Sashe 104
Azal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
YUSUF ya yi shiru, sai kuma ya girgiza kansa kawai ya mike yana ciro ky din aljihunsa ya nufi kofar
A rikice Habu ya rarafo yana fadin" Innalilahi ranka ya dade dan girman Allah kar ka barni a nan, ka ceci rayuwa.........."
"Kai ja baya dan ubanka kar na datse maka hannaye!" Taj ya fada da hargagin da ya sa Habu saurin yin baya fitsari na sake kubce masa a wandonsa, dan a zamansa a wajen nan fitsarin da ya yi a wando ya fi a irga, ranar da suka likira shi ya saki fitsari Taj cewa ya yi ashe yanada alkalami a jikinsa yake daura zani
Murya na rawa, jikinsa kaf na rawa, kana ganninsa ka san ya gama fita a hayacinsa ya ce" Ranka ya dade zan fada dan Allah kar ka barni da su, walahi kasheni zasu yi, ranka ya dade ko muryarsu tsoro nake yi, dan Allah kar ka barni da su, walahi a wata gawar wata budurwa da ta rasu a anguwar su Hajiar aka dinke layar da aka basu, sunne suka yi wankan gawar Hajiar ce ta saka da kanta dan aminiyar Uwar yarinyar ce, ita ta fada min cewar daga baya ta biya aka bi gawar aka dinke mata bakin dan kar layar ta fadi, ranka ya dade na san gidan su yarinyar, ama ban san inda kabarinta yake ba, dan Allah a sakeni zan nuna"
Kansa banda sarawa babu abinda yake yi, a hankali ya lumshe idannuwansa ya bude din ya fice yana jin ihun Habu ya nufi bangaren Mah idannuwansa na neman rufewa
Da kyar ya iya sada kansa da dakin Mah, a lokacin tana zaune tana shan maganinta ta dago da sauri tana kallonsa har ya karaso
Maimakun ta ga ya haye gadon ya zauna daf da ita sai ta ga ya zauna a kasa sannan ya dora kansa a saman kaffafuwanta
"Kai lafiya?" Mah ta fada da sauri tana dubansa
Sai dai bai dago kansa ba daga irin yadda ya dora kan nasa a cinyar nata
Da sauri ta saka hannayenta ya dago kansa sakamakon jikar da ta ji cinyarta ta yi , jika mai dumi , jika mai nuni da hawaye ke sauka a kan cinyarta na Yusuf
Da sauri ta sauko ita dinma daga saman gadon tana talabo fuskarsa ,, muryarta na rawa ta ce" Menene? subahanallah me yake faruwa? ina Bah dinka? ina Hajia? ina baby? ina Amnah ne? menene Ishak ne? ko Taj? menene YUSUF?"
Da sauri ya mayar da kansa cikin tafukan hannayenta ya ja wani irin numfashi hawayenshi suka sauka sosai yana rike da hannayen nata
gannin tana daf da sumewa dan shiga a halin kidima a dole ya budi bakinsa yana dubanta a hankali ya ce" Lafiyarsu kalau Mah"
Mah na dubansa idannuwanta sun gama cikowa da kwallah ta ce" Mememenene to? kuka fa kake yi fa"
Yusuf ya langwabar da kansa yana dubanta, a hankali ya ce" Mah, anya kuwa zan iya?"
Mah ta sake rikicewa tana dubansa ta ce"Mene? meye ba zaka iya din ba? sarautar kake son ajiyewa?"
Kai ya girgiza a sanyaye ya ce" Inama ace sarautar ce nake son ajiyewa, sai na ajiye dam na dauke ki mu gudu, kin ga abin nan ya fi karfin wannan Mah, walahi ya fi karfin wannan rigimar"
Zuwa yanzu kam Mah ta gama rikicewa, da dan karfi ya ce" Kai, wai uban meye?, zaka fada min ko sai na fala maka mari?"
Idannuwansa ya sada kirjinsa na dokawa, a hankali ya ce" Idan fa abinnan ya bi Ni har yayana?, Mah idan rashin jin da na ringa aikatawa na biye biyen mata ya bi Ni har yayana? yaya zan yi?"
Mah ta yi dif gabanta na faduwa tana kallonsa, ta kasa furta koda kalma daya ce
A hankali ya sake fadin" Kin ga, tun ba'aje ko'ina ba, matata , uwar gidana, bata jin magana, ta yiwu fiye da rashin jin da na aikata a da, dan abubuwan da nake gani a hankali da wa'inda na gani sunna karra rikita min lissafi, a yanzu Ban san ta ina zan fara ba, dan kuwa tsoro ya gama kashe min duk wani kuzarina da yunkurin daga nake iya yi"
"Rashin jin, na menene? kana nufin bayan da igiyar aurenka tana kara ci gaba da rashin ji? ko menene girman tashin hankalin da kake fadi dan Allah?" Mah ta fada a sanyaye tana dubansa, zuciyarta kuwa cike da tsoron amsarsa
Ajiyar zuciya ya sake saukewa yana dubanta ya ce" A yanzu, ai bata fita Bama bale ta aikata, koda ace zata iya ci gaban bayan auren, wanda ya shigo da sunnanta kuwa dan daudu ne anya zata iya zubar da kanta har haka?"
