← Book details Dattijon Arziki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 109 OF 118

Sashe 109

Dattijon Arziki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bata jimaba ta fito sanye da hijab pinky Kala, ta basa ya cire singlet ya saka ya d'auki makullin mota ya Kama hannunta suka fice.
★★★
*Istanbul*
Tsawon kwana *hud'u* Abie na jinyar Rahma, bai sake kusantarta ba, kulawa yake bata mai yawan gaske da nuna Mata zallar soyayya mai tsayawa azuciya, hakan ya saka Rahma ta sake fad'awa tarkon son Abienta, ya shagwab'ata ya sangartata da jikinsa, sosai suke zaga garin Istanbul, wuraran tarihi da wuraran shaqatawa, duk Inda sukaje sai an kallesu sabida dacewar da sukayi da juna.
Yau dai bayan sun dawo daga yawonsu Abie ya samu ya tisa wajan yasha shagwab'a da sakalci.
Yanzu ma bayan sunyi wanka tsarki ya shiryata, ya sanya mata wasu riga da wando masu kyau wandon iya cinya rigar bakin cibinta, ya baje Mata dogon gashinta ya sauka har gadon bayanta.
Zaune suke afalon yana manne da ita yana bata pizza abaki tana ci sai sangarta take zuba masa.
“My Honey rugima ko? Toh Bby haaaaa cinye wannan sai na Kira miki Jaddatu da Abienki.â€
Jin abinda Abie ya ce cikin d'auki ta bud'e bakin ya sanya mata, ta had'a da yatsarsa, ta ciza da d'an qarfi.
“Ushhhhh! My Baby zafi ni koh?â€
Kai ta d'aga masa tana masa kallon qasa² tana tauna pizza.
Murmushi mai shegen kyau ya sakar mata, ya ce“I love you sannu fa My Honey, wai kin gajine, akwai zafi koh?â€
Baki ta b'are masa zata saka masa kuka, yay saurin tura bakinsa cikin nata ya lalubo pizzar bakinta yana wasa da ita ya kwasheta ta koma bakinsa ya shiga tura mata tana had'iyewa.
Ya sanya hannayensa dukkan biyun ya qamqame bayanta yana bugawa sannu² ya tsareta da manyan idanunsa masu sakata shiga wani yanayi.
Lumshe idanunta tai tana amsar pizzar da yake d'ura mata sai da ta ha'de tass ya fara kissing d'inta yana qara aika mata wani irin salo yana murza k'ugunta zuwa bayanta had'e da manmatsa. mata kowace gab'a ta jikinta, still yana shan bakinta.
Rahma ta kasa jure kallon da yake mata, ta lumshe idanunta ahankali ta cije shi a harshensa.
Bakinsa ya zare anata ahankali, yana mata wani irin fitinannan kallon k'auna, ya furta.
“Ushhhhh! Baby love zaki cinyeni ne?â€
Da sauri ta bud'e kyawawan k'ananun idanunta, tana turo baki gaba ta ce.
“Abie Kira mun Jaddatun toh da Abie2.â€
Kissing d'in idonta yay yana shafa kumatunta ya ce“Okay my baby love gsky yau kin kusa mantar Dani ni waye zuwa dare babyna zaki qaromin pls?â€
Kukan shagwab'a ta sakar masa tana qoqarin zamewa daga jikinsa, yay saurin rungumeta qam, yana dariya ya ce.
“Sorry My Honey wasa nake miki bazan tab'a cutar da Ruhina ba, oya zo na Kira miki Jaddatunki.â€
Ya qarasa mgnar yana sumbatar tsakiyar kanta yana shafa bayanta.
Luf tai k'irjin Abienta tana jin gajiyar turmusar da yamata yanzu kusan awa 'daya yana abu d'aya sai taji yanzu duk tsamin da jikinta yay ya fara sakinta.
Hannunta ta tura cikin sumar kansa mai taushi ashagwab'e ta ce.
“Abie...â€
Bakinsa ya d'ora saman nata ido cikin ido ya ce“Na soke Abie daga yau yau kwana nawa ina bin kanki ki saka min wani sunan? Toh idan bazaki saka min wani sunan ba kina kirana da Abdulmajid sak OK? â€
Rahma ta ware kyawawan k'ananun idanunta ta ce.
“Wayyo na shiga uku Rabin raina kayi hkr, ni ina zan Iya Kama sunan garkuwata qiri² tabbb wlh bazan tab'a ba, amman kamin Afuwa zan saka ma wani sunan amman Abien yabi jinin jikina bazan Iya daina ba, zan gama ba Abienah.
“My sweet darling yayi koh?â€.
Ta qarasa mgnar agajiye tana tura kanta tsakiyar k'irjinsa.
Tattausan murmushi yay yana sumbata tsakiyar kanta, ya ce.
“Yes yayi my baby love Ngd.â€
Ya k'arasa mgnar yana dialing d'in number Jaddatu, ya sake matseta jikinsa, jin wayan ta fara ringing ya saitai nutsuwarsa.
Sallamar Jaddatu ta kard'e dodon kunnensa, tana fad'in.
“Kai Abdul! Sbd Allah duk kana ina Baku Kira idan an Kira ba'a samunku?â€
Abie ya amsa sallamar ya d'ora da cewa.
“Afuwan ummina ina wuni barka da yamma, ga baby Ummi.â€
Jaddatu daga Chan ta ce.
“Bani ita naji lafiyarta....â€
★‡★
*Gabon*

