← Book details Dattijon Arziki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 118

Sashe 74

Dattijon Arziki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Wallahi bana gani idanuna wayyo Anna Baba, idona zafi ka fasamin idanuna dan Allah ka kaini hospital.â€
Ta 'karashe mgnar da yaren French cikin kuka tana sake qamqameshi, tanajin wata irin nutsuwa da sanyi na ratsa dukkan jikinta. (wa'iyazubillah.)
Abie cikin zafin nama ya 'ban'bareta daga jikinsa ya ingijeta ya jefar da ita yadda bazata ji ciwo ba! Yana fa'din.
“Hasbunallahu wa ni'imal wakil. Kidana hankali kuwa? Ke jahilar ina ce? Bakya jin tsoron Allah ne? Kina MATAR wani haka kawai ki kamani ni muharaminki ne? Sakara kawai.
Bu'de idanunki nagani wallahi ko yanzu na miki shegen duka na karya miki wuya ki mutu Ja'afar ya huta da zama da jahilar mace irinki sakara kawai, bu'de idanun maza nagani munafuka!â€
Abie yay mata mganar cikin mugun 'bacin rai yana zaro mata manyan idanunsa.
Ai Ibtisam take ta shiga hankalinta ta miqe zaune daga wurgin da abie yay da ita, tana bu'de idanunta tana kuka, kallo 'daya tai masa tai saurin sadda kanta jikinta na mugun rawa, wani irin mugun kwarjini ya mata, ga tsoronsa da ya gama mamaye dukkan illahirin jikinta.
Abie da sassarfa yabar wajan yana dafe goshinsa, azahirin gaskiya ya tsani yarinyar sbd shi mutum ne mai 'kyamar abinda duk yake na haramun, sannan ya tsani mutum mai son kansa dayawa, ta gudo daga 'kasarsu domin Ja'afar sbd son da take masa, yanzu alamunta 'baro² ya nuna tana sonsa, me hakan yake nufi? Tsuki yaja aransa yana fa'din.
“'kasashen duniya dayawa ana ganin kimata, da darajata nafi 'karfin ki zubar min da kima wlh, sakaran yarinya kawai, da batasan me take ba!â€
Nutsuwarsa ya saita ya shigo falon Abie 2 da sallama.
Amsawa sukayi, Abie 2 na murmushi ya ce“Wai baka fita wajan meeting 'din ba?â€
Abie ya basa hannu sukayi musabaha ya murmusa ya ce“Wlh sai yanzu idan na fito daga masallaci zan wuce.â€
Hannu yaba Mal Adamu da Tanko and Ja'afar yana fa'din.
“Ina muku fatan alkhairi Allah ya saukeku lafiya.â€
Ya 'karashe mgna yana zura hannunsa cikin aljihun wando dakekiyar shaddar jikinsa Green ya zaro 'daurin 'yan
deux milles 'dauri uku ya be'kama Mal Adamu ya ce“Kaida Shamsu da Ja'afar kowa 'dauri 'daya ayi hidimar biki lfy sai munyi waya, Ja'afar ina jiranka fa!â€
Baki 'daya 'kasan 'kafafunsa suka zube suna godiya, da masa addu'u sabida ku'dine wanda dukkansu kowa zai ishesa sabgogin bikinsa har agama ba wanda ya nemi wani abun.â€
Sallama yay musu jin ana shirin tayar da sallah nan masallacin gidansa.
Laraba baki da hanci ta Saki tana kallon uban 'daurin ku'din da Abie yaba mazan ita banda ita ko meyasa ya hanata?
Abie ya ce“Ai sai mu hanzarta zuwa masallaci kar atayar da sallah da mun fito sai muwuce airport nayi rakiya.â€
Cike da murna dukkansu suka fito domin zuwa masallaci daman sunada alwala.
Ibtisam kuwa tinda ta kalli Abie ta sadda kanta bata 'dago ba saida ta ga ya shige ciki ta miqe tana zubar da hawaye, ta nufi cikin, amman bata shiga ba sai da ya fito ta nufo ciki nan taci Karo dasu Abie 2 zasu masallaci.
Jikin Laraba ta fa'do ta fashe da kuka mai cin rai tana fa'din.“Amatsayinki na mahaifiyata kimin addu'a Allah ya yayemin abinda yake damuna dan Allah.â€
Laraba ta ce“Ibtisam ki dawo hankalinki tashi kiyi sallah da sun dawo zamu wuce ni ina hutune.
Kinga mutumin nan ya rabamusu uban ku'di wlh ko sisin kwabo abi ban ba, ikon Allah.â€
Ibtisam ta ce “Balarabe ko?â€
Laraba ta ce“Eh amman nasan Babanki zai bani.â€
Ibtisam ta share hawayenta ta miqe tayo alwala daman tana sanye da hijib madedeci tahau darduma ta tayar da sallah.
Abie ana idar da sallah ya shige moto tare da securities suka fice.
Yahaya ne ya kaisu Ja'afar airport Abie 2 'dan rakiya, shi daau Yahuza, suna nan sai da jirginsu ya cira sama suka nufi gida.
Ja'afar da Ibtisam wajan zamansu 'daya amman ko kallo bata ishesa ba, sabgogin gabansa yake.

