← Book details Dattijon Arziki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 118

Sashe 35

Dattijon Arziki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da murmushi 'dauke akan fuskarta ta isa dab da shi ta tsaya tare da sallama ta nuna masa hanyar zuwa falon baqi.
'Kayataccan murmushi ya sakar mata, suka jera zuwa falon.
Abie da yake tsaye yana kallonsu sai da suka gefta shi ya girgiza kansa ya koma ciki ya 'dauko ruwan addu'a.
Suna shiga falon Ja'afar lumshe lumsassun idanunsa ya na shaqar dadda'dan 'kamshin falon, ya furta.
“Qalbina irin turaren wutar nan zakina sakamin agidana.â€
Ya 'karshe mgnar yana zama.
Murmushi tai ta 'dauki wani ha'dadd'an cup glass ta tsiyaya masa sansan lemon 'ya'yan itattuwa ta beqa masa ta zauna 'dan nesa da shi.
“Ngd Qalbina, amman zan fara koya miki hausa sbd ba kowa ya iya English a family namu ba.â€
'Yar dariya tai tana rufe fuskarta.
Kur'bar lemon yay ya ajiye cup 'din ya fuskanceta murya a tausashe.
“Qalbina ya mgnar auren namu? Kiga gwara ayita tin su Baabana suna nan.â€
Rahma cikin siririyar muryarta mai zaqi ta ce“Karka damu Habibyna za'ayi wlh na matsu ayi mutafi Espagne har na gama karatuna, idan kuma can zamuyi rayuwarmu Abiena baida matsala.â€
Fuskarta yake kallo murmushi 'dauke kan fuskarshi ya ce.
“Yauwa my Qalbi A'a bazamu zauna acan ba, Niger zamu zauna ok?â€
Ta waro idanunta zatayi mgna sai ga Abie 2 ya shigo da sallama.
Rahma ta miqe tana fa'din.
“Oyoyo Abie 2.â€
Murmushi yay ya zauna tsakiyarsu kamar yadda ya saba.
Ja'afar ya gaishesa.
Cikin fara'a ya amsa, ya 'dora da cewa.
“Yauwa 'diyar albarka beqo min cup ga ruwan addu'a kusha sbd aurenku.“
Cikin zumu'di da jin da'di Rahma ta ce“Wow! Abie 2 ka gama mana komai mun gode.â€
Ta 'karashe mgar tana beqa masa cup 'din. Amsa ya yi ya zuba ma Rahma ya beqa mata ya ce“Shanye duka fa!â€
Ba musu ta amsa ta shanye, ya zubama Ja'afar ba musu ya amsa ya shanye tare da bismillah.
Wani irin jiri suka din gaji atare, wanda sai da suka dafe Kansu.
Abie ya riqosu dukkansu yana tambaya.
“Lafiyar ku kuwa? Ku karanta AMANAN RASULU da KURSIYU da YASIN, da
LA'ILAHA ILLAHUWA WAHADAHU LA SHARIKA LAHU LAHUL MULKU WA LAHUL HAMDA WA HUWA ALA KULLI SHAY'IN QADIR (10).â€
Kai suka jinjina suka fara karantawa cikin ransu, sannu ahankali suka fara jin jirin na sakinsu, amman sai sukaji dukkan jikinsu ya 'dauki mugun zafi da ra'da'di sosai.
Abie ya qara musu ruwan suka sha yana addu'ar Allah yasa kafin kwanaki asirin ya sakesu sbd ya yarda da addu'o'in 'dari bisa 'dari.
Abie ganin irin yanayin da suke ciki ya dafasu ya ce“Ja'afar jeka gida zuwa gobe sai kazo. 'Diyar albarka je ki kwanta ki huta.â€
Ba musu suka miqe ya kama hannunsu suka fito Rahma ta shagwa'be.
“Habibyna sai munyi waya ka kularmin da kanka.â€
Kai ya jinjina mata sbd bazai iya mgna ba.
Sai da ya shiga mota Abie ya rakata har 'kofar falonsu ya juya yana mai farin ciki sbd yaga alamun nasara.
Ja'afar yana zuwa gida ya 'bingire bacci.
Rahma hakan ce ta faru bedroom Jaddatu ta shiga sbd jirin da yake 'dibarta bazata iya hawa saman bene har na 2 ba.
Koda su Abie suka dawo basu iskosu ba, nan Abie 2 ya basu labarin abinda ya faru.
Sosai kowane yaji da'din labarin Tanko addu'a yake Allah yasa Ja'afar yay gaggawar dawowa haiyacinsa.
★★★
Cikin kwana biyar Abie ya gama mgna da Dr Moha daga Australia, har an fara shirin tafiya,wanda Abie ya baiwa Tanko wadataccan ku'di ya koma Niger ya 'dauko Laraba zuzo a musu passport.
Rahma da Ja'afar kuwa har yanzu su na son junansu amman ba sosai ba irin nada, abin ya fara ja baya.
Daga Abie 1 har Abie 2 and mal Adamu, ba wani mai 'kwa'kwaran barci dare suke bi kullun cikin fa'dawa Allah suke, sbd canji ya fara zauwa.
Ga manyan malaman da Abie ya rabawa ku'di anata saukar Qur'ani ana yanka raguna anata sadaka, har tuyar wainar hatsi ake, Ana rabawa sadaka, toh komai sai lokaci ya yi.
Ja'afar ya fara maida hankalinsa wajan Ibtisam, abin har mamaki sukeyi, duk da har yanzu bai sakuba.
Ibtisam ana nan dai ba wani sauqi sai wajan Allah, karyata ce take qara sauqi bata fiye yarda da mutane ba sai Abie shima nesa da nesa dan yawan 'daukeshi take da Mari, bawan Allahn hakan bai hanasa temaka mata ba, sbd shine kawai take yarda ya bata abinci.

