← Book details Dattijon Arziki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 118

Sashe 13

Dattijon Arziki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gaba É—aya 800
Via 6850917335 Na'ima Shu'aibu Sulaiman Fidelity Bank, masu tura kati 08167888934 ga ƴan uwa na Niger +22796515805 za ku tuntuɓa. To show evidence of payment 08142105218

*Real Ladingo+22796515805* For more information😇

_*🤲ðŸ¼Ya Allah ka jiÆ™anmu kayi mana rahama badan halinmu ba.ðŸ™ðŸ¼*_
2/2/22, 09:19 - Buhainat: _*DATTIJON ARZIƘI*_

*BY*
_Rahma ladingo Ummu Fareesa😘_

*🔥FITATTU HUƊU🔥*

_*HOME OF QUALITIES WRITERS ASSOCIATION*_

_Ba wai tarin zallar soyayya ba ce kawai acikin wannan tafiyar, akwai tarin abubuwa tare da sarqaqqiyar mai wuyar warwarewa, akwai abubuwan anfanuwa masu tarin yawa cikin labarin dattijon arzi'ki. Sai dai A 'Bangaran soyayyar kuma abin akwai dagula lissafi, amman... Kuma fa zata 'kayatar zata burge zata bada citta matu'ka.🥰_

*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*

_*cнapтer 15&16*_

Wani dattijo ne gefen titin zaune fari ne, sa dai alamun datti ya zauna jikinsa sosai. kayan jikinsa duk sun tsufa sun fara cirewa, ya lullub'e rabin jikinsa da wani tsohon bargo. Robace irin ta almajirai da suke bara agabansa, da sandarsa ya na 'dagawa alamar bara yake, abin gwanin ban tausayi.
Rahma ta 'kura masa kywawan 'kananun idanunta, cike da mugun tausayin sa, ta ce.
“Ya Allah! Wannan bawan Allah ina family's 'dinsa yake zaune anan neman sadaka? Yahaya idan danja ta sakemu ka zaga wajan wancan tsohon zan basa sadaka.â€
Ta 'karashe maganar cikin shashe'kar kukan da bata san ma ya akayi ya su'buce mata ba.
Kasancewarta mai tsananin tausayi.
Yahaya ya ce“Hajiya meye toh na kuka? Kiyi hkr, jifa² idan nabi nan na kan gan shi.â€
Abbas ya ce. “Kawo akai masa ba sai kin fita ba.â€
Rahma ta girgiza kai tana fad'in.
“A'a muje dai.â€
Danja ta sakesu Yahaya ya zagaya da motar dab da inda dattijon yake zaune, yay parking.
Abbas ya fito ya bu'de mata 'kofar.
Handbag 'dinta ta bu'de ta ciro ku'di 'yan (1000 fran CFA).
Sun kai na jaka 20 ta fito ta isa wajan dattijon da sallama.
Abbas na tsaye abayanta.
Tsohon ya amsa sallamar.
Rahma ta rusuna gabansa da harshen larabci ta ce“Abba ina dangin ka kake bara anan? ai kayi tsufa sosai zamuje ka kaimu gidanka naga iyalinka zan 'dauki nauyin abincin ku da abin shanku.â€
Kuka ya saki yana magana irin tamasu karyayyan harshe.
“Allah sarki banda 'da banda jika banda mata, iyayena sun rasu tin bansan kaina ba, banda kowa sai Allah anan nake wuni na samu sadaka na siyi abinda zanci na koma kangon da nake zaune.â€
Rahma ta saki kuka ta kama hannun dattijon ta ce“Ta shi muje gidanmu daga yau kayi 'yan uwa da kowa...â€
Abbas ya ce.
Hajiya ki barsa ki dai basa sadaka don Allah mu tafi.â€
Rahma ta ce“Ba damuwarka bace malam ka kula da lafiyata akace ba wai ka tirsasani ba nabar abinda nayi niya. Temako nayi niyar yi meye toh aciki? duk abinda na zarta nasan ya zartu Abie bazai tab'a 'kin abinda na kawo da zumar na temaka masa ba.â€
Dattijon ya ce“A'a ngd barni naci gaba da rayuwata ahaka har lokacin mutuwa ya riske ni.â€
Rahma ta ce“Abbas kamasa muje gida na fasa ma zuwa yawon.â€
Abbas badan ransa yaso ba, ya kama dattijon ya mi'ke suka nufi mota.
Jama'a sai kallonsu suke dan basu ta'ba ganin wanda yazo 'daukarsa ba, sai dai abasa sadaka idan magarib ta yi ya tafi yana dogara sandarsa dan bai ko ganin kirki haka mutane suka fuskanta.
Bayan motar ya sanyasa Rahma ta zauna kusansa, Abbas ya koma mazauninsa. Yahaya yaja motar yana fad'in.
“Ina zamuje yanzu?â€
Rahma ta ce“Gida mana.â€
Yahaya ya ce“ Amman Hajiya da kin nemi izinin Yalla'bai.â€
Rahma takaici ya saka bata sake magana ba, kasancewarta marar son maimaici akan mgna, yanzu zata harzuqa tamkar mai jinnu, shiyasa ta sharesa, ta 'dauki wayanta, ta dannawa Abienta Kira.

