← Book details Dattijon Arziki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 118

Sashe 15

Dattijon Arziki Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

*Niger*
Laraba kamar yadda tai al'kawali bayan magarib, taje da kanta ta siyo musu gasashen nama.
Ibtisam zaune su Aydah anata cin gasashen nama, sai surutu suke, ita kam tana gefe juyin duniya Ibtisam ta'ki cin naman. Taslim ta ce“Wai aunty Ibtisam meyasa bazaki ci ba?â€
Laraba ta ce“Dan ubanta karta ci, shegiya me mugun hali, kuma wlh aure anyi an gama, sai dai idan bai ce abasa ba. Tafi son shegen ba'kaâ…” can, matsiyaci bai da taro bare sisi, satinsa nawa baya garin? Uwar me ya ta'ba aiko miki?â€
Ibtisam ta saki kuka ta mi'ke hankalinta mugun tashe, ta fice aguje ta bar gidan.
“Ibtisam ki dawo wlh zan wulaqanceki.â€
Ibtisam kai tsaye keke napep ta tare ta shiga sai gidansu Ja'afar, domin ta yi mgna da Mahmoud, tasan shi ka'dai zai iya temakon ta.
Dab da kwanar gidan ta sallami me napep cikin ku'din da Ja'afar ya bar mata.
Tana tafe sai ga motar Alhj Jamilu kamar an tunku'do shi. Gabanta ya sha da motar.
Dole ta tsaya, ta ri'ke 'kugu tana jiransa ya fito.
Baki ya washe ya fito da kwalin waya ya ce“Amman me kike nema nan unguwar? Kinga saqonki nazo amsa, sai 'dazu wayoyin su ka iso.â€
Tsaki taja ta ce“Ban bu'kata don girman Allah Baba ka fita daga sabgata, karka rabani da masoyina.
“Naji amshi wayan zamuyi mgna.â€
“Wlh bana so.â€
Ta qarashe mgnar tana barin wajan.
Da kallo ya bita yana lashe 'katon wargajejan bakinsa ya ce“Allah ya kai damo ga harawa.... Aure ni dake ba fashi ke matar manyace.â€
Ibtisam a 'kofar gidan ta la'be ta kasa shiga sai share hawaye take.
Cikin ikon Allah Mahmoud ya fito yana sauraron waqa, da jarkar mai ahannunsa alamun Inna mai waina ta aikesa amsar mai na wainar gobe kanti.
Sam bai lura da itaba, sai da ta kirasa.
“Mahmoud! â€
Juyowa yay ya na waige-waige.
â€Lah! Ibtisam! Ke ce? Amman kika qi shiga?â€
“Wlh Mahmoud tsoron Inna nakeji karta koreni.â€
Dariya yay ya ce“Mutum da surukarsa, muje ciki toh ki zauna na siyo mata mai nazo.â€
Cike da tsoro ta ce.
“A'a muje tare daga can sai na wuce.â€
Mahmoud ya gane mgna take son yi da yayansa.
“Ok muje.â€
Ya fa'da ya na lalubo number Ja'afar ya danna masa Kira, su na ci gaba da tafiya.
Can kuwa Tchad.
Unguwar clemate
Wani gida ne mai kyau babu laifi ya ha'du, kana ganin gidan kasan me shi ya tara ko ba yawa.
Baba Tsalha bayan sun shiga gidan suna tsaye jiran Lawi me gadi ya kirawo mutumin, dan daman shine ya saka ya masa cigiya.
Ja'afar kasan 'kasa yana danna wayarsa ko wasa bai tsaya kalle² gidan ba.
Wayar hannunsa ta 'dauki ringing.
Ja'afar ganin number Mahmoud ya 'dan tsotsi ba'kin lips 'dinsa na qasa mai taushi yay picking call 'din ya kai wayar kunnensa tare da sallama.
Daga can Mahmoud ya ce“Ya Ja'afar ka kirana Ibtisam ce gatanan.â€
Ja'afar ya lumshe manyan shayayyun idanunsa ya ce“Ok ok...ok!â€
Ya datse kiran ya duba yaga sauran ku'din zasu masa hira 3 minutes.
Kira yay kai tsaye.
Mahmoud ya 'daga kiran ya be'kama Ibtisam ya ce“Toh je jikin bishiyar can ku zanta bari na hanzarta na amso mai nazo.â€
Cikin farin ciki ta 'daga kanta, ta nufi gindin bishiyar dogon yaro.
Sallama tai masa cikin sanyin murya.
Daga can Ja'afar ya amsa, yana mi'kewa ya koma jikin wata flowers ya kira.
“Mon cÅ“ur tu me manque beaucoup , fatan yau lfy ta b'oye min ke?â€
Ibtisam wani irin magana 'disun son Ja'afar taji ya kuma fizgarta, taji ruwa da iska bazata iya rayuwa babu Ja'afar ba.
Ta fashe da kuka ta kirasa.
“Mon amour! Don Allah kayi wani abu kar arabani da kai...â€
Kuka yaci 'karfinta ta kasa 'karasa mgnar.
Ja'afar ya dafe goshinsa, ya ce.
