← Book details Dattijon Arziki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 118

Sashe 48

Dattijon Arziki Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Sosai Ja'afar yake zaro idanunsa, wanda suka numa zallar tsoronsa akan abin al'ajabin da ya gani.
Duk da ya kasance jarumin namiji marar tsoro amman lamarin na yau ya yi mugun tsorata shi, wanda ya nemi addu'ar da yake cikin bakinsa lokacin da ya farka amman ya kasa, sakkamkon abinda yake tsaye gabansa.
Yawun bakinsa ya ji ya 'kame baki 'daya. Da sauri ya rarumo Ibtisam ya rungumeta gam a 'kirjinsa, yana kallon ikon ubangiji.
Yaron nan makaho da ya temakawa sanye da wasu irin kaya ya yi shiga irin ta 'ya'yan sarauta, sandar da take hannunsa kallo 'daya zaka mata kasan ta zinarince.
Sai wasu irin manyan halittu masu 'kirar 'karfafa, kallo 'daya zaka musu kasan ba mutane bane.
Gabansa ya 'karaso yaga cikin halittun biyu wanda yafi tsayi da girman ya beqa dogon hannunsa wata lafiyayyar kujera ta lu'u-lu-u ya ajiye agabansa sai walqiya take ya zauna dab da gadonsu.
Cikin sansanyar murya ya ce.
“Assalamu alaikum Ja'afar.â€
Ja'afar 'yar zufar da ta karyo masa ya goge yana sake rungume Ibtisam jikinsa.
Numfashi mai 'karfi ya fizgo cikin jarumtarsa ya amsa.
“Wa'alaika salam, bawan Allah ba kai bane wanda na tsallaka saman titi? Shin ya akayi kazo nan? Sannan wannan halittun fa!?â€
Hussain yay murmushi ya ce.
“Ya kai bawan Allah Ja'afar haqiqa nine wanda ka temakawa, ni musulmi ne mu 'yan biyune 'dan uwana Hassan ba ruwansa da rayuwar bil'adam, ni kuma haka na taso da son bil'adam, da son temaka musu amman na 'kwarai fa!ni ba mutum bane aqalla yanzu inada shekaru dubu 'daya da 'dari biyu da goma sha 'daya da kwana 17 yau cif aduniya.
Najima ban samu wanda ya temaka min ba irinka, tinda nazo duniya cikin wannan shekarun nawa kaine mutum na tara da ya temakeni cikin mutane duk da ba wai ina buqatar temakon ba, inayine kawai dan ware bil'adam irinku masu Neman temako, mu tarbi inda mukasan zaku wuce da zaran kun temaka mana sai muma mu temakeku. Akwai wa'danda zakaga suna cikin halin neman temako ko wata gagarumar matsala,muke fitowa mu tarbesu mu nuna atemake ko abinci ko sutura ko halin rashin lafiya ko Neman sadaka ko atsallakamu titi, kawai sai zagi da cin mutunci ya biyo baya, wataran harda mari ana nuna mana 'kyama bayan mu'din cikin jansin mu ma babbar sarauta garemu mun gama samun duniya lahira muke nema. Amman duk da haka ni ban ta'ba 'daukan fansa ba akan kowa temakon ne kawai bazan ma wanda bai min ba, idan ka mareni nasan agaba zaka ha'du da daidai kai sabida nawa mahaifin bazan ta'ba cutar da bil'adam ba. â€
Ja'afar sosai yake atsorace amman ya jure yana kallon Hussain ya ce.
“Ai ni kuma aganina ban maka wani temako ba da ya cancanta ka sakamin, ai ba komai yiwa kaine toh da me zaka sakamin?â€
Hussain yay murmushi yace bari kaga yanzu na dawo asalina.â€
Yana qarashe mgnar yay wata irin girgiza take ya riki'de ya dawo Hussain 'dinsa sak babba kuma cikakken aljani.
Ja'afar ya ce.
“Innahu min sulaimanu wa innahu bismillahir rahamnir rahim.â€
Hussain ya ce “Ai banzo da niyar cutar da kai ba, zan temaka maka akan matarka dan wlh kafin Ku samu maganin da zai warka da ita zaku jima duk da ba abinda ya gagari Allah.â€
Ja'afar jin ya ce Ibtisam zaima magni cikin murya ya ce“Amman da naji da'di.â€
Hussain ya ce“Insha Allah 'dago kanta.â€
Ja'afar jikinsa na rawa ya 'dago kan Ibtisam, Hussain ya beqa hannun ya dafe goshinta.
Wani irin haske hannunsa ya fara idanunsa arufe bakinsa na motsawa.
Kusan 30 minutes, ahakan, kafin Ibtisam ta fara wata irin rawa jiki da kyarrrma numfashinta na sama da 'kasa.
“Karka ji tsoro Ja'afar sai mun cika awa 'daya cif.â€
Kai kawai Ja'afar yake 'dagawa.
Sosai ya girgiza da lamarin yadda Ibtisam take zanzana.
Sandar hannunsa ya 'daga ya fara karatu yana tofawa, wanda goshinsa ya fara fitar da zufa, ya buga atsakiyar kan Ibtisam, wanda atake ta 'kurama ihu ha'di da fa'din “Wayyo Allah nah! Ja'afar ka cuceni, zan mutu ban nemi gafara iyayena ba! Na tsaneka bana sonka...!â€
Sai kuma tai shiru tana sauke numfashi alamun bacci.
Hussain ya ce“Alhmdllh! Tana farkawa bacci lafiya zata farka sai dai baccin zai jima zata ita kwana da wuni ahaka karka damu tana tashi komai ya wuce Insha Allah, dan haka karku kaita asibiti dan batada wata matsala yanzun, na barku lfy ina muku fatan alkhair ki bi sannu ka saddo 'kasa ka 'kas'kantar da kanka ka lallashi yarinyar ka bata kulawa karka yi girman kai cikin lamarin sannan karka yi fushi ka biye mata ka yanke hukunci cikin fushi duk zakuyi nadama daga baya, idan kunbi son zuciya, da kuma 'bacin rai, ka riqe mganata ka rungumi matarka tana sonka da zaran ka ajiye jiji da kanka ka lallasheta komai zai wuce fatan alkhairi .â€
Ja'afar da'di ya rasa inda zai tsoma ransa sai godiya yake ma Hussain.
Iska da guguwa mai 'karfi wacce tafi ta farko ita ce ta turniqe 'dakin kafin giftawar idanu sun 'bace.
Kumaa daidai lokacin ake kiran sallar asubah.
Ja'afar ya kwantar da Ibtisam ya zuba mata idanu cikin farin ciki wai ta warke.
Miqewa yay ya shiga toilet yay wanka ya 'dauro alwala ya fito ya sanya jallabiya ya tayar da sallar raka'atanil fajir.

