← Book details Dattijon Arziki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 118

Sashe 37

Dattijon Arziki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wahida zaune gaban Malam tana kallon yadda yake baje qasa afaifai, yana siddabarunsa.
Sosai ya bada gaskiya akan binci ken da yake yi.
Kallon Wahida
ya yi ya ce“Mgnar gaskiya tsakanin Abdulmajid da Rahma na kasa ganin komai banda wasu taurari masu matuqar haske da nake gani. Amman da fatan ta ci strawberry da na baki yau da safe kika kai?â€
Wahida ta zayyane masa komai kamar yadda Rayyana ta fa'da mata.
Wasu kwalaban turare manya guda 2 ya bu'de ya shafe babban casbi nan mai dubu ya shafa agoshansa da fatar idanunsa ya shiga wasu irin sabbatu yana Jan dogon casbin nan.
Sai da ya kwashe awa 1 ahaka ya 'dago ya kalli Wahida ya ce“Tabb akwai babbar 'kura sbd sihirin jikin Rahma da Ja'afar yana dab da karyewa, sbd ba qaramin tashi tsaye akayi akan lamarin ba. Hanya 'dayace ba 'boye-'boye Raiyanatu ta amince na sadu da ita na ha'da maniyi da nata na mata wani gaggarumin asiri wanda inada tabbacin sai ya kamasu su dukkansu sai yadda tai dasu.â€
Wahida ta ce“Toh ba matsala zan mata bayani anutse idan bata amince ba ita ta sani.â€
Tana fita ta Kira Raiyana ta mata bayani.
Raiyana ta ce“Wlh tsoro nakeji bazan iya aikata zina ba tin farko kinsan duk mugun halina ban sha'awar aikata zina banda aure bare inada miji kamar Abdulmajid bazan iya ba wani kaina ba.â€
Wahida ta ce“Nasan hakan shiyasa nace kiyi shawara.â€
“Wahida ya sake wata dabara bazan aikata zina ba gaskiya, gwara na hkr nifa atsorace ma nake sbd ya gama ganoni fa sabi'de shagu'be da yake min, yana min magana me harshen damu.â€
Wahida ta ce“Ki dai bi asannu ki koyi hkr da siyasa.â€
Sallama sukayi ta koma ta sanar da malam abinda Raiyana ta ce. Malam ya ka'da kafa'da ya ce“Ku ta shafaâ€.

Ja'afar lokacin da yay parking da mota Abie ya fito yana sanye da farar jallabiya milk colour, ya 'dora hirami kansa, tafiya yake cikin nutsuwarsa yana waya ya doshi rumfar shaqatawa. Sai baza 'kamshi yake wani irin annuri na fita kan fuskar shi, baza ka kalleshi kace akwai abinda yake cin zuciyarsa ba, sai baza uban 'kamshi yake.
Ja'afar hango Abie ya saka ya kalli Rahma ya ce“Muje na gaishe da Abie na wuce gida, kinga Baaba Tsalha ya kirani wai nazo zamuyi mgna.â€
Rahma ta sakar masa murmushi ta ce.
“Ok muji Habibyna.â€
Hanan ta ce“Uhmm! Ba ko kunyar suruka ko?â€
Ja'afar fitowa yay yana murmuahi ya bu'de Rahma 'kofa, Raiyana ta fito tana riqe da hannun Iman suka nufi wajan Abie wanda yake cikin rumfar shan iska.
Ummu Adnan suka hango ta kai masa kayan motsa baki ta fito.
Da sallama suka shiga ha'daddiyar rumfar wadda take fitar da 'kamshin Franni.
Abie ya amsa sallamar yana fa'dda'da fara'ar shi, ya na amsa gaisuwar Ja'afar ya kamo hannunsa ya zaunar da shi kusan sa. Ya ce“ Baby ba shi lemo mana. Ja'afar ya mai jikin? Tana bacci ko?â€
Ja'afar ya ce“Eh Abie.â€
Abie ya 'dora iman cinyarsa ya ce“Baby Abunki ya kusa zauwa, ke Hanan ya tin jiya yana kiranki bakya 'dauka?â€
Ya tambayeta yana hararenta ya madai idanunsa kan Rahma.
Wacce ta zauna kusansa ta 'dauki cup 'din da yasha lemun inibi ta shanye sauransa ta ajiye cup 'din ta 'dauki wani ta tsiyayama Ja'afar ta beqa masa.
jingina kanta da kafa'dar Abie tai tana kallonsa, suna mgna da Hanan amman idanunsa akanta yana hararenta. Ashagwa'be can 'kasa² ta ce“Abiena bacci nake ji.â€
Abie suna mgna da Hanan bai katseba sai da ya idar ya ce“No! Bazaki ba Baby.â€
Ja'afar ya rusuna yama Abie sallama.
Rahma ta sumbaci kumatun Abien ta miqe ta tafi raka Ja'afar.
Hanan tana dariya ta ce“Wannan yarinyar taka Abie rigimammace.â€
Murmushi yay ya ce“Toh ya na iya Hanan.â€
Hirasu suka shiga tsakanin ta Wa da 'kanwarsa.
Rahma tana tsaye sai da Ja'afar yaja motar ya tafi yana 'daga mata hannu tana 'daga masa ta jiya ta koma wajan Abienta.

