← Book details Azal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 117

Sashe 46

Azal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da dan murmushi Rauda ta ce" Me kika gani Salima?"

Salima ta ce" Na ga daidai lokacin da kika fito daga wanka da yanzu ba daya bane yannayinki, ina fatan lafiyarki kalau?"

RAUDA ta yi mata murmushi bata ce mata komai ba har suka karaso kofar gidan suka sauka daga motar direba ya parker yana jiransu, domin bakon Salima ya fi minti talatin a motar a zaune yana jiranta, motar da Salima na gani ta gane ko wace irin mota ce domin Bah ya hau ta, ƴaƴansu ya bashi ita a lokacin da ya sauke su

Tunda suka sauka daga motar ya bude ya fito, fuskarsa ke dauke da murmushi yana kallonta har ya karaso inda suke tsaye yana sake sakin fuskarsa da walwala sosai ya ce" ina farin cikin sake gannin ki masoyiyatah"

RAUDA ta yi dan murmushi tana dauke dubanta a kansa ta maida kan Salima wace ke yin murmushi tana kallon Balarabe sak abinsa, hausarma gatanan dai, ama zai yi Sa'a Bah gaskiya

Da dan murmushi a fuskarta ta furta" Marhaban bika fi'akhi"

Murmushi ya yi sosai har kamar ya rungumeta ya yi mata irin gaisuwarsu ta larabawa, ama ta jima da sanar masa ta fi so su kiyaye hakan su yi koyi da abinda addini ya kawo

Yana kallonta ya ce" Na gaza hakurin sai gobe na gan ki, ku je cikin mu zauna ko?"

Da da ne, zata iya jan shi cikin gidan koda ta shekara bata nan, ko ta je motar tasa su zauna su zanta, ama a yau sai take jin wani iri kamar ba zata iya ba,
Saima da ta kalli Salima, sai ta ga kamar wace take mata gargadin zuwa ta shige motarsa
Kai ta dauke a tausashe tana kallonsa ta dan langwabar da kanta ta ce" Ka yi hakuri na Barka kana jira, ka san yanzu ina cen gidan.....gidan....."

"Gidanmu, take nufi, gidan garin Tsatsunburum, Ni yar uwarta ce, yanzuma mamah ce tace mu zo mu sanar maka, ana son ganninka a fada " Salima ta karɓe zancen, a tausashe ta sanar masa sakon da ta kula Rauda ba zata iya fada ba, dan tunda ta fara maganar nan ta shiga dan juye juye da dan shafa agogon hannunta ta tabata zancen bata gama karbar sa ba sai kawai ita ta sanar

Harda ajiyar zuciya Rauda ta sauke dan kuwa Salima ta taimaketa ainun, domin bata san yaya zata fada masa ba, dan kusan duk wani wanda zai fita da ita bayansa ne, shi din ya san komai nata, ciki harda marikiyarta

Abdullal Jabar abin ya daure masa kai ainun, sai dai wannan magana ta ana son ganninsa a fada ta saka shi rikicewa da farin ciki, kwarai Allah ya amshi adu'arsa, ga dukkan alamu abinda ya roka kan kar ta wahalar da shi ko ta ki shi Allah ya amsa

A hankali ya juya bayan Salima ta sake tabatar masa da maganar da yake tunanin haka ne, cike da shauki da farin ciki, Rauda na biye da shi har kusan motarsa, sannan ya sake juyowa yana kallonta da tarin mutanen dake ta kallonsu ba yaran ba, ba manyan ba ya ce" dama kina da alaka da HONORABLE BELLO?, "

RAUDA ta sada idannuwanta, a hankali ta ce " bayan tafiyarka, Allah ya hadani da shi da matarsa da kuma dansa, shine suka daukeni , matarsa tace ita din uwa take a wajena zata rikeni tamkar y'ar da ta haifa, hakama mijinta ya yarda"

"Wai kina nufin harda SS YUSUF ?" Ya fada yana zarro idannuwansa cike da mamaki

Dan tsaida maganarta ta yi tana kallonsa
Sai ya basar, gannin kallon da ta yi masa, ya dawo kan maganar da ta fada din ya ba abin mahimmanci sosai

Kwarai ya ga cenji, domin babu irin yadda bai yi ba kan ta tsaya ta amshi tsarabarta ta nuna an hannata sai ta tambaya a gida, karshe dai suka rabu da cewar gobe da dare zai je ta sanar a gidan nasu , ya juya ya tafi yana jin kwarai nutsuwa na shigarsa, a yanzu ya san idan ya buga da karfi Rauda tashi ce , burinsa zai cika kwana kusa kennan? Allah kennan mai yadda ya so da bawansa a lokacin da ya so

Tana juyowa idannuwanta suka sauka kan Salaha dake tsaye a dokin kofar gidan, jikinta sanye da wani zani baki wanda a ido kawai idan ka kalla ka san ya yi dati, rigarta kuwa kamar irin kannanun rigar nan da ake sakawa a ciki ne du ga nono nan ya bayyanar da kansa sai wani dan kwalin atampa ta yafa tana kallon Raudar da bakonta

Da sauri ta koma gidan gannin Raudar ta nufi gidan da wata bakuwa

Tana shiga da karfi ta ce" Mama, walahi gatanan shegiyar ta dawo, an gama yawon ta zubar din, kin ga balaraben da ya ajiye ta? Ni dai ko randa ta taba ba zan sha ruwan randar ba, kar na gogi kanjamau, kin ga wai yadda ta karra fari? Ta yiwu ita ta sake maki miji kina nan kina kuka a banza a wofi , ai na fada maki ki daina kukan nan tunda kin dauko Abdul zata zo ne!"

