← Book details Azal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 85 OF 117

Sashe 85

Azal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Metaforce online business ne na crypto
Wanda aka tabbatar da halaccin sa ,sannan aka tabbatar da cewa ba irin wannan platform din bane da ake gudu da kudin mutane.....domin Metaforce zaka shiga ne da kadan ka dauki da yawa, da wannan Hajia Ummu Khalil wace ke zaune a kasar Nigeria sananiya ce fitaciya ce mai dauke da numbobin waya kamar wanann 07038708382 ta kawo mana hanya mafi sauki dan samun ci gaba.......ku saurara dai
*METAFORCE*
Yana da level 1_12
Idan Zaki level 1 Zaki Fara da Doller 5,,level 2 Doller 10 ,level 3 Doller 20 Haka dai har 12
YADDA AKE SAMUN ALKAIRI A METAFORCE

💃🏼 Kina Gama register za'a Baki TR coins na adadin level din da kikayi,ko a iya su kin Mai da kudinki fa idan akayi lunching🏃🏻‍♀️🕺😁 .....WASHE BAKI SOSAI HAJIATA....YEAH KO A IYA SHI KIN MAIDA KUDINKI BALE GA WANI DANDANO MAI ZAKI.....

*Refferel bonus duk mutum 1 fa idan Kika kawo za'a Baki adadin abinda yasa yayi level din, banda 2 na farkon level 1 da 2*

💃🏼 Ga Kuma garabasa na spillover
Ko kin kawo mutane ko Baki kawo ba kina iya samu 💃🏼💃🏼musamman tunda Ni da Zan Miki register Ina aiki sosai (wauh fantastique)

Spillover shine zakiga ansa Miki mutum a kasanki ,Kuma a biyaki fa ko Kuma a cike Miki biyu ko dayan farkon nan💃🏼 (magnifique)

Da Dollars suke biya idan kinaso Zaki iya siyarwa duk dollers din Kika samu a take a tura Miki kudinki cikin account 💃🏼💃🏼💃🏼 (da wa kika ja Madame?)

Metaforce Babu FADUWA Babu asara a ciki...... Ku zo mu kafta duniyar sananu mu samu yanci, nema sai da nema, ki shigo Mu je, kasuwanci mu babu algus ba cuta, zaki kwashi kudinki koda baki kawo kowa ba😍😍😍 sai kun zo

Mah ta bi yadda du ta dan daburce kadan, a yanzu ta gane a yadda ta fito bata san da wani bayan ita a falon ba, tana kallonta ta nufi dakinta da sauri tana jan rigarta har ta shige, minti kadan ta fito sanye da zumbulelen hijab dinta wannan karron yannayinta ya nuna ta samu nutsuwar tafiyar ko dan ta suturce jikinta ne ko meye? a nutse dai ta nufi kicin din ta bude madubin ta shiga ta rufe

Murmushi Mah ta yi a nutse ta juyo dan yi masa magana, sai ta ga idannuwansa a kan kicin din duda bata nan , dan ta jima da rufewa, kuma yannayin fuskarsa ya dan kame kadan da yadda suke shan rikici tun dazu a kan tea dan da ya taba wanda ta dafa fuska ya tubure shi dai ba wannan ba kuma ya saba idan bai sha ba kansa ciwo yake yi masa, da tace Baby ke dafawa kafada ya daga irin shi dai ba ruwansa ko waye shi dai tea dinsa ya sani

Mah ta dan yi murmushi ta dan motsa dan tana so ya ji abinda wata fada

Cikin dabara ya dauke dubansa ya dan murza hancinsa sannan ya dubi Mah a nutse ya furta" Na gaji sosai yau Mah"

Mah ta yi murmushi tana fadin" Sannu d'an Mah, kana gani yarinyata ma ta gaji ka sa na tasota, yarinyar nan Allah Ubangiji ya nuna min ta samu miji na gari ta yi aurenta itama ta haifi wa'inda zasu bauta mata da jikinsu da lafiyarsu kamar yadda take hidima da Ni"

Dif ya yi, maganar da Mah ta yi ta saka shi yin shiru na yan dakiku kafin ya dago dubansa ya kalli Mah sau daya sannan ya dauke duban nasa yana dan dantse lebensa, a ransa yana ayana' Uhum, yanzunma ai ta haifa sai ya mata hidimar, Ni banma san takabar nan ta meye take yi ba, ko kafin ya rasun sai da ya mata wani abu shi marar jin tsoron Allah?, koda yake ba wace bata jin tsoron Allah sama da yarinyar cen, tana kallon mutun ido cikin ido ta iya raina masa wayo da yin tamkar bata san me yake yi ba, har Ni zan hanneta abu ta aikata, kuma ta ci gaba da kallona ido cikin ido, gata in kasheta ko? ba abinda zan maki RAUDAhhhhhh, ama bana jin in zan iya yafe maki, ba aure aure ba? bismillah ki sake yin wanin sai me daga ke har maman naki!'

"Magana nake yi YUSUF" Mah ta fada da dan karfi tana dan daga hannunta, dan sau uku kennan tana magana bai ce mata komai ba

kallonta ya yi da dan sauri yana furta" Na'am?"

