← Book details Dattijon Arziki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 118

Sashe 73

Dattijon Arziki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da sallama ya shigo falon, suna zazzaune harda Ja'afar wanda zuwansa kenan.
Hannu ya basu sukayi musabaha, yana zama kusan Abie 2.
Ja'afar ya gaishesa cikin ladabi yana masa sannu da zuwa.
Abie ya amsa fuska asake yana fa'din.
“Ja'afar na sameku lafiya? Ya hkr?â€
Aladabce ya amsa.
“Alhmdllh! Abie ga mota can compound ogana da na ma aikin tuqi ya ban Ku sanya min albarka acikinta nakeson mutafi Niger. â€
Abie ya murmusa yana sosa sajan fuskarshi ya ce“Ma Sha Allah ubngiji ya sanya alkhairi muje nagani Ja'afar.â€
Sosai Ja'afar yay murna shiyasa Abie yake burgeshi sbd baida girman kai.
Tanko ya ce“Abdulmajid ya gajiya sannu.â€
Abie ya amsa da“Alhmdllh! Shamsu na sameku lfy? Mal Adamu ya ce“Lfy lau ya jikin Rahma? 'Dazu ta fita daga nan Ashe batajin Hausa inata tambayarta shirk daga 'karshema ta tafiyarta.â€
Abie wani irin Smile yay yana fa'din.
“Mal Adamu ina Ummi zata koyi Hausa? Nima naci wuya kafin na koya .â€
Dariya sukayi Abie 2 ya ce“Ya kamata muyi mgna Abdulmajid akan Rayyana kaga kowa anan yasan komai bare nace mu ke'be don Allah Adamu Shmsu Ku tayani basa hkr ya yafe mata yabarta yaci gaba da zama da ita, ka hkr tinda ta gane kuskurenta.â€
Abie ya shafi sumar kansa yana shaqar 'kamshin babynsa da ya Kama jikinsa yana jin tamkar yanzu ne take wasa da harahenta cikin bakinsa tana zuqe dukkan yawun bakinsa tsabar yadda take mugun sonsa kome nasa so take.
Wani yammm! Yaji baida wani buri yanzu sai yaje ya shige jikinta ya lullu'besu da bargo yana shafarta har ta farka a baccin amman ina yanada uzururuka.
Abie 2 ya dafashi yana fa'din.
“Au sharemu kayi?â€
Abie ya numfasa ya ce“Haba! Abien ummina kai yanzu aganin ka zama da irin wannan matar ya dace? Wlh inada tabbacin idan abinda yake shirin 'bullowa cikin satin nan ya 'bullo zatayi abinda yafi Nada muni, ba mamaki kwanciyar mage ta min, bandai sallameta ba amman zan sallametan akwai abinda nake jira na gama, zamuyi rabuwar arziqi da ita idan taso.â€
Abie 2 a 'dan zaman da ya yi da Abie ya gano halaiyarsa mutum ne mai tsayawa akan mgna 'daya.
Ajiyar zuciya ya sauke ya ce“Toh Allah ya za'ba abinda yafi zama alkhairi.â€
Dukkansu suka amsa da “Ameen.â€
Abie yay gyaran murya ya ce.
“Yauwa Mal Adamu insha Allah jibi zaku wuce Ja'afar! Bar mgnar motarka har ka dawo jirgi zaku shiga daga nan har Niger, ka sake biyo jirgi ka dawo dan kawomin takardunka, muga yadda za'ayi.â€
Tanko da Mal Adamu baki suka ha'da wajan godiya da masa fatan alkhairi.
Ja'afar yay 'kasa da kansa yana godiya ya ce“Amman Abie ni wlh cigaba da karatu ya fita akaina, a samomin aiki daidai dani akan kasuwanci yafi min.â€
Abie ya ce“Ok ba damuwa kaje ka dawo, idan kuma kafi son Niger ka fa'damin gaskiya?â€
Ja'afar ya ce“Wlh har zuciyata Tchad ta min zanci gaba da zama acikinta.â€
Abie ya ce“Ma Sha Allah yaron kirki.â€
Mal Adamu ya ce“Amman idan yaje zai kwana biyu sai anyi bikinsu sai ya taho da matarsa.â€
Abie ya ce“Ok Allah ya sanya alkhairi za'a samoma gida insha Allah kafin su dawo an sanya musu kome aciki.â€
Tanko harda kuka wajan godema Abie Mal Adamu sai albarka yake saka masa.
Wayoyin Abie dukkansu biyu atare suka 'dauki ringing, ya miqe ya ce“Ja'afar muje naga motar inada baqi yanzu.â€
Miqewa Ja'afar yay suka fito Abie 2 na jeroma Abie addu'ar gamawa da duniya lafiya.
Tafe suke yana amsa wayar suka isa wajan motar Abie ya sanya masa albarka da fatan alkhairi, ya shige mota zuwa uzurorinsa.

