← Book details Azal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 117

Sashe 47

Azal Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ido Mama ta kwalalo tana ja baya tana kallonta, dan tunda suke, tunda Allah ya hada zamansu bata taba yi mata magana ido cikin ido da tabbacin furucinsta irin na yau ba, duk irin yadda kirjinta je hayaki a kan maganar mijinta sai ta kasa kwatar yaron da take gannin shi kadai ne hanyar da zata rika ta rike wuyan RAUDA sai yadda ta yi da ita ba

RAUDA ta dago fuskarsa tana kallonsa ta ce" In zane su? Kana so in zane su?"

Abdul ya ringa gyada kansa yana kuka yace " Aunty? Ke ce ko? Aunty ki zane Salaha, kin ji? Tace Ni ne wai mai kama da aljannu, kuma tace min mahaukaci......"

Ai bai gama rufe bakinsa ba ta maida shi bayanta a guje ta ridi Salaha

Kafin Salaha ta samu ta gudu daki Rauda ta yi mata rikon da ta fi jin tsoro, ta rike mata wuya daf ta watsota waje

Salima ta zarro ido abin na neman fin karfin ta tana neman kiran sunnan RAUDA wace ta shake wuyan Salaha sosai ta sake zarro ido gannin Mama ta dauko katon ludayin miya irin tafkeken nan ta daga ta makawa RAUDA shi a bayan kanta

Ihu Salima ta saka, da gudu ta nufo Mama tana neman rike ludayin ama sai da Mama ta sake makawa RAUDA shi tana fadin" Na maki alkawarin nice ajalinki, sai na kashe ki!, ba kin samu gidan sarauta kin labe ba? Dole zaki dawo inda nake ki nemo mana abinci ko ciyar da mu , dole zaki fito ki nemo min mijina , munafuka algunguma shegiya mai tafe da *AZAL* a duk inda kika shiga, iyayenki dan sun haife ko masifa kala kala sai da suka shige rami gaba dayansu koka huta, Ni da aka kawowa ke gashinan kulun cikin balaki nake karshe wanda ya dauko kin zaki jawa a rasa inda yake?, karya kike yi mai kama da kulba sai dai na kashe ki na kashe banza!"

A rikice Salima ta yi waje, dan abin ya fi karfin ta, kuma abinda ya bata tsoro du irin ihun da suke yi makota babu wanda ya leko ko wa'inda ke waje babu wanda ya shigo

Da gudu ta karasa wajen direba jikinta ma rawa ta shiga nuna masa tana haki tana fada masa lokaci daya kuma tana fadin" Ta kashe RAUDA, ta kashe ta, innalilahi wa inna ilaihi raj'une, ka kira police, ka sanarwa mai martaba kar Mah ta ji, kar ka sanarwa Mah!"

Magana take yi hankali tashe tana son juyawa gidan da sauri direban YUSUF ya fito daga motar ikon sauri ya ce" Hajia, ki dan tsaya kar k8 shiga bari na je"

Kana gannin yadda yake magana ka san irin mutanan nan ne da basa tsoron a mutu, direbansa ne wanda ke kai Mah anguwa idan baya nan, mutumensa ne da dalili ya haɗa har ya dauke shi aiki

Yana fada ya nufi gidan da sauri yana kautar da mutanen dake tsaitsaye, ita kuma tana biye da shi a guje dan gaba daya anguwar ta shiga bata tsoro

Salaha ya fara ganni rigar dake jikinta ta yage sosai, ama ba ta kirjinta dake fili take ba, sai kakari take ta cuje rufar da ta yiwa kanta, gashin kan a tsaitsaye sai kwalalo ido take tana cenza waje, sket din jikinta kuwa harda jika kamar wace ta zabga fitsarin kwonce

"Ina Hajiar?" Ya fada murya a kausashe yana kallon Mama, wace ke haki sai yade yaden magana take yi kan ta ga ubanda zai fitar da RAUDA domin bayan ta sumar da Raudar kama kaffafuwanta ta yi ta ja ta da kyar ta kaita falo, sannan ta hankada keyar Abdul ya je ya rukunkumeta yana ihun kuka , a nan ne Salaha ta mike kamar zata mutu ta sace wayarta dake yashe a nan ta boye a jikinta sannan ta ci gaba da murzar jikinta dan walahi ta shaku iya shakuwa

"Wace Hajia?" Mama ta fada tana kame kame dan daga yannayin tsayuwarsa ta san yana iya yi mata aikin gajanci la'ada waje

Tsaki ya ja gannin matar fa kamar wata cika ce Walahi, sai kawai ya shigo da kyau ya nemi zagayeta dan shiga dakin lokaci daya yana neman layin YUSUF