Mah ta fara magana RAUDA ta fito dauke da wata mahaukaciyar butar shayi da kofi na kwalba a saman plate dinta , a lokacin ne Mah tace" Yaya ina ta addu'a har sau uku ba zaka ce min amen ba? na yi maganar Allah ya ba y'ata miji na gari , baka ce min Ameen ba, na yi maganar Allah ya baku zaman lafiya ya kade duk wata fitina baka ce min amen ba, na yi maganar taimako da aka bayar wa mazan masu mana hidima Allah ya karra budi shima baka ce min ba fa"

A hankali RAUDA ta ajiye plate din a saman dan madaidaicin teburin dake dauke da taya biyu kadai wa'inda ake kafe su idan ba'a so teburin ya motsa, kuma ana sakin su idan ana son motsa shi, a nutse ta sake su sannan ta turo teburin har gabansa ta kafe masa shi, a nutse ta dauki dan karamin kofin ta zuba tea din sannan ta dauki zuma ta bude ta tsiyaya madaidaiciya ta saka dan karamin cokali tana motsawa a hankali ta dago idannuwanta jin ya yiwa Mamanta shiru bayan ana masa fada ko dai ya tafi ne?, sai ta ga yar yatsarsa ya kai wajen sajensa a hankali yana dan shafawa lebensa na fitar da alamun murmushin fadan da Mah ta dage tana yi dan kawai bai ce wai amen ba

Mah ta turo baki tana dauke kai, shi kuwa a hankali ya furta" Amen Mah"
Sai kuma ya juyo dan tunda ta fito ya ga fitowarta har zuwa yanzu

Hannunsa fari sal ya miko ya amshi tea din, idannuwansa a kanta da kallon da ya sake sakawa zuciyarta idasa hautsinewa kafin ya dauke dubansa yana sauke ajiyar zuciya a hankali ya kai kofin bakinsa

Da dan sauri ta furta" Bai huce ba fa!"

Mah da ta yi kamar bata nan da gangan dan zata so ta idasa ganewa idannuwanta ta sake dauke kai dan sai ta ji kunya na son kamata bayan ba wani abin suka ce ko suka aikata da zai iya bata kunyar ba, haka kawai dai ta ji inama ace rana ne sai ta bugawa wani kira ta bar wajen ko sa gama rainawa junna hankalin

Idannuwansa ya sake sakawa a cikin nata, da kaifin da sukai masa shi kansa zuwa ita da ta ji kamar zata lume ciki, yana kallonta yana danne harshensa da hanna kansa yi mata tambayar nan daya jal, cewa wai takabar me kike yi? ke takabar me kike yi? dan Allah takabar me kike yi? ama ya kasa dan ba zai so a masa wata fasarar ba, ga Mamanta nan zaune, sai kawai ya yi mata horon da ya fi sakata yin laushi ta hanyar amfani da idannuwansa ya ci gaba da surbar tea din da ta bashi bayan da zafin sosai

Ajiyar zuciya ta sauke a hankali ta dauke idannuwanta a kansa ta juya ta karasa wajen Mah a tausashe ta furta " Good night Mah"

Mah ta dubi fuskarta, du ta yi yaushi kana ganninta zaka ga cenzawar yannayinta, ta yi mata murmushin itama tana fadin" Good night baby, Allah ya miki albarka, ama daga yau ba za'a kuma taso ki saboda tea ba, zaki koyawa matarsa ne!"

A ranta ta ayana' Allah sai dai kar ya sha!'

Shi din kuwa ya ayana' Ita din dai zata dafa shi, wa ya sa ta saba min!'

A raunane RAUDA ta kai zaune tana sake jin irin yadda kirjinta ke yi mata zafi da ɗaukan mugun abinda ta gama yi masa fada dazu, sai dai kasancewar addu'a ce baban makamin da ta gama yarda zai zamo makamin yakin duk wani abinda ke kawowa zaman lafiyarta farmaki sai ta ringa jin sassauci da salama a cikin zuciyarta da kuma dangana, karshema sai ta dauko yabon mamaci ta yaba a zuciya ta bige da yi masa addu'a kamar yadda ta saba har barci ya kwasheta tana yi masa addu'a bata sani ba.

Ya dan jima tare da Mah, har sai da ta kore shi sannan ya mike ya nufi hanyar da ya biyo ya fice ya nufi bangarensa

Ya bude ya shiga mamakeken falon da ya raba bangare bangaren ginnin har sau biyar

Kwarai ya san dama a nan ne za'a fara ajiyeta matsayin bakuwar wajen, kuma ya tabata da wahala ya tardora a rufe kamar yadda bakin amare ke yi, dan tuni ya gama gane wannan fa idan ba'a gama raba hajar a titi Bama da sauki sauki dan yannayinta yannayin tafiyar kayanta

Tun da ya shigo AMNAH ta ajiye wayarta, waya suke yi da mahaifiyarta duk irin tsayin daren nan da kuma kasancewarta amarya tana sanar mata dukkan abinda aka yi daya bayan daya ita kuma tana shawartarta abinda zai fishe su

Murmushi ta sake yi masa tana dan sada dubanta, dan duk yadda take son kallonsa ido cikin ido sai ta ji ta gaza jurewa, bata san yaya aka yi shi baya jin nauyin kallo ko kadan

kansa ya dan kawar yana sauke ajiyar zuciya, da kyar ya danni kansa ya karasa saman falon ya zauna yana sake dubanta da tunanin abinda zai yanke a yanzu

Dubansa ta yi da wata murya ta kisa ta furta" Barka da shigowa ur majesty"

Idannuwansa ya dan lumshe a hankali, hakan ya tabatar mata amsar kennan, sai hakan ya sake saka mata dan shaku da gudun cika surutu

ya jima a hakan, yannayinsa a mace gaba daya sannan ya mike a nutse da nufin tafiya nasa bangaren

Mikewa ta yi zungwai zungwai ta bi bayansa har sai da ya dan dakata ya juyo a nutse yana dubanta
Chapter 85 · 0% Book details