← Book details Azal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 90 OF 117

Sashe 90

Azal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Salima ta rafka tagumi, sai kuma ta dauke tana kallon Mah da ta ci gaba da fadan a fada mata wanda ya taba mata y'a!, ta ce" Yau dai, da tabas mun samu abinda muka je nema harda kari,ke yanzu haka kike? Ki duba ki ga mutanen dake kiransa Bah, dan yace kar ki biyo ta babbar kofa shine zaki ce sai kin biyo?Bah karami ne fa?"

Mah ta yi dan tsai, a hankali ta furta" Dan kun bi ta babar kofa ne aka maku fada?"

Salima ta gyada kai tana kallon Mah ta ce" Eh Mah, shine ita wannan uwar bacin tace wai ta fita ida ai yanzun, shine fa ta sa ransa ya ɓaci "

Mah ta tabe baki tana mikewa hadi da kama hannun RAUDA ta ce" Mu je, tunda sunna gannin gaskiya suke son takewa, wuce mu tafi, zan yi kiransa da kaina mu yi irken kwanakin da kika dauka a dakan, ta yiwu yana tunanin basu cika bane, ama bayan wannan ai takaba kai kin gama kuma bi'izinillah fita ta babar kofa yanzu kika fara koda wani auren ya hau kanki bale babu, Allah na tuba yarinya karama da ke za'a sako min ke a gaba? walahi kowa ya ci kansa ko waye!"

Da ido suka raka su, Salima ta juyo tana dafe haba ta ce" Kai jama'a, kamar ita wancen da mamanta sun dauko wani hali ko?"

Atu ta saki murmushin da sai yanzu ta samu karfin gwuiwar yi, tana kallonta ta ce" ai kin san ko laifi gareta sai dai daga ita sai ita ta mata fada, yau da na san yan iskan kan Rauda har shi ba zata bari ba da ban bita ba, na tsorata ainun, ama kuma MALEEK akoy karfi ke ji walahi da ya dungumeta ya ajiye kamar bai yi wani yunkurin daukan balagage ba, Allah dai ya takaita fitinar nan dan Ni ban cika son neman rigima ba"

Salima ta girgiza kai tana kallonta ta ce" Ba zaki gane ba, kin san duk wani abin dake kanta, walahi yana kansa, kin ganshi nan baya tsoron kowa, sai dai daga kafa da kuma umarni idan ya zame masa dole, ama a kan lamarin ta ina gannin abubuwan da nake fatan gannin karshen game din, "

Atu ta yi shiru, tana ta sake saken dake ranta, itama Salimar tana ta tuna sakon nan na wayar RAUDA, .....kai da abu nasu maganin a kwabe su, da ta fi kowa farin cikin hakan walahi

A bangaren YUSUF tana barin wajen da su Salima ya zauna a saman kujerar yana daukan mayafin nata da ta bari a nan ya jimke a hannunsa sannan ya dago yana kallon Amnah da wani irin kakausan kallon da ya sakata zaunewa a wajen kanta a kasa ta kasa hanna kanta kukan nan

A birkice ta dago dubanta tana kallonsa, muryarta a raunane sosai, da yannayin tashin hankali ta karyar da kanta sosai ta ce" Ni kam, kamar wata wace take da kusanci da kai fiye da tunanina?, inace Mah ke rikon ta, Bama y'ar Mah din bace ko?, kuma Ni na san ba dai maganar soyaya ba, ba dai da ita ba walahi, dan Allah daukanta ka yi fa ka ajiye kuma ka kama fuskarta da hannayenka masu daraja, ka san girman darajar hannayenka kuwa....., Haba MALEEK......."
Ta idashe tana fashewa da wani kukan dan bata taɓa tunanin za'a wulakantata haka a rayuwa ba, kuma abin mamaki wulakancin ya sameta kai tsaye ta kasa yiwa abin rashin kunya, saima wata sabuwar lalabawa da take bin abin da shi a kan dole , dan ta sani tunda ta yi tsaye a gabansa ta gane mijinta ya gama dameta a duk wata kiririta da take tunanin tana da ita

Idannuwansa ya dauke a hankali a kanta, bai iya ce mata ci kanki ba ya lumshe idannuwansa dake masa zafi, a hankali yana sauke ajiyar zuciya

Ta jima da jiran tsamanin jin bayanin dalilin da yasa ya taba RAUDA, ko ya dan rarasheta ko dan kukan da take shekawa , ama fir ya murje tamkar baya wajen har sai da ta mike da kanta ta nufi nata part din bayan ta gama gane bata haife shi ba, ba zata titsiye ba kennan!, ya ilahil alamina, jikinta zafi ya ringa dauka na tashin hankali dan haka ta dokawa mahaifiyarta kira tana zaunawa kasa jikin gadonta tana ta murzar fuskarta ta shiga yin bayani da ita.......

