← Book details Azal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 117

Sashe 1

Azal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

🫶🫶🫶🫶🫶🫶🫶🫶🫶
🫶
*AZAL!*
🫶🫶🫶🫶🫶🫶🫶🫶🫶🫶

*SAJIDA NIJAR*

*PAID BOOK*

_Bismillahir rahamanir-rahim._

*1*

*wannan littafin na kudi ne 300 Naira account details 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi Gt Bank ka turo shaidar biyan ta wannan layin +22793811618, yan nigar kuwa zaku turo katin airtel ko sahelcom ta 500 francs ta wannan layin sai a saka ku 93811618 sai kun zo my lovely reader 😍😍😍😍😍*

*TALLAH, TALLAH, TALKAH*
_*TOH TO TO!*_
🗣_*YEKUWA JAMA’AR NIGER 🇳🇪 DA KEWAYE KU MARMATSO KUJI👂🏼NESA TAZO KUSA SAI HAMDALLAH🙌🏻*_
_Muna matukar farin cikin sanar daku cewa wanan shaharraren kamfanin nan na kasar waje *{CHAINA🇨🇳}* wanda yayi suna duniya tasan dashi fagen hada ingatattu kuma tsaftattun maganguna wato kamfanin *GHT* 💃🏻 yanzu haka yazo kwacokam a *Niger* sunce muma kar abarmu abaya, ina kuke Mataye?_
Wanda suka ansa sunansu cikakkun Mata isassu yan kwalisa shalelen oga? Daku nake
_Amarya_Uwar gida_
_Zawarawa_kai harma da yan Mata kuma kar a baku labari👂🏼_
_Muna siyarda ingatattu kuma shararru magungunan mu kamar haka👇🏼_
INA MASU FAMA DA MATSALOLI KAMAR HAKA👇🏼
🦠*INFECTION*, *🦠 RASHIN HAIHUWA*, *🦠RAGE TUMBI DA KIBA*,🦠 *CIWON HAKORI*, *🦠MAGANIN GYARAN NONO DA MAZAUNAI*
*🦠 CUTAR CANCER*,*🦠 RASHIN KUZARI GA MAZA KO KARANCIN RUWAN MANIYI*,*🦠ULCER*,*🦠DIABÈTE*,🦠 *FIBROID*,*🦠ASMATIC**🦠SKINCARE TRAITEMENT DE LA PEAU*
_KURAGEN FUSKA KO DASU AKA HAIFEKI DA IZIN UBANGIJI MATSALARKI TAZO KARSHE🥳 TAREDA *{GHT}*_
_SIRRIN GYARAN JIKI SAIDA KAMFANIN *{GHT}* KARKU SAKE KUBARI ABAKU LABARI, HAUSAWA SUKACE SAI AN GWADA AKE SANIN NA KWARAI👍🏻_
💁🏽‍♀️MUNA SIYAR DA TURARE KOWANE IRI NA JIKI DANA DAKI AMARYA DA UWAR GIDA *KAMSHI SHINE MARTABAR Y’A MACE🙌🏻*
💁🏽‍♀️MUNA GYARAN AMARE DA UWAR GIDA DILKA DA SAURANSU, ABUN SAI WANDA YAGANI…
_MASU NEMAN KARIN BAYANI SAIKU TUNTUBI *HAJIYA FATIMA* WAKILIYAR *{GHT}* A WANAN LAMBAR KAMAR HAKA👇🏼_
*ADRESSE 94536935 94.53.69.35*
*Muna nan a unguwar Lazaret NIAMEY/NIGER*
MASU BUKATAR SHIGA GROUP INMU DAN GANI DA IDO👀 AKACE YAKORI JI👂🏼
DANNA WANAN LINK DIN ZAI SADAMU DAKU🤝
https://chat.whatsapp.com/INwtTlr1yFQ5B0AQa2DM6d
KARKU SAKE ABAKU LABARI🥳

Litattafan marubuciyar
Duk karyar kada
Yar mahaukaciya
Bak'a ce
Bani da zabi
Daga tafia daukar soja
Neman na kaina
Kutkale
Mage
Bani da zabi
Idan ka raina inda kake
Umughuluk itifal
Duk nisan jifa
Wata kokowar
Ni zan ladabi
Dakika biyar
Da ciwo a zuciyata
Aure yakin mata
Alkalamin Kadarata
Dutse
Daga tafiya daukar soja
Makauniyace
ND now *AZAL*

Kwata kwata ya manta cewa wayarsa ce jone a jikin lasifikar motar dake tafiya da su daga sabon Gari zuwa Anguwar Jeune cadre, hakan ya sa ya gyara zamansa daga gaban motar dake dauke da su, su uku yana sake buga numbar yarinyar nan ama cikin ikon Allah sam ba'a daga ba.

