← Book details Dattijon Arziki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 84 OF 118

Sashe 84

Dattijon Arziki Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

“Kamar yadda kika sani sunana Abdulmajid nine babban 'dansu wanda bayana an haifi 'kannena sama da biyar suna mutuwa daga bayane aka haifi Hanan.
Mu biyune Allah ya ba iyayanmu, kowa yasan mahaifinmu a 'kasar morocco Abdulwahab shahararran me ku'dine.
Tinda na taso banda buri sai na son zama sojan qasa da qasa.
Cikin hukuncin Allah kuwa mahaifina ya tsayamin nayi karatu me nisa har na cimma burina na zama cikakken babban soja, wanda alokacin mata suka addabi rayuwata sbd kyawun da Allah ya min ga Ku'di ga zubina irin wanda kowace mace take son mijinta ya kasance.
Sai dai kashhh! Anyi rashin sa'a ni mata basa gabana, aikina kawai nake burina na kare k'asata.
Ana cikin haka aka turamu kwantar da wata tarzoma da ta tashi a iran wanda an kashema 'kasashe dayawa sojojinsu.
Mahaifina yaso hanani gani yake idan na tafi na tafi kenan.
Amman haka kawai naji ina buqatar zuwa 'kasar cike da 'kwarin haka muka tafi.
Kwananmu shidda ana bata wuta wanda Allah ya bamu nasara sosai duk an kashe mana mutane mutum ashirin da biyar, muna murna ranar da zamu tafi, sai ga Kira daga sama, an turama wani 'kasurgumin 'kauye ance an addabi mazauna wajan, alokacin ance an kashe sama da rabin garin an kashe sojojin saura ka'dan.
Haka muka 'dunguma zuwa 'kasurgumin 'kauyen nan.
Abinda muka iske ya yi mugun girgizamu, 'kwarorin jama'a muka iske, anyi ma jama'ar garin kisan gilla.â€
Ajiyar zuciya ya sauke tuna halin da ya tsinto Ummul Aymana alokacin tana cikin mutane da suka samu damar ceta ita ce ta uku ka'de wanda suka tsira, ahannunsu.
Rahma jin Abie ya yi shiru ta 'dago kanta cikin guntun hasken ta kalleshi.
Idanu suka ha'da yana mata 'kur da idanu.
Idanunta ta lumshi zuciyarta na tsanaita bugawa, ta ce“Abie pls kaji?â€
Face 'dinsu ya ha'de yana 'dora hannunsa saman 'kirjinta.
Riqe hannunsa tai, ya girgiza kansa, cikin wata irin murya ya ce“Pls my baby, bar Abienki kinji?â€
Rahma ajiyar zuciya ta sauke ta janye hannunta daga saman nashi.
Hannunsa na damar duka taji ya zura arigar yana shafar 'kirjinta anutse yana sumbatar dukkan fuskarta.
Ajiyar zuciya ta sauke tana jin yadda yake shafar breast 'dinta anutse.
Dakyar ta iya jarumtar kiransa.
“Abie pls labarin cigaba.â€
Ahaka yaci gaba da bata labarin hankalinsa yaji ya kwanta, a yanayin bai ta'ba zaton dukiyar fulanin babynsa sunka haka girmaba ga taushi.