Har zai shiga ya dan juyo gannin ta dauko ludayin nata ya dan zuba mata ido sannan ya kalli Salaha da Salima da suka yi zuru zuru sunna kallonsa

Alamu ya masu na su dan dakata , daga tsayen da yake ya risinar da kansa, ya jimke hannunsa da girmamawa sosai ya furta" Barka da warhaka Uban mai uba, marar ubanma kaine ubansa, Barka da warhaka ja gaba ikon Allah, Barka da warhaka dashen Allah, rubutace kake babu wanda zai goge, Allah ne ya nadaka uban gidana ba wani dan Adam ba, dama ina kira ne dan ya kama dole na yi kiran"

YUSUF ya girgiza kansa, ya fara gane abubuwan nan da da wahala a bashi lafiya da su, wato kirari kirarin nan sai kawai ya share shi , a hankali ya furta" Lafiya?"

"Dama su Hajia da na kawo ne aka samu matsala, dan inaga a summe take sosai, matar da muka zo gidanta ne ta shinfida mata koshiyar girki!" Ya fada da irin Muryar nan ta daba, yana sake gyara yannayinsa tamkar a gaban YUSUF din yake

YUSUF ya yi shiru yana tunanin ikon Allahn nan, kai jama'a summe kuma?, ga Mah a cikin zuciyarsa wace tashi daya ya yi tunanin idan har ta ji ai itama tana iya sumewar

A kame ya furta" ka dawo da ita yanzu yanzu, a shigar da ita ciki kafin su Mah su dawo likita zata yi jiran ku"

Daga haka YUSUF ya katse kiran nan ya shiga kiran layin likitarsu ta familly

A dayan bangaren kuwa ana katsewa ya mayar da wayar aljihun rigarsa ya juya da nufin shigar, sai ya ga still Mama na son yi masa ganganci

Juyowa ya sake yi yana murmushin da ya kashe zuciyar Salaha dukda halin da take ciki ta yi mutuwar tsaye tana kallonsa
Yana kallonta ya ce" Hajia yawa ne walahi, idan kika gwada ba zai haifar maki da d'a mai ido ba, dan tsaf zan moda maki shi a Keya numfashi ya dauke a kamani, ki dan bari mana na gama aikin oga dan har ga Allah mu yan a mutunsa ne, oya bani hanya dan dole na dauko Hajia!"
Yana gama fadi ya shige ciki , ya tarda Abdul zuwa yanzu muryarsa ta gama disashewa ta yi kwonce jikin RAUDA yana ta kuka mai fitar da hawaye ama babu amo

Dan zuba masa ido yayi yana mamakin meye ya haɗa matar nan da mutanen nan masu salihan fuskoki?, yaron nan ya bashi tausayi ainun, hakan ya sa da ya talaba RAUDA Abdul ya riketa tam yana kukan kar a tafi da ita ya fara tiso shi gaba suka fito da ƙafarsa ya nemi hangaje Mama da ta so riko Abdul din , da idannuwansa kuwa ya mata alamun yana iya daka mata kafa , hakan ya sa Mama kwasar kururuwa tana fadin yan anguwa su taimaketa kwarton RAUDA ne ya zo ya dauki harda Abdul marayan Allah zai tafi da su duka su kwato mata su, ama yan anguwa suka ki bin shi har Salima ta bude masa bayan mota ya saka RAUDA Abdul ya shige yana sake riko hannunta na dama dake yarfe, shi kuwa ya shige gaba Salima ta shige bayan itama ya tada motar ya figeta ya fice a anguwar

Sosai mama ke ihun kuka, kukan da take yi na yanzu mai shiga zuciyarta ne yana tarwatsa duk wani tunanin gannin mijinta da ta yi a kwana kusa, dan gani take idan har aka tafi da RAUDA da kuma Abdul shikenan babu mai nemo mata Umaru , hakan na nufin ya mutu bata ga gawarsa ba, hakan na nufin zawarci ya kamata da ciyar da kai da biyan haya, hakan na nufin rikon Yar nan cilo ya dawo hannunta gaba da baya, hakan na nufin ko a koma saide saiden abinci a bakin titi ko kuma a koma kauye in dai ana so a rayu? Ina , ba zai taba yiwuwa ba, walahi har garin nan da Rauda take sai ta bi ta dan itace kadai zata iya nemo mata mijinta a garin nan!

Tana komawa ta tarda Salaha zaune ta tafka tagumi da hannayenta bibiyu tana kallon kofar da Maman nata ta fita

Mama ta karaso inda take da tausayinta tana share hawaye ta ce" Salaha, kema kin fara shiga tunanin mahaifin naki yanzu ko? Ko ta jiyatar da ke ne? Tashi ki yi wanka ki je chemis ga yan cenjina nan a baki magani kar aje ta maki mugun rauni kin ji?"
Chapter 47 · 0% Book details