← Book details Dattijon Arziki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 118

Sashe 6

Dattijon Arziki Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Tsaye take gaban shower ruwa masu d'umi suna sauka tsakiyar kanta, amman gashinta ya na lullub'e cikin hular leda bataso ya jik'e, idanunta a lomshe sai tagwayen ajiyar zuciya take saukewa, ajere-ajere.
Sosai take jin dad'in yadda ruwan yake ratsa kowane kafar hudodin gashin jikinta.
Murya Latifa taji tana bugun k'ofa tare da fad'in.
“Uwar d'akina don Allah ki bud'e ga Jaddatu can na k'ok'arin hawa beni.â€
Rahma jin abinda Latifa ta ce ya sakata saurin bud'e kyawawan k'ananun idanunta, masu tsananin lumshewa tai saurin janyo towel mai girma ta d'aura ta fito cikin sassarfa.
K'ofar ta bud'e.
Raiyana da Latifa tsaye, suna rarraba idanu.
Fuskar ba yabo ba fallasa cikin zazzak'ar muryata ta ce.
“Uhm! Tana ina Jaddatina? Keko Latifa hawayen me kike? Jaddati barazana take dan na sauka nasan halinta da son rayuwarta, kamar ba zata mutuba!ba zata hayo ba, ga ninan zuwa.†Latifa ta ce“Wlh sanda ta kwad'amin wai sai nabar gidan nan, don Allah zo ki rabani da ita.â€
Rahma ta dafe kanta ta ce“Oh! Ya Rabbi! Ok ina zuwa.â€
Ta k'arashe mgnar tana k'ok'arin juyawa, dan sun saka ta yi mgna sosai.
Raiyana ta ce“ daughter! Don Allah me na miki kike fushi da ni?â€
Rahma ta juyo ta saki guntin smile wanda ya k'awata fuskarta ta shafi fuskar Raiyana cikin sanyinta ta ce“Ammi ba komai fa, kawai yau ban tashi da yanayi me dad'i bane ba.â€
“Ayyah! Sannu toh ki shirya ki fito don Allah, Abineki nata kiran Ummi.â€
Kai ta d'aga ta juya ciki, Latifa ta zauna k'ofar d'akin ta ce“Aunty Raiyana kije zan jira ta fito muje tare, ita kad'ai zata rabani da Jaddatu.â€
Raiyana ta tafi tana dariyar mugunta.
Wayanta ta kunna ta shiga shirya jikinta, cikin mintinan da basu wuce biyar ba ta shirya cikin riga da siket kayan Indian, ruwan toka abinka da fara fata, sosai su ka mata kyau, ta fesa turare ta saki gashinta, saura gefen fuskarta sauran har tsakiyan banyata, ta yi kyau sosai kamar ka saceta ka gudu, sai baza k'amshi take.
Fararen hannunta masu zanen Jan lalle ta sanya ta d'auki wayanta, fuskarta ba wata walwala ta latsa number Abineta ta danna masa Kira, ta nufi k'ofar fiti.

Zaune yake tsakiyar manyan mutanen da suke gudanar da meeting, harda gwamna, yaji ringing d'in wayan da mafi yawanci da layin suke waya da Rahma, sam ya manta bai bar wayan cikin mota ba, yadda yabar sauran biyun.
B'oyayyar ajiyar zuciya ya sauke, lokaci da ya zaro wayan cikin aljihun gaban rigansa. Kallo d'aya yama kiran ya sanya wayan a silent, yana sauke wani irin fitinannan numfashi ya Kira sunan Allah cikin ransa, yasan Baby ummi na cike da kewarsa.

Rahma jin bai d'aga kiran ba, tai rau-rau da k'ananun idanunta masu mutuk'ar kyawu farare, ta bud'e k'ofar ta fito.
Kallon Latifa tai tana zaune sai zazzaro idanu take kamar tama sarki k'arya.
Da hannu tama Latifa nuni ta mik'e su tafi.
“Yauwa uwar d'akina maganin kukana, don Allah ki lallashi Jaddatu ta barni ina son zaman gidan.â€
Rahma tai murmushi suka nufi matattakalar benin.

