← Book details Dattijon Arziki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 107 OF 118

Sashe 107

Dattijon Arziki Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Rahma tai murmushi ta ce“Ameen ya Rabb Shukran Habibty, ya oga da kowa?â€
Ibtisam ta ce“Komai lafiya Auntie. â€
“Haleesa ta Kama hannun Rahma ta ce“Muje za'a sake wanka turaren tsumi, jirginku k'arfe 5 na yamma zai tashi.â€
Rahma ta kalleta jikinta asanyaye idanunt sun tara ruwa ta langwab'ar da kanta ta ce“Toh amman ko Ummiterh ce zamuje da ita ko?â€
Haleesa ta bushe da dariya ta ce“Uhm ba shakka Babyn Abie ai harni ma.â€
Hanan ta ce“Ai kam tinda Abien na mahaukata ne, ai duk zamuje kuje dai agyaraki.â€
Rahma hawaye suka taru a idanunta ta sadda kanta qasa ta miqe Haleesa ta kamata suka nufi hanyar bedroom.
Ibtisam da kallon tausayi ta bita, batasan daliliba.

Idan nace zan tsaya na zayyane muku irin yadda wajan gidan Abie ya cika da filin gidan maza da Mata 'yan tayasu murna aure, toh zan kwana ina Baku labarin, awaje 'daya, Masha Allah almajirai ma sunyi son barka da wannan aure, sbd sunci sun Sha an musu rabon takalma wasu riguna mai d'uake da hoton Abie da Rahma, 'yan jaradu sunyi d'aukar rahoto sosai, sun samu Abie Wanda shine ya bada umarnin abarsu idan sun buqaci ganinsa ya basu had'inkai sosai, wajan basu taqaitaccan tarihinsu shi da Rahma Wanda ya tsakuro musu abubjwan da suka kacen baya, Wanda jin labarin ya girgiza 'yan jaridan sosai suka masa fatan alkahairi.
Abie2 Uban amarya shima sai da Abie ya saka yama 'yan jarida 'yan bayanai.
Misalin 'k'arfe 4 aka gama shirya Rahma, irin kyawun da tai bakina bazai fad'u dan k'amshinta kawai ya isa mutum yasan wannan amaryar fa ta musamman ce.
Wata irin doguwar riga ce golden mai shegen kyau taji adon stones aka saka mata haka mayafin kalar rigar takalmi jaka sarqa awarwaro komai na jikinta golden ne, dole idan ka kalleta ka sake kallonta, mai gyaran gashi ta mata wani irin coiffure, da dogon gashinta, abun ba'a mgna.

Tinda Abie ya gama shirinsa aka shigar da musu kayansu mota, yama Jaddatu da 'yan uwansa sallama ya koma wajan Abokanansa sukayi sallama duk suka tafi yaje wajan Abie2 yana jiran lokacin tafiyarsu.

Rungume take jikin Jaddatu, tana kuka Jaddatu ma kujan take kamar bazasu sake ha'duwaba.
Zainabu tace“Rahmatu ki saketa don Allah akaita wajan babanta ya Mata nasiha, kukan ya isa haka ba fa rabuwa kukayi, gida d'aya zaku rayu, matiqar suna qasar.â€
Jaddatu ta jinjina kanta tana faice majina, ta ce“Takwara don Allah ki zauna da 'dan uwanki lafiya kiyi masa biyayya kunsan halin junanku ke rainonsa ce dan haka ni bazan gayamiki halinsa ba, kinsani Ku riqe juna amana don Allah.â€
Rahma ta sadda kanta tana shasheqar kuka, sosai taji kewar iyayyanta Wanda bata sansu ba sai a hoto.
Zainabu ma nsihar ta ma Rahma.
dinga binsu d'aya bayan d'aya tana rungumesu tana kuka.
Ibtisam kallunsu kawai take tana qara jinjinawa soyayyar larabawa tafi tasu qarfi nesa ba kusaba.
Bata ankareba taji Rahma ta rungumeta ta ce“Na barki lafiya Ibtisam saduwar alkahairi.â€
Tana gama mgnar ta sake ta rungume Meerah tana kuka ta ce“Don Allah Meerah ki kulamin da Abie2 karki barsa yayi kewar rashina.â€
Meerah ma kuka take ta ce“Insha Allahu na miki alqawali Allah ya kaiku lafiya.â€
Rahma ta jinjina kanta, ta beqawa Ummu Adnan hannun da Latifa ta ce“Saduwar alkahir.â€

Kai tsaye wajan Abie 2 aka kaita.
Jikinsa ta fad'a tana kuka.
Abie2 yay gyara murya yana buga bayanta, ya ce“Haba 'diyar albarka! Kiyi hkr toh meyw na rigimar? Abienki ne fa! Yanzu dai kiyi hkr karki tayarmin da hankali, ko kinason nima nayi kuka baby? â€
Rahma ta had'iye kukan ta girgiza kanta.
Hawayen fuskarta ya goge mata ya ce“Yawwa d'iyar albarka, abinda nakeso dake kiyiwa mijinki biyayyar ki bisa sau da qafa, shi 'din duk duniya yafi kowa sonki, dan haka bakida kamarsa, fatana Allah ya Baku zaman lafiya, bana jin Abdulmajid akanki tabbas idan wata fitina ta fito toh daga gareki ne, dan haka kije kibi mijinki aljannarki na qarqashin qafafunsa, Allah ya saukeku lafiya sai munyi waya.â€
Abie2 Ya qarashe mgnar yana b'oye hawayen da yake neman zubo masa, tuna iyayansa da 'yan uwansa yanzu ace duk duniya Rahma kawai ta ragemasa.
Rahma cikin kuka ta ce“Abie2 muje toh airport idan mun tafi sai ka dawo.â€
Murmushi yay ya ce“Oh! Baby rigima toh shikenan muje Hanan kuje mota ganinan zan sauya kaya.â€

Hanan tai dariya suka kamata suka fice.

