← Book details Dattijon Arziki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 100 OF 118

Sashe 100

Dattijon Arziki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kai tsaye Aishatu tana fita ta hau taxi ta tafi gidansu Rabi'ah dan bata yarda da ita ba, tana gudun ta zubar da cikin.

Rabi'ah zaune tsakiyar falonsu qasa tana shan iska, sanye da doguwar Riga atamfa, duk ta rame sai uban fari tai cikin ba qaramin laulayi take sakata ba.
Hannunta riqe da cup tana shan ruwan tsamiya.
Aishatu ta shigo gidan da sallama.
Maman Rabi'ah ta amsa tana shanyar kayan da almajirinsu ya wanke ya bari igiyar ta cika.
“Ah Aishatu kece da rana haka?â€
Aishatu ta rusuna ta gaisheta tana ajiye baqar ledar hannunta, ta amshi shanyar tanayi.
“Wlh nice mama ina Rabi'ah kuwa?â€
“Tana ciki kawo nayi dan Allah Aisha ki bari kema ba lafiyar kirki gareki ba.â€
A'a mama zanyi.â€
Bayan ta qarasa ta Mata jagora suka shiga d'akin.
Rabi'ah jin murya Aishatu ya saka duk ta diririce.
Dakyar ta amsa sallamar tsabar kunyarta.
Aishatu ta zauna kusan Rabi'ah ta ajiye ledar ta ce“Rabi'ah barka da rana ya jikin?â€
Rabi'ah ta fashe da kuka ta rungume Aishatu tana kuka mai cin rai ayanzu arayuwarta ba abinda tafi so irin mutuwa duk da tasan bata tanadi abinda za'ace taso mutuwa ayanzu ba.

Aishatu ta janye ta matsa gefe tana tab'e baki, ta ce“Uhmm! Nazo na sake garga'dinki ne wlh karki kuskura ki zubar da cikin nan, yadda bakiji kunyar abinda kukayi ba har Allah ya Baku kyauta toh idan dai Allah ya yarda sai kun haifesa ya taka doron k'asa, sbd bakusan me zai zama ba nan gaba ko ta zama ba, dan haka kuji tsoron Allah karki zubar da cikin nan.â€
Rabi'ah ta ce“Insha Allahu dan Allah Aisha ki yafemin.â€
Baki Aishatu ta tab'e ta ce“Wlh da ban yafe muku ba Sam bazaku tab'a sake ganina arayiwarku ba, ni na tafi Allah ya qara lafiya.â€
Rabi'ah kunya ta hanata rakiya tana kallon Aishatu har ta fita.
Sallama ta ma Maman Rabi'ah ta tafi.
Tana fita Rabi'ah ta fasa kuka me cin rai tana qara nadama abin da tayi, tabbas ta yarda son zuciya b'acinta.

★★★
Rayyana zaune ta yi tagumi tana tuna rayuwarta agidan Abie.
Hawaye ya silalo mata tai saurin gogewa ta mai fad'in.
“Astagfirullah wa'atubu ilaik, ya Allah ka ciremin son abinda yamin nisa na har abadan.â€
Auntie Saro da take shigowa d'akin ta amsa da.
“Ameen ya Rabbi, wlh Raiyana ki fitar da Abdulmajid aranki ki fawwalawa Allah komai ki Saki jikinki ki mori 'kuruciyarki dan wlh har yanzu da sauranki, karki bari tunanin abinda bazaki samuba ya nakasaki, fa! Ki Saki jikinki kinga ba iddah akanki ki dinga daukan wanka kawai idan sabga ta samu muna fita insha Allahu za ki samu miji, amman idan kinyi tuba domin Allah. â€
Rayyana ta share hawayen da kuma silalowa saman fuskarta, ta sauke ajiyar zuciyata, ta kalli Saro ta ce“Uhmm! Bazaki ganeb wlh son so nake ma Abie, amman ba komai zanci gaba da addu'a, Allah ya ban Wanda zai soni.â€
Very good my sister, insha Allahu yanzu ki tashi muje tsakar gida musha iskar Allah ga Badiya qawata can tazo karki sake taga alamaun damuwa a fuskarki.â€
Rayyana ta miqe tai murmushi ta ce“Kai Auntie Saro bakida dama dole dai so kike kiga na sake koh?â€
Hararata tai ta ce“Eh mana.â€
Aikuwa Badiya tin daga nesa take kallon Rayyana Sam bataga alamar damuwa ba sai 'yar Rama da tayi.
Cikin fara'a Rayyana ta ce“Oyoyo Auntie Badiya barka da zuwa.â€
Badiya tai murmushi ta amsa.
“Yawwa Rayyana wlh naji dad'in ganinki zuciyarki fess mutuwar aure ba kanki farau ba, sai dai fa samun mini kaar takine ya sakeka haukama kayi wallahi.â€
Auntie Saro ta tsiyaya Mata lemo tana zama ta ce“Ah toh gayamata dai kawai ta manta baya ta Kama abinda yake gabanta duk Allah ya zab'a mana abinda yafi alkahiri...â€

