Sashe 69
Azal Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
"No, no, no, ba zaki tarka ba, ba zaki taba tarkar aikata abinda nake tunani ba, domin ban ga abinda zai saka ki aikata haka din a yanzu ba, waye nace wannan da yake tuna maki bakya son Abdullah? RAUDA wani kike so daban shine kika auri Abdallah? aure! RAUDA kin san menene aure kuwa? menene dalilin da zai saka ki aure shi ki halaka kanki a banza a wofi? an gaya maki shi idan baya son ki zai aure ki ne?, rayuwar aure fa ba rayuwar wuni guda bace wace za'a ce ka je kawai wuni daya ne ka jure , a kan me kika yarda kika....."
"Dan Allah ki rage muryarki, kar ki yi Mah ta ji, dan wanda kike tambaya ta ko wanene nima ban san ko wanda nake tunanin bane, haukana ke sakani tunanin shi ne, saboda abubuwan da suka hada Ni da shi, kuma walahi walahi Ni dai a yanzu Ban san shi din bane wanda kike tambayata a kai ba, ina zargin haka din ne kawai, kar ki yi Mah ta ji ki!" RAUDA ta fada muryarta a raunane, tana langwabar da kai dan ta ga ATU zata zuba mata hauka, bayan ita dai ta san eh lalle abinda ke cikin zuciyarta mai karfi ne da take tunanin an wulakanta mata zuciya, ama bata san takamaiman abinda take yiwa din in shine wanda ya yi mata msg ko ba shi bane
Salima da ta yi mutuwar Zaune tana kallon su cike da rashin fahimta ce ta taso da sauri ta amshi message din ko zata gane abinda suke yiwa din?
a lokacin da ta diro ta karbi wayar ta karanta numbar dake kai, kanta ya mahaukacin daurewa zata karanta sakon da numbar ta kunsa RAUDA ta saka ihu, har tana manta cewar wai bata da lafiya ne, ta diro a haukace ta warce wayar, daidai lokacin da Salima ta budi baki ta fara magana daidai lokacin ne kuma aka turo dakin aka shigo, SALIMA kuwa na fadin" WANNAN DIN, AI NUMBAR MALIK CE, NUMBAR BAH KARAMI CE, ME YAKE FARUWA NE?"
🥹🥹🥹🥹🥹🥹🥹🙄🙄 Gandar rubutu ta kama mar'atusaliha
a zo a yiwa mar'atusaliha solidarity a ringa karbar BONANZA ta LITATAFAINA SU 22 CIF a farashi mai RAHUSA 1k, 1k 1k
93811618 ne numbana
Sarai furucinta ya sauka a kunnen Mah, sai dai ba zata iya tantance abinda yake faruwa ba a lokacin da ta shigo dakin ta gansu a tsaitsaye tamkar zakarun dake fada
A tausashe Mah ta ceX Lafiya? ko jikin na baby ne?"
RAUDA ce ta yi gaggawar ba Mah amsa cewar" Ba komai Mah, fira ne muke yi"
hakan ya sa sauran kallonta, har Mah ta idasa shigowa tana fadin" To alhamdulilah haka nake son ganninki, ku yi zaman ku wajen nan Bama zai zaunu ba, zuwa yamma za'a kai ki wajen Hajia baba in sha Allah kafin a kaiki dakin ki, Atu kina da baki ne?"
Bara'atu ta ja numfashi a hankali ta ce" Eh Mah, mahaifiyata da daidaikun mutane zasu zo ama idan sun zo din zan zo na kai su wajenki su zauna saboda nan din ba zai yiwu ba"
Mah ta karasa ta dauki abinda zata dauka ta fice
tana fita Salima ta je da gudu ta saka ky a dakin sannan ta dawo tana kallon RAUDA ta ce" Bani msg din na karanta, menene a cikin msg din? me yake damunki ne? yaya aka yi na ga numbar ta yayanmu ce? numbarsa ce, pvt numbarsa, nima na hadaceta ne saboda yawan kiran Mah da yake yi da numbar "
RAUDA ta jimke wayarta ta kai zaune saman kujera tana hankalce da su
Atu ta ja wani irin tsaki ta zauna tana dafe gaban goshinta, a kufule ta ce" ki warware min abinda yake damuna tun kafin na hargitsawa kowa tunani a gidan nan RAUDA"
RAUDA ta sake hade fuska ta ce" Ke wai me kike so na fada maki ne?, abinda kike tunanin ba haka bane, kuma Ni na bada amsa ne a cikin lalube"
Jikin Bara'atu ya karra yin sanyi, Salima kuwa ta idasa shigewa a cikin duhu, dan gaba daya ta rasa inda tunaninta zai sauka a irin wannan lokacin
Shiru Bara'atu ta yi mata, ita kuwa ta yi tsuru tsuru, wayar nan a damke a hannunta, ciwon dake zuciyarta sai ta dane shi ta hanna shi kuma fitowa domin ba zata taba yarda wani nasa ya san abin nan ba, ba zata yarda ba sam!
