← Book details Dattijon Arziki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 118

Sashe 58

Dattijon Arziki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Meerah da take fitowa daga kitchen idanunta suka sauka akan Rahma ta zube 'kasa.
Aguje ta nufi wajanta tana salati, ha'di da kiran sunanta.
Gabanta ta zube tana 'dagota tana girgizata ha'di da kiran sunanta.
“Rahma me ya sameki? Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!â€
Duk ta ru'de ta rasa ya zatayi da Rahma.
Idanunta ya sauka akan Tv ganin irin labarin da ake, lokacin ana sanarwa jirgin da ya taso daga Australia zuwa Singapore ya fa'di, sai jirgin Turkey wanda zaije Istanbul shima ya fa'di.
Agigice Meerah wacce sam bata fahimci garin da akace ba tsabar ru'du jin ance ya taso daga Australia, ta 'kwalla ihu mai firgitarwa wanda ya haddasa me gadi da securities Rahma suka nufo hanyar falon aguje hannunsu riqe da bindigogi.
Ki shin 'kofar suke kamar zasu 'ballata.
Meerah ta kwantar da Rahma ta nufi 'kofar aguje ta bu'de.
Aguje suka shigo suna tambayarta menene?
Agigice take nuna musu Rahma da Tv tana fa'din.
“Ya mutu itama ta mutu.â€
Wajan Rahma suka nufa, tana kwance kamar gawa.
Me gadi ya ce“Ki kawo ruwa da sauri.â€
Robar ruwan da take ajiye saman center table ta 'dauko ta 'balle murfin ta zubama Rahma tana kuka.
Bata motsa ko gezau babu alamar zata farfa'do.
Securitien ta me suna Adeel yay saurin sunkuyawa ya cicci'beta ya ce“muje hospital karta rasa ranta.â€
Meerah haka ta bisu aguje ba ko 'dan kwali akanta.
Rungume take da Rahma abayan motar tana kuka har suka isa ha'dadd'iyar privet hospital dan a'kasar ma sai wane da wane yake zuwanta.
Cikin gaggawa aka amsheta aka shiga emergency da ita.
Temakon gaggawa suka shiga bata domin su samu numfashinta ya dawo.
Meerah ta kira Anee ta gayama tana kuka ba'a rufe 30 minutes ba sai ga Anee itama kuka take suna leqen Rahma ta 'kofar glass anata fama akanta har yanzu bata farfa'do ba.
Securities hankalinsu ya yi mugun tashi jin jirginsu Abie ya yi hatsari.
Misalin 9 na dare jirginsu Abie ya diro 'kasar Espagne.
Haka kawai yakeji fa'duwar gaba sam baya jin da'din zuciyarsa.
Shigar larabawa ce tsaf ajikinsa tamkar balaraben saudiya, kallo 'daya zakawa kayan jikinsa kasa na manyan ku'dine tin daga takalmin 'kafarsa har zuwa agogon gold da yake 'daure atsintsiyar hannunsa.
Farin glass ne manne akan fuskar shi.
Cikin nutsuwa yake sauko daga cikin jirgin, yana 'ko'karin canza layi.
Rahma ya kira tanata ringing ba'a 'daga sakammakon sun baro wayan agida.
Direban Rahma ya kira bugu 'daya ya 'daga cike da mamaki, nan ya sheda masa sun iso lfy azo 'daukarsa.
Nan ya shedama Adeel suka tafi 'daukansa cikin fa'duwar gaba, basu San irin tashin hankalin da Abie zai shiga ba jin 'yarsa hospital har yanzu bata farfa'do ba.
Daga airport kai tsaye hospital suka nufa.
Abie ya ce.
“He! Ina zamuje ne?â€
Adeel ne mai 'karfin halin cewa.
“Yalla'bai kayi hkr...â€
Ya basa labarin komai.
Wani irin juyawa kan Abie yake yana kira sunan Allah, hankalinsa amugun tashe.
Suna zuwa Abie ya nemi abarsa ya ganta, amman har lokacin ba damar ganinta, haka ya dinga kai kome ya rasa me yake masa da'di.
Misalin 10 na dare Rahma ta farfa'do tana wani irin fizge² da ihu tana kiran Abie.
Likitocin tsaye kanta, allura suka mata nan take bacci ya 'dauketa.
Doctor yana fitowa Abie ya taresa da rawar jiki yana tambayarsa.
Zofa ya goge, da harshen turanci ya ce“Muje officeâ€
Zaune suke Abie na fuskantar Dr.
“Yalla'bai zuciyar yarinyar nan tayi mugun bugawa sakammakon razana da abinda taji ko ta gani ya gigitata, har ya hasasa mata suma wanda ta kwashi sama da 4 hours kafin mu samu ta farfa'do, dan haka akiyaye 'bata mata rai, yanzu tana bacci da zaran ta tashi zata farka normal, ga magugun da za'a siyi ta sha su tsawon sati gudu insha Allah komai zaiyi normal. â€
Baki 'daya Abie baida wata nutsuwa bare kwanciyar hankali, tinda yaga Rahma kwace agadon asibiti, sai ga shi yanzu ana mgnar zuciyarta ta buga duk sakammakon taji jirgi ya yi hatsari tin bata tsaya taji wanda zaije wata qasa bane ba.
Numfashi ya sauke ya ce.
“Ok Dr ngd bari zan siyo magugunan yanzu, sai akaini wajanta.â€
Fita yay, sukayi mgna da Adeel, ya fita ba jimawa ya dawo da magugunan masu masifar tsada.
Doctor ya nunama Abie yadda zata sha sannan ya ce da ta tashi ayi qoqarin bata koda tea ne amman abari ya huce karta Sha da zafi sosai.
Abie ya tura direba da Meerah gida ta 'daukoma Rahma kaya Kala biyu ta tawo da kayan tea da komai harda girgin da Rahma ta shiryawa Abie.
Zaune suke sun sakata gaba bacci kawai take Abie na riqe da hannunta wanda baida drip, yana aikin murzawa yana shafa fuskarta.
Kallon Meerah da Anee yay ya ce.
“Dare ya yi kuje gida ku kwanta Ku huta, Anee a fara ajiyeki sai su Meerah su isa gida OK?â€
Tana share hawaye ta ce.
“Toh Abie Allah ya bata lafiya, gobe zan shigo daga makaranta.â€
“Ameenâ€
ya amsa suka tafi.
Dr ya sake leqowa ya dubata ya fice Abie ya rufe qofar ya shiga toilet ya 'dauro alwala ya fito ya gabatar da sallolin da ake binsa.
Koda ya idar nafila ya shiga, wadda sai 2 na dare ya miqe bayan ya yi doguwar addu'a Allah ya ba Rahma lfy.
Bakin gadon ya zauna ya rankwafo yana kallon kyakkyawar fuskarta.
Drip yaga sauran qiris ya qare ya cireta ya matsar da ita ka'dan ya haye gadon ya shigar da ita jikinsa sosai ya lullu'besu da tattausan bargo wanda Meerah ta kawo.
Wata irin ajiyar zuciya yaji Rahma ta sauke tana qara shigewa jikinsa ta tura fuskarta 'kasan wuyansa tana sauke numfashi anutsu irin baccin yana mata da'di.
Zagayeta ya yi da hannayensa yana buga bayanta ya manna mata kiss agoshi ya qura mata idanu yana jin mugun tausayinta.
Ahankali ya furta“Babyna da kin mutu ina tunanin ba lallai na jimaba zan biki, baki tsaya kinji da kyau ba Abienki kawai kike tunani har kunnuwanki suka jiyo miki jirgin da zaizo Espagne ne.â€
Kanta ya shafa ya tallabo fuskarta ya kirata cikin ra'da.
“Baby ummina!â€
Ina alluran da aka mata, sosai take aiki bacci take ta qamqameshi.
Tofeta yay da addu'ar bacci ya kulle idanunsa ba jimawa bacci ya sace shi.

