← Book details Dattijon Arziki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 118

Sashe 59

Dattijon Arziki Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Acan Espagne misalin 'karfe 4 Rahma ta farka tana fizge² tana kuka tana kiran Abie.
Cikin bacci yake jin shasheqar kukanta tana kiransa tana karya mutu ya barta.
Firgigit Abie ya farka yana bu'de gajiyayyun idanunsa.
Riqeta yay gam yana matseta cikin jikinsa, ya tallabo kanta yana girgizawa ahakali yake kiranta.
“Baby Ummi! Oya bu'de idanunki ga Abienki tare kuke ban mutu ba.â€
'Kananun kyawawan idanunta wanda sukayi jajir ta bu'de jikinta na tsuma ta kalli fuskar Abie.
Hannunta ta sanye ta shafi fuskar shi taja dogon hacinsa ta 'dora yatsarta akan lips 'dinsa ta shafa bakinta na rawa ta ce.
“Ya Allah karka tasheni daga wannan mafarkin da nake kasa na dauwama ahaka Karna tashi ace da gaske jirgin su Abie ya fa'di...â€
Abie ya girgizata yana shafa fuskarata, idanunta ya gwala mata ya hura mata sansanyar iskar bakinsa ya manna bakinsa saman kunnenta ya hura mata da 'dan 'karfi ya kirata.
“Babyna please ki nutsu Abienki ne ba mafarki kike ba, ba jirgin Espagne ne ya fa'di ba, na Singapore ne oya bu'de idanunki kinji Baby.â€
Ya 'karashe mgnar yana riqe fuskarta da hannayensa.
Hawaye na kwaranya saman fuskarta ta mari kanta ta shafa fuskar Abie tana Jan gemunsa ta kai fuskarta dab da tashi tana sunsunawa 'kamshinsa ya cika mata hanci ahankali ta kirasa “Abie Rabin raina!â€
Cikin farin cikin ya amsa “Na'am Babyna ruhina.â€
Wani irin kukan da'di ta Saki tana qamqame Abie ta shige jikinsa kamar zata koma cikinsa ta rungumeshi sosai tana kuka iya 'karfinta.
Abie ya sauke 'katuwar ajiyar zuciya, yana fa'din.
“Ya Rabbi! Oh! Baby pls kiyi shiru nine ga ni kusanki ba abinda ya sameni, yi shirunki kinji?â€
Ya 'karashe mgnar yana matseta gam yana shafa bayanta bakinsa dab da kunnenta yana hura mata iska cikin 'kofar 'kunnenta.
Shiru tai tana sauke ajiyar zuciya tana sake maqaleshi ta tura kanta cikin 'kirjinsa tana shaqar daddan 'kamshinsa.
“Baby bari na ha'da miki tea ki sha OK? â€
Kai ta girgiza tana sake shigewa jikinsa.
Dogon gashinta ya tattare mata, ya 'daure da ribbon ya sumbaci tsakiyar kanta yana sake matseta jikinsa ya lullu'besu da lallausan bargo.
Sauka numfashinta yaji awuyansa ta kuma bacci cike da nutsuwa ta maqaleshi gam bata barinsa yay 'kwa'kwaran motsi kamar za'a amshe mata shi, ga shi anyi kiran sallah yana son ya yi sallar raka'atanil fajir.
Sai da ya bari baccinta yay nisa sosai ya samu ya janye jikinsa ya runguma mata pillow ya sumbaci goshinta ya kamo tafin hanunta ya shafa ya sumaci zoben hannunta yana murmushi yaja hancinta ya sauko ya shige toilet.

