← Book details Dattijon Arziki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 118

Sashe 39

Dattijon Arziki Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ja'afar gaban mahaifinsa ya zube ya riqe 'kafafunsa ya ce.
“Don girman Allah Baaba kayi hkr ka yafemin na tuba bazan sake ba, wlh banqi bayyana muku Ibtisam na wajena ba, da wata manufa sai dan....â€
Laraba ce ta katse shi ta hanyar fa'din.
“Qarya kakeyi baqin munafuki da gangan ka...â€
Tanko ya rufe mata baki ya ce“Wlh kina sake mgna zan baki mamaki.â€
Adamu ya ce“Ja'afar ka ban mamaki wlh banzaci hakan daga gareka ba, yanzu gashinan ka janyoma yarinya mummunan ha'dari dalilinka.â€
Manyan idanunsa ya firfito yana fa'din.
“Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!â€
Ja'afar ya miqe hankalinsa atashe ya kira baba Tsalha awaya sukayi mgna ya kirasu Harisu duk sukayi mgna ya fice ya shiga mota yabar gidan.
Abie 2 ya ce.
“Adamu wannan yaron sai an masa uzuri abubuwan da suka faru, baya haiyacin sa, daga shi har Rahma kuma nasan kasan hakan, wannan ma shedace.â€
Abie suka shigo da sallama, yana duddubawa baiga Ja'afar ba.
Lura da hakan ya sanya Abie2 ya ce.
“Yana zuwa.â€
Zama yay, yayin da Rahma ta koma wajan Abie 2 tana son masa tambaya ta kasa ta shiga bin kowa da kallo.
Ja'afar bai rufe 30 minutes ba sai ga shi dasu baba Tsalha.
Bayan gaishe² Baba Tsalha ya shiga basu labarin Ja'afar tin randa ya 'daukosu daga tashar mota, har zamansa gidansa suna haya da zuwan Ibtisam wadda ta zauna ahannunsa wajan matarsa, da neman shawarasa da yay,akan zai maidata gida.
Ya 'dora da cewa.
“Wlh Ja'afar ba lalataccan yaro bane, sbd ana gobe zamuje Cameron wajan yayar mahaifin Ibtisam, wannan Iftila'in ya sauko musu.â€
Kowa ya yarda da mgnar baba Tsalha sbd kakaf ya girme musu shekaru nesa ba kusa ba, ga kuma su Harisu awajan sun bayar da shaidar hakan.
Abie 2 ya 'dora da fa'din.
Alhmdllh! Kawai zamuce amman yaran nan sun ha'du da sharrin jinnu wanda yake na ture ne ya shigesu sun qulla alaqar soyayya wacce basa haiyacinsu, lura da hakan yasa muka shiga kai kukanmu wajan Allah akan ya warware lamarin, idan kuma wani alkhairine sanadin hakan ya tabbatar mana da shi, toh Alhmdllh Ja'afar and Rahma kunji yadda kukayi soyayya ba tare da kun sanma kunyi ba ayanzu daman akin sihirine yay tasiri.â€
Ja'afar ya furta.
“Hasbunallahu wa ni'imal wakil,la haula wala quwata Inna billahil alliyul azeem! Ibtisam ki yafemin ki yafemin natuba haqiqa na cutar dake acikin rashin sani.â€
Gaban Tanko ya rarrafa ya riqe 'kafafunsa ya ce“Don Allah baba ka yafemin wlh sanin kankane idan ina haiyacina babu wata 'diya mace da zan kalla da sunan so bare har na juyama Ibtisam baya, don Allah Ku yafe min.â€
Tanko ya rungume Ja'afar ya ce“Wallahi ban ta'ba jin haushinka ba, tinda nasan me ya faru nakuma San kana son 'yata dan haka wlh na baka ita duniya da lahira, da zaran ta warke za'ayi bikin Ku.â€
Ja'afar ya shiga ma Tanko godiya.
Mal Adamu ya ce.
Ai ba nan gizo yake saqar ba Ibtisam fa yanzu da mutum 'daya take yarda Abdulmajid.â€
Abie gabansa yay damm, sai ya saki murmushi ya furta.
“Ai wannan ba matsala bane yanzu dai tinda abubuwa sun warware Shamsu muna nemawa 'danmu auren Ibtisam a 'daura ko zuwa gobe ne sai muje da shi akwai dubarun da za'ayi insha Allah sai ya dinga saka mask irin fuskata yana kulawa da ita.â€
Sosai kowa yay na'am da mgnar, banda Laraba da ta tsani Ja'afar.
Ja'afar ya riqe qafafun Abie yana masa godiya. Ya na fa'din.
“Wlh ban ta'ba zaton akwai masu ku'di irinka ba aduniya.â€
Abie ya ce.
“Karka damu wlh na 'daukeka tamkar 'dan cikina sbd kanada hankali cikin samarin yanzu da wuya asamu irinka mai tsoron Allah da riqe amana.â€
Haka taron ya tashi kowa na sakama Abie albarka temakon da zaiyi Ibtisam ta dinga kallon Ja'afar matsayin Abie.
Washegari kuwa bayan sallar juma'ah a babban masallacin wanda yake mallakin Abie, bayan waliyan ango da amarya sun bayyana da shedu bayan anyi komai akan tsarin musulumci aka 'daura auren Ja'afar da Ibtisam akan sadaki mafi daraja wanda Abie ya bayar, basu bar masallacin ba, sai da aka kuma sauke Qur'ani mai girma.
Duk wanda ya ga Ja'afar ayau yasan yana cikin farin ciki da samun abinda yafi so ya mallaka, sai dai wani gefe ganin halin da Ibtisam 'dinsa take ciki yana 'daga masa hankali..