*Gabon*
Aishatu sosai jikinta yake rawa gabanta yana fa'duwa, ganin paper 'din hannunsa tasan sakinta yay.
Danne abinda takeji tai ta sanya hannunta wanda yake rawa ta amsa tana fa'din.
“Allah yasa haka yafi alkhairi.â€
Ta 'karashe mgnar zata zauna, taji ya fizgota ta fa'do jikinsa ya rungumeta ta baya, ya 'dora ha'bar akan kafa'darta, cikin kwantar da murya ya ce“Yanzu don Allah kinason na sakeki?â€
Fizge jikinta tai tana nunasa da 'yar yatsa ta ce“Karka raina min hankali mana, kana nufin ba sakin nawa kayi ba?â€
Sake damqota yay ya rungumeta ya ce“Wlh bazan iya sakin ki ba! Don Allah ki yafemin zan dai barki har lokacin da za ki sauko dawo gida wlh Allah ban ta'ba zina ba, abinda dai da na fa'da Munnira shine gaskiya wlh bana haiyacina komai ya faru ki fahimceni dan Allah.â€
Jikinta ta janye ta zauna tana bu'de takardar, da abinda ta fara cin karo ya sanyaya mata jikinta.
BAN HKR MY AISHERðŸ‘ðŸ½ðŸ˜­

HMM! KI YARDA DA NI.
A dukkan lokacin da dare ya yi, ki d’aga kanki sama ki kalli sararin samaniya, za ki ga wani tauraro yana saukowa izuwa gare ki, karda ki yi mamakin me ya sa haka ya faru? Ki yarda da ni, hakan zai iya faruwa a zahiri domin kuwa ni ma na yi hakan har ta kai ga na same ki.
INA SON
KASANCEWA A TARE DA KE HAR ABADA my Aisher.
A lokacin da na samu soyayyarki sai na ji tamkar ni ne na fi kowa sa’a a duniya. A dukkan sanda na rintse idanuwa na sai na hango ni tare da ke muna tafiya a bisa gajimare. Idan na kwanta bacci sai na yi mafarkin mun zama mata da miji. Ina sonki, tare da son kasancewa a tare da ke har abada. Ki Huta Lafiya.
A CIKIN IDANUWANKI AKWAI WANI SIRRI.
Sama cike take da taurari masu hasken da ke haske duniya a cikin kowanne dare. Amma haske mafi haskaka fuska da yaye duhun zuciya, na gan shi ne a cikin idanuwanki. Ki Kula Min Da Kanki. Ina Son ki.
HARSHEN ZUCIYA.
Furanni na furta kalmomin yabo a kanki a dukkan lokacin da na shiga lambu mai d’auke da ‘korama gami da korayen ciyayi da bishiyu masu d’auke da tsintsaye. Sukan rera baitukan yabo a gare ki, cikin harshen da zuciya ce kawai ke iya fahimtarsa. Ina Son Ki.
BA ZAN IYA RAYUWA IDAN BA TARE DA KE BA.
A mafarki da kuma a cikin soyayya babu abun da ba zai iya faruwa ba. Ina son ki sosai hakan ya sa nake ji tamkar ba zan iya rayuwa idan ba tare da ke ba. Ba na fatan rasa ki a rayuwa ta, domin kuwa a dukkan lokacin da na rasa ki, na tabbatar da rayuwa ta za ta shiga garari. Ina Son Ki kuma ba zan tab'a canjawa a kan hakan ba, don Allah ki yafemin my dawo kamar da nayi miki alqawalin zama dake bisa amana, ina sonki my Aisher.â€

