← Book details Dattijon Arziki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 114 OF 118

Sashe 114

Dattijon Arziki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jaddatu ta kai masa duka tana fad'in.
“Abdul bakajin magana, yanzu dai kuje kuyi wanka kuzo Ku cika cikinku da girke-girken da aka muku. Takwarata me kikeson ci gayamun kinji?â€
Rahma kamar ta nutse ta ce.
“Ummina komai ma idan kin ban zanci.â€
Jaddatu ta sumbaceta tace maza kuje an gyara komai sama.â€
Rahma kamar k'wai ya fashe mata aciki ta miqe ta fara takawa cike da kunyar Jaddatu taga cikinta.
Da kallo suka bita lokacin da take hayewa saman.

Jaddatu ta ce“Wlh wani irin farin ciki nake ji ganin Rahma haka, ubangijj ya sauketa lafiya.â€
Abie kunyar Jaddatu yakeji ya kasa mgna sai azuciya ya amsa da Amin.
Ya miqe ya ce.
“Bari watsa ruwa.â€

Rahma makullin da Jaddatu ta bata ta sanya ta bud'e b'angaran Abie ta shiga.
Sanyi k'amshin dad'i ya daki hancinta, ta lumshe idanunta, tana sauke ajiyar zuciya, ta d'ora hannunta saman cikinta Wanda yake motsi sannu ahankali.
Bedroom ta shige ta rage kayan jikinta tashige toilet.
Bathtub ta cika da ruwan d'umi ta zuba turaruka da sabulun ruwa masu qamshi ta tub'e ta shige ta kwanta lub abinta.
Abie sosai tsarin d'akin yadda aka masa ya burgeshi, kayansa ya cire ya d'aura towel ya nufi bathroom d'in.

Kwance ya hangota luf cikin ruwan.
Ba b'ata lokaci ya shige ciki tare da rungumeta yana murmushi.
Rahma ta shiga tureshi ta ce.

“Ni ai ba ruwana mun b'ata...â€
“No! My baby har abdan bazamu ba'ata ba sam, my baby ina sonki ina k'aunarki fiye da kaina da kowa da komai idan aka cire Ummina kinsan ba ta gaba dake yi hkr, oya zo muyi wanka.â€
Qamqame sa tai tana murmushi tana kallon kyakkyawan fuskarshi ta ce.
“Abieh na na nidaya kowa Rabin raina?â€
Bakinsa ya tura cikin nata ya kamo harshenta ya tsotsa ya Saki ya tsotsi lips d'inta ya Saki yana fad'in.
“Insha Allahu my ruhina.â€
Wanka sukayi atare suna tab'e-tab'ensu.

Bayan sun rama sallalolinsu suka shirya suka sauko k'asa, suka kwashi girke² masu dad'i.

Ja'afar sai zuwa dare yazo yama Abie sannu da zuwa, Wanda ya basa tsarabarsa shi da Ibtiaam.

A Cikin kwana biyar dasu Abie sukayi da zauwa har yanzu bai fara fita yana gida hutawa abinsa, ta waya yake business d'insa ga baqi masu sannu da zuwa ake da masu kira awaya.

Jaddatu sai nan nan take da Rahma sosai take kulawa da ita da abinda yake cikinta kamar k'wai haka suke jin Rahma agidan.
Soyayya ita da Abie idan nace na dinga Baku labarin irin soyayyar da suke zubawa da kulawa da junansa wlh bazan k'are labarin nan ba sabida soyayyar tasu akwai wuyar samun irinta, akullun son junansu da kulawar junansu qaruwa yake azuciyarsu.

Alhj Nafi'u ya turo masu neman auren sa gidansh Rayyana an tsayar da magana sati mai zuwa za'a d'aura har tarewar insha Allahu, Rayyana tana cikin farin cikin lamarin ga shi kowace da b'agarnata wata batasan me wata take ba.

