← Book details Dattijon Arziki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 118

Sashe 29

Dattijon Arziki Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ja'afar yana isa gida, ya zauna dab da Harisu, ya ciro wayarsa ya kira Malam Adamu, suka sha fira sosai da Inna mai waina.
Bayan sunyi sallama, ya kira Ibtisam dan ya lallasheta wayar switch of.
Kansa ya dafe ya mi'kewa ya nufi 'kofa yana fa'din.
“Bari naje naga halin da take ciki.â€
Kansan yaji ya sara yay saurin dafewa yana karanta duk addu'ar da ta zo bakinsa.
Harisu da Yahuza suka ce“Ya jikin Ibtisam 'din? Baba ya yi ta fa'da ya ce kun tafi asibiti ba sanin kowa.â€
Ja'afar ya juyo zai mgna,
Baba Tsalha ne ya shigo bakinsa 'dauke da sallama ya ce“Wai ina kuka tsaya haka? Ina Ibtisam 'din?â€
Ja'afar ya ce“Baba rabona da ita tin bayan sallar isha lokacin zan fita, ina take? Me ya sameta¿â€
Baba Tsalha ya ce“Kaci gidanku ta ce tana tsamki nace taje ta fa'dama mutafi asibiti naji shiru nazo su Harisu sukace sunji kana mgna a 'kofa 'kila kun tafi ne.â€
Ja'afar gabansa yay mummunar fa'duwa ya ce“Wlh Baba bamu fita tare ba banma san batada lafiya ba tin yaushe? Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Yanzu ina zamu nemonta.â€
Baba Tsalha ya ce“Hasbunallahu Wa ni'imal wakil, zama bai samemu ba, ko dai ka mata wani abun ne don Allah me ya ha'daku?â€
Ja'afar ya ce“Wlh ban mata komai ba, kawai taji dai ina wayane da Rahma kuma lfy lau muka rabu, na fita.â€
Baba Tsalha ya ce“Wacece Rahma?â€
Ja'afar ya sosa kansa ya ce“Allah ya ha'damu balarabiya ce, kuma wlh ina masifar sonta su biyu zan aura idan Rahma ta amince.â€
Baba Tsalha ya zazzaro idanunsa waje ya ce“Ok muje bamuga zamaba ina zargin ta gudune mu fara zuwa tasha.â€
Ja'afar hankalinsa ya yi masifar tashi jin Ibtisam ta gudu ne.
Baki 'dayansu suka shiga motar Baba Tsalha suka bar gidan Ja'afar sai wata irin zufa take keto masa.
Duk wata tashar mota da take cikin garin (Ndjamena) su Ja'afar sunje neman Ibtisam basu sameta ba.
Lokacin kuma 'yan sanda sun zo sunyi duk abinda ya dace, an 'dauke motar daga wajan shiyasa basu ga komai ba.
Ja'afar ya rasa inda zai sanya kansa sunata yawon neman Ibtisam har shabiyun dare ba labarinta.
Baba Tsalha ya tisasa gaba da fa'da akan me zaiyi waya da mace agabanta ga shina ta gudu 'kilama ta tafi cameron wajan 'yar uwan babanta.
Kasa ko motsi yay abin duniya ya damesa, shi fatansa duk inda take ta kasance tana cikin 'koshin lafiya.

