Sashe 15
Azal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Litattafan marubuciyar
Duk karyar kada
Yar mahaukaciya
Bak'a ce
Bani da zabi
Daga tafia daukar soja
Neman na kaina
Kutkale
Mage
Bani da zabi
Idan ka raina inda kake
Umughuluk itifal
Duk nisan jifa
Wata kokowar
Ni zan ladabi
Dakika biyar
Da ciwo a zuciyata
Aure yakin mata
Alkalamin Kadarata
Dutse
Daga tafiya daukar soja
Makauniyace
ND now *AZAL*
Daga nesa da watsetsiyar restaurant din ta saka ya ajiyeta sannan ta shaida masa duk rintsi kar ya yi nisa zata tabo shi
A Nutse take jefa kafarta cikin takun salon tafiyarta mai tsarin gaske da ɗaukan hankali ta nufi hanyar shiga ta asalin Babar hanyar tana mamakin yau wajen babu tarin tarkacen yan mata da samari da cikar abubuwan hawa kala kala
Mai tsaron kofar ne ya dakatar da ita yana fadin" Yau Akoy baki a ciki ba'a shiga ko tare kike da ita ISHAK?"
A ranta ta ayyana ' Ku ga sakarci, ai yau ko wa ya siye wajen nan tunda na fito sai na shiga'
A bayyane kuwa sai ta yi dan murmushi tana dubansa ido cikin ido ta ce" Tare muke mana, bai ce maka zan bane?"
Gaba daya yannayin Rauda ya saka shi gaza yi mata gardama, irin sansanyan kanshin da take fitarwa da yannayin shigarta kuwa ya tabbatar masa tabas ita din kalar tafiyar manyan dake cikin wajen nan ce, dan haka ya kauce mata ba tare da ya ja ta wata maganar ba ya bata damar shiga ko tikitin shigar bata cira ba dan yau ai ba zancen ka ciri tikiti restaurant baki daya yau babu mai cin abincinsa sai wa'inda ke ciki sun tafi, dan yan oder kadai aka amshi odarsu, suma an fada masu sai fa daga bakin karfe goma sha daya zasu fara zuwa amsar abincinsu, duka kaf ma'aikatan wajen yau sun dukufa ne dan biyan buƙatar BIYA MARADI da bakonsa.
Bata ji Dar ko daya ba a zuciyarta har sai da ta shiga filin da ake cin abincin idannuwanta suka sauka saman manyan kujerun dake ajiye da asalin VIP da mutanen dake zaune, gashi su dinma hanyar shigowar suke kallo, hankalinsu a nan wajen yake sunna fira ne kadan kadan , inda muryoyi biyu suka fi tashi ta ISHAK sai ta bakon Yusuf wanda ya masa ja gabar kawo masa wasu motoci tun daga Chaina a jirgi, motocin ne da yawan gaske kuma manyan motoci ba kannanu shi yasa abokinsa wanda suke harkar motar tare kampanin kerata ya ga dole shi zai kawo motocin ya biyo su a baban jirgin da ya sauka yau din a kasar ta Nijar, to tunda ya zo bai ci abinci ba, yace babu irin abincinsu shine Yusuf din ya kawo shi nan ya ci su wuce, domin daga nan cen park dinsa zasu wuce sai kuma ya sayi tiket komawa dan ba zama ya zo yi ba shima
Bata san me yasa ba, bata taɓa tsintar tsigar jikinta da mikewa ko alamun jin tsoron shiga cikin duban mazama ba wai kwaya ukun cen da dake zaune ba sai yau, a hankali ta lumshe idannuwanta sakamakon jin Muryar wannan matar mai dauke da tufafin wajen tana fadin" Bismillah ki karaso"
A hankali ta dan hadiye yawu gannin kusan su Dukansu dake kallon wani abin da wannan mai kama da kwai dan haske wanda du jan dan Chainar nan baya ɗaukan hankali kamar nasa yannayin fatar , yana sanye da wandon da za'a iya kira 3/4 damatsunnan kaffafuwansa a wani irin cike ga gashi kwonce jikinsu luflufluf , sai riga mai ruwan baki sidik karamar riga domin ta lafe a jikinsa ta bayyanar da yannayin jikinsa irin na mai abdo, harda wata sarka a wuyansa wace tashin farko ta ayanawa ranta cewa Christa ne suka dago jin an ce da mace ta karaso, ISHAK yana tunanin ko Nafisar ce ta shigo bayan ya fada mata idan aka bata damar shigowa ta tsaya daga baya ta yi kiransa ya taso bosss na tare da bako kar ta zo inda suke ta zo? Sai dai kafin ya idasa tunanin ya samu kansa da zubawa wace ke tsaye ido itama tana masu wani kallon da zuciyarsa ta shiga dokawa da gudu gudu
Dawowar babar masu kula da bakin hannunta rike da wata kwalba da kuma wani kofi na kwalba fari kal mai dan tsayi ta ga Rauda a tsaye bata karasa ba ta samu kanta da tsayawar itama ta kalli Rauda ta juya ta kalli wajen su YUSUF ta karasa tana fadin" SIR ba bakuwarka bace wannan?"
A hankali ya dauke dubansa tun kafetan da ya yi da ido ya kalli kwalbar jus din dake hannun matar zai yi magana Ishak ya rigaye shi yana fadin" Bakuwarsa kuma?, ba Bakuwarsa bace!"