★★★
Ibtisam zaune kusan Falmata tana amsa waya, sai murmushi take.
Yanzu aka gama mata k'unshi.
“Kai Anna wlh lfyta lau wai kinga irin k'ibar da nayi kuma fa ciki wlh duk kayana sunhi min kad'an. Ina Taslim wai? Kwana biyu Baba baya ban ita muna gaisawa.â€

Falmata kallon Ibtiama take cike da mamaki wai daman yarinyar batasan tanada ciki ba abun ya fito qiri² kuma mijinta bai gayamata ba?
Bari tai sai da ta qare wayan ta ce.
“Wai ibtisam kina nufin qiba ce ta kumbura miki ciki hakan?â€

Ibtisam tai dariya ta ce.
“Eh wlh Umma.â€
Falmata ta ce“Gsky bakida wayo Ibtisam toh wlh kibar shasancin nan cikine cake fa! Kina ganin abu haka kice qiba? Ai wlh bakya bina bashin rantsuwa cikin nan naki hakai wata shidda.â€
Ibtiama ta firfito da manyan idanunta ta dafe 'kirjinta ta ce.
“Ni umma? A'a wlh ai me ciki kullun baida lfy baya cin abinci ni kuma lau nake.â€
Falmata ta ce.
“Lallai sabida bakya laulayi shi kenan? Sai akace miki kowace mace take laulayi? Ai wlh wata sai dai ki ganta da cikinta kamar nakin nan, wata kuma tin ranan da Allah ya bata toh zai fara nuna alama, har sai yayi k'wari ita da lafiya. wata kuma sai ya kai wata zuwa wata biyu take fara laulayi wata kuma idan ta fara laulayi abin ba sauqi sai ta sauke wata ba laulayi amman bata son namiji ya kusanceta wata kuma k'amshinsa ne bataso wata kuma fad'a da yawan b'acin rai, ba ta yadda ciki baya zuwar ma mace dan haka ki dawo haiyacinki ciki gareki, Wanda inada tabbacin zai kai 6 ko 5.â€
Ibtisam tai tagumi sai yanzu ta tuna ita fa dudu jininta biyu a nan garin idan hakane kuwa hakane cikinta watansa 6.
Shiru tai kamar ruwa ya cinyeta ta kasa magana.

Koda Ja'afar yazo d'aukanta yaga ta sauya sosai yana driving ya kamo hannunta yana murzawa ya ce.
“Mah Love me ya farune?â€
Ibtisam ta silalo hawayen da taru cikin idanunta ta kalleshi ta ce.
“Mon Amour Ashe ba qiba bace cikine gareni.â€
Ja'afar yay murmushi ya ce.
“Au wai da baki saniba matar Ja'afar?
Ai wlh nasani ina kallonki ne naga iya wayon Mon cherie, yanzu dai kin gane ko? Ai ni ba sakarai bane wata shidda bakiyi period ba wlh nasani ganin bakya ciwo ba laulayi na qara dagewa wajan kulawa dake da abinda yake cikinki wallahi ina sonku fiye da kaina addu'ata Allah ya sauke min ke lafiya.â€

Kuka ta fashe da shi tana rungumeshi.
“Hahaha Beby bari kuka ko bakyason haihuwar?â€
Ibtisma ta girgiza kanta ta ce.
“Mon amour ina mamakine sam da ban tab'a ankarewa ba.â€
Ja'afar ya sake gyara mata kwanci jikinsa ya ce“Ai yanzu an Ankara dake dan haka Allah zamuma godiya gobe sai mufara zuwa asibiti duk da nasan zamusha fad'a.â€
Murmushi tai bata sake mgna ba dan ganin abun take a Almara.

Yau aka d'aura auren Rayyana akan sadaki mai daraja, ayau kuma ta tare agidanta, Wanda lokacin da za'a tafi da ita kuka take tamkar budurwa sabida yadda auntie Saro ta tsaya tsayin daka wajan gayara da mata nasiha tasan abinda take ta Kama kanta karta kuskura tace zatayi irin rayuwar da tai agidan Abie.
Tabbas ta d'auki nasihar tayi alqawalin ruwa da iska zata masa biyayya.
B'angaran uwar gida aka kai Rayyana, hajiya Sha'wanatu batada matsala har tsokanar Rayyana tayi, sosai 'yan uwan Rayyana suka yaba da halin Sha'awanatu.
Daga can suka nufi b'angaran hajiya Zakiya me d'akin tsaka toh ita ma ba laifi.
Kowa ya yaba dagin Rayyana ba laifi duk da bai kai rabin² gidan Abie ba amman fa gidan ya had'u.
Wajan k'arfe 10 na dare ya had'asu b'angaran hajiya Sha'awanatu ya musu nasiha akan su zauna lafiya kamar baya baya son yaji wata fitina ta billo kowa yaba d'an uwansa girma.