Ajiyar zuciya ta sauke a'boye amman azahiri tai kicin² da fuska ta miqe ta shige toilet ta banko 'kofar.
Murmushi yay ya juya ya tafi.
Rabi'ah wasa² tana cikin tashin hankali duk ta fige ta lalace komai baya mata da'di, sai tayi yin'kurin zuwa ganin Aishatu sai ta fasa gabanta na fa'duwa amman ta 'dauki alqawalin zuwa dubata da neman gafarata idan abun ya lafa.

*Niger*
Inna Hansatu an kasa zaune an kasa tsaye anata murna Ja'afar da babansa zasu zo, an yanke zabbi guda uku manya anyi farfesu an dafa macaroni da shankafa, an gyara musu salad da kwai anyi kunun gyad'a kai abun Masha Allah.
Sadiya tazo ta Kama mata girkin da Deluwa Maimou ta 'kwal'kwale gidansu tasa tana turaren wuta abin gwanin ban sha'awa ta share 'dakin Ja'afar ta goge an canza zanin katifa, Mahmoud ya wanke wanda yake kwana Asama.

Can ma Dadda da yaran sunzo sun gayara gidansu Laraba, Taslim Masha Allah, ta share 'dakunan ta goge ta kunna turaren wata, Dadda ta sayo zakatu biyu aka yanka ita da Taslim suka 'Dora girkin.
Dadda tana mota miyar Taslim ta ce“Don Allah Dadda ki daina zatayi 'karni fa!â€
Aydah tai dariya tana fa'din.
Kince Dadda bata iya girki ba.â€
Dadda ta ce“Barta Aydah 'Yar ashatta ko uwata ta gwadamin girki bari na kammala muci kuji.â€
Taslim tai dariya ta ce“Yo abinda duk Rabin miyar nice ni da nafi Auntie Ibtisam ma iya girki.â€
Dadda tace“Ai shagwa'bar ta barta iya girki ja'ira ai Ja'afar zai ga tab'ara.â€
Dariya sukayi bayan sun kammala firkin bayan Maghreb sunyi sallah Dadda ta zuba musu sukaci suka 'koshi dam nan suka Kama hira dan Dadda na tare dasu sa iyayansu sun zo sai ta wucce gida.
Inna Hanssatu zaune an kakkame an sha wanka masha Allah ga 'kunshin gargajiya ansha 'kafa da hannu, gida ko ina sai baza 'kamshi yake.
Deluwa ma ansha kwalliya ba laifi tana 'kofar 'dakinta da yaranta.
Abinci Hansatu ta raba, Mahmoud na gefe ta kirasa.
“Mahamoud! Zo 'dauki naka kai da 'yan uwanka, Maimouna zo kema ga naku. Deluwa matso muci.â€
Maimou ta ce“Yaufa akwai kwasar ganima, bari muci kafin su Baaba su zo suci su rage muci sauran.â€
Inna Hansatu ta ce“Ai sai kici uwar cikin ci tinda ubanki ya bayar da ku'di.â€
Deluwa tai gum da bakinta tana gun abincinta kar ta tofa tasha gori.

*Morocco*
Wata dattijuwa ce zaune a'kalla zata kai shekaru sittin da biyu, sai wata 'yar matashiya wacce bazata wuce shekaru 28 ba sai dattijo zai kai shekaru saba'in yana waya cikin harshen larabaci yana sakin murmushi.
Sai wasu kyawawan twins maza zasu kai shekaru 9.
Falon kawai zaka kalla kasan an tara dukiya.
Tv suke kallo tashar Aljazeera ana labarai, yayin da yaran nan game suke a wata Tv plasma suna tsereran jirgi.
Chapter 74 · 0% Book details