*Niger Tahoua*

Misalin 'karfe 8 na safe.
Inna na hura wuta tuyar waina, sai ga Dadda ita da Taslim, suna kwa'da sallama.
Inna Hansatu ta kallosu tana amsawa fuska ba yabo ba fallasa.
Tabarma ta shimfi'da musu, suka gaisa ta isa ta hura wuta.
Dadda ta ce“Hansatu dan Allah ko kinada labarin su Ja'afar tinda duk tare suke? Wlh hankalina ya tashi tin shekaran jiya Tanko ya ce zasu taso har yanzu bana samunsu awaya.â€
Inna ta gyara zamanta saman kujerata, tuyar wainarta, tana zuzuba mai acikin tandar.
“Eh Dadda jiya da dare suka iso Malam ya kira yana fa'damin, Masha Allah Ashe yarinya ta warke barka Allah tsare gaba...â€
Mahmoud ne ya shigo da sallama yana fa'din.
“Ya Ja'afar ga Innar kana jina?â€
Inna ta washe baki tana fa'din.
“Kai Masha Allah yaron albarka tinda safe ya nemi mahaifiyarsa su gaisa.â€
Ta amsa tana kara wayar akunnenta tare da sallama.
Lokacin Ja'afar suna cikin taxin baba Tsalha zasuje gidan Abie.
Amsawa yay yana gaisheta ya 'dora da cewa“Innata jiya muka sauka Alhmdllh! Ibtisam ta warke, inna umma deluwa aban ita mugaisa.â€
Inna ta washe baki ta ce“Masha Allah yaron albarka haka akeson 'da nagari Allah ya maka albarka, ina baaban naka? Deluwa ta yi sammakon zuwa asibiti bata dawo ba 'diyar 'kaninta aka riqe. Ga Dadda zauna kakar matarka tana neman labarinsu Tanko surukinka.â€
Dadda da Taslim suka kalli juna suna mamakin lamarin innar.
“Toh gata bari abata amshi Mahmoud. â€
Mahmoud ya amsa yabama dadda.
Sallama ta amsa suka gaisa cikin mutuntaka, tana tambayarsa su Ibtisam.
Ja'afar ya ce“Wlh layinsa tin jiya bai gansa ba amman suna lafiya yanzu idan na isa sai na basa wayana ya kiraku da numberki insha Allah.â€
Dadda ta masa godiya tai masa barka da arziqin samun lafiyar Ibtisam, sukayi sallama ya kashe wayar jin innar na 'kananun magana.
Dadda ta ce “Hansatou zamu tafi mun gode sosai Ashe sun dawo Tchad sai gida.â€
Ta ce “Eh insha Allah. â€
Waina zubin farko ta zube musu duka da miya, dadda ta yi godiya inna ta saka Maimou tuyar ta rakasu har 'kofa suka tafi da mamakinta akwai kirki akwai tsiya inna haka take.
Suna zuwa gida su Aydah suka baibayesu suna tambayar labarin Ibtisam da babansu.
Taslim ta ce“Kai Ramadan kamar kafimu son Baba da Anna da auntie Ibti akanmu.â€
Labari dadda ta basu sai lokacin hamkalin yaran ya kwanta sukaci wainar suna hirasu suna jiran kiran Tankon.

Acan kuwa Tchad.
Ja'afar yana zuwa bayan sun gaisa ya basa wayan ya kira Dadda, aka kira su Laraba har su sukayi hira, dadda jin murya Ibtisam harda kukanta dakyar ta lalla'bata tai shiru.
Ja'afar sai satar kallon Ibtisam yake lokacin da take wayan.
Ku'din ne da suka qare ta basa wayansa suka koma ciki, bayan sunyi breakfast Ibtisam aka koma bacci saman lafiyayyan bed.
Ja'afar kuwa can gidansu suka koma su Harisu sun ce bazasu je aiki ba, yau.
Falmata ce ta matsa ma Ja'afar tana son ganin Ibtisam, suna son zuwa ganinta ko za'a barsu su shiga gidan?
Dole ya rakasu.
Ibtisam sosai tai farin cikin ganinsu Falmata da suka tashi tafiya ta ce zata bisu da yamma sai ta dawo, Ja'afar bai hanata ba, murna ma yay zai samu damar ke'bewada ita.

