← Book details Azal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 117

Sashe 39

Azal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hankali ya lumshe idannuwansa jin wani abu daban wanda ya zarce wanda yake ji a da a kan yan uwansa, a yanzu abinda ya ji wani mai girman da yake ji kamar ubansu yake, ko dan SALIMA ya sani a soyayar da take masa na yayanta ba karya ciki ta kire shi tashi daya da BAH ne?, a tausashe ya sakar mata murmushi bayan ya sake bude idannuwansa daga lumshewar da ya yi, sannan ya ringa daga masu hannu na gaisuwar da suke masa daga su har iyayensu

Juyawa ya yi bai tsaya ya tantance waye da waye a wajen ba ya tafi tare da tarin jama'ar dake jiransa da Hajia a tsakiyarsu har ya zauna sannan ta tafi nata bangaren ta ci gaba da zaman makoki

A cen kuwa bayan tafiyarsu iyayen nasu kowace shigewa ta yi giki, hakan ya sa Mah ta yi tsaye kan yan matan su zuzuba abincin kowa ya karya sannan kowa ya kama yan ayyukan gidan, har tana tsokanarsu cewar yau ba za'a kirayi mai aiki ko daya ba, masha ALLAH yan mata birjik haka, yau har Auta sai ta yi guga
Da wannan suka tafi wajen abincin suka shiga zubawa, Rauda ta kasa hakuri gannin Salima ta kasa daina kuka tana kallonta ta ce" Kukan me kike yi wai?"

Salima ta kalli RAUDA, dan bata yi tunanin zata wani damu da wani abinda ya shafi wani

Dan murmushi ta yi ta ce" Baku ga yayanmu ba? Baki ji kamar zaki summa ba da ya fito?"

RAUDA ta dan zarro ido tana kallonta, ta girgiza kai
Salima za kalleta da mamaki ta ce" Wai Allah?, baki ji kirjinki na bugawa ba?"

RAUDA ta sake girgiza kai harda dan dafe haba, dan ita gaskiya bata kalle shi bama bale har ta wani ji ko zata summa ko me?

Gaba ta yi da plate din dake hannunta na Mah, Salima ta bita da kallo baki bude har ta bacewa ganninta, Salima ta gyada kai kasa kasa tana zuba na su Musulima ta ce" Aman a wajen nan waye bai zubar da hawaye ba fisabililahi? Kai RAUDAH".........

😂😂😂😂🤲🏼🤲🏼🤲🏼🤲🏼🤲🏼
Azl 22
*Tallah, tallah.....tallah manyan hajiyoyina*

Bismillahi rahamanin rahim

Metaforce online business ne na crypto
Wanda aka tabbatar da halaccin sa ,sannan aka tabbatar da cewa ba irin wannan platform din bane da ake gudu da kudin mutane.....domin Metaforce zaka shiga ne da kadan ka dauki da yawa, da wannan Hajia Ummu Khalil wace ke zaune a kasar Nigeria sananiya ce fitaciya ce mai dauke da numbobin waya kamar wanann 07038708382 ta kawo mana hanya mafi sauki dan samun ci gaba.......ku saurara dai
*METAFORCE*
Yana da level 1_12
Idan Zaki level 1 Zaki Fara da Doller 5,,level 2 Doller 10 ,level 3 Doller 20 Haka dai har 12
YADDA AKE SAMUN ALKAIRI A METAFORCE

💃🏼 Kina Gama register za'a Baki TR coins na adadin level din da kikayi,ko a iya su kin Mai da kudinki fa idan akayi lunching🏃🏻‍♀️🕺😁 .....WASHE BAKI SOSAI HAJIATA....YEAH KO A IYA SHI KIN MAIDA KUDINKI BALE GA WANI DANDANO MAI ZAKI.....

*Refferel bonus duk mutum 1 fa idan Kika kawo za'a Baki adadin abinda yasa yayi level din, banda 2 na farkon level 1 da 2*

💃🏼 Ga Kuma garabasa na spillover
Ko kin kawo mutane ko Baki kawo ba kina iya samu 💃🏼💃🏼musamman tunda Ni da Zan Miki register Ina aiki sosai (wauh fantastique)

Spillover shine zakiga ansa Miki mutum a kasanki ,Kuma a biyaki fa ko Kuma a cike Miki biyu ko dayan farkon nan💃🏼 (magnifique)

Da Dollars suke biya idan kinaso Zaki iya siyarwa duk dollers din Kika samu a take a tura Miki kudinki cikin account 💃🏼💃🏼💃🏼 (da wa kika ja Madame?)

Metaforce Babu FADUWA Babu asara a ciki...... Ku zo mu kafta duniyar sananu mu samu yanci, nema sai da nema, ki shigo Mu je, kasuwanci mu babu algus ba cuta, zaki kwashi kudinki koda baki kawo kowa ba😍😍😍 sai kun zo

Cikin hukuncin ubangiji a haka cikin sama da kasa da fari da baki har aka wayi gari aka yi adu'ar sati ta mamacin, wace a tsakanin satin nan babu abinda Mah da YUSUF basu gani ba na mamaki daga mutane daban daban-daban na waje da na cikin gida , abubuwa na girmamawar da a da basu samu ba, zumuncin da a da Mah bata samu ba ta gan shi, dan har aka yi kwana bakwai din nan ras da rasuwar nan ya'yan yan uwanta na nan sunna kwana a dakinta su tashi a yi dukkan ayuka da su, kuma da zarar karfe goma ta yi a fara ba mutane damar shigowa yan uwanta tasu zo su wuni da ita sai da magariba suke juyawa, tun tana dari dari har yanzun ta saba gannin wulagawarsu ta kuma gano eh da gaske suke yi yanzu suke zumunci da ita, sunna nufin yanzu take mutun, itama sai ta ari yannayin wasan su, a ranta ta yafe masu ana zumuncin da ake son yi na nesa da nesa da dariyar hakorin,ama bata jin daga nan zasu samu yadda suke so daga gare ta, domin sunna sun harda su shawara su ringa yi tare da sauransun nan, hakan take gannin idan har ta yarda ta yaudari kanta da kanta kuma ta zama sakarya kennan!

