← Book details Dattijon Arziki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 118

Sashe 69

Dattijon Arziki Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Acan kuwa Espagne Rafeek kamar zayyi hauka, lokacin da sukazo da Anee basu samu su Rahma ba, sai su Adeel wanda aue zasuci gaba da kula da gidan.
Anee cikin kuka ta ce“Amman Habibty bata kyauta min ba, ya zata tafi bata fa'damin ba! Toh me ma yasa ita da ko sati batayi ba acekuma ta koma.â€
Rafeek harda hawayensa ya riqe hannayen Anee ya ce“Don Allah idan ta kiraki ki fa'damin wlh na shirya har Tchad zanje idan dai Abie zai ban aurenta.â€
Anee ta ce “Insha Allah da ta kirani zan fa'da maka.â€
Haka suka rabu bayan yakai Anee gidansu kowane zuciyarsa ba da'di.

*Canada*
Washegari Rahma kasa ha'ada idanu tai da Abie ta gudu 'dakinsu tai wankan tsarki tana kuka ta ya za'ace da ubanta tai romantic, har ta jiqe hakan? Koda tai sallah kuka ta fara harda shasheqa tana ta istigfari akan Allah ya yafe mata.
Bayan sunyi breakfast Abie ya shigo 'dakin cikin baqaqen suit wanda suka masa masifar kyau yana baxa 'kamshi takalmin 'kafarsa da agogon hannunsa kawai abin kallone.
Rahma ta gaishesa kanta a'kasa.
Ya amsa yana murmushi ya ce“Meerah ki shirya kayanku nan da 40 minutes zamu tafi Baby zo mana.â€
Rahma ta rufe fuskarta da tafin hannuta.
Abie ya 'karaso bai damu da Meerah ba ya rankwafo ya 'dora tattausan hannunsa saman nata ya miqar da ita tsaye ya mannata 'kirjinsa ya sumbaci kumatunta, yana shafa cikinta murya 'kasa ya mata ra'da akunnenta.
“Babyna menene um? Fa'adamin.â€
Zagaye hannunta tai bayansa ta 'dago kanta ta kalleshi ta runtse idanunta ashagwa'be ta ce“Abie nah kayi kyau mata duk kalleka zasuyi abin haushi wlh sai na fa'dawa Ammi Rayyana.â€
Ta 'karasa mgnar cikin kuka tsakaninta da Allah kuka take tana sake shigewa jikinsa.
Murmushi yay ya 'dago da fuskarta yana goge mata hawayen ya ce“Ok ya isa My Baby ni bazan kallesu ba kinga kuwa ai sunyi banzar ko My Baby?â€
Rahma ta sake nrkewa ajikin Abien ashagwa'be ta ce“Toh Rabin raina wa zaka kalla?â€
Tsakiyar kanta ya sumbata ya manna bakinsa saman kunneta ya sakar mata numfashi me 'dumi sai da ta qamqameshi ta Kira “Abie nah!â€
“Na'am Babyna ke 'daya zanyi ta kallo kinji?â€
Cikin murna ta 'daga kanta.
Meerah mutuwar tsaye ta yi tana mamkin anya Rahma ba matarsa bace wani 'boyayyan lamarine a'kasa amman ko arna ai bazasu irin abin nan ba idan 'diyarsa ce. Sai dai tsantsar kamar da suke yana bata mamaki.
Abie kunya ya ji sosai dan tsakaninsa da Allah ya manta akwai wata halitta bayan su biyu a 'dakin.
Janye Rahma yay yana fa'din.
“Ku shirya yanzu ku fito muje jirgi baya jira.â€
'Karfe 9 na safe jirginsu ya 'daga zuwa Tchad, kamar a farko yanzu ma haka sukayi ita da Meerah wajansu 'daya Abie na gefen damarsu, Rahma bacci take tayi matashi da cinyar Meerah wacce take shafa kanta, jin Rahma take kamar 'kanwarta Uwa 'daya uba 'daya.

*Gabon*
Duk yadda Ma'aruf yake tunanin al'amarin Aishatu ya wuce nan, dan fafur taqi yarda da shi, yana kusantota jikinta zai rikice, dole ya hkr yake baya-baya.
Alhaji babba ya nemi jin dalilin abinda ya ha'dasu ta ce ba komai kawai hakan taji ta tsaneshi kawai arabasu bata son zama da shi.
Al'amarin ya yi zafi dan anyi lallashin duniya taqi, ta ce zata kashe kanta idan Ma'aruf bai fita daga rayuwarta ba.
Munnira zaune kusanta tana riqe da hannunta cikin kwantar da shi murya ta ce.