*Gabon*
Misalin 'karfe 8 na dare jirgin su Ma'aruf ya shiga Gabon.
Nura direba yazo 'daukarsa, kai tsaye gida suka nufa.
Rabi'ah kuwa murna sosai take jin Ma'aruf ya ce wajanta zai fara zuwa, girkin da Aishatu ta turo masa shine ta tanadar masa sai lemuka da ta ha'da masa, da dambun nama.
Aishata najin tsayuwar mota ta miqe cike da murna ta leqa ta window.
Anutse yake tafiya waya manne da kunnensa.
Tin kafin ya iso ta bu'de 'kofar yana shigowa ta 'dare samansa tana fa'din.
“Oyoyo masoyina.â€
Sama yay da ita yana 'kyal'kyala dariya ya ce“Aishatuna iyayan rigima ya babyna?â€
Kumatunsa ta sumbata ta ce.
“Wlh kaji yana motsi kamar yasan kana nemansa.â€
Sauka tai ta Kama hannunsa suka nufi saman kujera.
Zaunar da shi tai ta tsiyaya masa lemo mai sanyi ta basa abaki ya Sha.
“Thank u my life. â€
Murmushi tai ta Kama hannunsa suka nufi ciki taje ta ha'da masa ruwan wanka suka tafi ita ta temaka masa yay wanka ta shiryasa tsaf suka nufi kan dining area.
Sosai ta cika masa cikinsa da dadda'dan girkinta.
Rungume take ajikinsa yana kissing 'dinta hannunsa saman cikinta yana shafawa, bata hanashi ba.
Akunne ya mata ra'da “Fa'damin kinyi kewata sosai?â€
Kai ta 'daga masa sbd yadda yake lalubarta da kissing 'dinta ya gama kashe mata jikinta.
Wayarsa tai ringing yay sallon kallonta ya 'dauke sbd kar Aishatu taga sunan Rabi'ah.
Janyeta yay, ya ce.
“Masoyiya zanje gida na dawo.â€
Rigima ta kafa masa sai sun tafi tare, baida za'bin da ya wuce ya tafi da ita sai ya barota gidan nasu daga can yaje wajan Rabi'ah ya dawo ya 'dauketa.
“Ok je ki shirya mu tafi.â€.
Cikin murna ta nufi bedroom'dinsa sbd mafi yawa kayanta na nan.
Tana fita sai ga Uwani da gudu ta iso cikin girmamawa ta zube gabansa ta beqa masa wayar da take record mgnar Aishatu idan 'kawayanta sun zo ko tana waya. Ta 'dora da cewa “Bata wani yawo yalla'bai duk Inda ta tambayeka toh can take zuwa Nura direba na kaita.“
Cikin sauri ya ce“Ok! Ok jeki ngd zan saurara.â€
Miqewa tai ta fice.
Shi kuma daman cikin shiri yake ya leqa bedroom 'dinsa dan ya ga nan ta shiga.
'Karan ruwa yaji ya ce“Wai wanka nema kike? Pls my life ki zauna gobe sai muje na tafi.
Kuka yaji ta saka masa, ya bushe da dariya ya ce“Wasa nake miki ina mota.â€
Yana zauna cikin mota ya fara sauraren irin ta'bargazar sakin zancan da take sam batasan rufawa aurensu asiri ba.
Kai ya girgiza ya ce“Wato Rabi'ah da wannan damar ce zatayi anfani ta shigo rayuwarmu? Toh 'karya kike wlh zan koya miki hankali.â€
Aishatu tana cikin shiryawa 'karamar wayar Ma'aruf ta fara ruri bata 'dauka ba, sai da aka Kira sau biyar ta 'daga da niyar cewa baya kusa taji abinda ya kusa 'dauke numfashinta.
'Kasa ta zauna jikinta na tsuma tana jin kalaman mutumin tamkar zasu tafi da numfashinta.
Saurin kashe wayar tai baki 'dayanta ta miqe dakyar ta shiga toilet taci kukanta ta wanke fuska ta fito da qudirin insha Allah sai Inda 'karfinta ya qare wajan ceto mijinta dan bataji 'digon sonsa ya ragu ba.
Sosai ta sanyama kanta jarumta ta 'ka'kalo murmushi ta shiga motar yana Jan hancinta ya ce“Kin 'batamin lokaci.â€
“Sorry.â€
Kawai ta iya fa'da.
Gidansu ya ajiyeta bayan ya gaisa da iyayasa da 'kannensa ya nufi gidansu Rabi'ah wanda da kwantaccan yazo har qofar gidan.
Har falon baqi wanda yake 'dan qarami sbd basuda wani 'karfi nan ta ajiyesa ta jera masa komai na ci gabansa tai serving 'dinsa
Ma'aruf ya 'kyal'kyale da dariya ya ce“Wai kina nufin irin girki matata kika min? Gaskiya na qoshi ta cika min cikina dam, sannan me ya saka kika za'bi kici amanarta bayan ta yarda dake?â€
Rabi'ah kukan kissa cike da takaicinsa ta saki tana fa'din.
“Ba laifina bane ba zuciayta ke sonka.â€
“Ok naji bari kuka amman abinda nakeso dake ki bari idan ta haihu sai ki tinkareta ki nemi alfarma kice ta amince na aureki idan ta yarda ba matsala zan temka miki kiji abinda ta kwa'daita ki da shi, idan kuma bazaki iya tunkartaba karki sake kirana.â€
Yana gama fa'damata hakan yasa kai ya wuce daga falon.
Rabi'ah ta duqe tana sakin kuka mai ciwo, amman ta qudirta aranta sai ta 'dauki mataki akan Ma'aruf.