★★★
Masha Allah yau su Ja'afar suka iso Tchad lfy, kwanan su biyu ahanya.
Kai tsaye Abie ya tura direba aka 'daukosu a tasha aka nufi gidansu 'dan madedeci mai shegen kyau, tsaf nacin amarci, ya zuba musu komai na anfanin abinci, motarsa ta wajan Ma'aruf na 'yar rumfar ajiye motar gidan.
Ja'afar zaune kusan Ibtisam, sunyi muguwar gajiya, dukkansu jikinsu ciwo yake musu.
Ja'afar ya shafi fuskarta ya ce“Beby gajiya ko?
Idanunta ta lumshe tana kwantar da kanta saman kafad'arsa, ta ce“Wlh kuwa Mon amour ko ina ciwo jikina yake min.â€
“Sorry bari na duba naga toilet na ha'damana ruwan wanka kiyi wanka ki kwanta ni fita ma zanyi.â€
Ibtisam ta janye jikinta tana miqewa tsaye ta ce“Muje ka nunamin sai na ha'dama toh idan ka fita sai nayi.â€
Murmushi yay ya ce“Ai wlh yau ba Inda za ki sai na fanshe gajiyata ai na raga miki.â€
K'walla ta taru mata a idanunta ta ce“Dan Allah ka bari koda bayan wata 'dayane nida bana sallah ma tin jiya...â€
Hannunta ya kamata ya ce“Beby kalli wannan gida wai namune Allah kenan mai yadda yaso alokacin da yaso Allah ya kare Abie da dukkan family's nasa albarkar Annabin tsira.â€
Ibtisma ta ce“ameen mon amour.â€
Bedroom ne guda biyu ajere kowace akwai gado madedeci tsaf masha Allah.
Ibtisam ta ce“Mon amour gsky bawan Allah nan ya gama mana komai wai 'dakin ma kowa da nashi...â€
Hannunta yaja suka shiga bathroom, ya ce“Eh fa na zab'i wannan ha'damin ruwa ki tafi naki ko zamu zauna tare?â€
Kunya taji ta ha'da masa ruwan gumi sbd zaman da tai gidan Abie da Australia ta koyi abubuwan wayewa.

Bayan ya yi wanka ya shirya ya shiga motarsa ya nufi gidan Abie, dakyar Ibtisam ta barsa ganin ya koma Mata Ja'afar d'inta dan ta ce tsoro takeji, dan da faeko ta d'auka wasa yake ba Inda zaije, ganin hakan yasa ya lallab'ata ya fice.
Wanka tai ta nufi 'dakinta ta kwanta kasancewar tin jiya bata sallah sai bacci.
Can kuwa Ja'afar da Abie sun keb'e bayan sun gaisa, Ja'afar ya basa dukkan takardun makarantarsa, ya duba, daga nan suka nufi company'nisa na sarqoqin zamani masu masifar kyau zaka rantse gold ne, sam ba gold bane ana sarrafasu ne dan masu 'karmin k'arfi amman ina har masu 'karfin rububin siya sukeyi.
Wanda hakan ya saka ba qaramin ku'di ake samu wajan ba, suna isa wajan ya mayar da Ja'afar manager. Ja'afar kasa mgna yay sai hawaye kawai, na farin ciki nan take ya Kira gida yana sanarwa da Mal Adamu Wanda shima ya cika da farin cikin lamarin.