“Aisha don Allah don Annabi ki fa'damin gaskiyar abinda ya ha'daki da Ma'aruf nasan ruwa baya tsami banza?â€
Aishatu ta ce“Wallahi tallahi har Abadan bazan fa'daba na barma zuciyata kawai dai ya sakeni na yafe shi, na godema Allah ma da 'dan ya rasu.â€
Munnira ta rufe mata baki ta ce“Ko 'danku ya rasu ai agoge bazaki goge jinin Ma'aruf daga jinin ki ba! Hkr kawai zakiyi ki koma 'dakinki idan kin warke kowace mace da kika gani zaman hkr take agidan mijinta duk da'din da zai jiya miki daman dole wani wajan sai kinyi hkr duk kuwa irin soyayyar da kukewa junanku...â€
Ma'aruf ne ya shigo yana fa'din.
Munnira zan miki bayani da kaina sannan zan mata abinda take so matuqar ta yafemin sannan zata ajiye hankalinta.â€
Aisha tai saurin runtse idanunta ta juya masa baya, har yanzu mugun sonsa take amman dole zata haqura da shi hkr na har abadan kallo 'daya ta masa taga yadda ya rame ya yi baqi cikin kwana biyu.
“Munnira ta ce“Yauwa fa'damin Ma'aruf wlh nayi alqawali zan riqe muku sirrinku.â€
Aishatu tana son ta masa mgna kar ya fa'da amman ta kasa,sbd tsabar baqin cikin sake masa mgna take arayuwarta.

Ma'aruf kakaf bai 'boyema Munnira ba komai abinda ya shiga tsakaninsu da Rabi'ah da yadda 'kamshin turarenta ya gigitashi lokaci 'daya.
Ya 'dora da cewa“Munnira komeye ita ce sanadi duk abinda mukayi tsakanin ni da ita har kwanciyar aurenmu sai ta Kira Rabi'ah ta fa'da mata, idan abu na siyomata kafin ya iso gareta yadda ta gansa ahoto kan nakowa ta turama Rabi'ah, idan abinci ta dafa mai da'di kafin taci sai ta kira Rabi'ah kakaf rayuwar aurenmu nida Aishatu ahannu Rabi'ah shin yanzu wa gari ya waya? Ni da ita duk abinda take nasani Ana ban rahoto amman sabida son da nake mata ban ta'ba nuna mata na Sani ba, na rantse da Allah ban ta'ba aikata zina ba sai akan Rabi'ah Allah ya isa tsakanina da Rabi'ah.
â€Aishatu kuka kawai take tanajin zuciyarta na zafi haushinsa takeji duk da ta gano ta inda aka samu matsala bakinta ya jaza mata da yarda da 'kawarta shi ya janyo mata.
Munnira ta ce“Wala haula wala Quwwata Inna billah! Haka abin ya faru? Wlh Aishatu akaso 'dari kaso tamanin laifinki ne. Kai Ma'aruf kana sakaci da addu'a dan wallahi bazanyi kaffara ba turaren sihirine ka shaqa, alokacin da ka shaqa da kayi addu'a tabaas bazatayi nasara akanka ba aniyarta zata koma mata ne, Aisha hkr zakiyi don Allah karki ce ya sakeki ki yafe masa wlh ba laifinsa bane laifin munafukar 'kawarki ne ai daman ni sam yarinyar bata kwanta min ba idanunta irin na munafukai.â€
Ma'aruf ya ce“Wlh idan dai zata yafemi ba damuwa zan mata abinda take so.â€
Ya 'karashe mgnar yana zubar da hawaye ya fice.
Kuka sosai Aishatu take ta rungume Munnira tana cewa“Wlh ni dai bazan yafe ba asakeni kawai...â€

Acan kuwa Tchad.
Tin safe ake girke² gidan ya 'dauki 'kamshi, duk wata cima da Rayyana tasan Abie da Rahma naso an girka, anyi lemuka iri-iri, ko ina sai 'kamshin turaren wuta yake tashi.
Jaddatu abin dariya yake bata yadda Rayyana ta zage Ana girki da ita, Ibtisam kuwa haushin Rayyana ne ya cikata ko hanyar kitchen bata kalla ba, Laraba kuwa da ita akayi komai.
Bayan sun gama girki Rayyana ta kira me make-up aka 'dan'dasa mata kwalliya masha Allah Rayyana ba qaramin kyau ta yi ba, ga wani irin turaren wuta na jiki da tayi wani ratsantsan lace baqi mai adon flowers Ja da fararan duwatsu ta saka, ta sanya wani takami shi ba mai tsayi ba shi ba 'kasa ba ya mata 'dar an zuba gwala-gwalai a wuya da hannu.

Misalin 'karfe 3 na yamma jirginsu Abie ya diro 'kasar Tchad.
Abraham direban Abie da securities 'dinsa Abbas da Khalifah suka tafi airport 'daukosu,dan Abie ya ce kar kowa yazo tarbansu sai sun iso.
Rahma da Meerah na bayan mota ya yin da abie yake gaba motarsu Abbas na bayansu riqe da bindigogi tamkar gwamna.
Rahma lokacin da motocin suka shigo harabar gidansu ta sauke ajiyar zuciya wanda sai da Abie ya waigo ya ce“Ya dai My Baby?â€
'Yar dariya tai ta ce“Abie naji sanyine ganin munzo lafiya nai hamdalah azuciya azahiri na sauke ajiyar zuciya.â€
Kai ya jinjina lokacin aka bu'de musu 'kofa Rahma ta fito Meerah na biyota.
Chapter 69 · 0% Book details