Raiyana kuwa d'akinta ta shige ta zauna tana kiran number Auntie Saro.
Bugu d'aya Auntie Saro ta d'aga daga can tana fad'in.
“Toh uwar gajan hkr wani abun ko?â€
Raiyana ta ce“Humm Auntie bazaki saurara kiji da me nazo ba? Nifa kinga agaskiya bazan d'auki wulak'ancin uba ba na d'auki na d'iyarsa, haba! Abin yayi yawa, yarinyar nan jiji da kai gareta, ke muma fa jansin larabawane, banga wata d'agawa da zasu mana ba, dan suna larabawan Marooco ...â€
“Ke! Raiyana ki rufawa kanki asiri ki zauna gida mafi daraja da miji mai kima da daraja da dattaku,yanzu kaf layin unguwarmu da gidanmu ake kwatance, ko kinfi son kizo mu zauna mu had'u muna zawarci ana zaginmu a unguwa? Bakya tausayin kanki, shekaru talatin da d'oriya baki aura ba Allah yaji k'anki ya miki gyad'ar dogo, amman kikeson watsar da ni'imarsa ki kaso auren? Toh wlh ba ruwana, wannan yarinyar da ba damuwa tai da lamarin mutane ba me zata miki?â€
Raiyana jikinta yay sanyi ta ce“Uhmm! Auntie Saro bazaki ganeba, tsakani da Allah dan dai najima banyi aure ba nayi shine sai na d'auki cin fuska? Ni fa bansan me na mataba take shareni.â€
Saro ta ce“Dan Allah ki sawwaqa ma kanki da damuwar mutanen gidan nan, zauna kici arzik'i iya cinki idan kinci kin tara bai kusancekin ba sai musan yadda zamuyi akwai hanyoyi masu sauqi fa!â€
Raiyana ta ce“Nifa mugun sonsa nake ba wai kud'in kawai nake so ba.â€
Auntie Saro ta kwantar mata da hankali tana fahimtar da ita abubuwa daban-daban tabi asannu har ta fahimci wasu abubuwan ta watsar da mgnar Rahma.

Jaddatu tin daga nesa take fad'in.
“Taje ta shiryo miki k'arya ko? Latifa akwai naci wlh.â€
Rahma zama tai dab da Jaddatu ta kwantar da kanta kafad'arta ta rungumeta tana sakin murmushi, ta shafi fuskarta, tai mata kiss akumatu ta ce“Ina sonki Jaddatina.â€
Ta kalli Latifa ta ce“Jeki karki damu.â€
Latifa ta zube gaban Rahma ta ce“Ngd Allah ya tsareki da tsarewarsa uwar d'akina insha Allahu miji mafi daraja da tsad'a za ki aura.â€
Ta mik'e ta tafi cikin murna.
Jaddatu bata ce komai ba, ta sumbaci goshin Rahma ta ce“Je kiyi abinci, meyasa kika kashe wayanki Abdul Majeed ya buwayeni da Kira? Me Raiyana ta miki kika shareta?â€
Rahma ta yamutsa fuska tana rau-rau da k'ananun idanunta, ta turo jajayen k'ananun labb'anta gaba ta ce“Yo ni me nayi?â€
Daga wannan mgnar bata sake magana ba, ta janye jikinta ana Jaddatu ta nufi k'aton dining area d'in mai d'auke da kujeru 12.

Bayan ta idar da cin abincin ta dawo falon, Raiyana da Jaddatu sunata hirasu.
Bata ce musu komai ba, daman sunsan bazata ce ba, ta shige jikin Jaddatu ta canza channel, zuwa MBC 2 tana kallon wani film na larawa. Sosai ta shiga kallonsa atsanake.
Raiyana ta kamo lallausan hannun Rahma ta ce“Baby ummi! Abienki ya ce idan kin ta shi kinyi abinci muje akai mu ki zagaya k'afafunki.â€
Rahma ta juya kyawawan k'ananun idanunta, ta ce“No! Ammi Thanks bari sai gobe.â€
Raiyana ta amsa da “Allah ya nuna mana.â€
K'asan labb'anta ta amsa da.
“Ameenâ€
Abdul Majeed aranan bai samu kansa ba sai dab da magarib ya shigo gida, acan b'agaransa na k'asa yay alwala ya tafi had'add'an masallacinsa da yake game da gidan, wanda k'ofofinsa suke daga waje, wanda, bai fito ba sai da akayi sallar isha'i, shima yana fitowa ya taras da bak'o ak'ofa wanda masu gadi sun hanasa shiga sun ce ba'a fad'a mu su bak'o zai zo ba.

*Niger*
Su Ja'afar sai kusan goma na dare suka shigo garin damagaram, agajiye sabida sosai direbansu yay gudu.
Bayan bus ta saukesu nan cikin k'aton gidanta na ( *Sonef*) akwai bandaki wajan wanna ga bokatai nan da panpo.
Bayan sun yanki ticket d'in zuwa diffa, wanda bus d'in zata tashi k'arfe 4:30 am na asubah, wanka sukayi su ka siyo abinci sukaci, daman sunyi sallolinsu ahanya, suna gama cin abinci suka kwanta.
Ja'afar ya kasa bacci sai juyi yake yana tunanin iyayansa da Ibtisam.
“Ya Allah!â€
Ja'afar kira cike da damuwa kwance akan kyakkyawar bak'ar fuskarshi.
Wayansa ya zaro tuna lokuta da dama, Ibtisam na kwana da wayan Babanta, wajanta, idan ya bata tai game, sabida yanada waya mai yin WhatsApp sabida 'yan uwansa nan Cameron.
Ta nan suke samun suyi zumunci sabida kud'in kira tsada.
Cikin k'warin guiwar samun Itibsam Ja'afar ya kira number Tanko.
Chapter 6 · 0% Book details