Da mamaki ya sake dubawa, eh lalle numbar ce, tunda aka turo masa numbar da hoton mai numbar bai cenza komai

Da dan dabara ya kalli wanda ke hakimce a bayan motar yana kallon hanyar nan baya ko kiftawa hannunsa sama wajen girarsa a hankali yana shafa wajen yana tunanin abinda ke cikin ransa

A kira na kusan tara aka daga wayar, sai dai babu amsar da aka bada da ta wuce shiru da shuuuuuuuuuuu tamkar karar fanka

"Asalamu alaiki, dan Allah ina magana da RAUDA ne?" Ya fada yana sauraro da tabacin zai ji amsa daga ɓangaren wace aka kira da RAUDA domin a irin labarin da aka bashi na ita din wacece ya san ko Muryar yaro karami ta ji in dai namiji ne zata saurara

Shiru ya dauki wayar da motar baki daya

Sai da ya ja numfashi ya sake furta" Wai ko ba'a jin muryana daga wayar ne?"

Daga ɓangaren wace aka kira da RAUDA ta ja wani arnen tsaki sannan ta datse kiran
Tsakin da ya ratsa baki daya motar har cikin kwakwaluwar mutumen dake bayan motar nan zaune

A hankali ya lumshe idannuwansa sannan ya bude a kan wanda ke gaba zaune daidai lokacin da ya zarro ido ya ciro wayar a rikice ya zuba dubansa yana duban wayar tamkar wanda ke son karantar wani abu a jikin wayar

Muryarsa a yannayin dimauta ya shiga magana tamkar ba abokinsa ne ke zaune a motar Ba ya ce" YUSEF, Walahi ban san bata da mut......"

Shiru ya yi da maganar da yake yi sakamakon gannin motar na tsayawa dan a bude masu get YUSEF din ya bude motar ya fice bai ce da shi ci kanka ba

A kafarsa ya shige baban get din gidan nasa , du irin tsayin tafiyar dake gabansa cikin tafiya ta nutsuwa da kwonciyar hankali

A birkice wanda ke cikin motar ya dafe gaban goshinsa lokaci daya ya shiga kiran numbar wace ta bashi numbar

Nafisa na dauka ya shiga masifa yana fadin" Yar gidan uban waye kika bani numbarta? Dama bata da mutunci ko bata san abinda ake iya kiranta dominsa bane? A kan mi zaki bani numbar baki min bayanin komai ba?"

Nafisa ta yi dan firgigit sakamakon barcin da ya fara fizgarta na bakin magariba dan ta gaji ainun , daga wajen biki take har juwa ke kwasarta dan gajiyar rawar da suka tika tana wara idannuwanta ta ce" Ban gane ba da ka kireta me ta ce da kai?"

Rai bace ya ce" da na yi kiranta tsaki ta yi ta katse wayarta, ke kin san waye za'a kawowa ita?"

Nafisa ta dantse lebe cike da takaici ta ce" Ba yar uban kowa bace , dama a yadda na ga alamun fadin ranta sai da nace da kai oga du yan matan nan ita ta maka? Kace eh, menene kake nema a wajenta wanda babu a wajen sauran? Ama ka yi hakuri zan tardata sai na mata rashin mutunci, Duda ba ni ta ba numbarta ba , Ni ko magana bata taɓa hadani da ita ba dan na tsani ire irin yan matan nan masu shegen dagin kan tsiya!"

