← Book details Azal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 92 OF 117

Sashe 92

Azal Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Metaforce Babu FADUWA Babu asara a ciki...... Ku zo mu kafta duniyar sananu mu samu yanci, nema sai da nema, ki shigo Mu je, kasuwanci mu babu algus ba cuta, zaki kwashi kudinki koda baki kawo kowa ba😍😍😍 sai kun zo

Mah ke fada jefi jefi a hankali, har bata san shigowar Bah ba, sai da ya karaso da sauri ya zauna yana saka hannayensa ya kamata sosai da kula da tarin tausayinta kamar yadda ya saba ya ce" Subahanallah, Anmi YUSUF menene? jikinki ne? ko saboda maganar daurin auren ne Hajia ta fada min yadda kuka yi, bakya tunanin a Daura din ya fi alkhairi maman Yusuf idan ya so sa daidaita kansu?"

Kanta ta ɗora a gefen hannunsa idannuwanta a rintse tana tunanin anya maganar nan abar ta yi 'e da shi? duba da wace ta yi jan ragamar zaman watsa ahalinta matarsa ce,
A Raunane ta dago tana dubansa, muryarta a tausashe sosai ta ce" Ba'a daura auren bane?"

Yana dubanta ya gyada kai a hankali ya ce" Shedu muke jira, Shaheed yace min gayanan zuwa, kuma liman baba ne zai wakilci YUSUF, bakya so a Daura ko?"

Mah ta lumshe idannuwanta a hankali ta furta" Ina so, ina so a Daura, idan da hali a Daura shi yanzu yanzu, kuma a sanar a lasifika, ka bani wayarka ka samo min YUSUF din, Ni zan sanar masa sannan in bashi umarnin ƙafarsa kafarta, ka ji?"

Da mamaki yake kallonta, sai dai bai yi mata gardama ba, ya dauka cewa adu'ar da aya yi ta yi kwana biyun nan ne Allah ya amsa, dan haka ya shiga neman Layin YUSUF, sai dai bata shiga, aka sheda masa yana waya, ya dan jima ya sake bugawa wannan karron aka ki dagawa, ya rasa dalilin da ya sa ba'a daga din ba, dan ya buga ya kai sau hudu ama ba'a amsa ba , a dole ya mike bayan ya daukowa Mah maganinta ta sha yace ta je dakinta ta kwonta ta nuna a'a bata jin barci akoy abinda take jira, shi kam a dole ya fice dan ana ta nemansa a waya a masallacin Masarautar

Bayan fitarsa Mah ta samu ta daidaita kanta, ta je ta dauro alwallah ta zo ta ajiye salayarta ta maida gabanta gabas ta yi raka'a biyu sannan ta zauna rike da carbinta tana ja idannuwanta lumshe, dan tunda ta nemi kadaicewa din ta nuna bata son damu daga kowa sai ya zama ko yan aiki dake lekowa jifa jifa sunna karra kimtsa waje da karra turaran wuta basu shigo ba, hakan ya sa ta samu nutsuwar da take da Muradi ta ringa yiwa Allah kirari, tana ta karra neman kusanci da ubangijinta, ba ji ba gani tana karra yiwa Annabi salati , shauki da nutsuwa na ratsa ta kunnayenta n sauraron babar lasifikar Fada, lalo lalo har ta fara tsinkayo ana gayatar duk wani namijin dake iya halartar daurin aure yanzu yanzu.....hakan ya sa daurin auren ya ringa dan jan lokaci , ama a inda take bata motsa din ba, dan bata tunanin tana iya motsawa in ba kunnayenta suka jiyo mata abinda take son ji ba

......................................................

A lokacin da motarsa ke yin cikin Damagaran ya dauki hanyar gidan Bara'atu kamar yadda direban ya sanar masa ga inda suke, a lokacin ne Shaheed da yan rakiyarsa suka je taron daurin auren sa ba tare da ya sani ba

Zuciyarsa yana iya rantsewa ta kumbura a irin yannayin nan da yake ciki, gumin da bai daina ba kuwa ya tabatar masa gudun jinninsa ya jima da wuce ka'ida, idannuwansa kuwa yana iya rantsewa hudu hudu suke gani bama bibiyu ba

'Shin me yasa ake tayata kaucewa umarninsa?, me yasa mahaifiya a gare shi ta kasa taya shi daidaita kansa ya zama cikakken da ake so ya zama?' Wannan sunne tambayoyin da yake yiwa kansa a zaune cikin mota, a harabar gidan Atu, domin yana isowa ya yiwa abokinsa texte cewar yana kofar gidansa, shi kuwa ya yi kiran mai gadi yace ya bude masa gayanan zuwa yana gidan dayar matar tasa ne ba nisa, hakan ya sa ya shigar da motar ya samu waje karkashin wata innuwa ya parker motar ya salami direbanta da tsoro da mamakin ganninsa da kansa yana tuka kansa kuma a nan kuma ga dukkan alamu Hajia da ya tuko ya zo nema? shi dai bashi da halin yin wata tambaya a dole ya juya din ya bar gidan ba tare da ya yi mata salamar cewa an ce ya tafi ba