Daga can Gabon Abie da yake tsaye 'kofar company, suna sallama da ba'kin da suka gudanar da taro.
Bugu 'daya ya 'daga kiran tare da sallama, yana sakar mata Sumba ta wayan.
“Muahhhhh! Baby I miss u so much. â€
Ya qarashe mgnar ya na ke'bewa daga cikin jama'ah.
Rahma ta karkatar da kanta ashagwa'be ta ce.
“Uhmm Abie ba yanzu muna chart ba, kace na jiraka ka sallami ba'ki? na sauka zan baka labari mai da'di Abie nawa.â€
Ta 'karashe mgnar tana murmushi.
Daga can Abie ya shafi yalwatacciyar sumar kansa, zuwa gemunsa ya Saki 'kayataccan murmushi ya marerece kamar wani matashi 'dan kimanin shekaru 25 ya ce.
“Baby ummina pls gayamin menene um?â€
Rahma ta ce“Naqi Abie sai mun ke'be ina cikin mota na fasama zuwa yawon mun juya gida.â€
Daga can Abienta ya waro idanunsa waje ya ce“No! Baby pls mana kije kinji?â€
Rahma ta ce“Wayyo Abie na fasa bye.â€
Ta tsinke kiran ta mayar da wayan cikin Jakarta.

Ja'afar Masha Allah ba laifi suna samun ku'di ka'dan², cikin satin da sukayi a Tchad.
Baba Tsalha na nema masa aikin tu'ki har yanzu dai ba'a dace ba, shi Ja'afar bai wani son driving 'din.
Ya siyi layi suna gaisawa da 'yan gidansu, harda Ibtisam, ta wayan Tanko.
Yau da wuri suka dawo daga wajan aiki, wanka yay ya sanya jans da t-shirts, sai 'kamshi yake, ya gyara sumar kansa, Masha Allah, su Ja'afar ba'kin buzu akwai kyawu.
Zaune suke a tsakar gidansu, sai zuba suke, shi kuma yana gefe waya ri'ke a hannunsa, ya na latsawa duk ta ko'de.
Kiran gida yake baya samu.
Tsaki yaja “Mtswww!†cikin dadda'dar muryasa ya ce“Na tsani rashin network 'din nan fa, ku tashi mu zagaya a'kafa muga gari.â€
Harisu yay dariya ya ce.
“Duk rashin jin Ibtisam 'din ne?â€
Idanuwansa ya lumshe ya bu'de ya mi'ke ya zura hannunsa cikin aljihunsa,ya ce“Allah ya mana bu'di na alkhairi na tura mata ku'di ta siyi waya, muje zagaye don Allah.â€
Dariya suke masa, da tsokana bai kuma tanka su har suka bar gidan suka fita zagaye.