A can Espagne
Abie dakyar ya samu ya tashi Rahma ya ha'da mata ruwan gumi tai wanka, tai sallah, ya bata tea ta sha ya bata mgani ta Sha. Dr ya dubata ta koma bacci wanda fafur taqi, sai jikin Abienta dole ya hkr ya mannata jikinsa ya lullu'beta ya zagaye hannayensa gadon bayanta tana baccinta anutse.
Misalin 11 Meerah ta kawo musu ha'daddan kayan breakfast ta gaishesa ya amsa tana tambayar me jiki ya ce “Da sauqi yauwa Meerah bari naje gida nayi wanka na canza kaya kafin ta tashi zo zauna kusanta.â€
Ahankali ya zameta daga jikinsa Meerah ta maye gurbinsa.
Ai kuwa ya zame jikinsa tana farkawa.
Yana dab da fita ta sanya masa kuka tana kiransa “Abie!â€
Tamkar 'karamar yarinya.
Da sauri ya dawo ya ce“Meerah sauko.â€
Meerah ta sauka ya zauna ya ware mata hannaywnsa tai saurin shigewa jikinsa tai luf, tana kuka ahankali.

Bayanta ya buga can 'kasa² yake mata mgna kusan kunnenta.
“Baby kiyi shiru ba abinda zai sameni insha Allah sai wanda Allah ya rubuta ba ganiba, taso kiyi breakfast pls kinji Babyna.â€
Shiru tai ta bar kukan ta yi lamo jikinsa tana saqalo hannayenta wuyansa, ta tsura masa kyawawan 'kananun idanunta wanda suke ciki da ruwan hawaye.
'Shima kallonta yake yana shafa dogon gashinta wanda rabi ya zubo kan fuskarta.
'Dan 'karamin bakinsa ya 'dora saman gazar² 'din gashin idanunta ya sumbata.
Idanunta ta rumtse tana kwa'be fuska.
“Pls baby ummina abinci ka'dan zakici.â€
Idanunta ta bu'de ahankali ta bu'de 'dan qaramin bakinta ta ce“Abienah kai kaci wani abun ne?â€
Hancinta yaja ya ce“Ta ya kina gadon asibiti kike tunanin zan iya sakawa cikina koda baqin ruwa ne babyna?â€
Zabura tai da 'dan sauran 'karfinta tana son miqewa ta ce“Abie pls kaci wani abun zanci nima wlh.â€
Cikin farin ciki ya kamata ta zauna sosai ya jingina mata pillow, ya sumbaceta agoshi ya shafi fuskarta, ya sauko ya nufi toilet ya fa'din.
“Meerah ha'da mana tea mai kauri sai ki zuba mana abinda kika kawo.â€
Meerah da gama shagala da kallonsu tai firgigit ta amsa da “Toh Yalla'bai.â€
Ta shiga kiciniyar ha'da masu tea.
Abie ya shiga toilet.
'Kofar aka turo da sallama Anee na gaba Rafeek na baya wanda hango Rahma zaune ta amsa kyau matuqa sanye take da wata Riga da skirt Ash kala kayan Espagane , marar kwaramniya sun 'dan kameta, wanda ya bayyana kyawun surata, kanta bu'de gashinta ya baje gefen fuskarta, tayi wani irin kyau, 'kafarta zuwa 'kwabrinta waje sarqar 'kafarta sai walwala take. Hakan ya saka
Rafeek yay saurin wuce Anee, ya nufi wajan Rahma fuskarsa na nuna tsantsar damuwarsa, masoyiyarsa gadon asibiti.
Rahma ganin Rafeek amugun tsorace ta zaro kyawawan 'kananun idanunta waje, tana kallon 'kofar toilet....

_💃ðŸ»'Yar Ajin Ma Sha Allah🥰_

_*🤲ðŸ¼Ya Allah ka jiÆ™anmu kayi mana rahama badan halinmu ba.ðŸ™ðŸ¼*_
3/12/22, 00:27 - Buhainat: ```D A```

```59&60```

_*My Sisters Don Allah Don Darajar Annabi Karki Karanta Idan Baki Biya Ba, Na Ku'dine Idan Kinga Yana Yawo Na Satane Ga Hanyar Da Za Ki Samu Naki Akan.😟👉ðŸ¼300N +22796515805*_
Chapter 59 · 0% Book details