Cikin kwana 'daya da wuni Abie ya shiga ya fita, abinka da mai ku'di, har an samu passport 'din Ja'afar har biza.

*Niger*
Inna Hansatu mai waina sai suntiri take tsakanin bayi da waje.
Bata wucce minti goma cikakke, sai ta koma aguje, sbd zawo take tin lokacin da Mahmoud ya kawo mata waya, Mal Adamu ya fa'da mata an 'daure auren Ibtisam da Ja'afar ta sanya musu albarka.
Yanzu ma aguje ta shige tana gwalo idanu waje.
Sadiya da Nuratu 'ya'yanta sun shigo kenan, suka hangota har suna ha'da baki wajan cewa.
“Inna lafiya kuwa?â€
Deluwa da take zaune ta ce.
“Ina fa lafiya daga jin labari ta tayar da hankalinta sai zawo take, taqi kuma tasha magani.â€
Zama sukayi suna fa'din.
“Subahanallahi!â€
Maimou ta ce“Dan Allah su aunties idan ba rigimar inna ba, meye dan Ya Ja'afar ya auri Ibtisma tana halin jinya? Duk ba dalilinsa bane hakan ta sameta ai, ba wanda ya cancanci zama da ita sai Ya Ja'afar ko?â€
Inna da take fitowa tai jifa da buta tana tafe a 'dan duqe ta ce.
“Inji uban waye yace 'dana ya cancanci zama da ita? Uban wa yace taje can ta iske shi? Wlh Allah yana gani ni wannan auren ina baqin cikinsa banyi farin ciki ba, yaro qarami ya qare ajinyar mahaukaciya sbd Allah. â€
Nuratu ta miqe tana kwance goyen 'danta Ra'ees ta bama Deluwa ta amsa tana masa wasa.
Ta nufi wajan inna da ta ra'be 'kofar bayin tana surfa ruwan masifa.
Nuratu ta kamota tana bata hkr.
“Haba innarmu kiyi hkr ba'aja da lamarin ubangiji don Allah kiyi shiru bari fa'din mugun alkaba'i akan auren 'dan lelenki. Ke! Maimou amshi siyo mata 'dan hakkin da ka raina ta Sha yanzu zawon zai tsaya da izinin Allah.â€
Zaunar da inna tai saman tabarma tana lallashinta, ba wanda yay qoqarin saka baki masifar ta dawo kansa.
Bayan Maimou ta kawo maganin inna ta sha dakyar Nuratu ta bada ku'di aka siyo mata indomie da kwai ta shiga ci tana santi.
Sai da ta nutsu Nuratu ta ce“Innata dan Allah karki sake cewa komai akan auren nan, kinji?â€
“Inna ta ce“Wai daman shine abinda ya kawoku?â€
Sadiya ta ce“A'a Inna ba shi bane kiyi hkr dan Allah.â€
Nuratu ta kira Ja'afar cikin sa'a ta same shi, ganin ita ce ya katse kiran ya kirata.
Da sallama ta fara.
Ja'afar ya ce“Inada niyar kiranki anjima yau da dare muke tafiya. Kinga innata bata 'daukan kirana fa!â€