Alhj baisan dawan garinba cewar Rayyana bata tab'a sanin namiji ba ashekarunta sai da yaje kutsawa aguje yaji Abu gark'ame.
Ai kusan haukacemata yay lokacin da yaji zamzam ya kuma samu ya tila ya shige tasha zantuttuka ba laifi da kyaututtuka.
Rayyana tasha wuya matuqa girmanta bai hanata kuka ba.
Amman fa washegari tasha lele ko nan da can Alhj ya kasa fita dakyar yaje ya gaido iyalinsa.
Cikin kwana ukun da yayi wajanta matasan sosai sukaga rawan k'afan da yake akan amarayan tasa sai sukaji ba dad'i.
Rayyana kulawa take samu wajan alhj Nafi'u abun ba'acewa komai sai yanzu tasan tayi aure kuma aurema na mijin da yake sonta.

★★★
Bayan wasun 'yan kwanaki.
Gabon.
Alhamdulillahi za'ace b'angaran su Aishatu Ma'aruf kamar wasa harakan gwanjo ta amshesa yana samu ba laifi har an gyara masa motarsa da wuta taci abinda taci, komai na rufin asiri bai gagaresu ba.

Yau tin safe Rabi'ah ta tashi da naqud'a ganin ba'a wani kulata sosai agidan ta shige uwar d'aka tana shan azaba.
Ai wuya da tayi wuya ta shiga kiran mahaifiyarta.
Arikice suka nufi hospital.
Murtala ne ya kira Ma'aruf ya gayamasa halin da ake ciki akan Rabi'ah bazata haihu da kanta ba sai an mata cs.
Yana gayama Aishatu hankalinta ya tashi harda kukan tausayama Rabi'ah dan ayanzu tausayi take bata tasna tata k'addarace hakan.
Tin safe suke can har akayi aiki aka fito da yaron kyakkyawa fari Tass k'aton gaske sak Ma'aruf kamar anyi kakinsa a tofar.
Aishatu tinda ta kalli yaron ta k'ara yarda ba wanda ya isa ya goge zanen k'addarasa aduniya.
Amman abin tashin hankalin Rabi'ah har dare ya fara bata farfad'oba hankalin kowa ya tashi sosai.
Aishatu tana maqale da yaron ta kasa zuwa gida ba yanda Ma'aruf baiba amman taqi ya hasala yayi ya tafi ya barta.

Misali 10 na dare Rabi'ah ta farfad'o Aishatu ta fara nema.
Aishatu tana rungume da yaron ta riqe hannun Rabi'ah t ace.
“Ga ni Rabi'ah ga yaronki Masha Allah. â€
Rabi'ah cikin fitar hayyaci ta ce.
“Don Allah ki temaka ki basa abincinsa ajikina,kuma na baki shi kyauta dan Allah ki yafemin wlh bazan gaji da naiman yafiyarki ba.â€

Aishatu ta rufe mata baki ta ce.
“Na yafe miki duniya da lahira ba yauba tsaya abasa nono mama temaka min na basa dan Allah. â€
Mahaifiyar Rabi'ah tana mamakin shin Aishatun nan wace irice ne?

Taimakawa sukayi wajan bawa yaron nono ya Kama yana Sha.
Rabi'ah tana zubar da hawaye ta shafi kan yaron ta ce.
“Allah ya maka albarka ya rayaka, Allah yasa kazama wani Abu aduniya Allah yasa duniya tai alfahari dakai ka yafemin ka qara nema min gafara wajan mahaifinka, Aishatu ki riqeshi amana dan Allah karyasan bake bace mahaifiyarsa...â€

Aishatu ta rufe mata baki tana girgiza kanta.
Shaquwa sukaga tanayi mama ta fita aguje kiran doctor kamar jiran fitarta take numfashin Rabi'ah ya tsaya cak bakinta na motsawa sam bakajin abinda take fad'a.
Aishatu idanu ta zuba mata ganin bata motsi jikinta ya d'auki rawa.

Dr yana dubawa ya ce.
“Kullun nafsin za'ikatul maut. Allah ya mata rasuwa kuyi hkr.â€

Aishatu nan ta zube k'asa asume.
Mama kanta abun ya girgiza k'asa ta zauna dab'as ta dafe kanta wasu hawaye mai zafi ya zubo mata tana fad'in.
“Rabi'ah wallahi na yafe miki duk qamar da make nuna miki sabida ki gyara rayuwarki ba dan na tsaneki ba.â€
Chapter 114 · 0% Book details