A can kuwa 'kasar Tchad.
Jirginsu Ibtisam misalin 8 na dare ya sauka, Yahaya direba da Abie 2 and Mal Adamu sukazo tarbansu.
Ibtisam sosai gidan ya burgeta dan yafi ma na Australia tsaruwa da kyau.
Bayan sunyi wanka sunci abinci Tanko ya nemi izinin suje gaishe da Jaddatu, Abie ya musu jagora har falon.
Jaddatu ana zaune ana jan casbi suka shigo, da sallama.
Ibtisam da manyan hotunan Abie da Rahma ta fara cin Karo akowane kusurwar bango wasu suna tare rungume da juna wasun kowa daban sai Jaddatu da wani kyakkyawan tsoho balarabe sai wani guda sun kusa su goma suna cikin anushuwa.
Ibtisam tsirawa hoton Abie da Rahma ido tai, yadda suke 'kam'kame da jina suna dariya.
Tsaki taja 'kasan le'be duk da kuwa taga tsantsar kamarsu da Rahma, baki ta murgu'da ta janye idanunta daga kallonsu.
A'kasa suka zube suna gaisheta.
Jaddatu cikin sakin fuska ta amsa tana kallon Ja'afar da yake yanzu ya iya larabci ta ce.
“Barka da arziqi Ja'afar, Ibtisam ya jikin? Allah ya 'Kara sauqi na tayaki murna amman don Allah ki kiyaye ko gaba karki sake yinqurin guduwa sbd za'a miki auren dole, idan kin tsayawa kin gayawa Allah tabbas zai miki maganin komai.â€
Ja'afar ne ya fassarama Ibtisam tinda dukkansu bayan Abie 2 da Ja'afar Tanko da Adamu and laraba da ibtisma ba mai jin larabacin.
Ibtisam tai 'kasa da kanta cikin ladabi ta ce“Ngd ummi Allah ya saka da alkhairi.â€
Laraba ma godiya tai jin yadda Jaddatun take fa'dawa 'yarta gaskiya.
Hanan ta ce“Ya Abdul sai ya wuce wajan 'Yar lelensa ko? Amman ya ce gobe zai zo.â€
Abie2 ya girgiza kansa ya ce“Da wuya har mugani.â€
Dariya sukayi.
Latifa ta ajiye musu lemo da ruwa kayan motsa baki anata hira abin gwanin ban sha'awa hira Ja'afar ne me fassarawa.
Rayyana ce ta sauko ganin harda Ja'afar ta zube tana neman gafarasa.
“Wlh ba komai na yafe miki Allah ya yafemu baki 'daya.â€
Da “Ameen suka amsa, sun jima sosai kafin su miqe Jaddatu ta ce“Ja'afar Ibtisam da mamarta ga bedroom can hanyar kitchen su zauna kafin Abdul 'din yazo su wuce.â€
Ja'afar yay godiya ya fa'dawa Laraba sukayi godiya nan aka ha'dasu da Latifa kasancewad tana jin hausa ita ta kaisu har'dakin da zasu zauna.