Muryasa kanaji kasan yana cikin wani yanayi da yake masa da'di yay gyaran murya ya ce“My Babyna kina jina?â€
Kai ta 'daga tanajin yadda yake shafar mutanan nasa, ahankali, yana sauke numfashi, idan ta ce batajin da'din yadda yake shafasu ta yi 'karya, kawai dai nauyinsa takeji bazata nuna masa yanayin tanajin da'din ba.
Abie ya sake gyaran murya hannunsa na ririta mutanen nasa.
“Kina ji My Baby?â€
Rahma ta 'daga kanta,tana sauke ajiyar zuciya.
“A 'kauyen *Abyaneh*
Mun shiga tashin hankali 'bangaran da aka turamu mutum uku kawai muka ceta, biyun basu kwana ba suka mutu 'dayan na cemin mutafi da ita duk an kashe danginsu karmu barta don allah mutafi da ita, matashiyar budurwa 'Yar kimanin shekaru 20 wacce muka taho da ita ahaukace sakammakon ganin anyima iyayanta da yayunta da kanninta kisan gilla.
Ataqaice ni aka damqawa amanarta muna zuwa Morocco na kaita asibitin mahauka, Ana bata kulawa Ana magani sai da ta shafe shekara 'daya kafin ta samu lafiya.
Nan ta sake bani labarin Iran da 'kauyansu tabbas duk wani danginsu da ta Sani take taqama an kashe mata su.
Ummi da Abbuna sune suka amsheta da hannu biyu cike da tausaya mata suka maidata tamkar 'yarsu.
Ummul Aymana kyakkyawace tanada 'kananun idanu tamkar naki sai da farinta baika namuba...â€
Rahma ta rushe da kuka ta qamqame Abie ta ce.
“Wayyo Allah Abie mamanace shi kenan yanzu ba inda zaka nemomin dangin mamana Abie?â€
Shiiiii! My baby bari na gama baki labarin zan nemo miki mgnar gaskiya ina zargin Abie 2 'dan uwan mamanki ne, sabida idan kin lura duk a hotone kika santa akwai kama shi da ita, abinda yasa nake zargin ko shine, sbd na koma 'kasar sau uku an tabbatar min akwai yayan ummul aymana ana zargin baya gari aka kawo harin sbd tsabar kamar da yake da mamarki idanu kawai yafita shiyasa na k'yalesa sai ta fashe na tambayesa tarihinsa.
Kafin shekara ta rufe soyayya muke me tsafta nida Ummul Aymana kowa ya Sani cikin danginmu har an saka auremu, ban ta'ba son wata 'diya mace ba sai ita, ina mata son so, haka itama tana sona tana gudun duk wani abun da zai 'batamin rai....
Sai dai kashhh! Ashe 'kanin Ummi anmu Aliyu ya mutu akan sonta bamu saniba.
Ana sati 'daurin auremu aka kwantar da shi hospital ya kamu da ciwon zuciya me tsanani, wanda ance idan ba'a basa abinda yakeso ba zai iya rasa ransa.

“Babu yadda bamuyi ya fa'damana damuwarsa ba, ya ce babu komai, kawai ciwone.
Nine nama Dr mgnar akan cewar ya masa dubara ya gayamasa ko meye insha Allah zai temaka masa.
Ai kuwa ya gayama likita wata yarinya yakeso kamar ya mutu, amman 'dan yayarsa ne zai aureta bikin ya kusa dan haka ya riqe masa amana ya yi alqawalin zai cireta aransa.
Lokacin da Dr ya sanar dani na shiga tashin hankali, matuqa sbd son da nake mata ba na wasa bane, amman tuna ceton rai zanyi wa 'kanin mahaifiyata kawai sai naji 'kwarin guiwar zan iya barmasa ita.
Shirye² ake tayi na biki ba wanda na gayama 'kudirina, sai Ana kwana uku biki na samu Ummul Aymana na mata bayanin kome na roqi alfarma akan ta maida duk wani so da take min akan Aliyu mu ceto rayuwarsa, a 'daura auren da shi.
Kuka dai ba wani abuba ta Sha, ta rungumeni cikin kuka tana fa'din.
“Sojana bazan qi duk abinda yake jininka ba, na amince amman bazan ta'ba daina 'kaunarka ba, sbd sonka ajinina yake tin kafin ka shigo rayuwata nake ganinka a barcina, sai dai don Allah inaso kamun alqawali idan Allah ya bamu haihuwa da Aliyu muka samu mace lokacin nasan ka fara manyanta amman zamu baka ita bakada mata sama da ita, tin tana tsummanta zamu baka ita pls kace ka yarda ina kwa'dayin jinina ya 'hada zuri'a dakai Soja.â€
Ajiyar zuciya nayi na janyeta ajikina na riqe hannayenta na ce.
“Wlh Aymana tin baki Haifa ba har naji son abin na ratsa jinin jikina, na amince Allah ya tabbatar da alkahirinsa.â€
Ta amsa da “Ameen Soja.“

Haka kuwa akayi ranar 'daurin aure Aliyu na can kwance harda su aman jini kawai sai shelar 'daurin auren akaji tsakanin Ummul Aymana da Aliyu kowa yasha mamaki banda Abbuna da Abby dan na musu bayani sun kuma gamsu.
Aliyu labarin da ya zomasa gabaki 'daya komai NASA daina aiki yayi harda suma sai muka kwasa muka nufi asibiti dan dama ya 'buya agida ya dinga aman jini bamuda labari,sai lokacin da akazo masa da labari muka riakeshi ahalin mutuwa ko rayuwa.
Chapter 84 · 0% Book details