Takaici ya saka shi kashe kiran ya bude motar ya fice shima ya shiga a kafar yana takawa da sauri dan burinsa ya je ya bashi hakuri , dan shi ya san shirunsa ba alkhairi bane

A lokacin da ya karasa bangarensa da kyar ya kama madubin kofar ya bude ya shiga , a nan ya sake yarda cewa mutumen da ya tsane su na wajen, dan haka sai ya kama kansa bayan ya yi salama ya nufi kujerar zaman mutun daya ya zauna yana sake kama kansa

Tunda ya shigo RISLAN ya yi shiru da bayanin da yake yi sannan ya daure fuska yana jin kirjinsa har zafi yake yi saboda yawon da ɗan uwansa ke yi da ISHAK , yawo na shashanci, yawo na watsar da kai da watsar da adini

Murmushi kadan YUSEF ya yi yana dauke dubansa daga kan RISLAN ya dan dubi Ishak ya ga ya gyara zama bashi da niyar tashi bayan ya tarda magana suke yi wace ta shafi family isu

Dan gyaran murya ya yi a hankali ya ce" ishak shiga ciki mana "

Ishak din ya mike yana jin zafin RISLAN har kasan zuciyarsa, domin a duniya wannan mutun yana matukar saka masu ido a shige da ficensu da YUSEF, ama shi jiransa yake yi wata rana ya shiga huruminsa WALAHI sai ya nuna masa bashi da wayo! Dan ya nuna masa dan duniya ne shi

Ciki ya shige yana hura hanci,

Sai da ya shige RISLAN ya iya sauke ajiyar zuciya ya sake fuskantar YUSEF

A tausashe ya ce" ya dace ka san me kake ciki zuwa yanzu, ya dace ka yiwa kanka wa'azi ka kuma gane a kulun shekarunka karuwa suke yi ba ragewa ba, ka sada kanka ka yafe wasu abubuwan ka kuma kyale wasu ka rayu da su a haka, ka je ka ga HAJIA ana ruwan saman nan na jiya ta fadi ta samu karaya kuma an kirayeka an sanar maka, HAJIA fa mahaifiyar mai martaba ce YUSEF"

Murmushin nan nasa wanda yake kama da ashariya ya sakar masa kafin ya dauke dubansa a Nutse ya ce" To "

RISLAN ya zuba masa ido da duba irin na tsoron yannayinsa

Hannayensa ya hade yana dubansa ya ce" Yaya zaka ce to bayan na san ba yi zaka yi ba? Dan Allah na roke ka ka je....."

"Kar ka saki ka rokeni kan abinda bai zame mini wajibi ba!, na goge zumuncina da ita, ubana ta haifa ba Ni ba shine dolenta, maganar na bar abinda nake yi nace maka to zan bari, me yasa kake so sai ka saka na daga maka murya ne?" Ya fada a kausashe, ama a hankali dan ko me yake yi tsakaninsa da ɗan uwansa bai taba yarda wani ya ji ba

RISLAN ya rintse idannuwansa da suka cika taf da kwallah, wannan wani irin Fitina ne ke yawo a jinnin ahalinsu, sai kace ba jinnin sarauta ba? Daga mashaya sai mazinata, sai masu halaya irin na bera? Ya Allah ka dubu lamarin wannan ahali

A hankali ya ce" Ka tabbata zaka je dan uwana?"

Shiru ya yi da farko, sai kuma ya sakar masa murmushi a hankali ya gyada masa kai ya ce" Zan je bi izinillah"

"Ka san me Abanmu ke buri? Burinsa ya ga ka yi aure kaima, ka san burinsa ya ga kaima ka kawo matar da kake so ka yi aure Dan uwana" RISLAN ya fada a tausashe yana sake zuba masa ido dan gannin reaction dinsa

Mikewa YUSEF ya yi a Nutse ya bale rigar dake jikinsa ya cireta ya ajiye nan saman kujerar falon ya zamto abinda ya rage a jikinsa farar singileti ce

cikin nutsuwa ya juya ya nufi wajen frij din falon ya bude ya ciro galan din ruwa mai sanyi ya juyo ya dawo falon ya bude yana mika masa

Amsa RISLAN ya yi yana furta" Thank you"

YUSEF ya zauna yana janyo computersa ya bude ya yi connecting da wifi din gidan sannan ya ajiye ya juyo ya zubawa RISLAN ido kamar yadda shima yake kallonsa

Murmushi ya yi a Nutse ya ce" Ni fa ba mata bane bana so, Idan na ki mata waye zai bani abin sakin mara?, Usatz soyayya da mace daya ne nake yiwa lakabi da *AZAL*!, ba zan taba yarda ganganci ya jani wannan ba, aure kuma ka cewa babanka kar ya damu idan na shiryawa hakan zan kawo mashi hudu ya kula!"
Chapter 1 · 0% Book details