← Book details Dattijon Arziki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 118

Sashe 61

Dattijon Arziki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Can kuwa gidan bikin daman da rana za'a saka ankon atamfa Aishatu Ashe ta manta tata da lace kawai ta zo, ta Kira Ma'aruf ta ce ya biyo mata da anko 'dinta taji bai 'daga kiran ba, har Kira goma, sai kawai ta kira Rabi'ah sbd ta ce mata tana hanya dan ta ce ta biya ta kawo mata itama shiru, dole ta kira Nura direba yazo kai uwani ta kawoma lokacin da yazo Uwani an aikesu kasuwa kawai sai ta fito har yayarta Munnira na cewa.
“Aishatu nasan halinki da shiririta kije ki biyema Ma'aruf kiqi dawowa da wuri.â€
Dariya tai ta ce“Wlh baya gida tinda na kira bai 'daga ba, haba Aunty yanzu zan dawo bikin Mimi ina naga damar wuni agidana Tabb wlh ban 30 minutes zan dawo kinga ya hanani tuqi ya ce sai na haihu, idan su Rabi'ah sun iso don Allah su zauna sai na dawo.â€
Ta fice tana dariya.
Bayan motar ta shiga suka nufi gidan.
“Nura Ma'aruf ya fitane? Ina kiransa baya 'dagawa.â€
Nura direba ya ce“A'a Hajiya yana gida naga motarsa ajiye.â€
“Ok nasan wani aikin yake.â€

*Chad*
Rayyana zaune saman kujaran bedroom 'dinta ta yi tagumi, rayuwa sam bata mata da'di, an kasa fahimtar irin nadamar da tayi.
Number Abie ta 'kurawa idanu ta danna kira.
Cikin ikon Allah bugu 3 ya 'daga tare da sallama.
Rayyana ta amsa tana gaishesa da tambayarsa jikin Rahma ta 'dora da cewa. “Yanzu ne naji su Ummi na mgnar ance tana hospital, Allah ya bata lfy.â€
Abie da yake miqewa dan zuwa hospital ya amsa da “Ameen Amin Ngd Rayyana ya jikin naki?â€
Cikin murna ta amsa “Da sauqi har yanzu tana hospital 'din?â€
Abie ya amsa da “Eh amman nasan za'a sakemu yau insha Allah. â€
Addu'a taimasa na fatan samun lafiya ya amsa sukayi sallama.
Idanunta kan wayar ta danna kiran Auntie Saro.
Har ta gama ringing bata 'daga ba, sai da ta sake kiranta ta 'daga.
Dakyar take amsa gaisuwarta.
Rayyana ta ce“Auntie Saro! Dan Allah ki sassautamin wajanki nake ganin zan samu sauqi amman kema ga shi kina shareni wlh nayi nadama, ni yanzu ki ban shawara ya zanyi Abdulmajid ya sauko ya zauna dani wlh ina sonsa.â€
Auntie Saro daga can taja ajiyar zuciya ta ce“Ga irin ranan da nake jiye miki nan ta zo, babu irin nasiha da ban miki ba akan ki ajiye hankainki ki zauna da mijinki kiyi hkr jarabawar da zai miki ta lokaci qalilance, ki kawar da kanki akan 'diyarsa amman fafur kika qi kika biyema Wahida ita gatacan tana aurenta lafiya lau ke zata kaso miki naki, humm! Kiyi addu'a ba abinda ya gagari Allah amman kin tafka kuskuren ba lallai bawan Allah'n ya zauna dake ba!â€
Rayyana kuka ta saki tana sambatu dakyar Saro ta lallasheta tana kwantar mata da hankali,has taji nutsuwa ka'dan.

'Bangaran Ja'afar kuwa cikin murna da farin ciki suka tafi gidan Ma'aruf dasu Yahuza ya amso motar takardunta da kome suna cikinta, ya kira baba Tsalha suka sanya masa albarka.

