← Book details Dattijon Arziki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 96 OF 118

Sashe 96

Dattijon Arziki Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Rahma ta gyara zamanta tana kallon Abie2 ta ce“Wh Abie2 Meerah dai.â€
'Dan murmushi yay ya ce“A'a wlh 'diyar albarka, ba mgnarta zan miki ba, tinda bansan me zance miki ba.
Zanyi miki mgna ne akan keda mijinki ne, kinga dai Masha Allah 'yar gata kike gaba da baya, suna sonki duk farin cikinki suke so, abunda suke miki ko mahaifiyarki da mahaifinki suna da rai iya abinda zasu miki kenan.
Ni amtsayina na babanki yayar mahaifiyarki, ki 'daukeni tamkar nine Ummu Aymana, ina son don Allah ki zauna da Abdul Majid lafiya, ki masa biyayya iya biyayya ki kula da shi kamar yadda ya kula dake ki kiyaye duk abinda baya so, ki kasance me tsananin biyayya agare shi ki kyautata masa kamar yadda ya kyautata miki, duk abinda ya kasance yana sonsa don Allah ki tirsasawa zuciyarki son abin domin ki masa shi, matuqar bai sa'bawa addini ba, Abdul Majid dalilinki ya rasa abubuwa masu mahimmanci arayuwarsa, 'dansa ubansa da dai sauransu, wallahi bazan kaffara ba sonda 'dan uwanki mijinki yake miki yafi wanda iyayanki da ni nake miki zai iya rasa dukkan abinda ya mallaka harma da rayuwarsa akanki, shin wannan mutumin 'diyar albarka kinada kamarsa ne?â€
Kai Rahma ta 'daga cikin sanyin jiki, idanunta na tara ruwa, ta ce“Babu Abie2 kuma insha Allahu zan kiyaye dukkan abinda ka lissafomin, zan kasance mai basa kulawa da dukkan iyawata.â€
Abie2 ya ce yauwa Ngd Allah ya miki albarka, Abdul Majid nason kulawaki da tattalinki, gare shi bai ta'ba jin da'sin aureba da kwanciyar hankali sbd sonki kawai ya Sani acikin zuciyarsa, ki zama mai hkr da juriyar zama da shi na har Abadan duk da nasan zo mu zauna zo mu sa'bane watarana dole a samu matsala tsakanin ma'aurata toh da hakan ta faru karki yarda kiyi fushi da shi ki cije ki daure kici gaba da kulawa da mijin ki idan ta Kama ki basa hkr ki basa, dole zan fa'da miki gaskiya sbd nine matsayin mahaifiyarki da kike gani ayanzu.â€
Rahma ta jinjina kanta ta ce.
“Nagode Abienah insha Allah zan kiya.
Ta kamo hannunsa tana fuskantarsa ta ce“Dan Allah Meerah bata ta'ba burgeka ba?â€
Abie2 ya ce“Ikon Allah! Babyn Abie yau kuma da wace irin mgna kika zo?â€
Rahma tai murmushi ta ce“Ni wlh sonake ka aureta tanada hankalina nasan bazata qika ba don Allah idan ka amince zuwa dare zan mata mgnar.â€
Abie2 shi kunya ma Rahma ta basa ya kasa mgna.
Dariya tai ta ce“Abie2 shiru ma mgna ce bari kaga naje muyi mgna da Meerah nasan bazata qiyaba, sai muyi mgna da Abie.â€
Ta 'karashe mgnar cikin murna tana miqewa, ta fice harda gudunta tana tsalle.
Abie2 kai ya girgiza yana murmushi.

Rahma tana shirin Kama handle 'din 'kofar falonsu Abie na bu'dewa waya manne kunnensa, yana mgna yana sakin murmushi, ya sake sabon shiri wani hatsabibin yadi ne blue ajikinsa sai baza 'kamshi yake.
Rahma ta tsareshi da idanu, ganin naso wuceta ba tare da ya mata mgna ba.
Hannunsa ta riqo, ta shiga gabansa kamar zata shige jkinsa, ta marerece fuska, tana kallonsa kyawun da ya mata yasa ta manta da 'yar kunya take da shi.
Asangarce ta kirasa.
“Abienah!â€
Ajiyar zuciya Abie ya sauke, yana damqe hannunsa cikin nata me 'dauke da safa yana murzawa ayanzu Babyn nasa baya son abinda ya rabasa da ita nan da can.
“Hello pls Nasir zan kiraka.â€
Ya katse wayar yana zurata cikin aljihun wandonsa ya amsawa da.
“Na'am My Baby menene um?â€
Kasa jurewa kallonsa tai ta sadda kanta 'kasa tana wasa da zoben yatsarsa, cikin sanyin murya ta ce“Uhmm! Abienah karkayi fushi dani pls kaji? Idan laifi na maka ka yafemin.â€
Jikinsa ya shigar da ita yana 'dago kanta ya janye niqab 'din fuskarta ya sumbaci kumatunta ya lashi 'kananun la'bbanta, ya ce“I love you my baby oya shiga ciki sai na dawo, zan siyo miki abun da'di.â€
Kallonsa tai ta ce“Abienah idan ka dawo zanzo muyi mgna akan Abie2 kuma Nima ina son....â€
Sai ta kasa qarasawa cewar tana sonsa ta shige cikin falon da gudunta cike da kunya.
Murmushi yay yana shafa sajansa yana binta da kallo mai cike da tsantsar 'kaunarta.
Kai ya girgiza ya rufe 'kofar yasa kai yay tafiyarsa.