“Subahanallahi! Baby menene? Kiyi shiru wlh har 'kasan zuciyata nakejin kukan ki, nutsu kima Sahibinki bayani, ku'din basuda yawa karsu 'kare, muahhhh! Ina sonki babu abinda zai rabamu sai mutuwa.â€
Ibtisam tai luf abinta ta lumshe idanunta tana sauraron dadda'dar muryashi, taja dogon numfashi ta narkar da murya ta shagwa'be ta ce.
“Mon amour yo ba wani tsoho bane d'azu....â€
Tsaf ta masa bayanin komai bata 'boye masa, har naman da aka siyo da ku'din ta'ki ci, da tareta da yay yanzu ya bata waya ta'ki amsa.
Ja'afar ransa ya yi masifar 'baci zuciyarsa ta harzu'ka matuk'a manyan idanunsa suka riki'de lokaci d'aya sukayi jajir jijiyoyin kansa suka fito ra'dau-ra'dau. Mur'da'ddan jikinsa ya soma rawa, ya kasa mgna sai bakinsa da yake motsawa alamar sunan Allah yake anbato.
Ibtisam cikin kunnuwanta banda hucin numfashinsa batajin komai sai ajiyar zuciya ajre².
Kuka ta saki ta kirasa.
“Mon amour!â€
Dakyar ya motsa labb'ansa ya amsa.
“Na'am Baby mon cÅ“ur, maza yi shirunki na sanki nasan bazaki gujeni ba sabida ku'di saïi dai ni ma bazan zugaki ba ki bijirewa iyayan ki, ina Baba?â€
Ibtisam ta ce“Ya tafi Bouza sai gobe zai dawo don Allah mon amour ka kirasa kaji.â€
“Ok baby karki damu yanzu ni nutsu insha Allahu muna tare, kinga ku'din sun 'kare gobe zamuyi mgna, yanzu Mahmoud ya rakaki har 'kofar...â€
Ku'din suka 'kare bai ida mgna ba.
Kansa ya dafe, jarumta yake yasan wannan abun babban abune, amman tuna mahaifin Ibtisam atsaye yake sai yaji sanyi aransa.
Dai-dai lokacin da Ja'afar ya dawo ya zauna.
Ma'aruf ya fito daga falon, sanye yake da 3 quarter sai wata jibgegiyar rigar sanyi mai hula, ya yi kyau sai baza 'kamshi yake, yana tafe yana waya.
“Haba! Aishatuna kin fiye rigima, da mitar tsiya kullun cikin waya muke. sati 3 kawai zanyi na dawo, naga lafiyar ki da ta baby na koma. Hope kina lfy?â€
Daga can Aishatu ta turo baki gaba ta ce“Uhmm! Da dama dai, ya tarin 'yan mata da aka tara acan?â€
Ma'aruf ya yi tsaki ya ce“Ban saniba masifafiya kawai, shi kika iya.â€
'Kitt ya tsinke kiran.
Yana tafiya cike da gadara, yana bubbu'de hanci. Kasancewarsa mutum mai shegiyar gadara.
Tin daga nesa yabi su Ja'afar da kallo. Gabansa yay mummunar fa'duwa, sabida yanayinsa kamar yaron da ya ta'ba marinsa shekaru biyu baya,jinsa da ganinsa suka 'dauke na wani lokaci Tahoua,ya zubamasa ruwan kwata me tsami, mafarin da ya haramta masa shiga niger. ta'be baki yay aransa yana fa'din ai kuwa da ya shiga masifa ramuwa mai zafi zan masa.â€
sai da ya kusa yaga Ja'afar ingarman namiji tsayayye mai sufar 'karfafa, ajiyar zuciya ya sauke aransa ya ce“Yes! Wannan shine na goma kuma shine zai Iya. Kuma wlh shine ya mareni ramuwa har gida. Wannan Irin mazan nake son su na driving na, da kuma 'dayan aiki tabbas wannan shi zai iya fito min da.....†wani shu'umin murmushi ya saki, ya ce“Zan sakar maka masu gidan rana, sai na gama business 'dina da kai na rama abinda kamin.
Bakisan d'auke da sallama ya iso wajansu, yana bek'awa Baba Tsalha hannu.
Ja'afar ya amsa sallamar. Lokacin su ka ha'da idanu. Ja'afar Sam bazai gane Ma'aruf ba, sbd ranan bada fuskarsa ta asali bane.
Ma'aruf ya tsorata da kyan Ja'afar, sai yaji ya raina kansa agaban Yaron, sbd abaya ransa a'bace bai ga kyansa ba.
Gaisawa sukayi, Lawi ya ce“Yalla'bai ga su sai ku dai-
dai-ta.â€
Ma'aruf ya ce“Ok Ngd gobe da safe sai kazo, duk Inda zanje kaine zaka kaini sai aike idan inada, amman kafin direbana ya dawo, maybe har zanje Gabon na dawo Ok? Sannan awuni kakeson ku'dinka ko sati? Ba lallai ka kai wata ba?â€
Ja'afar ganin yadda Ma'aruf yake komai agadarance, sai kace wani ubansa ya saka ya ce“A'a barsa asatin ko kuma har wancan ya dawo.†ya na fa'din haka yaja bakinsa yay gum, shi damuwarsa ma ta ishesa.
Ma'aruf aransa ya ce“Tabb yaron nan 'dan jin kaine.â€
ya ka'da kafa'da ya ce“Ok ba damuwa kazo da sassafe.â€
Ja'afar ya ce“Ok.â€

