← Book details Dattijon Arziki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 118

Sashe 77

Dattijon Arziki Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

*Niger*
Misalin 'karfe 10 na safe, Ja'afar tsaye cikin shigar 'kananun kaya, yana fesa turare mai sanyin da'din 'kamshi, wayarsa ta 'dauki ringing.
Ganin Harisu ya saka ajiye kwalbar turaren ya 'dauki wayar yay picking call 'din tare da sallama.
Daga can Harisu ya ce“Abokina fatan kun sauka lafiya? Ga Baba Tsalha nason magana dakai.â€
Ja'afar ya amsa sallamar yana fa'din.
“Alhmdllh! Oh! Mon dieu! Pardon Harisu, wallahi tin safe bacci nake, tinda na dawo daga masallaci, yanzu ma Inna ce ta tayar dani, fatan kuna lafiya! Ina Yahuza har yanzu baku fita ba? Bani Baban.â€
Harisu ya ce“Lafiya lau eh yanzu zamu fita, ga Baban. â€
Ja'afar ya gaishesa cikin girmamawa baba Tsalha ya ce“Daman dan muji kun isa lafiya ya gajiya?â€
Ja'afar ya ce“Baba ina tune daku da anjima zan saka Kati na kiraku, Alhmdllh! Baba.â€
Sun 'dan ta'ba hira sukayi sallama, Ja'afar ya jefa wayarsa cikin aljihun wandonsa,ya fito ya nufi cikin gidan nasu.
Innah mai waina ana zaune bakin nan awashe kamar gonar auduga, Mal Adamu ya baje musu tsaraba, ma'kota sai shigowa barka dazuwa ake.
Mal Adamu ya Innah Hansatu turaman atamfa biyu masu kyau da takalmi da mayafi biyu, sai turaren wuta na jiki da na 'daki.
“Oh! Allah haihuwa me albarka Ja'afaruna ya janyo mana alheruruka Masha Allah Malam mun gode Allah ya qara rufa asiri.â€
Mal Adamu ya amsa da “Ameen Hafsatou.â€
Ya beqama Deluwa nata kamar yadda yaba Innah Hansatu haka ya bata.
Godiya take tana fa'din.
“Ubangiji ya qara arzi'ki da hanya ta alkahiri.â€
“Ameen ya Allah. Maimunatu ga naki abayace da lufaya keda 'yan uwanki duk 'iri 'daya ne sai ki ajiyemusu duk wacce tazo ki basu.â€
Ja'afar ne ya shigo da sallama.
Maimou ta miqe tana murna ta rungumeshi tana dariya, ta ce“Ya Ja'afar ashe haka ka zama Allah jiya kallon duhu namaka, sannu da zuwa Ya Ja'afar kalli kayanmu da Baaba ya kawoma.â€
Janyeta yay yana hararata ya ce“Ke banson iskanci ji yadda kika cikuikuiye min rigata.â€
Inna Hansatu ta ce“Ai wlh baqin buzuna ni wannan 'dabir ta runguma ma bana sonta sai kace wasu larabawa.â€
Murmushi Ja'afar yay ya ce“Inna idan basu rungumi yayansu wa zasu runguma? Baaba ina kwananku?â€
Mal Adamu ya amsa shi da Deluwa fuska asake Deluwa na tambayarsa “Ya gajiya Ja'afaru?â€
Zama yay kusan Innarsa ya ce“Tabi jiki Umma.â€
'Yan 'kanninsa suka gaishesa ya amsa yana tambayarau karatu.
Innah ta 'dauko masa shayin da ta ha'da masa yaji madara an sayo masa biredi ta soya masa wainar 'kwai.
Ja'afar ya fara ci yana danna waya.
Mal Adamu ya ce“Hafsatu da Ja'afar har kwai aka soya masa mu aka soya mana awara da kunu.â€
Dariya tai ta ce“Haba! Ina laifi.â€
Murmushi yay ya ce“Ja'afar idan ka kammala sai leqa ka gaka ya MATAR taka ya ta kwana ko?â€
Fuska ya ha'de shi fa ya fita sabgar yarinyar bai ta'ba zaton Ibtisam zata iya sauya halinta ba, amman ba mamaki tinda tin farko ita ta nuna masa so yay saurin tarar numfashinta amman sai ga shi tana son raina masa hankali zai koya mata hankali.
“Tom Baaba insha Allah.â€
Ya amsane amman ba wai zaije bane.
Innah Hansatu ta ce“Ka gaisheta da jiki idan kaje.â€
Deluwa ta ce“A'a baza'ayi haka ba zamuje ni dake mu dubota dan Allah Hafsatu.â€
Mal Adamu ya ce“Kwarai kuwa zakuje.â€
Ja'afar yana gama breakfast 'dinsa ya miqe ya fice zai zaga gari, ya dawo ya ce yaje.