*Niger*
Tahoua
Laraba ta rabka tagumi tana kallon Tanko.
“Haba! Laraba wai kin fini son Ibtisam ne? Ai bawa baya tsallake 'kaddarasa. amman ki sa ni komai ya faru da ita mune sila, mu muka janyo mata wlh ni basan she'dani da ya shiga kaina ba har na amince zan bama Jamilu 'diyata.â€
Laraba ta ce“Wai yanzu ina zamu bar yaranmu har rai biyar? Gaskiya Tanko bazan jeba tinda kace ma bata gane mutane kaje kawai zan dage mata da addu'a, ko kutafi da Dadda.â€
Ta qarashe mgnar tana share hawayen takaicin kanta da ta siyama 'yarta larura.
Tanko ya ce “A'a dole sai dake wanka da sauran abubuwan da ya kamata ke zakina gwada mata, ni ya zanyi da ita¿ yaran can zasu koma wajan Dadda har mudawo.â€
Kirane ya shigo wayarsa yana dubawa ya ga Karime ce daga Cameron.
'Dagawa yay tare da sallama.
Karime ta amsa ta ce“Shamsu ya ake cikine har yanzu baku wuce Tchad bane?â€
Tanko ya ce“Gobe insha Allah zamu wuce, gatanan tana son gardama wai bazata jeba.â€
Karime ta ce“Na rasa meke damun Laraba wlh, ban ita.â€
Tanko ya bata wayar ta amsa tana kum'bure² ta gaisheta.
Karime bata amsa gaisuwar ba, ta ce“Laraba bakida hankali, yarinyar ba lafiya an turo kije ku tafi yaran sai zauna wajan Dadda amman kin ce bakya zuwa?â€
Laraba ta ce“Toh ni ko naje me zan mata sbd Allah? Banda takaici ya nemi kasheni.â€
Karime bata sake mgna ta katse kiran.
Tanko ya amshi wayar ya sake kiran Karime suka tattauna.
Gidan Dadda ya tafi daga can ta biyo shi tazo ta wanke Laraba tass ta 'dora da cewa“Wlh tallahi idan bakiyi shirin tafiya ba, ayau zan saka Shamsu ya yi aure sutafi da amaryar ta kular masa da 'yarsa.â€
Laraba hankalinta ya tashi ta fara kuka ta ce“Ai duk basu fahimceni bane ni bawai naqi zuwa bane, wlh ina baqin cikin zuwa naga halin da Ibtisam take ciki ne.â€
Ba Dadda Tanko ma sai da abin ya basa dariya.
Ai kuwa zuwa dare su Taslim suka harha'da kayansu sai gidan Dadda. washegari su kuma suka tafi, yaransu na kukan halin da yayarsu take ciki.