Ma'aruf ya shiga muguwar damuwa akan dukiyarsa da wuta ta cinye.
Ganin hakan yasa Aishatu ta sauko daga dokin fushin da take da shi, ta shiga masa nasiha tana kwantar masa da hankali, dangi kowa hankalinsa ya tashi, dan ayanzu Ma'aruf ko maganin rabin million 'daya bazai maka ba, dan account d'insa 'yan canji ne kawai.

Zaune take kusansa tana basa abinci abaki Wanda idan ba hakan tai ba tana lallashinsa bai ma damu da yaci ba, duk da kuwa ya fawwalawa Allah kominsa na shi yasan alhakine yake binsa.
Asanyaye ya ce.
“Masoyiya na qoshi bari nayi wanka muje gida mu gaishesu.â€
Hannunsa ta Kama ta ce.
“Don Allah ka Saki ranka bafa aja da ikon Allah jarabawace idan ka cinyeta sai Allah ya maka falalar da baka tab'a zatoba, amman idan ka damun sai ya barka da damuwarka don Allah ka manta komai.â€
Rungumeta yay yana buga bayanta yace“Wlh ba komai na barma Allah komai ikonsa ne yanada ikon yimin hukuncin da yafi wannan sabida na sab'a masa dayawa daman kuma baka tab'a Allah kace kaci bulus.â€
“Hakane amman ai ka tuba kuma Allah gafuru rahim ne, insha Allah zai kalleka da idon Rahma muje ka shirya.â€
Bedroom suka nufa sai suka Fara jin ihu, Ana buga musu 'kofa.
Ma'aruf jikinsa na rawa ya nufi k'ofar aguje hankalinsa atashe yana fad'in.
“Ko wata musibar ce ta sauko min hallau.....â€