Ahanya komawane Ja'afar ya ce“Anya Baba wannan mutumin zan iya aiki 'kasansa?â€
Dariya Baba ya yi ya ce“Haba! Yarona ai tinda ka baro 'kasarka ka shigo wata 'kasa domin neman halak 'dinka toh fa sai kakai zuciya nesa, kayi hkr ka 'kas'kantar da kanka har ka samu abinda kake so, kaima kaje kaci gashin kanka.â€
Ja'afar ya ce“Insha Allahu Baba Ngd. â€
Su na zuwa gida yama su Harisu bayani komai, suka tayasa murna. Lokacin ya saka Kati ya gwada kiran layin Tanko mahaifin Ibtisam amman baya samunsa, sai Mahmoud 'kaninsa shima bata shiga, ya so ya ji ko ya raka Ibtisam 'din.

Can Niger kuwa Ibtisam sosai taji sanyi aranta, mgna da tai da Ja'afar.
Mahmoud ya isowa yajata suka tafi, ta tsaya awaje ya kaima Inna manta ya fito ya raka Ibtisam har gidansu sai da ta shiga gida ya tafi.
Kamar munafuka da ta shigo.
Laraba ta ce“Kinje kiyin waya da ubanki Ja'afar kin fa'da masa koh? Toh wlh rubuta ki ajiye sai na aura miki Alhj Jamilu ai yazo yanzu ya fita yakuma gayamin Inda ya ganki ga wayarki nan.â€
Ibtisam Sam yanzu batada damuwa tinda ta yi mgna da masoyinta, shiyasa uffan bata ce ba.
Chapter 15 · 0% Book details