★★★
Bayan kwana biyu.
*Gabon*
Aishatu jiki ya yi sauqi yau aka sallameta da safe, har yanzu tana kan bakanta akan sai Ma'aruf ya saketa.
Shi kuma ya ce tai masa alqawalin zata kwantar da hanaklinta, ba zata sanya tunanin aranta ba, sannan zata yafe masa ya yarda zai saketa.
Amman taqi bada amsa.
Zaune take a 'dakinta na gidansu saman 'katuwar katifa tana sanye diguwar Riga marar nauyi tayi tagumi tana nazarin duniya, bata ta'ba tunanin Rabi'ah zata ci amanarta ba!
Wasu irin hawaye masu 'dumi suka shiga ziraro mata akan fuskarta.
'Kamshi turarensa ya kawoma 'kofofin hancinta farmaki, tai saurin 'dago da kanta.
Tsaye yake 'kofar 'daki ya har'de hannayensa a 'kirjinsa, hawaye na zuba akan fuskarshi.
Kanta ta kauda ta ce“Natsani ganinka don Allah ka fita kaban waje please. â€
Takunsa taji yana kusantota, ta waiwayo paper fara tass ta gani ahanunsa yana beqo mata, tsaye ta miqe zuwat 'kirjinta na bugun uku-uku....

A can Tchad kuwa
Abie ya gama shirya musu tafiya ayau flight 'dinsu zai 'daga 'karfe 2:30 na rana zuwa Niger Tahoua.
Abie yaba Rayyana ma'kuddan ku'di sabida sake gwadata, ya ce suje da Ummun Adnan tayoma su Tanko siyayya, cikin ikon Allah dala 'daya bata ciba, ta siyo komai tsakaninta da Allah, Abie kansa ya yaba da siyayar.
Ibtisam tana nan haukan son Abie na qaruwa cikin zuciyarta duk yadda taso yaqice shi, abun ya faskara da ganagan take wuni afalon wanda dole idan Abie ya fito zasu ha'du bayan amsa gaisuwarta baya sake kallonta, da ya gane dan shi take wuni sai ya fasa shigowa ta waccan hanyar yanzu yake fita, abinci ma sama Rayyana take kai masa, bakinsa da falon gaishe da mahaifiyarsa.
Rahma kuwa fushi take da Abie yaqi korar su Ibtisam, amman da gangan ya qyaleta sai sun tafi ya yi lallashi dan yana kewarta da 'dumin jikinta da zaqin yawunta, kawai shi dai haka yake mutum ne wanda idan baiyi ra'ayin abu ba, toh ba wanda ya isa ya saka shi ya yi, duk tarin son da yakema Rahma bazai ta'ba yarda ta saka shi ya wulaqanta mutum ba, ba tare da babban dalili ba, iyayansu Ibtisam yake dubawa ba wai Ibtisam ba, dan bata gabansa.
Rayyana an saki jiki Abie ya sauko duk da ba abinda yake ha'dasu sai gaisuwar mutunci amman tana qoqarin ganin ta goge laifinta.😂
Ja'afar bai sake shiga sabgar ibtisam ba jira yake su koma Niger ayi bikinsu ya koya mata hankali, tara ne yake.

Misalin 'karfe 1 na rana dukkansu sun gama shirin tafiya, har sunyi ma su Jaddatu bankwana suna 'bangaran su Abie 2. Ibtisam sai kuka take Laraba ta mata tambayar duniya ta ce kanta ke ciwo, nan kuwa kukan barin Abie take.
Jaddatu zaune Rahma kwance saman sofa ta yi matashi da cinyarta tana Sosa mata dogon gashinta, idanunta alumshe.
Sanye take da riga da zani na shadda Ash kala da ganin 'daurin zanin ba wai an iya bane.
Meerah na tausa mata qafafunta.
Latifa ta dire tray'n kayan marmarin da ta yanko musu.
Hanan agefe tana waya, Iman tana rungume ajikinta.
'Kamshin turarensa ya kawoma hancinta farmaki.

