Sashe 94
Azal Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da sauri dayar da suke tare wace hijab din ta masa wani irin sakawa ta duka tana kwashewa jikinta na rawa da sauri ta ringa cusawa a jakar sannan ta matse jakar, hakan ya sa YUSUF sake duban kaffafuwanta lokaci daya yana dauke kansa hadi da dantse lebensa na kasa cikin kawar da kai kirjinsa na neman yi masa zafi
Da sauri mahaifiyar Amnah ta tareta jikinta tana fadin" Amnah, meye haka, subahanallah meye haka, ki nutsu mana,, ga mijinki zaune ki nutsu mana, menene haka ne wai?"
AMNAH ta rukunkume hannayen mahaifiyarta ta fashe da wani irin ihu tana cuje dankwalin kan nata
Da Sauri mahaifiyar Tata ta sake riketa tana rufe mata baki ta dan sake risinawa tana fadin" A gafarcemu yalabai bari mu kaita ciki mu rarasheta, ta yiwu abin ne bata sani ba shi yasa ta rikice haka, ama in ba Amnah ba meye a ciki, Allah ya sanyaya Allah ya saka alkhairi"
Hannunsa mai dauke da agogo na wajen hancinsa yana kallon mahaifiyar Tata tsai cikin ido har ta gama kisisinarta ta juya da Amnar da karfi , a lokacin ne ya ga sauran biyun sun juya zasu bita
Kasa hakura ya yi a nutse ya mike ya fara nufo su , sai dai gannin RAUDA ta nufi hanyar fita ya saka shi dakatawa yana dubanta ya ce" Ina zaki je?"
Turus ta tsaya ta juyo ta dube shi, ido cikin ido kanta na sake daukan ciwo da sarawa
Da hannayenta ta ringa nuna masa sai kuma ta budi baki kamar bata da Hausa tana fadin" Mah, Mah,, Mah zan je"
Idannuwansa ya lumshe da hannunsa ya yi mata alamun ta shiga wani sashe a cikin sashen falon
kafadunta ta make ta sake juyawa da sauri sauri gudu gudu
Da sauri ya juyo ya bar niyar abinda ya yi ya damkota ya cirata sama, hakan ya sa ta kwala ihu ta shiga kokarin kwace kanta ido rufe tana fadin" Kai, wayo Allahna ku taimakeni, wayo ka saukeni ka saukeni in tafiyata, wayo yau yan masalaci kuma sun haukace ko menene? innalilahi Mah, Mah....."
Tana zunduma masa ne yana tafe da ita har ya karasa wajen gadon nan ya dire ta
gannin zata kuma tashi ya saka shi saka hannu guda ya mayar da ita ya zarro idannuwansa yana kallonta ya ce" Idan kika tashi ba tare da nace ki tashi ba sai na baki mamaki yau!"
A rikice ta yi tsugune tana kallonsa hawayenta na zuba, shi kuwa ya karasa wajen wayar dake jone ya ciro ya saka numbobi ya dana kira
jim kaɗan aka daga, a tausashe aka ce" Yanzu ka ga damar kirana ko? ai tun dazu Ni nake kiranka ka ki dagawa, na zata ba zaka nemeni ba isashe!"
Kai ya sada yana dan murza goshinsa, a hankali ya furta" Me yake faruwa ne Bah?"
Bah ya tabe baki yana cikin ba dama , dan kuwa jama'a sai Allah sanya alkhairi ake yi, ya ce" Ka gane cikin haya haya nake, an kuma tabbatar an isa da kai ne an daura maka aure da Baby, ka kashe kawai idan na ga dama ma idasa tattaunawa "
Daga haka Bah ya katse kiran ya ci gaba da shagaalinsa
Tsai ya yi da wayar a hannunsa, a hankali ya juyo ya zuba mata ido, sai mutsu mutsutu take yi a saman gadon a tsugune da takalmin ta abinta
Ajiyar zuciya ya sauke bayananiya sannan ya saka numbar Taj ya danna kira
yana dagawa a hankali ya ce" Cikin bakin iyayen nan na Amnah akoy namiji, mai sanye da farin hijabin nan, idan sun fita ka bi su a boye bakin inda suka rabu da shi ka sake binsa a boye, ina son duk wani informe a kansa, kafin ka dauko min shi ka kai shi baya ka rufe............."
Hankali tashe Taj ya amsa yana tunanin abinda zai je ya dawo, innalilahi Wa inna ilaihi raj'une namiji? yau sun shiga uku, Allah ya takaita fushin sir dan walahi sai ya wujijiga masu kwonciyar hankali, innalilahi duk irin yadda suke takatsantsan ashe akoy wanda ya fi su? koda yake tare suka zo da Amnar suka shige kowane da hijab da wahala su iya ganewa Kai Amnar nan walahi sai ya ji ya karra tsanarta, shi baya son mace marar kamun kai a rayuwa, yau kuwa zai ci ubansa namijin nan,dan walahi kafin ya rufe shi sai ya masa salatu ta biyu, ta yiwu bai yanku da kyau bane ya sa yake iskanci!
Yana datse kiran nan ya dubeta da dan karfi ya ce" Ke wai meye kike wannan abin?"
A rikice RAUDA tana sake matse cinyarta cike da nauyin maganar ta ce" Fififitsari ne nake ji tun a gidan Atu wowowwollah yi zan a nan"
Ido ya dan zarro yana kallon a inda tace zata yin
Da dan sauri ya karaso yana girgiza kai yanuna mata kasa yace" A'a gaskiya sauko sauko je bayi ki yi"
Ya fada yana dubanta
Saukowa ta yi tana dubansa sai kuma ta wuce da sauri tana jin kamar zuciyarta zata fito daga kirjinta ta wuce bayin
tana rufewa ya dago idannuwansa a hankali ya kai zaune saman gadon yana dan sake bude idannuwansa a hankali ya furta" What?, Really? Yah Rab"
Yana rufe bakinsa ta fito sai sake baza hijab din take ya ja ta tsaya a gabansa ta ce" Tafia zan yi wajen mamana!"