A falon kuwa ya jima yana hanna kansa magana ne dan kawai irin zafin dake saka masa tunani kala kala a kan wancen sojan........abu daya tak ya sa ya zauna din nan har sai ya gama samun nutsuwar zuciyarsa kafin ya dauki mataki dan girman da aka kakaba masa rana tsaka, ya sani a yanzu idan ya fita cen ya ketsawa wancen mari koda ba'a ce masa komai ba sai an baza shi duniya saboda wannan, shi yasa ya yi zamansa sai da ya samu ya dan sauka kadan sannan ya yi kiran uban gidansa da ya bashi shi ya sanar masa a dauke shi bai san aikinsa ba sannan ya katse kiran ya mike ya nufi Part dinsa da mayafin nan ya je wajen tufafinsa ya bude yana kallon wasu jerin abubuwa harda abin hannu wanda aka cire mata ranar da suka yi accident, harda mayafinta na ranar nan, a hankali ya ninke wannan dinma ya saka shi ciki sannan ya karasa wajen gadonsa ta baya baya ya fada yana rintse idannuwansa da karfi dan magance abinda ke masa yawo a idannuwan......a saman lebensa ya furta" Mai kukan banza kawai, sai neman fada ana zaman lafiya, kina tunanin zan kyale ki ki kasheni ne? dilla ma malama!"

kwana biyu tsakanin wannan rikici nasu Mah ta aiki RAUDA cikin garin Damagaran, kuma aiken Mah ta hanna direbansa ya kaita, ta sa wani direban cikin direbobin gidan ya kaita, ta bata damar ziyartar duk wanda take so, wanda suke zumunci, ta bata kudade masu yawa koda zata yiwa wani kyauta, ama ta kula da mutuncinta
Baban tashin hankalin irin kwaliyar da ta sa ta dauka ita da kanta zata iya rantsewa tunda aka haifeta bata taɓa saka sutura mai tsadar nan ba, kuma bata taba hauda jaka da takalmi da mayafi masu kudin nan a jikinta ba, haka kuma bata taba Hauda siririyar kwaliyar da ta fitar da asalin sirin kyan fuskarta irin na yau ba, dan mai kwaliyar nan ce ta zo har gida kamar kwaliyar amarya jama'a ko ta bikin sunna ta yi mata abinta har a daki, sunna yi sunna dariya ta yi mata siririyar kwaliyar da ta matukar birgeta, kuma ta kafe mata dauri dan daidai da kanta ba mai hayaniya ba,...kai kwaliyar kwaliya ce har kwaliya walahi, tana gama mata ta watsa mata hotunna da vidio ta shiga karra gyara su kamar yadda ake yi, dan harda Mah sai da ta yi mata sau uku sannan suka tafi ita kuwa ta yi tsaye saman turaran wutar da Mah ta saka mata yana bin jikinta tana karra jin gargadin Mah, kar ta yarda la'asar ta yi mata a cen, ta juyo da wuri, kuma ta kula da kanta , Allah ya tsare

Wayarta ta dauka ta fice, mayafin tana jin kamar girmansa ya yi mata ƙadan dan bashi da wani girma, ta karasa wajen wawatsetsiyar motar da aka parker ta bude bayan ta shiga, direban na zaune ya gaisheta da girmamawa, shima saurayi ne da ya san aikinsa sosai, ta amsa tana fada masa inda zasu fara zuwa dan amso sakon Mah din kafin su wuce tsohuwar anguwarsu wato gidan Mama, sannan su je ta ga Abdul , sai gidan Atu shikenan yawon nata , ta daga wayarta tana sanarwa Salima ta fita, sannan ta bude datar ta ta shiga kale kale hankali kwonce har suka gama fitowa a gidan suka dauki hanya

Sunna ta tafia , sunna daf da isa gidan yayar Mah mai kwaliya ta tura mata hotunan nan, ita kuwa tana budewa tana murmushi ta turawa Mah su gaba daya sannan ta yi kiranta ta sanar mata ta tura mata hotunan, kuma har sun iso gidan aunty baba

Mah dake falon Hajia tana murza mata kaffafuwanta dake ciwo saboda yau ta tashi da rashin lafiya , hakan ya sa YUSUF sanarwa Mah din, dan yana ɓangaren Hajiar sunna firar wasu filayenta ya ga sosai ƙafafuwan na damunta shine ya sanarwa Mah dan ya tabata ba za'a rasa magani ba duba da itama ciwonta kennan kafafu

Tana murmushi ta mika masa wayar ta ce" Dan bude min wajen sakon baby ta turon hotunanmu da aka yi mana yanzu kafin ta fita , bude min in wanko hanuna in gani"

Ta fada tana mikewa ta rufe maganin ciwon kafar ta nufi bayin dake falon dan wanke hannu, shi kuwa ya dan yi jimmm, jin ta ce ko kafin ta fita? fita ta yi? zuwa ina?

Baki ya dan tabe ya shiga bude hotunan harda vidios din, sai dai bai idasa budewar ba ya ji tamkar ciwon nan na hawan jinni dake sangaye bari daya na jikin mutun ya sangaye masa zuciyarsa, kafin ya saketa da karfin gaske ta ringa bugawa da mugun bugun da ya saka shi saurin rintse ido gumi na tsatsafo masa

"In gani?, sun budu ko?"
Mah ta fada tana kallonsa

Yannayin da ya dago yana duban Mah ita da kanta sai da ta ji karsashin da ta fito da shi na neman barinta, Hajia kuwa lokaci daya ta dube shi tana fadin" YUSUF lafiya?, subahanallah, meye kake haki?"

Gannin numfashinsa na iya barin gangar jikinsa a zaunen nan ya sa ya ajiyewa Hajia wayar ya mike ya fice ta babar kofa da saurin da ya sa Mah wace ta zauna mikewa a birkice tana kiran a kirawo mata shi, dan fitowa ta yi da sauri din, ta saka dogarin dake wajen bin baya da gudu, sekwani kadan ya dawo da sauri yana dukawa ya sanar mata cewa ya fice a mota hakan ya sa ta koma dakin hankali tashe tana kallon Hajia ta ce" Hajia dan bani wayar na yi kiran baby"
Chapter 90 · 0% Book details