Bayan kwanaki.
Yau ta kama Alhamis ya zama auren Abie da Rahma sauran kwana 3, fa'din kyawun da Rahma ta yi da yadda suka maida mata, jikinta wani matsiyacin laushi, duk da daman jikinta laushi kamar auduga tofa yanzu abin yaci uban na baya, wani irin tsumi Jaddatu da Zainabu suke mata ga na wajan Hanan da Haleesa, abin ba'a mgna ga shegen 'kamshin turaren tsumi da na jikin da ya gama kamata ko cup 'din da tasha ruwa ko lemo ka d'auka masifar k'amshinta yake, matsalarta biyu rashin ganin Abie da jin muryasa sai yadda taga tana tsiyaya yanzu kam pant baya mata pad take sakawa sabida zuba take sosai, da farko kuka ta fara duk ta gigice, tama Hanan da Haleesa bayanin abinda yake faruwa da ita, Hanan ta ci dariya sosai ta yarda Rahma yarinya ce, zaunar da ita sukayi sukayi mata bayani yadda zata gane sai lokacin ta daina kukan.

Kowa yasan bikin 'yan gata ake sabida yadda aka qara k'awata gidan masha Allah duk wani ma'aikaci na gidan Kama daga secretary's masu wanki mota na kaya direbobi masu ba flowers ruwa mai kulawa da tsuntsayen gidan tin daga kan baru 'kwa'kwa jimuna talatalo aku 'dawisu. Kai kowa na gidan an musu 'dinkunansu na kece raini Wanda zasu saka ranan biki Latifa da Ummu Adnan, ba'a cewa komai Uwa uba Meerah da take jansin su.

Rahma zaune cikin bedroom 'din Jaddatu, Meerah na kusanta zaune tana gyara Mata faratanta.
Rahma ta ce“Auntie Meerah kiyi hkr karkiji shiru akan mgnar da na miki har yanzu bamu samu lokaci ni da Abie ba zan masa bayanin insha Allahu kinji? But ke dai ki kasance cikin shiri insha Allah, kin kusa shigowa cikin family's nawa.â€
Meerah kunya taji sosai sai ta qara qasa da kanta, ta ce“Haba! Rahma ba komai ai daman har a gama biki ki nutsu.â€
Rahma tai murmushi ta ce“Uhmm! Ba haka ba kawai Abien nawa ne ya yi tsada, wlh nafi 'karfin kwana 11 ban gansa ba da ko giftawarsa.â€
Meerah ta ce hakan shine daidai ai.â€
Murmushi tai ta d'aga kanta tana kallon qaton hotonsa manne a bangon d'akin Jaddatu.

Abie kwance saman makeken gadonsa daga shi sai singilet da wando iya guiwa, Ac na ka'dasa ta ko ina, waya manne kunnensa, murmushi d'auke kan kyakkyawar fuskarshi mgna yake, shi kansa ya qara wani irin kyau sbd ya fasa fita kwana biyu hutawa yake abinsa, shima ya b'oyewa kowa ganinsa, sai 'yan gidansu, auma basa wani ganinsa.
“Ok Nasir ba damuwa idan kana ganin zuba hannun jarin companyn mai nasara bazai zama matsalaba za'a zuba but yanzu banda lokaci ka bari har na nutsu nan da kwana 3 jirgina zai 'daga Turkey (Istanbul) zan yada zango, daga chan zan shiga zagayen qasashe, but zan nemaka naji yadda za'ayi Ok?â€
Alhaji Nasir daga chan yay murmushi ya ce“Tabbb zan dai saurara idan ka gama cin amarcin zan waiwayeka mu dai atemaka mana shigar da kud'inka companyn mai nasara akwai qaruwa sosai wallahi sbd kowa rububin ka zuba dukiyarka companynsa suke, sun san komai naka domin ilahi kakeyi.â€
Abie ya miqe zaune yana shafa kwantacciyar sumar kansa mai laushi tana fitar da k'amshi.
“Ok..OK! Nasir zamuyi mgna ka bari na nutsu insha Allahu.â€
Sallama sukayi, yana ajiye wayan ya miqe ya sauko daga bed domain shiga bathroom kiran Ja'afar ya shigo wayarsa , ganin Ja'afar ne ya sanya ya dawo ya 'daga kiran.
“Hello Ja'afar kana ina?â€
Cikin girmamawa Ja'afar ya ce“Abie ina company don Allah idan da dama kazo yanzu...â€
Abie ya ce“Ja'afar ba nace maka ba na ajiye komai sai na dawo daga tafiya tsawon wata 3 ba? na jiye komai na amince ma kaida matemakinka Sadi da Kamal komai na wannan company kuyi komai amana na baku Okay?â€
Ja'afar ya dafe goshinsa yana shirin mgna yaji an fizge wayar hannunsa.........!

Whtspp number😊
_*+22796515805*_
Chapter 100 · 0% Book details