*Tchad*
Misalin goma na dare Tanko da Laraba suka shigo Tchad cikin garin Ndjamena.
Yahaya direba Abie ya tura ya 'daukosu.
Laraba tinda motar ta shigo tamqameman gidan na Abie ta fara zaro idanu tana dafe 'kirjinta ta ce“
Na shiga ukuna! Baban Ibtisam ina aka kawomu nan? Karfa siyar damu akayi.â€
Yahaya dariya ta ku'buce masa yana fitowa ya bu'de musu qofa suka fito.
Laraba jikinta ko ina rawa yake tana kallon ko ina haske ra'dau tamkar Rana sbd waau irin 'kwayayan fitulu masu haske da bada Kala.
Malam Adamu ya taresu ya musu jagora har ciki ya nuna musu 'dakin wanda yake ware ya ce“Abie ya ce Ku zauna anan kafin ku tashi tafiya wajan, sannuku ya hanya?â€
Tanko ya amsa “Alhmdllh! Muje sai kiyi wanka ki huta.â€
Abie 2 ya iso yana musu sannu da zuwa ya kira Rahma awaya ya ce Latifa ta kawo musu abinci.
Rahma tana falon cikin sa'a ta kira Latifa ta saka ta kai musu abinci.
Adaren Abie ya musu jagora zuwa asibitin Ibtisam na barci Dr ya ce su koma dan basa buqatar kowa kusanta akwai ha'dari hakan.
Washegari tin safe Abie ya fita dasu domin ayi musu passport.
Cikin ikon Allah kwana uku kacal an gama passport Abie ya nema musu biza aka fara shirin tafiya wanda jirgin dole sai zuwa jibi zai ta shi zuwa Australia.
Laraba tin tana kukan halin da Ibtisan take ciki har ta hkr ta barwa Allah, dan jiya dukan tsiya ta mata wanda taurin kanta ne ya janyo mata, sbd ance tabar shiga idan ba bacci take ba Abie kawai yake iyamata sai Dr.
'Bangaran gidan ma tin tana 'kauyanci har ta saba da wannan 'katon gida har lambu take zuwa batada aiki sai tsinko lemu da guiba da magwaro.
Chapter 37 · 0% Book details