Abie amakare ya farka dan lokacin an fara sallah, masallaci, agaggauce yay wanka ya 'dauro alwala yay sallah.
Bayan ya gama ya fara azkhar.
Bayan ya idar ya miqe ya fito falo yana Jan cazbi.
Da mamaki yake kallon Ja'afar da Tanko zaune falo suna magana cikin zallar farin ciki wanda ya ga Laraba sai washe haqora take.
Sallama yay musu suka gaisa cikin mutuntaka.
Abie ya ce“Ya dai ko an samu wani ci gabane wajan Ibtisam?â€
Cikin farin ciki Tanko ya ce.
“Alhaji daman zaman jiranka muke bai kamata kana hutawa atasheka ba,Allah ya dubi kirkin ka da temakon ka, ya ragema wahala, jiya cikin ikon Allah cikin tsakiyar dare......â€
Tsaff ya labartawa Abie yadda Ja'afar ya labarta masa daga kan temakon da yawa yaron makaho zuwa zauwarsa da abinda yama Ibtisam zuwa ihunta da kiran sunan Ja'afar da tai da yadda Hussain ya ce da zaran ta farka zata tashi normal kar aje asibiti abari har ta farka.
Abie ya sauke ajiyar zuciya zaiyi magna kiran Rahma ya shigo wayarsa.
Bai 'daga ba ya kallesu ya ce.
“Ma Sha Allah Alhamdllh! Abu ya yi kyau toh ba damuwa zamu jira muga farkawar tata amman duk da haka zamuje aqara dubata idan ta tashi.â€
Ja'afar cikin murna ya ce“Abie Allah ya qara girma da bu'di.â€
Abie ya 'daga wayar yana amsawa da “Ameen ya Allah Ja'afar.“
Wayar ya kai kunnensa yana miqewa ya nufi bedroom 'dinsa.
Zazzafan numfashi ya sakar mata ta cikin wayar ha'di da sauke ajiyar zuciya, cikin sansanyan murya ya mata sallama.
“Assalamu alaiki Ya Baby Ummina.â€
Rahma daga can ta turo baki gaba tana amsa sallamar, ha'di da cewa.
“Abiena I miss you fatan kana lafiya? Ya gajiya? Jiya nayi bacci marar da'd, pls Abie ka biyo Espagne na ganka pls karka wuce Chad.â€
“Alhmdllh Babyna hope kina lfy ya shirye² tafiya? Na miki alqawali zuwa nima bazan iyaba nayi kewarki sosai Habibaty Ummiâ€
Ashagwa'be ta ce“Uhmm! Anjima ka'dan ne Abie zamu tafi, ok sai kazo, rabin raina.â€
A tausashe ya ce“Masha Allah babyna sai na shigo jibin insha Allah ki kularmin da kanki zan kiraki OK? Pls kici abinci nasanki bakya cin komai cikin jirgi.â€
Asanyaye ta ce“Ok Abiena bari na kwanta ka'dan bye.â€
Murmushi yay ya sumbaci wayar ya ce“Allah saukeku lfy bye baby Abienta.â€
Asakalce ta kirasa.
“Abienah!â€
“Na'am babyna! Oya kwanta kiyi bacci ki huta kafin lokacin tafiyarku.â€

Abie Dr Moha ya Kira ya ce ya ya qara hkr zuwa dare ko yamma zasu shigo hospital. Daga nan ya Kira Jaddatu da Hanan and Abie 2 suka sha fira.
Misalin 9 Abie ya kirasu Tanko duk suka fito sukayi breakfast wanda kukun Abie ya musu breakfast mai da'di da ha'daddan tea, bayan sun gama Abie ya ce suje su kwanta su huta, su jirayi tashin Ibtisam.
Chapter 48 · 0% Book details