_*+22796515805*_

_*🤲ðŸ¼Ya Allah ka jiÆ™anmu kayi mana rahama badan halinmu ba.ðŸ™ðŸ¼*_
5/24/22, 15:22 - Fiddausi Yunus left
5/27/22, 10:51 - Buhainat: ```D A```

```101```

_Rahmerh Ladingo😉_

_*Alhamdulillahi Am backðŸ‡ðŸ»*_

😅🙈🥳😒🚶ðŸ»â€â™€ï¸

Ma'aruf na bud'e k'ofar falon yaci karo da Nura direba tare da mai gadi, hankalinsu atashe.
Ma'aruf ya ce.
“Wai lafiya? Me ya faru ne?â€
Nura ya ce“Yallab'ai ga mota can ta kama da wuta a qofar gida, zanje aiken da ka kamin, ta Kama da wuta Allah yay da kwana na gaba na fito cikin hukuncin Allah, ba yadda bamuyi ba mu kasheta taqi mutuwa, ga jama'a chan na famar kashewa .â€
Ma'aruf banda sunan Allah babu abinda yake fad'a, bakida 'daya ma duk wasu addu'o'i da ya sani ya ji sun tsaya masa cak, jikinsa na rawa ya nufi hanyar wajan, suna biye da shi.
Aishatu da take tsaye a k'ofar falon tai zaman 'yan buri, ta d'ore hannayenta saman fuskarta, tana fad'in.
“Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Allahumma ajirni fi musibatihi waklifni khairan minha!â€
Ta k'arashe cikin sakin kuka zuwa yanzu Ma'aruf na bata mugun tausayi tabbas ya had'u da iftila dayawa.
Miqewa tai ta koma ta d'auko hijab ta saka ta fito.
Ma'aruf yana tsaye yana kallon 'yan kwana-kwana suna kashe wutar, Wanda mak'ocinsa Salisu ne yay wannan jihadin na kiran 'yan kwana-kwana.
Motar ta k'one sosai ba lallai ta anfana ba.
Aishatu ganin yadda Ma'aruf yake tsage kamar gumki, sai jaje jama'a suke masa yana d'aga musu kai, ya saka ta isa wajan ta Kama hannunsa suka shigo cikin gida har wasu na biyosu suna k'ara masa jaje.
Mai gadi ya rufe gidan, yayin da Nura yake tsaye wajan motan da ta kusan cinyewa k'urmus, dan ba lallai ta anfana ba.
Zaunar da shi tai saman kujera a falon, taje fridge ta d'auko ruwan sanyi,ta bud'e ta kafa masa bakinsa.
“Please kasha.â€
Ba musu ya dinga kwankwad'an ruwan sanyin, sai da yasha kusan rabi, ta janye masa goran ruwan daga bakinsa, ta Kama hannayensa ta ce.
“Kayi hkr babu wani abu da yake wanzuwa adoron duniya ba tare da izinin Allah ba! Dan haka kayi hkr ka amshi dukkan jarabawarka wana Allah zai wanke ma dukkan zunubanka ne ta wannan hanyar, amman ba wai na Tara Sani ga ubangiji na bane, ka tattara komai ka barwa Allah, kayi ta maimaita.
Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Allahumma ajirni fi musibatihi waklifni khairan minha, Allah ya bamu ikon cinye jarabawarmu.â€

Ma'aruf ya rungumeta, gam yana sauke numfashi, cikin aro jarumtarsa ya ce.
“Wallahi Aishatu na amshi dukkan k'addarata tinda dai ina tare dake Alhmdllh!â€
Sake rungumeshi tai ta ce“Allah ya bamu juriyar cinye dukkan jarabawar da Allah zai jarabemu da ita.â€
Ya amsa da.
“Ameen ya Allah.â€

Rabi'ah zaune da cup d'in kunnun tsamiya, Wanda ta saba, duk ta rame sbd yadda cikin yake bata mutuqar wahala, sai wani uban fari da tayi.
Kunnuwa ta kasa kiskirin, tana jin mamanta da yayanta Murtala suna mgna, qasa².
“ Murtala! Wlh da akwai inda zan kai Rabi'ah da na kaita, ganinta agidan nan ba qaramin baqanta min rai yake ba, Allah kana gani kai shedane akan yadda nabawa yarana tarbiya, amman shegiyar yarinyar nan, tai watsi da tarbiyar dana basu taje ta kwaso min abun kuya, ya Allah kamun maganin wannan masifa da ta tunkaro mu...â€
Murtala ya katseta ta hanyar cewa.
“Maama dan Allah kiyi hkr, mu rungumi k'addara, ina zamu turata? Mu muna gudun abin kunya sai muturawa wasu ai sam hakan baiba, kowa yasan gidanmu munada nutsuwa da tarbiya ita da taje ta kwaso abin kunyarta ita da shi, mu rage nuna mata qyama, sabida ba wanda ya isa ya wuce k'addarasa, amman ita wannan koh, Allah ya rufa asiri kawai.â€
Mama ta amsa da.
“Ameen.†ranta duk ajagule.
Rabi'ah hawayen da take dannewa ne suka sulalo, ta sanya tafin hannunta ta goge, dakyr ta iya bud'e busashen bakinta ta furta, “Astagfirullah wa'atubu ilaik.â€
jin motsin Murtala zai shigo d'akin tai saurin ajiye cup d'in ta miqe ta shiga bedroom, tana danne kukanta.
Chapter 109 · 0% Book details