← Book details Dattijon Arziki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 118

Sashe 38

Dattijon Arziki Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Zaune take a falo tana sanye da abaya pink, ta yane kanta da mayafin fuskarta sam ba walwala.
Jaddatu ta kalleta ta ku'bi shayi ta ce.
“Yo Allah na tuba mu za'awa shan 'kamshi.â€
Abie na danna laptop ya 'dago yana kallon Rahma ya murmusa ya ce“Zo baby fa'damin nine ko Ja'afar ne? Ko Ummina ce? Nasan hanan da Raiyana basa tsokanarki.â€
Asakalce ta ta taso ta nufo wajansa ta zauna dab da shi tana kallonsa tana narai-narai da 'kananun kyawawan idanunta.
Raiyana takaici kamar zata ha'di zuciya ta mutu.
Abie ya ce“Bazaki fa'di wa ya saka min ke fushi ba?â€
Ashagwa'be ta ce“Yo Abie ba wani bane ya takura min tin 'dazu an nkusa awaya ina baccina me da'di ya kirana sai masifa yake min wai sai na fa'da masa yaushe muka qulla soyayya yaga numbata an saka sunan Qalbina wayasa, kuma wlh ni ban sansa ba kuma naga sunan Habiby nima wayata Allah ban san shi ba shine nace yazo ayi qurayya muga juna, kuma fa bayajin larabci sosai sai français, na kwatanta masa gidan, ya ce zai zo.â€
Jaddatu ta ce“Alhamdulillahi! Allah abin godiya, tsira da amincin Allah su tabbata ga shugaban halittun duniya Annab S.A.W.â€
Abie ya ce“Ja'afar 'din kika manta Babyna�
Rahma ta tsira masa idanu ta ce“Wlh Allah ban San shi ba waye¿â€
Miqewa yay ya miqar da ita yaja hannunta suka nufi hanyar barin falon.
'Bangaran Abie 2 suka nufa sai yaga motar da Ja'afar ya danno cikin gidan. Tsaye Abie yay har Ja'afar yay parkint ya fito ya nufi wajan masu gadi.
Gaisawa sukayi cike da izzarsa murya 'kasa ya ce“Pls Rahma nake tambaya.â€
Masu gadin abin ya basu mamaki. Hango Abie da Rahma suka nuna masa.
Bai ce 'kalaba sbd halinsa na shiru ya nufi wajan cike da takunsa na 'kasaita.
Rahma ta kalleshi ta waro idanunta waje cikin sanyinta na asali da ya dawo ha'di da zafin zuciyar da gareta idan taga abinda ya 'bata mata rai.
Hannayen Abie ta damqe sosai ta ce.
“Abiena wannan yaron nan ne da ya ta'_ba bugar mana mota kwanaki me yazo yi gidanmu?â€
Abie ya lakaci hancinta ya ce“Baby ban sanki da fushi ba ki nutsu.â€
Ja'afar da sallama ya iso wajan ya gaishe da Abie ya ce“Don Allah kece Rahma?â€
Hararansa tai ta kwantar da kanta kafa'dar Abie ta ce.
“Ban saniba kaje Inda ka samu number tawa sai ka tambaya yaro kayi gaggawar goge numbata...â€
Abie ya rufe mata baki da tafin hannunsa, ya mata ra'da akunne ta saki kukan shagwa'ba tana diddira 'kafa.
Ja'afar tsabar haushinta da takaicinta ya saka ya juya ya fara tafiya cikin zafin zuciya ganin marar kunyar yarinyar nan ce yana goge number ta, sauri yake yabar gidan dan ya tsani shiga gidan masu ku'di Sam.
Number Ibtisma ya kira akshe ya dafe goshinsa yana sake sauri.
Abie ya kirasa Ja'afar! Dawo ga mahaifinka nan fa!â€
Idanuwa Ja'afar ya waro waje yana juyowa cike mugun tsoro da ki'dima kar dai ace babansa ya gane Ibtisam na wajansa?
Juyowar da yake yaga Tanko malam Adamu Abie 2 Laraba gefe.
Badan namijin gaske bane da ya zube 'kasa sabida muguwar ka'duwa da abinda ya gani agabansa.
Idanunsa ya murza da kyau tsaf yaga malam Adamu mahaifinsa tsaye yana Jan casbi.
Adaidai wannan lokacin Aljannun da malam ya turama su Ja'afar suka dira gaban Malam Rabin jikinsu a 'kone halittar tasu ba kyan gani.
Malam ya ce“Maza kuje wajan wacce ta ta 'dauki alhakinku ba niba.â€
Wanda adaidai wannan lokacin Raiyana da take ganin abinda yake faruwa, tana la'be sulalewa tai 'kasa sumammiya tsabar bugawar zuciyarta, da tuno sharu'dan malam...........!