Da sauri ta bu'de kyawawan 'kananun idanunta, masu matuqar haske.
Shi da Rayyana ta hangosu suna saukowa anutse suke taka steps.
Idanunta ta runtse, lips 'dinta ta ciza da 'karfi, sai da taji zafin har cikin zuciyarta.
Kusan Jaddatu ya zauna yana amsa waya, ya gaisheta. Ta amsa cikin sakin fuska. Meerah ta gaishesa, ya amsa.
Rayyana ta ce“Ummi 'karama bacci kikeyi?â€
Rahma muqus ta yi bata tanka ta ba.
Meerah ta ce“Eh inaga dai tayi baccin ne.â€
Abie kallo 'daya ya mata yasan idanunta biyu.
Hannunsa ya 'dora saman goshinta.
Ajiyar zuciya suka sauke atare ya shafi fuskarta akaikaice ya tura mata, 'karamar yatsar shi cikin bakinta, ta tsinci kanta da lasa tana shirin tsotsa yay saurin janyewa dan kar a ankare da su, ya miqe yana fa'din.
Ummi ko zan dawo sai zuwa magarib yanzu sallah zamuyi mu shiga meeting, zanje muyi sallama dasu Mal Adamu. â€
Ya 'karashe mgnar idanunsa akan Rahma wacce taqi bu'de idanunta, amman ji take kamar tabi Abienta.
Jaddatu ta ce“Toh adawo lafiya, wai ni kam me kayima takwara naga kamar fushi take dakai?â€
Abie ya shafi sumar kansa yana murmushi ya ce“A'a banyi kome ba shagwa'barta ce ta motsa ace mata na fita idan ta farka.â€
Rayyana harda su rakiya.

Ibtisam na la'be daman jiran Abie take ai kuwa tana hangosa cikin murna ta sake mannewa jikin bango.
Sai da ya kusa shigowa ita kumaa ta fito aguje kamar an aiketa tana fa'din.
“Toh bari na amso...â€
Abie bai shirya ba yaji ya yi karo da mutum yana qoqarin matsawa yana fa'din “Subahanallahi!â€.
Yaji ta shige jikinsa ta 'kam'kameshi ta tura kanta 'kirjinsa ta fashe da kuka tana fa'din.
“Wayyo Allah na!!â€

_*Please 'yan team Rahmaa da Abienta kuyima Ibtisam hkr, wallahi kowane irin mutum akwai 'kaddarasa da jarabawarsa, ba wai ina goyen bayanta bane, A'a wallahi Ibtisam Allah ya jarabeta da mugun son Abie wanda duk yadda taso ta yaqice shi abin yaci tura, kuga barazanar da Tanko ya mata harda yace zai saki mahaifiyarta, amman kamar tunzurata ake matsalar da aka samu 'karancin shekarunta ta kasa ganewa babban zunubi take aikatawa son wani da auren wani akanta, ta jahilci kanta bayan tayi karatun addini daidai gwargwado, dan Allah Ku mata uzuri ta gamu da jarabawa wanda ta ha'du son zuciyarta. Allah ya yaye mata dan ko batada miji yadda Abie yake son Rahma zamansa da wata mace wlh zata cutu sbd zuciyarsa baki 'daya Rahma take so kenen ko agaban waye zai nuna mata so, duk da bance lallai bazai iya son wata koda bai kai na Rahma ba, sbd Allah shine yake zartar da hukuncinsa akan kowane bawansa yadda yaso, kenan baza'a ce bazai so wataba, Allah yasa mudace ya mana mai kyau Ameen.*_

_Rahmerh ladingo😉_

_*🤲ðŸ¼Ya Allah ka jiÆ™anmu kayi mana rahama badan halinmu ba.ðŸ™ðŸ¼*_
3/25/22, 22:55 - Buhainat: ```D A```

```73&74```

_*My Sisters Don Allah Don Darajar Annabi Karki Karanta Idan Baki Biya Ba, Na Ku'dine Idan Kinga Yana Yawo Na Satane Ga Hanyar Da Za Ki Samu Naki Akan.😟👉ðŸ¼300N +22796515805*_

Not Editing
Chapter 73 · 0% Book details