Abie na hakimce bayan motar cikin wata irin rantsatsiyar shiga ta kece raini, kayan jikinsa ban ma San kayan wata qasa zan kirasaba tsabar kyau d'insu suma kalar golden ne.
Wani fitinannan k'amshi take.
Bai ankareba yaji an bu'de motar Ana shigar da Rahma.
Tsabar masifar k'amshinta da ya shaqa yasa ya lumshe idanunsa kansa qasa yana danna casbin da yake maqale a yatsarsa.
Haleesa da Ummiterh and Hanan sukace “Toh sauka lafiya ubangiji yasa adawo mana da guzurin k'asashen da bamusan Inda za'a bada ajiyar ba.â€
Suka sheqe da dariya suna rufe motar basu jira me Abie zai d'ago ya ce ba.
Rahma tai saurin kallon Abie ta ce“Abie kar a tafi Abie2 na zuwa rakiya airport. â€
Sai da ta kai qarshen mgnar Abie ya 'dago da kansa ya zuba mata manyan idanunsa, yana Mata wani irin kallon so and k'auna mai tsanani ji yake kamar ya ha'diyeta.
Dakyar ya samu kuzarin gyara zamansa yana sauke ajiyar zuciya, ya kamo hannunta mai 'kunshi ya ce“Allah ko? Baby?â€
Kai ta 'daga tana kukan.
“Ok..Ok! Yi shiru zai iskomu Abraham Oya tada motar muje lokaci ya qure.â€
Ya qarashe mgnar ya shigar da ita jikinsa, Wanda suka sauke wata irin ajiyar zuciya atare.
Bayanta yake bugawa ahankali ya kasa mgna, idanunsa a lumshe, yanajin yadda zuciyar Rahma ke bugawa, wani k'ayataccan murmushi yake Saki.
Motoci guda ukune suka fice daga gidan zuwa rakiya airport.

Suna isa airport ba'a wuce 17 minutes ba jirginsu ya cira sama, ya lula sai fatan sauka lafiya.

Tafiya ce me dogon zango Abie da Babynsa sukayi acikin jirgi, sbd jirgin ya ratsa wata qasar kafin wuce k'asar Turkey,Abie yana maqale da abarsa qwaqwaran motsi tai ya ce mata “Sannu me kike so Babyna?“
Sai wajejan Asubah jirginsu ya diro airport d'insu me sunan, (Atatürk Internationaux) Wanda yake
k'asar Turkey cikin garin (Istanbul.)
Rahma tsabar gajiyar zama qafafunta sun fara kumbura.
Jirgin na tsayawa Abie ya sanyawa Rahma jibgegiyar rigar sanyi sanin sanyin Istanbul.
Anotse suke saukewa daga cikin jirgin Rahma ta fara bin airpor 'din da kallo wani irin shegen sanyi taji ya fara ratsata duk ta gaji, ashagwab'e ta ce“Abie qafafuna ciwo wollahi.â€
Gefen fuskarta ya shafa, cikin rad'a ya ce.
“Nasani My baby ina ankare yi hkr mu isa masaukin mu zan gasa miki sai na miki massage Ok?â€
Kanta ta d'aga tana jin sanyin k'asar na ratsata sosai, duk da ta Saba shiga k'asashen duniya amman sanyin k'asar nan na daban ne.
Bayan an gama duk abinda zasuyi na shigowa k'asar da ba takuba a Abie ya kwashe kayansu ya zuba cikin abin turawa suka nufi wajan tarbar baqi.
Wani matashin balarabe yazo tarbarsu, daga nesa Abie ya gane shine sabida sunansu b'aro b'aro.
Takardar da take riqe ahannunsa da sunan Abie and Rahma ajikinta yasa Abie ya isa wajan da sallama, saurayin ya amsa yana sakin fuska ya 'daga takarda wacce aka rubuta WELCOME.
Abie yana riqe da hannun Rahma ya ce“Thank you.â€
Kayan naso ya amsa yana turawa ya musu jagora zuwa wajan mota.
Wata irin mota mai masifar kyau, ya bu'de musu baya suka shige ya rufe, ya bu'de booth ya shigar da kayan ya zagaya ya shiga tayar da motar ya sulale yabar airport, cikin nutsuwa yake driving.........

Whtspp number😊
_*+22796515805*_

_*🤲ðŸ¼Ya Allah ka jiÆ™anmu kayi mana rahama badan halinmu ba.ðŸ™ðŸ¼*_
5/18/22, 10:58 - Buhainat: ```D A```

```100```

_Rahmerh Ladingo😉_
Chapter 107 · 0% Book details