏃🏻‍♀️🕺😁 .....WASHE BAKI SOSAI HAJIATA....YEAH KO A IYA SHI KIN MAIDA KUDINKI BALE GA WANI DANDANO MAI ZAKI.....

*Refferel bonus duk mutum 1 fa idan Kika kawo za'a Baki adadin abinda yasa yayi level din, banda 2 na farkon level 1 da 2*

💃🏼 Ga Kuma garabasa na spillover
Ko kin kawo mutane ko Baki kawo ba kina iya samu 💃🏼💃🏼musamman tunda Ni da Zan Miki register Ina aiki sosai (wauh fantastique)

Spillover shine zakiga ansa Miki mutum a kasanki ,Kuma a biyaki fa ko Kuma a cike Miki biyu ko dayan farkon nan💃🏼 (magnifique)

Da Dollars suke biya idan kinaso Zaki iya siyarwa duk dollers din Kika samu a take a tura Miki kudinki cikin account 💃🏼💃🏼💃🏼 (da wa kika ja Madame?)

Metaforce Babu FADUWA Babu asara a ciki...... Ku zo mu kafta duniyar sananu mu samu yanci, nema sai da nema, ki shigo Mu je, kasuwanci mu babu algus ba cuta, zaki kwashi kudinki koda baki kawo kowa ba😍😍😍 sai kun zo
Chapter 67 · 0% Book details