Ibtisam zaune ita da Binta da Falmata baba Tsalha ya shigo yana washe baki, ya ce“Kuje Ku sanyawa Ja'afar albarka me gidansa ya masa kyautar mota.â€
Ibtisam baki ta ta'be a'boye tana kauda kanta.
Binta ta Kama hannunta suka fito.
Ja'afar da kallo ya bita ganin tana hararensa.
Kicin² yay da fuska ya dawo Ja'afar 'dinsa sak ya ce“Wuce muje na kaiki gida lokacin shan magani ya yi.â€
Ganin yanayinsa ya saka ta Sha jinin jikinta, tai 'kasa da kanta.
Falmata sabulu da turaren wuta ta ba Ibtisam ta ce zasu zo kafin su wuce Niger.
Gaba ya ce ta shiga Su Harisu na baya dan Ja'afar ya ce suje idan sun ajiyeta zasuje yawo sbd yaji da'din kyautar fiye da tunanin mutum.
Har suka iso bai kalli idan take ba sbd yaga take takenta sai ya yi da gaske zasu shirya zai shareta daga nan har zuwa bikinsu.
Kallon yay daqile ya ce“Fitar min a mota malama.â€
Kallonsa tai ganin fuska ba wasa tai saurin ficewa daga motar aranta tana fa'din.
“ Motar sadakar aikin banza. Eh dai ban sonka sai ka gaji ka sakeni jaraba kawai, ni ban ma San ya akayi na soka da farko ba mutum sai baqin ran tsiya, balarabe mgnarsa ma murmushi ne.â€
Fuuu tai ciki sashen su Abie 1.
Ja'afar basu bar gidan Abie ba sai da ya nunama Mal Adamu moto dasu Tankon and Abie 2 suka sanya masa albarka Mal Adamu ya saka Ja'afar ya kira masa Ma'aruf ya yi godiya amman wayan tana shiga ba'a 'dauka.
Yo ina zai 'dauki kwaya yana can agajimare yana yawo.😂🤣ðŸƒðŸ»â€â™‚ï¸

A can Kuwa Espagne Rahma baccin 'karya tai, har na gaskiya ya 'dauketa, Anee da Meerah and Rafeek suke hirasu gwanin burgewa.
Dr yazo ya duba Rahma tana bacci ya ga ba wata matsala da zasuci gaba da riqeta ya ce idan babanta yazo yaje office sai abasu sallama taci gaba da shan magani.
Anutse ya turo 'kofar bakinsa 'dauke da sallama.
Rafeek ya amsa yana masa barka da zuwa Abie ya sha mamakin Rafeek bai tafi ba.
Fuska asake ya amsa yana isa bakin gadon ya janye bargon daidai kanta ya ta'ba goshinta ba zafi.
Anee ta ce“Abie Dr ya ce kaje idan kazo. Abie zamu tafi Allah qaro sauqi munada lecture qarfe 3 idan mun taso zan biya can gidan.â€
Abie ya jinjina kai ya ce“Mun gode Allah bada lada.â€
Rafeek aladabce ya masa sallama suka fita Abie ya nufi office 'din Dr.
Takardar sallama ya basu.
Merrah ta kwashe kayan ta kai mota tana jiransu.
Zaune yake bakin gadon ya sanya hannayensa ya tattarota jikinsa ya tallafo fuskarta ya 'dora 'dan 'karamin bakinsa kan goshinta ya sumbata ya dawo kumatunta, ya sumbata.
Manyan kyawawan idanunsa masu matuqar sakata ta yi taushi, ya zuba mata ya zura hanunsa cikin rigarta saman lafaffan cikinta yana shafawa.
'Dan zabura tai tana mutsitsika 'kananun kyawawan idanunta.
4 eyes sukayi da Abienta.
Sosai ta kafesa da idanunta wanda suka fara tara ruwa ta kwakwa'be fuska ta zura hannunta cikin rigar ta 'dora hannunta saman nashi wanda yake shafa mata cikinta tanajin wani irin abu na ratsata, gashin da yake kwance abayan hannunsa ta shafa, tana lumshe idanunta ashagwa'be ta ce“Abie Rabin raina pls karkayi fushi dani wahala nakeji kaji?â€
Cikin wata kasalalliyar murya yay mata mgna dab da kunnenta yana zaro hannunsa waje daga cikin rigarta gudun kar ya kauce arashin Sani.
“Babyna me kika min zanyi fushi dake dan kin kira saurayinki yazo ganinki bayan kinsa ke 'din matar wani ce?â€
Ya qarashe mgnar yana cizon fatar kunnenta.
Kukan shagwa'ba ta sakar masa tana qamqameshi ta ce“A'a wlh ban kirasa ba ni dai kayi hkr karkayi fushi dani nafi Sonka akansa ai.â€
Tallafo fuskarta yay zaiyi mgna ya ga ta kafe jajayen 'kananun la'bbansa da 'kananun idanunta masu saka shi shauki,tana musmus da 'dan 'karamin bakinta, idanunta sun tara ruwa, harara ya zabga mata ta sadda kanta qasa tana wasa zabon hannunsa.
Akunnen ya ra'da mata.
“Idan na gane kina sonsa Babyna?â€
Da sauri ta 'dago rinannun idanunta ta kalli Abie sai tai saurin runtse idanunta, sbd yadda bugun zuciyarta ya tsananta kallon da Abie ya mata 'kwa'kwaluwarta bazata iya daukarsa ba, fuskarta ta tura cikin 'kirjinsa tana sauke ajiyar zuciya ta zagaye hannayenta bayansa.
Ahankali ta kirasa “Abienah!â€
Murmushi yay, ya saka mata babban hijab 'din da yazo da shi ya 'dauketa cak kamar baby ya mannata 'kirjinsa ya nufi 'kofar fita.
Kallonsa take ba ko 'kiftawa wani irin abu me girma takeji wanda ta rasa meye shi abun ji take tamkar bazata iya rayuwa ba Abienta ba gashi watarana gida mijinta zai badata.
Hawaye suka wanke mata fuska ta sanya tafin hannunta tana shafa sajan fuskarshi tana Jan dogon hancinsa.
Kallonta yay ya 'daga mata gira, ya ce “No! Bana son kuka bari zamuyi mgna zuwa dare OK baby ummina?â€
Ya 'karashe mgnar yana 'daga ma gira ya karkace kansa.
Rahma tai saurin goge hawayen sai ta tsinci kanta da sakin dariya tana jan gemunsa.
Duk inda ya gilma cikin asibitin kallonsu ake cike da sha'awa.
Baya ya zaunar da ita Meerah ta zauna kusanta shi kuma yana gaba kusan direba suka nufi gida, Rahma jinta take kamar ma batayi ciwo ba,ta shiga wani irin yanayi me da'di ganin Abienta baiyi fushi da ita ba.