Can kuwa asibiti sai wajan 1 na dare aka gama ma Ibtisam komai.
sai da suka saita kome aka d'ora hannun Ibtisam da 'kafarta, hankalin likitocin ya kwanta.
Har lokacin suna asibitin.
Abie yana ganin an bu'de 'kofar room 'din ya janye Rahma daga jikinsa wacce take bacci, ya kama hannunta suka nufi wajan Dr.
“Doctor wane halin bayin Allah suke ciki?â€
Dr Salis ya gyara kwalar rigarsa yana sharce zufa ya ce“Alhmdllh! Mun saita komai shi wancan nasa da sauqi mun jima da 'dorasa mun 'dinke masa goshinsa, an 'Dora masa karayar hannunsa, yana bacci, muje sai na maka bayanin ita yarinyar.â€
Abie ya jinjina kansa ya kalli Abie 2 ya damqa masa hannun Rahma ya ce“Kuje gida Yahaya maidaku insha zan taho kafin asubah,ummina kiyi bacci cikin amincin Allah da kariyarsa bye.â€
Ya qarasa mgnar ya manna mata kiss a goshi.
Kai ta 'daga Abie 2 ya ce“Bari na kaita sai mu dawo ai bazamu barka ba kai 'daya.â€
Abie “A'a don Allah je ka huta.â€
Dole suka tafi shi kuma su ka nufi office 'din Dr Salis.
Bayan sun zauna ya ce“Yalla'bai yarinyar nan ta bugu dayawa, yanzu dai mun mata 'dorin hannu da 'kafa, 'dinki goshi da kai, amman mgnar gaskiya alamu sun nuna kamar ta yi doguwar suma, yanzu haka mun shigar da ita coma, amman karka damu komai na Allah shi keyin komai alokacin da yaso ba lallai bane yadda na'urori suka nuna mana ya tabbata ba, ko adaren yau Allah ya ga dama zai farfa'do da ita.
Dan haka za'a kula da ita, har lokacin da zata farfa'do, shi namijin yanada kyau 'yan uwansa zuzo jinyarsa.â€
Abie ya tura hannunsa cikin yalwatacciyar sumar kansa, yana fa'din.
“Wa la haula wa la Quwwata illah billah! Hasbunallahu Wa niimal wakil. Ok ok, Dr Salis zan saka abazama cigiyar 'yan uwan bayin Allah nan zuwa gobe gidan Tv radio har asamesu.â€
Dr kwantar masa da hankali ya shiga yida bayanai dalla² har yaji 'yar nutsuwa, sai 2 shi da securities 'dinsa suka nufo gida.
Acikin tsakitar Daren ya saka aka shigar da sanarwa duk wani godan radio da Tv da yake cikin garin Ndjamena.
Ja'afar kasa bacci yay adaren, ya shiga salloli da karatun Qur'ani akan Allah ya bayyana Ibtisam.
Rahma kuwa baccinta tai anutse, wanda da bayane ba zata ta'ba runtsawa ba Abienta na wani hali.
Yayin da Abie bai iya runtsawaba hakan ta saka shi 'dauro alwala ya shiga sallah.
Abie 2 kamar yadda yay alqawali zai duqufa da sallolin dare ya fa'dawa Allah akan Allah ya ganar da shi abinda yake son ganewa akan Rahma da Ja'afar, zai duqufa tsawon sati yana kaiwa Allah kukansa, kafin yay qoqarin cire musu aljanun sbd yasan Allah bai abu abanza, bai kamata yay garajen warware matsalar ba, sai ya kai kukansa gurin Allah.
Washegari kuwa gidan radio da Tv na Ndjamena, ko ina sanarwar Ibtisam ne dan tin tsakiyar daren me taxi ya dawo haiyacinsa ya fa'di sunansa da unguwarsu tin da safe Abie ya tura aka taho da matarsa da yaransa uku.
Baba Tsalha yana tsakar gida ya kasa fita radio ahannunsa kamar a mafarki yaji sanarwar, da 'karfi ya ce“Ba shakka Ubtisam ce Falmata taho muje mugani.â€
Falmata ta ce“Allah yasa itace.â€
Ja'afar ne yay parking a'kofar gidan zauwar kenan daga gidan Ma'aruf wanda yace yaje amso motar, ya fito ya shiga cikin gidan 'bangara Baba Tsalha ya nufa, ya shiga yana fa'din.
“ Baba naji sanarwa Hôpital général muje don Allah ko itace mugani ance acikin taxi hatsarin ya faru.â€
Baba Tsalha ya ce“Muje.â€
Su biyar suka nufi asibitin hankulansu atashe.
Jaddatu zaune tana balbala fa'da.
“Sbd Allah yaron ashe jiya ha'dari ya samu shine bazai fa'damin sai yanzu da safe.â€
Hanan ta ce“Ummi dan kar hankalinki ya tashi ne ai, kiyi hkr ya ce anjima za'a kaimu lokacin Rahma ta tashi.â€
Raiyana ta ce“Allah dai ya kare gaba nama rasa ina zaije adaren har yay tuqin ganganci haka, ya saka hankulamu tashi, dan wlh ni ban rantsa ba jin bai shigo ba, Ummi qarama sai 1 na dare ta iso. â€
Jaddatu ta ce“Ya wuce damuwar rashin walwalar Rahma ne.â€
Anutse take saukowa tana sanye da wata English Morocco maroon gown,tai masifar mata kyau, ta baza gashinta har tsakiyar bayanta,wani irin matsiyacin 'kamshi yake tashi jikinta. Wani hills ne aqafarta mai shegen kyau.
Wayarta (iPhone 13 pro max)
Ta Danna kiran Ja'afar wanda ya kirata tana wanka.
Bugu 'daya ya 'daga kiran lokacin sun shiga hospital.
“Hello Qalbina kiyi hkr zan kiraki anjima munzo hospital ne muna sa ran Ibtisam ce tin jiya ta 'bata.â€
Rahma ta dafe saitin zuciyarta jin wani abu ya suki zuciyarta sbd jiya yace Ibtisam matar da zai aurace.
ta dafe qarfen benin cikin zafin kishi ta ce“Ni dai wlh yanzu nake son ganinka idan ka wuce 15 minutes sai dai ka isko gawata na mutu tinda baka sona wayyo 'kirjina zafi wayyo Allah na! Zan mutu!â€
Ta 'karashe mgnar tana sakar masa kukan shagwa'ba.
Daga can Ja'afar ya dafe goshinsa kasancewarsa mutum marar son hayaniya, cikin raunin da jinnu suka saka masa ya ce“No! Ga ni nan Qalbi pls kar wani abu ya sameki wlh nima mutuwa zanyi.â€
Su Baba Tsalha suka Saki baki da hanci suna kallon shi.😂
_(Allah dai ya 'debema Raiyana albarka ta maida mutane biyu wanda suka kasance miskilanci da izza ga kamun kaida rashin son hayaniya tamkar 'ya'yan sarauta. Amman yanzu ta saka an mayar dasu tamkar sakarkaru.)_
Ja'afad kai tsaye ya juya da sauri ba tare da ya tsaya ma su Baba Tsalha bayani ya fa'da mota ya fizge aguje yabar asibitin... *💃ðŸ»'Yar aljin tubarkallah*

_*🤲ðŸ¼Ya Allah ka jiÆ™anmu kayi mana rahama badan halinmu ba.ðŸ™ðŸ¼*_
2/14/22, 14:09 - Buhainat: ```D A```

```29&30```
Chapter 29 · 0% Book details