Nuratu tai murmushi ta ce“Ya Ja'afar barka Allah ya sanya alkhairi yaba Ibtisam lafiya, ya kaiku lafiya, ga innar ta huce yanzu zata sanya albarka insha Allahu.â€
Ta mannawa inna wayar akunnenta.
Ja'afar cikin kwantar da murya ya ce.
“Assalam ya mahaifiyata ki daina fushi da 'dan lelenki.â€
Inna ta buntsiro baki kamar yana ganinta ta ce.
“Kaci sa'a ina sonka na hkr amman wlh idan wannan sakarar uwar tata ta nuna 'kiyayyarta gareka zan 'dauki mummunan mataki, Allah ya albarkaci aurenku ya kaiku lafiya ubangiji yasa adace kayi hankali fa! kar ta jiyata min kai.â€
Ja'afar ya ji da'din addu'ar sosai yay murmushinsa wanda daman bai fiye wa kowa shi ba, daga innarsa sai Nuratu ko Ibtisam itama bai fice sau uku ba tin ha'duwarsu.
Ya shafi yalwatacciyar sumar kansa ta asalin baqaqen buzaye ya ce.
“Ngd innata, agaishe min da kowa da kowa, ban Nuratu.â€
Wayar ta ba Nuratu sun 'dan ta'ba hira Sadiya ta amsa tai masa barka Deluwa ma suka gaisa Nuratu salin halin yayan nata tai masa sallama tare ta fatan alkahiri, ya katse kiran.
Inna aka washe baki akace“Allah mai iko wai yau Ja'afaru na zai hau jirgin sama kai jama'ah.â€

Dadda na zaune tana tsafema Aydah kanta Taslim tana musu girkin rana, Fu'da da Nadra sunata wasansu.
Wayar Dadda ta 'dauki ringing.
“Toh mutan Tchad ne ko Cameron?â€
Ramadan ya ce“Allah yasa Babane.â€
Dadda ta 'daga kiran tana rabka sallama.
Tanko ya amsa daga can yana gaisheta.
Dadda ta ce“Shamsu jiya shiru bamu jika ba yara duk sun damu, ya me jikin?â€
Tanko ya amsa“Da sauqi ya yaran? Yauwa dadda dan Allah kiyi min kyakkyawar fahimta na kira Karime munyi mgna yanzu...â€
Tsaf ya zayyanewa mahaifiyarsa komai game da auren Ibtisam da Ja'afar da aka 'daura jiya juma'ah, ya 'dora da cewa.
“Jiyan wlh duk hankalina ba kwance ba shiyasa ban kiraki ba kiyi hkr dan Allah.â€
Dadda ta ce“Masha Allah wlh naji da'di hakan sosai shima yaron ya yi halacci na kuma gamsu da 'kaunar da yake mata, shi kuma wannan balarabe Allah ya saka masa da gidan aljannatul Firdausi, Inda Ana samun irinsu dayawa aduniya wlh talakawa da basu shiga wani hali ba.
Allah ya basa dukkan abinda yake nema gidan duniya da lahira, gaskiya yanada kirki irin wannan temako haka? Duk da shine yay sanadin shigarta mawuyacin hali amman ya yi jihadi sosai.â€
Nan ta ba yaran 'daya bayan 'daya wayar suka gaisa da mahaifinsu suna masa fatan sauka lafiya.
Chapter 39 · 0% Book details