A can Gabon kuwa, Nura na isowa bakin gate Aishatu ta ce“Yauwa Nura bari na 'dauko kayan sai mu juya ban 5 minutes. â€
Ta fa'da tana 'balle murfin motar ta nufi cikin gidan ta qaramin gate ta shiga.

Motar Ma'aruf ta kalla ta girgiza kanta ta ce“Ko me ya tsayar da shi, yanzu hka bacci yake hamm wannan mijin nawa 'dan hutune, Allah na gode maka alamun shiriya qarara sun bayyana wajan Masoyi.â€
Tai murmushi ta nufi hanyar da zata sadata da falon.
Ido biyu tai da takalmin mace a'kofar falon, taji 'kirjinta ya buga dammm! Da sauri ta mur'da 'kofar jin ihu ta kutsa cikin falon........!

_💃ðŸ»'Yar Ajin Ma Sha Allah🥰_

_*🤲ðŸ¼Ya Allah ka jiÆ™anmu kayi mana rahama badan halinmu ba.ðŸ™ðŸ¼*_
3/12/22, 17:42 - Buhainat: ```D A```

```61&62```

_*My Sisters Don Allah Don Darajar Annabi Karki Karanta Idan Baki Biya Ba, Na Ku'dine Idan Kinga Yana Yawo Na Satane Ga Hanyar Da Za Ki Samu Naki Akan.😟👉ðŸ¼300N +22796515805*_

```Wow! 'Yan Paid Group nah wlh banda bakin yi muku gidiya sbd yadda kuke zumabin ruwan sharhi da comments billahi abin na matuqar burgeni, yana sakani nisha'di, hakan na nuna min kuna anfanu da saqonnin cikin labarin da darusan duk kuna 'dauka, My Habibaties ina yinku much love Jazakumullahu Khairan.💃ðŸ»â¤ï¸â¤ï¸â¤ï¸ ```
Babu editing
☹ï¸
Chapter 61 · 0% Book details