Gaba daya Mah sai 5a dawo bata gane yarensa, kallonsa take yi ta kasa gane komai, sai take gannin kamar wanda yake yi mata wata maganar ta wasu daban, dan haka a tausashe ta ce" YUSUF, dan Allah ka min bayanin yadda zan gane ko zan iya taimaka maka da addu'a, sannan na yi maka nasiha? domin na sani ko menene ba zai gagari yafiyar ubangiji ba in sha Allah "
"Mah, mahaifinta fa ba shi ya haifeta ba, kuma ana jibi aurenmu ta aikata zina da likitan da ya yi mata aiki ya dinketa bisa jagorancin mahaifiyarta, Mah kin ga dai mahaifiyar Amnah ko ta gama kuncen kaina da na ji cewar wannan hali da mahaifinta ke ciki wai asiri ne kuma a gawar y'ar kawarta ta anguwa suka saka, to yanzu Ni gaba daya na gama rikicewa, inaga da wahala in Allah zai yafe min, tunda da ace mutumen kirki nake da wahala Allah ya hada hanyata da mutanen nan, Ni da kaina na daina yarda da kaina yanzun Mah....." Ya karashe yana rike hannayenta , ta yadda zafin tafin hannayensa ke ratsa nata da irin yadda bugun kirjinsa ke shiga kunnayenta kawai sun isa su tabatar mata tabas a mugun yannayi yake ciki
A hankali ya dora da fadin" Na rasa ina zan kama, dan kuwa na san ba zan iya zama da ita ba Ni dai, wannan tashin hankali dake tare da ita ya fi karfina, ina bibiye da su ne a hankali tun daga ranar da Taj ya zo min da magana a kanta kan binciken da na sa ya yi, domin a ranar da aka kawo ta fa kanta ta kai cen bangaren tace min wai gata, sai na ji tsoron kar aje banda rashin kunyar akoy wani halin ko na tabuwar hankali ko makamancin haka dai, sai kawai abubuwan nan ke fitowa, Mah a sanadiyar asirin da mahaifiyarta ta yi , mahaifiyar Elhaji ke daka daka dan ta ci abinci a daya daga cikin kangonsa, matar nan tana ji tana gani, ba zata iya taimakawa wannan baiwar Allahn ba ko dan rabata da ta yi da d'anta, sai da muka ji ne aka kawo ta nan take zaune har mu ga abinda Allah zai yi, yanzu Mah wannan ai ba tsatson hada zuri'a da su bane ko? shi yasa nace kawai tunda malan ya tabatar min akoy aurena a kanta sakinta zan yi in komai ya daidaita"
Mah ta jima tana innalilahi Wa inna ilaihi raj'une, da kyar ta daidaita tunaninta ta kalle shi har ta iya sauke ajiyar zuciya tana sake dubansa ta kuma sada kanta sannan ta dago a tausashe ta ce" Ka saketa ka ce?, to kai kana tunanin kowa zai so hada zuri'ar da kai ne Yusuf?, kaima fa abin gudun mata da yawa ne in fada maka gaskiya, kuma a bayanan nan da ka yi inaga in dai ba ta san dukkan shiga da fitar mahaifiyarta ba laifinta daya ne irin sana'arka wace idan Allah ya sa ta shiryu ne ta dalilinka sai ka ga ka kilaceta har Allah ya sa ta zama abar kwatance gobe, domin da yawa a rayuwa ai ana aikata laifi idan an tuba ka ga an yi kyakkyawan tuba an shiryu har an zama abin kwatance, in ba wannan ba YUSUF ai da an halaka sosai a duniya, dan kuwa da yawa sun ci gaba da aikatawa kansu tsaye tunda dai tubar ba wani anfani ko Yusuf? ko dan Amnah mace ce ta aikata irin halayanka zai zamo abinda za'a yi riko da shi a kasa yafe mata har a bata second chance din da zata rayu itama rayuwa mai kyau? ko so kake ka nuna min cewa lalle kai din jinnin Hajia ne da basa yafe irin wannan?"
Da sauri ya kalli Mah, hankalinsa na neman tashi ya ce" Mah, a'a fa, ya Salam ba haka nake nufi ba fa,Mah ki duba ki ga halayanta, ki kuma dubi iyayenta, inace addini ne ya koyar da mu samawa yayanmu iyaye na gari dan gobe su yi alfahari da mu ba? halayarta nake ta dubawa, ina ta yi mata uzuri , Mah sai dai bata da wasu qualities da zan so, kin san da na san bata son ki, haka bata son Hajia, kin san da na san Hajiar su Salima ce aminiyarta wajen zuwa shawararta, idan fa aka wayi gari abinda ya kasance da mahaifinta ya kasance da Ni na yi yaya? Mah bayan ku da kuke a wuyana garina ke wuyana, idan na zama sai yadda mace mai son kanta ta yi da ki ai na bani na lalace ko?"