*Niger*
TAHOUA

Ibtisam zaune ta yi tagumi yau duk bataji muryan Ja'afar ba, batada nutsuwa Babanta baya gari sun tafi (Bouza).
Laraba tana fifita wuta ta 'dora girkin dare. “Ibtisam! Zo nanâ€.
Baki ta turo gaba tana matso 'kwalla ta mi'ke ta taho kamar wacce 'kwai ya fashewa aciki.
“Ga ni Anna.â€
Ta 'karashe da murya kamar zatayi kuka.
Laraba ta ce“Gyara min kayan sai kije kiyi ta famar ba'kin tunanin ba'kin yaron can tinda Allah ya 'dora miki jaraba.â€
Ashagwa'be ta ce“Ni Babana nake tunawa, ai da yana nan da mun gaisa da Ja'afar...â€
Maka ta kai mata, ta goce aguje ta nufi 'daki.
“Dawo ki gyara min kayan miyi ko wlh na jibga miki tsinannan duka, ai jarabarce ta hanaki zuwa islamiyya kikace kanki na ciwo Aydah ta fa'dan lafiyarki lau. Munafuka
tinda ke bakisan inda yake miki ciwo ba.â€
Ibtisam ta fito tana goge hawayen fuskarta, rashin jin Ja'afar ayau ba 'karamin tayar mata da hankali yake ba.
Tana tsakiya da gyaran kayan miyar ne wani yaro ya shigo da sallama, ya ce“Ana sallama da Ibtisam.â€
Ibtisam ta ce“A'a wlh ba dai ni ba...â€
Laraba ta ce “Sai ubanki ko? Ta shi dan ubanki. Kai waye me sallamar?â€
Yaron ya ce“Wlh ban sansa ba amman alhajine aqatuwar mota.â€
Laraba ta gwagwalo idanu ta dafe 'kirji ta ce“A me? Mota fa?â€
“Eh wlh mota.â€
Ya fa'da yana fita.
Laraba ta warci mayafi ta nufi qofar.
'Dam ta le'ko karaf idanunta sukasauka akan wata jibgegiyar mota fara kirar Ferrari, wani mutum tsaye zai kai kimanin shekaru arba'in, wankan tarwa'da mai bu'dadd'an hanci bakin wannan gari guda idanunsa kamar na biri😂.
Laraba ta dafe 'kirji ta ce“Shi kenan ubangiji ya amshi ro'kona, yarinya zata shiga gidan huta haka babban mutum wanda yasan darajar mace.â€
Aguje ta iso ta ce“Maza dan ubanki jeki babban kamune, wlh idan kika masa rashin kunya ni dakene.â€
Ibtisam ta fashe da kuka ta ce“Wlh kowaye ban sonsa Ja'afar 'dina nake so.â€
Laraba da qarfin tsiya ta saka Ibtisam fita wajan.
Daga nesa Ibtisam ta tsaya tana addu'a dan ita tsoronsa ma take ji.
Baki ya washe ya ce“Ba gaisuwa baby? â€
Ibtisam ta ce“Baba ina yini? Kayi hkr babana baya gari.â€
Alhj Jamilu ya ce“A'a ni ban haifeki ba, zance nazo, wlh ina sonki inada mata da yara uku, mgna nazo muyi ta fahimta kinji.â€
Ibtisam ta ce“Don Allah kayi hkr inada wanda nakeso yana sona Allah ya baka agaba.â€
Ta na gama fa'din haka ta shige ciki yana kiranta ya bata Ku'di ta'ki komawa.
Ashe laraba tana lab'e tako shiga jibgarta tana fa'din.
“Wlh sai kin aure shi bazaki mana asaraba shegiya uwar ba'kin ciki.â€
Ibtisam taci kukanta har ta gaji dan ta daku. Yaro aka turo da 'katuwar leda shaqe da kaya. Laraba baki yaqi rufawa lokacin da ta bu'de taga kayan lashe², harda turaruka sabulu da ku'di jaka arba'in.
Ihu tadinga yi ta shi'de tukunyar tuwon ta ce“Wallahi gasashen nama zamuci da lemon Oriba, jaka arba'in afarkon dance?â€
Baki 'daya Laraba ta ru'de sabida murna, yayin da Ibtisam ta la'be tana kallon ikon Allah wajan uwar tata.

Unguwar Moray
Inna mai waina zaune gindin murhu tana girkin dare, Deluwa na wanki salad su na ta'ba hira. Mahmoud 'kanin Ja'afar ya shigo da sallama ya be'kawa inna mai waina waya.
Amsa tai tana washe baki ta ranga'da sallama.
Ja'afar ya gaisheta daga can, ya 'dora da fa'din. “Inata nemanku yau shiru innata fatan kuna lafiya?â€
“Yaron kirki duk lfyrmu lau wayan babanka ruwa ta fa'da yau ta'ki tashi shiyasa baka jimu ba. Fatan kana lafiya?â€
Ya amsa mata“lafiya lau, ya kowa da kowa? agaishemin su.â€
“Zasuji ya aiki? Har yanzu ba'a samu mai 'kwari ba? Allah ya temaka ya yi bu'di na alkhairi.â€
Deluwa ta ba wayan su ka gaisa tai masa fatan alkhairi, yama Mahmoud sallama ya ce zai kira zuwa dare idan Babansu ya dawo gida...
Chapter 13 · 0% Book details