A cikin falon Atu, zaune suke a tsakiyar falon sun baje, RAUDA ta cire lesh dinta tunda ta zo Atu ta bata wando irin mai lafewa a jikin nan da riga katuwa sosai budadiya ta saka ko dan kwali bata saka ba ta yi masu danwake a kicin din Atun sun baje sun zabga masa yaji sunna ci sunna ihu da fira da dariya irin ta aminan da suke aminan junna din nan na kud da kud, dan Atun ta tabatar mata mijinta yau yana gidan uwar gidanta shi yasa ko hijab basu dauko kusa ba

Atu na dubanta a lokacin da ta gama shan ruwan sanyi da kyar yaji ya bar harshenta tana haki ta yi yar dariya ta ce" Ina son tambayarki wani abu Ni kam, wai yaya usulin mesg din ku da MALEEK?"

RAUDA ta saka birki a kokarin sake kai dan waken nan bakinta, sai kuma ta tabe baki ta ce" Dama bakina da naki nace maki Shi ya min message?"

Atu ta dan zarro ido tana kallonta ta ce" Kar ki raina min wayo mana, Ni dan Allah gaya min, dan matar nan tasa tsaf na nemo wace ita, dan a ranar da kika so sakawa ya zane mu ta bani mamaki, ke kin san kirarin da ake yiwa uwarta kuwa? baiwar Allah kishiyar Mamanta tunda aka auro uwarta ta zama kamar hoto a cikin gidan, ke su fa harda tsafi kina ji suke yi, kuma duk daraja irin ta babanta kina ji mamansa surfe take yi a garin nan, dan gaba daya ya manta da tana raye fa, ke Ni sai da na tsorata da na ji wannan abin nace Allah , Allah ga MALEEK ya rab ga Mah, kuma ga RAUDANA, Allah ka sa su fi karfin mugu ya Allah!"

RAUDA ta tabe baki tana kallon ta ta ce" Ba zaki gane bane, ki daina hada sunnana da shi da matarsa, dan Ni bana iya cin sauran tuwo!, kuma kina maganar tsafi sai dai lamari na Ubangiji idan har ya kadarto hakan wa Mah dina, bayan wannan Ni so nake na zane yarinyar nan walahi, haka kawai nake tashi da muradin in zaneta, na dai yiwa kaina alkawarin ba Ni ba su ne, da ba wannan ba yarinyar nan so nake in dauraye mata jiki ta yadda man nan da ya gama jika mata fata ya sa ta zama kala biyu, wajen man da kuma wajen bulalar ke dai kamar bayan kado dai ya dace fatar ta zama ko?"

Atu ta zarro ido cike da mamaki zata yi magana RAUDA dake kallon wajen kofa a rikice ta duke tana hade jikinta da dan karfi ta furta" Innalilahi, aminin aminiyata kar ka shigo dan Allah!"

Ja ya yi ya tsaya ya juya bayansa gaba daya, hakan ya sa Atu mikewa da gudu ta shige ta dauko mata zumbulelen hijab ta dawo ta miko mata ta zurma tana fadin" Aban karima dama kana dawowa warhaka ban sani ba har muka baje? bismillah kai ɗaya ke tafe"

Juyowa ya yi yana murmushi,
idannuwansa ya dan sauke kan RAUDA, sai kuma ya dauke zuciyarsa cike da matsanancin mamakin abinda ya tarar yau a wajen MALEEK

a tausashe ya ce" Eh Ni daya ne aminiyar, aminiyar aminiyata shine kika so ki kawo ziyarar ki gudu Ni ba'a yi zumuncin da ni ba ko?, to tashi ki je Mah ta turo sako wai, zaki ga motar cen wajen shukokin cen na mangwaro a parker "

Jin an ce Mah ya saka ta mike da sauri, ko wayarta bata dauka ba ta nufi wajen tana fadin" Sako? ko wani aiken Mah gareta ? ama bata yi kirana ba, ina zuwa Atu"

Daga haka ta fita
Sai da ta tsaya ta dan dafe kugu kadan tana duduba filin gidan, hakan ya sa ake gannin wandon dake kasa karara sannan ta gano motar ta nufeta a ranta tana ayana' Kai motoci sai a gidan Mah, duk wayewarka sai ka bi watan da kallo alkur'an '

Gannin ba'a bude aka kawo mata sakon kamar yadda aka saba idan wani abin ne ya sakata tunanin ko ba kowa a motar? hakan ya sa a nutse ta karasa ta saka hannayenta wajen madubin dan ta ga ko zata iya gannin ciki, duba da motar a lulube take da bakin madubin nan
Chapter 92 · 0% Book details