← Book details Azal Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 117

Sashe 45

Azal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kayan ta kai ta ajiye ta koma kicin din ta zauna sai turo baki take yi,a ganninta wannan sam ba adalci bane, yaya zai fara mata magana mai mahimmanci ya wani gimtse dan daukan alhaki? Ita fa dama tunda ta ganshi ta san mutumen nan zai yi daukan alhaki, da wasu idannuwansa tamkar na Sarkin kwartaye!

A tsayen nan da yake bai koma ya zauna ba sai da ta bacewa ganninsa sannan ya zauna daf da Hajia wace ranta ke mugun bace ta kalli Mah da ta yi summar tsaye, ba dan komai ba sai dan a gaban Hajia aka fadi haka, in daga su sai su ne ai zasu waske ne su bada hakuri ita da yarta, ama a yanzun bata san me zata ce dan su kwaci kansu ba

Hajia rai bace ta ce" Dama wace kike rikon nan bata da hankali?"

Mah ta sake sada kanta, a sanyaye sosai ta ce" Ki yi hakuri Hajiya, yarinta ce"

Hajia ta dauke kai tana sauke hatatarta a saman Salima, da sauri ta bar wajen itama ta koma kicin din , Hajia ta ce" ta wuce misalin yarinta tunda ba yarinya mai shekaru uku bace , wannan din raini ne, wanda ba zan dauka ba, dan ko matansa basu isa su yi irin maganar nan da shi haka ba bale wata wai BARE!"

Mah ta sake sada kai a tausashe ta furta" A yi hakuri in sha Allah ba zata kuma ba"

Shi kuwa Hajiar ya zubawa ido, har sai da ta juyo dan ta sake tambayarsa maganar mata hudu ta ga irin kallon da yake yi mata ta dauke kanta, dan ta sani sarai saboda ta yiwa mahaifiyarsa magana da zafi zafi ne zai sauke a kanta, ita kuwa sai dai ya yi hakuri a gaskiya darajarsa ta fi karfin ta ga irin haka ta yi shiru ko daga wajen uwar tasa ne bale wata wai y'ar riko

Daga nan fa maganar ta cenza salo, domin tunda Hajia ta yi maganar nan sai ya zamo ta bata komai, ya yi mata shiru du tambayar da take masa kan abinda za'a saka masa a zanen sai yace da ita ta yi yadda ya mata ya kame bakinsa yana kallon yadda mahaifiyarsa ke kai kawo

Gannin ransa ne ya bace Hajia ta salami mai zanen nan tafe zata tabo shi a idasa daga baya

Yana tafia ta dubi YUSUF ta ce" Malik, shikenan ban isa na yiwa mahaifiyarka magana ba? Kennan Ni ba uwa bace a wajenta?"

YUSUF ya dubi Hajia da kula sosai ya ce" kin tabata idan kina mata magana a matsayin y'arki kike yi mata ko a matsayin sarakuwarki wace kike mutuntawa kike yi mata?"

Hajia ta zuba masa ta kasa cewa komai

A hankali ya shafa gashin kansa gannin Mah ta fito dauke da abin spoon a tausashe sosai gannin Mah a wajen dan kar ta dakatar da shi ya ce" Babu ruwanki da gaban wa take, babu ruwanki da me zata ji a zuciyarta, babu ruwanki da Ni tawa zuciyar ta ɗan da ta haifa, idan ta dan bata maki ko wani abu da ya shafe ta ya bata maki zaki yi mata sumul ba daga kafa ba jin nauyi ko gannin darajar ta...."
Ya dan dakata dan ya ga Mah ta tsaya tana masa kallon me kake yi haka?
Sai dai Mah ta yi hakuri a yau bashi da niyar dakatar da abinda ya fara sai ya kai aya idan ya so in Hajia ta ga zata iya zama ta yi nazari ta yiwa kanta fada ta daina toh, in ta ga ba zata iya ba tabas zai ci gaba da yi mata abinda ya fara ba fashi
A tausashensa ya ce" ko ba komai ita din nan mai girmamaki ce, tana girmamaki ne dan kin girmeta kuma kin haifa mata miji har ga ƙaruwar ɗa a tsakani, Hajia mutun ce fa, da zuciya a jikinta, koda ta hanna kanta raina ki, ko rama abinda kike yi mata a duniya a lahira kina da abin kare kanki ne?, yaya kike so ki sameni yadda kike so bayan kina hamayya da abinda na fi so a duniya? Hajia bana hada mahaifiyata da kowa, a kanta kuma ina iya dukawa ko waye dan ta ji sanyi....................., Hajia, dan Allah ki dubeni ki dagawa uwata kafa ki bata lafiya, idan ba zaki iya yin magana da ita a sanyaye ba ki kyaleta, ki bar min ita,a hakan zan fi girmamaki fiye da tunanin ki......Please......."
Ya karashe yana kamo hannayen Hajia, wace ta yi tsuru jikinta na daukan nauyi tamkar wace ta sha aiki ta gaji, ita kuwa tarin nauyin yaron ne ke lulubeta, a bayane kuma tana gannin kwarai haka din ne, mahaifinsa fa ya sha kwatanta mata, yakan ce mata Andiya bata taɓa nunawa YUSUF ya tsaneta ba, YUSUF nada muguwar shakuwa da mahaifiyarsa, ko shi yana girmamashi duk irin abinda yake masa ne dan yana gannin yadda yake kula da mahaifiyarsa, ya sha fada mata ta ringa yin hakuri ta ringa kiyaye idannuwan Yusuf idan zata yiwa mahaifiyarsa fada, yana dawowa inda take ne dan ya zame masa dole, ya sha fadin ba shi ba gidan nan, idan mahaifiyarsa ta sako kafa ne yake sakowa koda bai shirya ba