Inna zaune ta cika ta yi famm sbd takaicin abinda Ja'afar yay musu, ashe yarinyar na wajansa?
Deluwa ta ce“Hansatu ki daina damuwa komai da kika gani na faruwa adoron duniya rubutacce ne.â€
Baki ta ta'be ta ce.
“Wlh abin yaban haushi sosai kinsan matar can da baqin surutu wlh sai ta gauraye garin Tahoua duk girmansa, tana cewa 'danmu ya 'boye mata 'yarta har hakan ta faru da ita.â€
Deluwa ta ce“A'a da wuya kema don Allah kiyi shiru, Allah ya tsare gaba, ita kuma ya bata lfy...â€

*Gabon*
Aishatu zaune an ca'ba kwalliya ana jiran me gida, wanda ko jirginsu bai taso ba.
“Uwani!â€
Cikin girmamawa uwani ta iso ta zube gabanta tana fa'din.
“Ga ni hajiya.â€
Aishatu ta ce“Yauwa idan kin kammala jera komai ki 'dauki basket 'din nan kije Nura ya kaiki ki kaiwa Rabi'ah, kiyi sauri ki dawo fa!â€
Cikin girmamawa Uwani ta ce“Toh hajiya an gama.â€
Aishatu ta ce“Oh! My god! Nace ki daina cemin hajiyar nan aunty Aisha kawai ya isa.â€
Uwani ta amsa da
“Toh†ta miqe.
Aishatu ta kira Rabi'ah tana dariya ta ce“Toh ah kwa'daitu yanzu Uwani zata kawo miki, daga nuna miki abubuwan da na girkawa Ma'aruf kin rikice, sai na fa'da masa na ce kina 'kwalama gidansa.â€
Ta 'karashe mgnar cikin dariya.
Daga can Rabi'ah ta yatsina fuska tana hararan wayar, dakyar ta tattaro nutsuwa ta qaqalo murmushi ta ce“Ayyah! Ai na ha'da miyau ne gwara kawai ki ban nima naji da'dina.â€
Dariya sukayi atare.
Aishatu ta ce“Wai Rabi'ah kinga wasu ha'dadd'in lafaya da jakukuna and takalma na Tchad da Ma'aruf ya turo min hotonsu ya siyamin. Da dogayan riguna.â€
Rabi'ah sai da ta kusa ha'diyar zuciya tsabar baqin ciki, harda tari ya sarqeta.
Dakyar ya tsaya ta ce“Ƙawata pls zan kiraki anjima.â€
Ta katse kiran.
Miqewa tai tsaye ta fara zirganiya.
Number Ma'aruf ta kira bugu 'daya ya 'daga kiran.
Kuka ta sakar masa mai cike da kissa.
Ma'aruf wanda yake cikin jirgi su na dab da tasowa ya qyalqyale da dariya ya ce“Allah ya baki hkr idan nine bari zanji dake komin dare sai na zo munyi ido hu'du.â€
Ashagwa'be ta ce“Me kake so na ajiye maka pls gayamin na girka yanzu?â€
Cikin tsokanarsa ya ce“Duk abinda zuciyarki take so ki girka idan dai son gaskiya ake min abin zai kasance irin wanda nakeso ne.â€
Dariya tai ta ce“An gama Mon Cheri.â€
Wata number Ma'aruf ya kira bugu biyu aka 'daga.
Dariya ya busshe da ita tamkar ba acikin jirgi yake zauna ba, ya ce.
“Kayan suna dab da zuwa fa! Kuma masu ingancine...â€

Abie 2 killun sai ya karanta Kursiyu 'kafa 5 ya tofa ajikin dabino ya ba Ja'afar da Rahma suna ci idan sun cinye sai ya 'kone 'kwallon.
Abie zaune cikin hamshaqin falonsa, sanye da wani yadi marar nauyi milk da ganin 'dinkin kasan dan kasan na shan iskane agida akayisa.
Ya yi wani irin kyau Masha Allah, kwarjininsa da haibarsa kwance kan fuskarshi, wacce ya manna mata farin glass.
Laptop ne gabansa yana dannawa cup 'din coffee agefansa, yana kur'ba.
Fuskar shi bazaka ta'ba gane halin da yake ciki ba farin ciki ko akasin hakan.
Wayarsa ta 'dauki ringing ya kalli screen 'din wayar.

Kansa ya dafe cikin taushin murya ya furta.
“Ya Rabbi! Ba 'kasar da zan iya fita a wannan yanayin bayan Australia.â€
Wayar ya 'daga ya fara da sallama atausashe.
Chapter 35 · 0% Book details