Shima ya dago ya zuba mata ido wata yar diris abinta sai tarin rashin kunya
Ya tabe baki ya ce" Ba inda zaki je, ki bari mutane su ragu mu je nima na ji abinda ake nufi da min auren dole a Yau!"
Ido da baki ta saki tana kallonsa, dan yadda ya yi maganar da harde hannayensa sai ta ji eh walahi kamar dai da gasken auren dole aka yi masa
Baki ta tabe ta dafe kugu da yannayin tashen fitsara ta ce" Eh kam, nima abinda zai kaini kennan, dan kuwa in dai auren aka yi niyar min a kaini wajen da ya dace, ba wai gidan da matar gidan take mahaukaciya ba!"
Ido ya kausasa yana kallonta da gaya ya nunota da yatsarsa guda ya ce" Kin ga, kar ki zagar min matata, kar ki saki ki zagar min matata!"
RAUDA wani irin bakin ciki da daci ya tsaye mata a zuciya tana kallonsa ta ce" Ita din banza ita din wofi, bi bata isheni kallo ba Allah la kuwa, kuma sai na zane ta duk inda na hadu da ita, ita nan har ta iya raini ko? zan gwada mata na fita iyawa, banza mai kan munafukai da ita algunguma yar daudun banza da wofi, Ni da ita Allah ya isanama walahi!...." ta karashe tana fashewa da kuka ta nufi darduma ta kabarta sallah tana hawayenta, shi kuwa ya zuba mata ido a ransa yana ayana' Ka shiga uku YUSUF, ka dai ganta nan ko tanada hankalima ko babu? Allah masani, gatanan dai ita kadai ma sai ta shiga fada, kai kuma haka taka kadarar ta kaika ko? Allah kennan, ko sallar ta meye take yi? ko la'asar ce bata yi ba?'
Gaba daya tarin fushin da yake ciki na dazu nema ya yi ya rasa, sai wasu abubuwa da suka same shi suka tsaya masa a rai, ya zuba mata ido kawai yana kallo a zaunen nan
"AMNAH!, baki da hankali ne? ki nutsu nace maki yar iskar banza da wofi kai!"Mahaifiyarta ke fada da karfi, bayan sun hadu sun ririketa ta kubce masu ta ringa watso kwalaben turarukan wuta da na ruwan dake jere masu tarin kudi, ta gama ta ringa fasa kayan saman sif duk abinda ta hadu da shi sai ya rotsa tana ihu tamkar sabuwar kamu
A haukace tana ihu da kuka ta ce" Aure?, mijin nawa aka yiwa aure? Kishiya aka min ko tarewa ban yi ba da mijina?,Ni Amnah aka yiwa kishiya? kishiyar ma wannan yar matsiyatan da suka mutu basu da ko tufafin kansu masu kyau?, Lalle nice ajalin yarinyar nan, kuma ko uban waye ya aurawa mijina wata sai na zame masa balaki da masifa a duniya, walahi sai na zame masa Azal din da zai gwamaci mutuwa da rayuwa, wayo Allahna sun kashe Ni sun kashe min kuruciyata!......."
ita ihu ta iya yi, Bata san mahaifiyarta ta fi ta Shiga mummunan yannayi sakamakon wannan abin da suka tardo
Basu taba hasashen ko nan da shekara goma an nemi yiwa Amnah wannan cin zarafin ba domin sun yarda da isar y'arsu dari bisa dari....shin me Amnah ta rasa? in me ake so idan aka zo kanta za'a samu, yanzu ace ita ce aka yiwa y'arta kishiya? y'ar da ta kawo shekaran jiyan nan? y'ar da ko fuskar mijin bata gani ba? yau ko ita uwar wane kakar wane ta fi karfin kishiya bale Amnah sabon jini?, Amnah yarinyar da samari suka ringa wawa ama suka ki basu dan sai ta zaba ta darje, gashi yau sun shigo da abinda suka yi niyar fara binewa a yau din sai gashi ya shigo gidan a lokacin da basu shiryawa ganninsa ba?, sunna cikin kokarin ganin ya shige nasa dakin wannan abin ya faru? da ace Amnah zata yi shiru ta bincika zuciyar mahaifiyarta da sai ta tsorata da abinda zata gani wanda ya dame nata ya shanye
"Hajia ya dace a tausashi Hajiar Tsatsunburum, ta kwontar da hankalinta auren nan a yau in ya kwana shege nake ba dan halal ba, meye na daga hankali mu da muke da masu bugun kasa a hannayenmu, sunne karyar mu, sunne gatan mu, dan Allah ta yi hakuri kar ta yiwa kanta rauni mu tsaya jinya mu kasa magance matsalar nan" Dan daudun ya fada yana sake riƙe hijabinsa a jikinsa da kyau dan gudun kar a shigo a ganshi ba hijabin, ama a dazu ya tsorata fiye da tunanin bawa, kai, bai taba Sannin ana rawar haba ba sai dazu da ta zubar da abubuwan nan, yau da an kama da ina zasu saka kansu? shegen Tsatsunburum ya fi shegen kowani gari iya iskanci, ya tabata a dame an dame shi, shima shegen kwadayinsa ne da sai ya kai ya baro shi!