A karro na biyu kennan da RAUDA ta sake yi masa kallon tsaf, kallon da bai tafe da jin haushi har sai da Salima ta zungura kafadarta sannan suka wuce da dan sauri suka nufi dakin Mah dauke da kayan karinsu su Dukansu harda su Musulima

A dole Mah ta nufi ciki itama dan ba zata so Hajia ta kuma dago da idannuwanta ta ganta a wajen ba, dan tsaf take iya sauke mata abinda jikan ya yi mata a kanta, domin itace kuka dadin hawan Hajia, wani da jan fada wani da shan duka za'a yi a wajen nan ,shi yasa ta nufi dakin Bah ta ja kofar ta shiga tatarar dakin da gyarawa tana dantse lebe da tunanin cikin ya'yan nata biyu waye ya fi ja mata magana a yau? Dayar da ta cewa Sarkin ya rantse a gaban kakarsa ko shi dan neman da yake yiwa kakar kashedi a kanta? Allah shi kyauta

Ta dan jima a dakin tana aikinta dan har bayi ta wanke fesssss ta rufo ta kunna gawayi ta saka turaren wuta mai daɗi tana sakawa a lungu da sako na dakin ya shigo da salama hannunsa dauke da plate dauke da abincin ta da ya zubo mata

Juyowa Mah ta yi, sunna hada ido ta zabga masa harrara sannan ta dauke kanta harda kyaftu tamkar wace ke nunin da zata kama shi ne

Murmushi ya yi ya kai abincin saman dan table din dakin ya ajiye yana kallonta ya ce" Mah, zo ki ci Please"

Mah ta juyo ta kalli abincin, ta ajiye burner din ta karaso ta zauna daf da shi ta kai hannunta tana shakunar kuncinsa hadi da hancinsa ta ce" Baka jin magana, uwata sa'ar wasanka ce?"

Dan murmushi ya yi ya ki bada amsa dan da haka yanzu zata yi fushi

Mah ta bude tana kallon abincin da ya zubo ta yi yar dariya ta ce" Yaushe ne zaka fara samun ziyarar abokanan naka? Ko sai an gama ginin?"

Hannayensa ya watsa , masu yi mata alamun shi din da kansa bai sani ba, dan haka sai ta dan gyada kai itama ta shiga cin abincinta hankali kwonce

Cen ta koro da ci ta ga yana murmushi hadi da girgiza kai, da kula ta masa alamun lafiya?, sai ya sake girgiza mata kai bai ce da ita komai ba, to me zai ce? Jama'a rana tsaka Mah ta dauko ƙatuwar budurwa ta zo zata ƙaryata shi a cikin gidansu? Wannan abu da me ya yi kama? Rabonsa da ace ya tabatar da maganarsa har ya manta gaskiya, dan ko Bah in dai ya fadi abu yana yarda tunda ya san ba zai masa karya ba ai, rayuwa kennan idan baka mutu ba ka sha kallo

Sai da yama liss Mah ta sanarwa RAUDA eh da gaske an ga Bah dinta, sannan ta bata damar ta je gidansu ta sanarwa maman nasu kuma su dawo da bakonta wanda da kyar ta sanarwa Mah ya iso Nijar din kuma yace zai zo bata san yaya zata fada masa tana nan ba,

Da kula sosai Mah ta ce" Zaki tafi da ke da Salima ne, idan kun je ki yi kokarin sanarwa bakon inda kike, ki fada masa sak gidanku nan ne, kuma Ni ce mamanki, ki kula, ki kama mutuncin kanki, ko wanene shi in dai da gaske yake ya fara neman izinin ganninki wajen manyanki kafin ku ga junna a ka'idance, a yanzu na baki damar nan ne dan yadda kika kwatanta min darajar da ya baki ya sa shima na bashi darajar gannin y'ata a haka, ki sani kina da daraja wace take tafe da darajaza daga bakin lokacin da kika amsa sunnan y'ata, ki kula da mutuncinki, ki kula da mutuncinki, idan ya baki wani kyauta kar ki amsa ko menene , ki bari sai kin sanar a gida kin ji?"

RAUDA na tsaye ne Salima na ja mata zif din Abayar da ta saka, dan irin egypcien Abayar nan ne budadu masu kyau da tsari, Mah na yi mata maganar dan idan sun tafi itama zasu fita ne da su Hajia matan Bah gaba dayansu dan zuwa ganninsa a asibiti

Har ga Allah bata san ta shagala da kallon Mah ba sai da Salima ta ankarar da ita sannan ta sada dubanta ta amsa Mah din kafin ta karasa ta yi tsaye wajen turaran wutar da Mah din ta saka masu tana fadin su tabatar sun turaru sannan kar Salima ta yi tuki direba zai kai su ya dawo da su, ƙafarsa kafarsu du inda suka shiga ya bi su

Daga haka Mah ta fice , Rauda ta gama tauraruwa ta dauki mayafinta blue mai haske sosai ta yafa a kanta , hakama Salima ta rufa mayafin abayarta sannan suka fice

Tunda suka kama hanya Salima ta kula da yannayin sanyin da jikin Rauda ya yi, har ta kasa hakura wajen Danja ta yi mata tambayar abinda yake damunta
Chapter 45 · 0% Book details