Turus RAUDA ta yi jin magangannun da Salaha ke yi

Ai kau idannuwanta suka sauka a kan Abdul dake zaune gaban pampo yana wanke wanken kwanoni, kana gani ka san ba a hayacinsa yake ba, tsoro ne fal a fuskarsa kuma wankewar sai yi yake kamar an aiko shi

A raunane sosai ta ce" Abdul"
Ya ji ta fa, ama yaron nan ya gaza waigowa dan a tunaninsa ba ita din bace kunnayensa ke masa gizo

"Munafuka, annamimiya, yau sako ya je maki baya nan kin zo nan nemansa ko? Kwarai ni na dauke shi ko zaki tuna da ubanki wanda ya rike ki ki zo ki nemo shi, in banda rayuwa irin ta wanda baida imani ke har kya manta Umaru? Ko fitar nan da ya yi ai sanadiyar ki ne, dan kin kawo masa kudin karuwanci gida, shine zaki tafi ki yi kwonciyarki ance a masarauta ko? Sai ki zo ki samo min mijina idan ya so ki biya Ni bashin da nake bin ki sannan ki dauki wancen mahaukacin ,dama rikonsa sai ke ai!"

Bata tsaya bi ta kan magangannunsu ba, magangannun da suka saka Salima daskarewa a waje daya cike da tsoro da mamaki,

idannuwanta rufe ta karasa wajen da Abdul yake da sauri ta dago dago shi, jikinsa da dati da abin fitsari da abin miya gaja gaja ta rungume shi a jikinta a birkice murya a rarrabe tana fadin"
Azl 26
*Tallah, tallah.....tallah manyan hajiyoyina*

Bismillahi rahamanin rahim

Metaforce online business ne na crypto
Wanda aka tabbatar da halaccin sa ,sannan aka tabbatar da cewa ba irin wannan platform din bane da ake gudu da kudin mutane.....domin Metaforce zaka shiga ne da kadan ka dauki da yawa, da wannan Hajia Ummu Khalil wace ke zaune a kasar Nigeria sananiya ce fitaciya ce mai dauke da numbobin waya kamar wanann 07038708382 ta kawo mana hanya mafi sauki dan samun ci gaba.......ku saurara dai
*METAFORCE*
Yana da level 1_12
Idan Zaki level 1 Zaki Fara da Doller 5,,level 2 Doller 10 ,level 3 Doller 20 Haka dai har 12
YADDA AKE SAMUN ALKAIRI A METAFORCE

💃🏼 Kina Gama register za'a Baki TR coins na adadin level din da kikayi,ko a iya su kin Mai da kudinki fa idan akayi lunching🏃🏻‍♀️🕺😁 .....WASHE BAKI SOSAI HAJIATA....YEAH KO A IYA SHI KIN MAIDA KUDINKI BALE GA WANI DANDANO MAI ZAKI.....

*Refferel bonus duk mutum 1 fa idan Kika kawo za'a Baki adadin abinda yasa yayi level din, banda 2 na farkon level 1 da 2*

💃🏼 Ga Kuma garabasa na spillover
Ko kin kawo mutane ko Baki kawo ba kina iya samu 💃🏼💃🏼musamman tunda Ni da Zan Miki register Ina aiki sosai (wauh fantastique)

Spillover shine zakiga ansa Miki mutum a kasanki ,Kuma a biyaki fa ko Kuma a cike Miki biyu ko dayan farkon nan💃🏼 (magnifique)

Da Dollars suke biya idan kinaso Zaki iya siyarwa duk dollers din Kika samu a take a tura Miki kudinki cikin account 💃🏼💃🏼💃🏼 (da wa kika ja Madame?)

Metaforce Babu FADUWA Babu asara a ciki...... Ku zo mu kafta duniyar sananu mu samu yanci, nema sai da nema, ki shigo Mu je, kasuwanci mu babu algus ba cuta, zaki kwashi kudinki koda baki kawo kowa ba😍😍😍 sai kun zo

Tana fadin " Abdul, Abdul, Abdul Nine, auntynka ne, kalleni Nine fa"

Tunda ta rungume shi, ya shiga maganganu hadi da kuka, magangannu irin wa'inda mutun kan tarawa idan wani wanda ke hanawa a wulakantashi baya nan aka wulakanta shi idan ya dawo dan ya sanar masa
Ido a rufe hawaye a fuskarsa yake fadin" Auntyna, auntyna ko? Sai ta zane ku, ku dukan ku, idan ta zo sai na fada mata Salaha ta zane Ni, ta hanna min tuwo, ta hanna Ni zuwa makaranta, dan ta ce na mata wanki nace ban iya ba ta saka na yi ta zane Ni, ta saka na yi shara, Abdul bai iya komai ba ama tace sai na yi sai na yi wanke wanke, har na kone hannuna da mama tace sai na hura wuta, sun ce Abdul maye ne sai kallon mutane, bayan auntyna tace Ni ba maye bane, sun ce wai sai sun yankani idan baki zo ba, kin gansu sun doke Ni, sun rufe daki sun barni na kwana a waje , ina tsoro ina tsoro ina tsoro......"
Sai kawai RAUDA ta fashe da kuka, a rikice ta dago tana kallon Mama wace ta karaso tana son kwalkwatar Abdul dan ba zata taba bari ta tafi da shi ba, domin idan ta tafi da shi ta san shikenan kuma labarin mijinta ba zata kuma ji ba, ita kuma walahi wannan abin sai ya haukatata, rashin Umar tuni yana daf da zautar da ita,

A rikice ido a kausashe Rauda ta yi mata nuni da yar yatsarta ta ce" idan kika kuskura kika taba hannunsa , yau sai na yi kason ki!"
Chapter 46 · 0% Book details