A falon daga Jaddatu sa Ummiterh da twins d'inta suna fira.
Akunya ta zauna kusan Jaddatu, sai take ganin kamar duk abinda sukayi da Abienta angansu, duk da kuwa nisan 'kofar falon zuwa cikin ga corridor amman sai ta tsargu, sbd 'kamshi Abie da yake tashi ajikinta.
Ummiterh ta ce “ y'ar gidan Abie an dawo?â€
Rahma ta kalleta ta ce“Eh ina Meerah ko tana samane?â€
Jaddatu ta matso ta rungume Rahma ta ce“Ni kam wai me kike nufi dani?â€
Rahma ta sunne kanta jikin Jaddatu, ta ce“Kai Jaddatu wlh ba kome fa! Bari na hau sama zanyi mgna da Meerah.â€
Twins suka ce“Auntie Rahma Abie zai kawomana chocolates da biscuits. â€
Rahma tai murmushi ta shafi Kansu ta ce“Ok nima bari na dubo acan sama zan kawo muku.â€
Ta fa'da tana meqewa, ta tafi su kuma sai murna suke, suka koma suka zauna kallon Tv tashar MBC 3.

Rahma tana hawa sama kallon 'kofar 'dakin Abie tai ta girgiza kanta tai gaba.
Tana hayewa sashensu 'dakin Meerah ta bu'de tana sallama.
Shiru ba kowa nata ta shiga a falo ta ga Meerah na gyaran falon da goge².
Rahma ta ce“Ashe kina nan? Toh zo zauna muyi mgna.â€
Meerah ta ce“Eh ina nan ina miki duk da kinyi hijira.â€
Rahma kai ta girgiza tana murmushi.
Meerah ta zauna 'kasa dab da 'kafarta.
Rahma ta Kama hannunta ta ce“Haba! Miqe don Allah wlh bana son ganin wanda ya girmemin yana min irin haka.â€
Kusa da ita ta zaunar da Meerah tace.
“Toh Meerah shawarace nazo miyi amman ba dole sai idan zuciyarki ta kwanta da lamarin.
Kinga yanzu aqalla shekarunki zasu kai 27 koda 28 shiyasa tin a Espagne naso kije gida kema ki samu ki aura kikace A'a kina tare dani, har Allah ya baki miji.â€
Meerah ta yi murmushi ta ce“Bakiyi 'karya ba Rahma shekaruna 28 aduniya, wlh ina son aure Allah baiyi baâ€
Rahma ta kamo hannunta ta ce“Kina son Abie2 da aure? Don Allah karki ji kunyata ki fa'di min gaskiya?â€
Meerah kanta ta sadda tana wasa d yatsun hannunta, ta jinjina kanta ta ce“Wlh madam bazan ta'ba 'kin jininki ba, duk abinda yake tare dake bazan 'kisa ba Rahma.â€
Murmushi Rahma tai cikin farin ciki ta rungume Meerah ta ce“Ngd ngd ngd Allah ya tabbatar da alkhairi.â€
Meerah ta ce“Ameen nima ngd da kika za'beni na zama d'aya daga cikin zuri'arku.â€
Rahma ta miqe cikin farin ciki ta sauko ta koma wajan Abie2 ta zayyane masa duk yadda sukayi da Meerah.
Abie2 haka kawai ya tsinci kansa cikin farin ciki amman kunyar 'yarsa tasa ya yi shiru baice komai ba...

*Niger*
Ibtisam ta Sha bacci sosai, kafin ta farka cikin ikon Allah ba zazzab'in.
Kunyar maimou ya saka taqi miqewa ta yi tafiya, cikin sa'a Maimou ta fita ta koma falo ta miqe ta shiga toilet dakyar tana cije baki, ruwan zafi ta 'Kara shiga kamar yadda Karime ta gayamata.
Tana fitowa daga wanka yana shigowa 'dakin.
Jikinta ya fara rawa tana zaro idanu.
Kamota yay yana murmushi ya ce “mon cÅ“ur nutsu ba abinda zan miki, kinyi sallah?â€
Kai ta girgiza cike da tsoronsa.
Jikinta ya goge mata ya shafa mata mai, ta sanya kaya doguwar rigar atamfa ta mata kyau, ya Kama hannunta ya ce.
“Kiyi sallah sai muje kici abinci kisha magani.â€
Kallonsa kawai take cike da mugun tsoronsa hawaye ya wanke mata fuska ta ce“Wlh bazan iya sallah atsaye ba.â€
Bakinta ya sumbata ya ce“Ok kiyi azaunen.â€
Saman darduma ta hau ta zauna ta tayar da sallar.
Falon ya foto Maimou na zaune.
Kallonta yay ya ce“Ke! 'Dauko plates ki zuzzuba mana abinci idan kinci sai ki tafi gida ke zakiya mana na dare, ma kai kaji ana gyara.â€
Maimou ta miqe tana fa'din.
“Lah! Ya Ja'afar ai da ka kawo na dafa.â€
Hararenta yay ta fita kitchen.
Ja'afar ya dawo 'dakin ya zauna saman katifa yana jiran Ibtisam ta gama sallah.
Chapter 96 · 0% Book details