Ibtisam tinda ta tashi yau batajin da'din jikinta, wani abu takeji ya danne mata 'kirjinta, daurewa kawai take, haushin kowa takeji yau agidan, tin safe ta fito tai breakfast ta'ki.
Tanko ne ya shigo da sallama hannunsa 'dauke da baqar leda 'danyan kifini ya siyo da kayan miya.
Laraba suna zaune saman tabarma sunata kallon kayan da Tanko ya fito musu tsaraba yaran harda nata Tasha mamaki dan bata San dasu ba,bakinta yaqi rufuwa.
Taslim ta ce“Baba sannu da zuwa gaskiya Baba kayanmu sunyi kyau Masha Allah, mun gode kowane na gwada sunmin gaskiya wannan 'kasar akwai kaya masu kyau.â€
Tanko ya zauna yana fa'din.
“Madallah Taslim Allah miki albarka.
Laraba ga kifi amana farfesun kifi sai adafa shinkafa 'yar Cotonou. Ina Ibtisam?â€
Laraba ta ce“Tana 'daki taqi cin komai wlh ba yadda banba.â€
Miqewa yay ya nufi 'dakin.
Kwance take ta du'kun'kune waje 'daya ta 'daga kanta sama tana kalon silin 'daki.
Tanko ya shigo yana kiranta.
“Ibtisam!â€
Za'bura tai ta miqe zaune tana rarraba idanu.
“Wai Ibtisam kasheni kikeso kiyi? Me ya sauyaki haka lokaci 'daya? Wallahi kibi duniya asannu ina jiye miki nadamar da batada anfani wlh kin ban mamaki kin jahilta kanki kina Neman hallakar da kanki kina son wani da auren wani akanki? Kin kyautama kanki ke yanzu dan Allah idan ba daliliba me ha'dinki da babban mutum kamar Abdulmajid mutumin da Jar fatarma masu ku'din maza da mata ba da kowa yake alaqaba, idan ba dalilin dalili ba ina za ki gansa? Mutumin da jansin Ku ba d'aya ba kike neman jefa kanji halaka, wlh ki dawo hayyacinki tin kafin na 'daukar miki hukuncin da zai miki tsauri, tashi kije kici abinci, wallahi ina kan bakana matuqar kikayi abinda yaron nan ya sakeki Allah bani bake sakara marar tunani.â€
Kuka take tana basa hkr ya ce“idan kina son na hkr ki saki ranki kamar da kar na sake ganinki ahaka.â€
“Insha Allah Baba zanyi ka tayani da addu'a.â€
Hannunta ya Kama suka fito da kansa ya zuba mata abincin ta fara ci ba dan tanajin 'dan'danonsa ba, dan ta farantawa mahaifinta ne, ga 'kirjinta na ciwo.
Tana idarwa ta daure ta saki jikinta suna sake duba kayan.

Acan Tchad kuwa sai shabiyu Rahma ta farka daga bacci, ta shiga tai wanka ta fito da towel ta goge jikinta ta shafa lotion 'din Abie ta zura jallabiyarsa sai lokaci idanunta suka sauka akan sabuwar wayar waccan baqa ce wannan kuwa pink kala ce.
Tsalle Rahmaa tai ta ce“Wow! My Abie sabuwar waya ka siyamin? I love you Rabin raina I kiss you My Abie.â€
Ta 'karashe mgnar tana sanya santalelan farin hannunta ta 'dauki wayar akunne take an cikata da charge, ta shiga contacts taga lambobin family 'dinsu ne kawai, kuma sabon layine.
'Yar dariya tai ta yi far da 'kananun idanunta masu matuqar kyau da haske.
Number Abby Morocco tai dialing.
Bata jima ba tana ringing aka 'daga tare da sallama.
Rahma ta nufi falo tana amsa sallamar ta ce“Tsoho mai ran 'karfe matarka ce nayi sabon layine sabuwar waya kasan kuma aikin waye.â€
Daga can kyakkyawan dattijon mai nutsuwa da kamala ya ce“Aff ya wuce Sojanki, ga Zainabu tana nemanki wai yaushe za ki zo?â€
Rahma ta karkatar da kanta gefe ta ce“
Abbyn Ummana kace Zainnunu me ta ajiyemin wlh zan shigo wannan satin idan Rabin raina Abie ya yarda. Yaushe Auntie Saleeha zata dawo da Yemen ne?â€
Dariya ya yi ya ce“Zai ma yarda amman muma ai munkusa zuwa, Auntin ki sai azumi fa ta ce anan zatayi azumi nna da wata hu'du kenan.â€
Rahma ta ce“Pls Ku jira nazo sai mudawo tare ina Ummiterh ne dasu Irfan iyayan surutu?â€
Abby ya ce“Basa nan sun fita, ga Zainabu.â€
Rahma ta amsa tana tsokanarta sun jima suna hira ta tsinke kiran ta kira numbers Abienta duk basayi kamar ta yi kuka ta nufi 'kofar falon ta bu'de taji gam da key.
Sai lokacin ta tuna ta ga key kusan wayan, ta koma ta 'dauko ta ajiye saman center table ta koma bedroom 'din ta wanke toilet tas ta fesa turaren toilet ta gyara masa bedroom tsaf daman ba alamar datti, ta gyara shimfi'dar gadon ta goge TV plasma, ta kunna turaren wuta ta fesa na 'daki, ta koma toilet ta zuba kayan acikin (machine à laver) ta wanke masa kayansa na jiya wanda su ka d'aine masu datti sai na barcinsa ta shanyasu a abin shanyar toilet, ta fito ta rufe bedroom ta fito ta gyara falon tsaf nan ta kunna turare ta goge TV'n falon da fridge, tsaf komai a muhalinsa sai 'kamshi kawai ke tashi ta bu'de 'kofar ta fito ta murza key ta zare ta haye sama.
Agurguje ta shirya cikin Riga da wando jeans da wata crazy 'din riga yellow ta mata kyau kamar yadda jeans 'din ya zauna Masha Allah sai 'kamshi take ta sanya slippers a qafarta ta fito.
'Dakin Meerah ta buga taji shiru ta gane tana 'kasa.
Chapter 77 · 0% Book details