Yau tunda sassafe yan matan nan suka samu matsala sakamakon abinda daya ta dora a Tiktok saman sunnanta na Tiktok, wato Mrs mai martaba.....hakan ya sa Musulima yiwa abin dariya har ta kasa rikewa sai da ta fadi sunnan a lokacin da ta fito daga wanka daure da tawul rai bace ta ce" Iko sai Allah, wai duniya ana kani'iba in ji bahaushe, in ba cune cunen kaza ba me ya kai bakinta cikin zazafar miya?, ana gannin abubuwa a duniya masu ban mamaki, su matan mai martaba manya!"

Sosai abin ya yiwa Akilah ciwo a zuciya, har ta kasa hakuri ta dubi Musulima ta ce" Da kyau tunda na iya na iya bambance abin kunya da wanda ba na kunya ba, kuma tunda lamarin nan halal ne tabatuwarsa alkhairi ne ina da yakini, sai dai kuma in wace ta fi kowa kiyaye Sannin mai kudi ne ta dawo son hada zuri'a da mai mulki dan a yanzu ta gane dan kana da kudi baka da mulki shirme ne ya sa har take iya yafe zagin da ta yi a baya na nasaba to sai ta auna shirinta tsaf mu gani, domin na fito a shirye jinnin dake yawo a jikina kuwa ba na abu ya BARNI bane sai dai na bar shi, dan ko wane ka dauka an dauko, kuma Ubangiji ya kawata halita!"

Hindatu ta yi mamakin su gaba dayansu, sai a nan ta yarda da furucin mahaifiyar kan kasantuwarsu a gidan nan, tana kallon su suka yiwa junna tas ta hanyar gorace goracen abubuwan da iyayensu suka sani a tsakaninsu, sai dai basu daki junna ba, dan karrara Mah ta nuna masu gaba da suke bata so, ba zata iya dauka ba bale a kai ga dukan junna? Lalle ta yarda sunna son abinda take so, hakan ya sa ta sake zage damtse dan ita ta fi ganewa ta bi ta kasa ko zata samu biyan bukata!

Haka aka yi wunin nan, yan matan kowace na falon da ta fi so tana chating dinta Salima na karatu a dakin kayan karatunsu Rauda kuwa tana zaune da wayarta ta dauko layinta wanda kowa yake da numbarta ciki harda aminiyarta Bara'atu ta saka layin tana murmushi a ranta tana ayana' ta yiwu Bara'atu sai ta min gaba, na tabata ta neme Ni, ki yi hakuri kawata, ban kashe wayata dan kar na yi zumunci da ke ba, na yi haka ne dan na baki damar fuskantar gidanki da mijinki a tsanake ta yadda ko menene zaki fi fahimtar abinki da kanki, dan na san halinki kin ga damar da ya fita ki kirayeni mu dasa fira har ki manta da girkinsa, gashi magidanci kike aure ba saurayi ba bale nace ya saba, a hakan tsaf yana iya fara jin haushinki balle idan matarsa na cika masa kullu'

Har zata tura kiran numbar Bara'atu da layin, sai ta fasa ta ajiye ta shige wanka dan tana so ta je dakin Mah ta gaisheta rabonta da ita yau tunda safe da suka gaisa, ta yiwu ta sameta a dakinta ko kuma ta tafi wajen BAH?

Wanka ta tsalo ta fito daure da tawul ta dauki pant baki ta saka da riga mai siraran hannaye doguwa irin mai dan lafewa a jiki din nan, rigunnan da Mah ta bata ne a cikin akwati wa'inda ake daura masu lafaya masu laushi ne, ita sai take saka su ta dora masu zumbulelen hijab, takan jita sakayau ba wani damuwa dan harda tsaga garesu wace ke hanna rigar hardeta

A nutse ta dauki turarenta mai sunnan bonbon mai blue din gidan nan mai sansanyan kanshi da dadi ta shiga fesawa a jikinta tana karawa tana dan murmushi dan tana son kanshi a rayuwarta sosai sannan ta dauki hijab mai ruwan blue mai duhu sosai ta zumbula ta fitar da hannayenta ta hannayen ta saka bak'ar Safa dinta mai kwaliyar nan wace ke nuni kamar ka yi kunshi sannan ta juya hankali kwonce ta dauki wayar ta ringa gannin Msg na shigowa ta whatsup din da ta dora layin ta yi murmushi dan layinta ne da aka fi sanninta da shi, dama ta san sai ta tarda tarin msg a ciki, ta sauke layin da suke waya da Mutumen ta dan dazu yace yau zai taso daga maroko ya zo Nijar , tafiyar wuni daya da kwana ne a jirgi dan jirgin yawo ne dole ya shiga domin ya kasa samun special har gashi tana so ta sake daga hankalinta, shi kuwa abinda ya fi komai rikitashi a yanzu kennan
Chapter 39 · 0% Book details