Ja'afar bayan sun koma 'bangaran Abie2 yamusu sallama yace zaije gidan Baba Tsalha ya kwana wajansu Harisu ya yi kewarsu sosai.
Fatan alkhairi suka masa ya tafi.
Ibtisam ta baje saman bed tana qarewa 'dakin kallo tana jinjinawa wai nan wajan saukar baqine toh ina wa 'yan gidan gaskiya masu ku'di na morewa inji Ibtisam.
Fuskar Abie take mata gezu sai tsaki take ja taji haushin ganinsa da balarabar yarinyar nan.
Laraba ta ce“Ibtisam dan Allah ki ajiye hankalin ki,kinji?â€
Kai Ibtisam da 'daga sbd tasan duk abinda zatayi dan sugane bazasu ganeba gwara ta barma zuciyarta.

Baba Tsalha ganin Ja'afar awannan daren ba qaramin farin ciki yay ba, kamar ya goyasa yana tayasa murnar samun lafiyar Ibtisam.
Yahuza ya ce“Wai Ja'afar kaga yadda ka zama kwana ukune ko nawa har ka canza baqar fatarka tana sheqi.â€
Harisu ya kauma Ja'afar duka ya ce“Ba dole ba 'kasar waja ai akwai da'di ga Hutu ga amarya agefe.â€
Ja'afar bai ce musu uffan ba bayan murmushi haka suka kwanta awannan dare cike murnar ganin Ja'afar.
Chapter 58 · 0% Book details