"Bakuwarsa ce" RAUDA ta fada a hankali a lokacin da ta karasa wajen kujerun da suke ta zauna a warariyar dayar dake facing dinsu tana hadiye yawun da ya kafe mata a baki dan ta samu kwarin gwuiwa "
A karro na biyu ya sake zuba mata ido, ita kuma matar gannin bai bada umarnin komai ba sai kawai ta budewa Rauda kwalbar nan da abin budewa ta ajiye mata bata cire marfin ba da kofin a daf da ita saman wani dan table din ta juya dan kawo mata takardar abinda suke sarrafawa ta zaba
Kirjinta ne ya yi wata irin bugawa sakamakon idannuwanta da suka shiga cikin nasa saboda tun dazun basarwa take ta yi danma kar ta yi ido hudu da wani ya koreta
" *A salame su, bana son takura!, mu je mana bana son shirme zaka tsaya kana magana da yarinya ka salameta idan kana salamarta bana son takura* " magangannun da ya fada a shekaran jiya Kennan tun a wajen kaiwa maza abinci da wajen hanyarta ta dawowa gida
A hankali ta ji lebenta na bushe mata Duda irin man leben da ta dan goga
Kasa kasa ta yiwa idannuwanta tana jin wani yannayi mai kama da muzantuwa ko rashin jin dadin zama a haka a kusa da su da kokarin rasa kuzarinta har kunnayenta suka jiyo mata murya a shake ta Dan Chainar nan yana fadin" Wauh, a yau na yarda da maganarka ISHAK, da kake cewa kuma a nan Akoy yan mata masu classs da iya gyaran jiki, ban taba gannin buzurwa a nan da ta yi gyara irin wannan ba, ka ga wannan wani level ne da sai macen da ta san kanta take yi, mu a cen mun saka shi cikin Layin tarbiyyar Yayanmu, koyar da su zuwa ana gyara masu jiki a saloon, ka ga hannunta da kaffafuwanta ta yi manicure da pedicure, kalli fuskarta tamkar santsin kwai, lebenta ga alamun taushi ne da su, idanun........................."
Kallon da YUSUF ke masa ya dan bashi mamaki har ya saka shi dan takaita maganarsa, dama ba wai wani zuuuuuuuuu bane yake yin maganar ba tsari, no a hankali ne yake yi sai dai duk abinda yake magana kansa ya kura masa ido ne kuma a hankali yake fadan cike da mamakin yannayin RAUDA da kuma yarda eh ashe da gaske ne a nanma Akoy yan mata masu classs haka
Shiru ya yi a zuciyarsa yana tunanin ko dai budurwar YUSUF ce?, wannan duban ba dan kawai ya yi magana a kanta bane, ama da mamaki yaushe ya fara yin budurwa daya kwal? Ko a Chaina ai YUSUF mai yanmata ne bale a nan kasarsa
Wani irin takaici ya rike mata zuciya a lokacin da aka bata dan litafin restaurant din dan ta zabi abinda zata ci, ba komai yasa ba sai gannin eh fa da gaske yau babu Sa'a a fitowar domin Wadinnan ukun ne kawai zasu zauna a nan din su isasu, sai kawai ta ba matar litafinta tana mata alamun ba zata ci komai ba ta maida dubanta kan ISHAK dake magana a hankali maimakun da dan karfi karfin da ya fara maganar dazu, yanzun kamar wanda baya so ta ji abinda ke bakinsa ya ce" Sir, na fitar da ita ne?"
Bai san dalili ba, tambaya aka masa da Yaren da ya ji bayan Yaren mahaifiyarsa Larabci, ama sai amsar ta so gagararsa har ya dan zuba masa ido na yan SAKWANI ya ki ce masa eh ko aa, ya dai dauke dubansa ya maido duban nasa kan bakonsa ya ce" Wannan motar da ka gani ita nake so a kawo ama kwaya biyu, daya Moma zata hau, dayar kuwa Baban YUSUF"
Yar dariya mutumen ya yi ya ce" Man kana ririta iyayenka fa, to ba za'a zuba su a park bane?"
Kai ya dan girgiza kasa kasa sosai yana sake dago kaifafun idannuwansa ya ɗora saman hannunta a lokacin da ta amsa waya tana sauke kafarta da ta dora kafa daya kan daya ya ce" Sai sun hau kafin wani ya hau a nan"
Kasa kasa RAUDA da zaman ya gundureta da tarin haushin mutanen wajen kansu take amsa wayar wani tsohon saurayinta wanda ta masa lakabi da 'ANDADI' , ba yaro bane, mutun ne mai shekaru sai dai kuma ba tsoho bane, a yadda ya fada mata shi Maraya ne gaba da baya, kuma wai bashi da Kani ko kanwa, mutumen maroko ne yanzu haka lambar ta kasar marokin ce ya yi kiranta da ita, ya yi ya yi ta gwada masa gidansu ta kiya har ya yi tafiyar nan a yadda ya fada mata zai je ne ya gama dukiyar iyayensa kaf ya siyar na SIYARWA na bayar da na bayarwa ya tattara ya dawo Nijar da zama ɗan yanzu maroko bata masa dadi tunda bashi da shakiki ko daya, ya jima a kasar Nijar yana dan jin Hausa da French sosai da larabci, ya nunawa RAUDA da gaske ya zo wajenta hakan ya sa ta sulube, dan ita kam bata ganta a duniyar aure ba , kuma fa zai kai uncle dinta a shekaru fa, ba zata so ta ja shi a kasa kamar yadda take jan kannanun samarinta, ama shi baya ji , ga kyauta irin mai gigitatan nan