Salima ta jima tare da su, a dole ta sake tafiya saboda baki ne da ita sosai kuma sunna ta kiran wayarta
Tana Fita Atu ta sake tado zancen tana kallonta cikin ido ta ce" Ki dan bani haske, RAUDA me hakan yake nufi? soyaya kuke yi da shi?"
RAUDA ta girgiza kanta a hankali, sannan ta sake dago idannuwanta ta zuba mata su a raunane sosai ta ce" Kina tune da ranar da na ki zuwa makaranta safe da yama, har washe gari kila zo gida tunda sassafe kika ga ko Lafiyana?"
Atu ta daga mata kai, dan a lokacin sai da RAUDA ta yi kwana uku cif bata fita ba
RAUDA ta yi murmushi tana girgiza kanta ta ce" A ranar da na fita da wani saurayina da dare yace zamu je mu siyo abinci, da muka je siyan abincin ashe da aka zuba nawa an zuba magani...., kuma ban san yaya aka yi ba dai shi ya gani, ban sanshi ba, ban taba haduwa da shi ba ama ya biyo bayan saurayin nawa har mota sai da ya shiga ya fido shi ya tambaye shi abincin dayan na waye?, shi kuwa irin da abin garajen nan yace bai sani ba waye shi? ya sake tambayarsa a kausashe , ke dai in kare maki zance a ranar da ya ce min sai in gyara zama dan an zuba magani a abincina, Ni shi nake kallo, jin furucin nan na fito hankali tashe na so yiwa saurayin nan nawa rashin kunya shima ya so ya nuna min sakaran halin namijin dake fada da mata, Atu ban shirya ba ya daukeni cimak ya maida bayansa ya ci uwar saurayin nan, da kyar aka raba su, sannan ya rufeni da fada harda kashedin ya gane fuskata na yarda ya kuma gannina da wani dan iskan zan fada...."
Ta yi murmushi ta ci gaba da fadin" Babu wata alaƙa da ta shiga tsakaninmu ta wani alamu, tun daga ranar ban kuma ganninsa Bama sai ranar aurenki, sarai na gane shi, sai dai irin yadda yake ta hade rai da furucinsa kamar mun zo neman wani abu sai na share shi na dauke kaina, ko da muka kai ki mun hadu da shi a hanya ina dawowa, sai kuma ranar da na je restaurant na ganshi , kuma a ranar ne muka yi adaidaita daya muka yi accident. ......, a kaf maganar nan da nake yi maki maganar da ta hadani da shi bata fi sau hudu ba, na farkon nan da ya min, na biyu a cikin adaidaita da ya nemi na bari a kai shi wajen Mah, na uku fadan da ya min dan na fita da dare wajen ABDALLAH, sai ranar da yace kunshina ya yi kyau!"
Ta karashe tana dantse lebenta, Atu kuwa zuwa lokacin kirjinta har sama sama yake yi saboda yarin tashin hankalin da take gannin RAUDA ta gama sakata
Murya da gagawa ta ce" Kina nufin, da gaske MALIK din ne ko dai ba shi ba?"
RAUDA ya kalli yannayinta, kamar firar na neman rikita mata lissafi, kamar kuma wace take iya kai mata naushi, dan haka ta sake gyara zamanta tana kallonta ta ce" Shine mana, ke sunansa YUSUF ne"
"Innalilahi Wa ina ilaihi raj'une!" Atu ta fada da karfi har sai da RAUDA ta zabura ta mike tana duba bayanta domin yadda ta yin walahi ta zata wani abu ta ganni a bayanta
Rai bace Atu ta ce" Ke zauna dan ubanki! zauna nace, yanzu Ni kika yiwa wannan danyen aikin? Ni kika watsa haka? innalilahi yanzu jira kike yi bayan yaba maki kunshi da ya yi ya ce wance ina son ki? an gaya maki manyan nan haka suke? RAUDA Sarki ne fa, kuma tun kafin nadin sarautarsa mahaukacin mai kudi ne, wanda yake tafe ko a cikin abokansa cikin izarsa, ke kin ji in Alhaji na maganarsa irin yadda yake fadi? shine kike jira yace maki me bayan abinda ya nuna maki a aikace?"