_*🤲ðŸ¼Ya Allah ka jiÆ™anmu kayi mana rahama badan halinmu ba.ðŸ™ðŸ¼*_
2/24/22, 16:54 - Buhainat: ```D A```

```39&40```

_*My Sisters Don Allah Don Darajar Annabi Karki Karanta Idan Baki Biya Ba, Na Ku'dine Idan Kinga Yana Yawo Na Satane Ga Hanyar Da Za Ki Samu Naki Akan.😟👉ðŸ¼300N +22796515805*_

_Wai 'yan *Fitattu 4* me yasa kuke fitar min da littafina? Ko dan kunji nace bazanyi Allah ya isa ba? Ku tuna haqqina ne fa! Don Allah kuyi hkr ku daina sbd wlh Nagano kune ba 'yan paid group 'Dina bane, sbd shedar da nakeyi. Wlh bana so har can 'kasan zuciyata ban ta'ba roqonku ba yau na roqa ku daina, don Allah wlh idan nagansa bakusan yadda nakeji ba, ku daina pls.ðŸ™ðŸ¼ðŸ˜­_

Jaddatu da Hanan da suka biyo bayansu Abie, su ga meke faruwa ne suka saki salati, ganin Raiyana ta zube 'kasa sumammiya.
“Hanan yi sauri kawo ruwa.â€
Robar ruwan da take hannun iman Hanan ta amshe ta shafama Raiyana afuska ta zuba mata saman 'kirjinta.
Ajiyar zuciya ta sauke, wani irin 'bari jikinta ya fara.
Jaddatu ta ce“Mun shiga uku! ke! Raiyana lfy kuwa? Kike abu kamar mai ciwon farfa'diya?â€
Raiyana sai shure² take bakinta na fitar da wani irin baqin ruwa, idanunta sun firfito waje duk sun juye baki 'daya.
Sai lokacin hankalin su Abie yay wajansu, sbd abinda Jaddatu take fa'di. Gudun zargi ya sanya Abie yaja hannu Rahma suka nufi wajanta.
Su malam Adamu ganin kamar MATAR gidan ce ba hijab mayafin kanta ya fa'di suka qi zuwa Abie 2 ya ce.
“Mu shiga ciki har su gama Allah ya bata lfy, Ja'afar bismillah shigo.â€
Ja'afar har lokacin idanunsa kan mahaifinsa mugun mamakin abin yake.
Jin abinda Abie 2 ya fa'da, ganin sun shiga ciki harda mahaifinsa yana masa wani irin kallon da bai ta'ba masa ba, yay saurin binsu abaya hankalinsa a mugun tashe, shi bai damu da kallon tsanar da Laraba take masa ba.
Abie kallo 'daya yay ma Raiyana ya gano tabbas 'kai'kayine ya koma kan masheqiya.
Baice musu komai ba, ya sunkuya ya riqe hannunta ya fara karanto mata addu'a yana tofa mata.
Rahma duk sai ta tsorata ganin abinda Raiyana take yi, ta koma bayan Jaddatu ta la'be.
Anjima sosai kafin jikinta ya daina rawa ya sanya tattausan hannunsa ya 'dauketa ya nufi ciki da ita.
Nan wani 'daki da yake 'kasa ya sanyata saman wani lafiyayyan gado ya kwantar da ita, ya juya ya fice.
Zauna ya gansu falo sunyi tsuru².
Jaddatu ta ce“Wai daman Abdul Raiyana ciwon aljanu gareta ka kwaso mana?â€
Abie kallon mamaki yama mahaifiyar tashi, kamar ba ita ta matsa ba ya aureta.
“Ummi wlh ban saniba yau nagani, insha Allah za'a mata mgani da ayar Allah ta warke. Baby taso muje.â€
Rahma ta maqale kafa'da.
Hanan ta ce.
“Duk tsoron ne? Jaddatu ta kalli Abie ta ce“Kamata kuje ina mai maka tuni lokaci ya kusa, na fara gajiya da wahalar da kake Sha fa!â€
Abie ya murmusa ya ha'de hannayensaðŸ™, cikin taushin murya ya furta.
“Afuwan ya mahaifiyata, ki bari don Allah...â€
Katse shi tai ta ce“Kamin shiru Abdul, banson maganar banza, kai wace irin zuciya gareka ne¿â€
Rahma ta kalli Jaddatu ta kalli Abie ganin yanayinsu ya canza.
Ashgwa'be ta ce“Wai Jaddati meye kike matsawa Abiena?â€
Jaddatu ta harareta ta ce“Gata nake muku Rahmata.â€
Abie hannun Rahma ya kama ya miqar da ita yajata suka tafi.
Hanan ta ce“Wane irin gata Ummi?â€
Jaddatu ta ce“Aikin ki kenan gulma da shegen bakinki kamar tsutsa, ni wlh idan so samune kar Rahma ta koma Espagne.â€
Tafe suke Rahma ta kalli Abie zatayi mgna ta fasa.
Murya shi taji yana fa'din.
“Baby ummina yi mgnarki kai tsaye.â€
“A'a Abiena babu komai fa!â€
Kai ya jinjina.
Chapter 38 · 0% Book details