← Book details Dattijon Arziki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 118

Sashe 9

Dattijon Arziki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Malam Adamu yana tsakiya da cin abinci, wanda kullun sai yayi sallar azuhur 2 yake zauwa cinsa agida, ko kusa baya cin abinci wajan sana'arsa.
Kiran da ya shigone ya sanya shi saurin kai lomar abincin bakinsa, ya d'auki wayan da take gefensa ajiye.
Ganin Ja'afar ne ya fad'ad'a fara'arsa, ya d'aga kiran tare da sallama, yana fad'in.
“Ma Sha Allah Ja'afar yanzu kuna ina? Tin jiya wayan take kashe na barta a chaji yanzu na cirota.â€
Ja'afar wanda motarsu ta fita daga cikin Tasha, ya ce“Baaba ina yini? Asamu cikin addu'a gamu zamu Kama hanya, abani innata idan tana kusa.â€
Malam Adamu ya ce“Allah ya saukeku lafiya ya rabaku da sharrin dukkan abin k'i Allah ya baku sa'ar tafiya, bari na kaiwa Hansatu wayan.â€
Daga can Ja'afar ya ce“Ameen Baabana Ngd. â€
Malam Adamu ya fito wayan akunnensa sai addu'a yake jeroma Ja'afar.
Inna Hansatu tana zaune a inuwan dalbejiya, ita da Deluwa tana lissafin ribar da ta hayo mata ayau sai washe baki take, sabida kusan d'ari uku taci riba, ta ce“Ina laifi sbd Allah ga shi anata cin ta sadaka agida ai na zaune baiga gari ba wlh.â€
Deluwa ta ce“Allah ya qara albarka hannu ya kuma k'aro kasuwa. Hansatu kinyi mgna kuwa da Ja'afar?â€
Inna ta ce“Ameen fa kam tinda ana cin ta sadaka sosai. A'a wlh ni da wayana taci battery sai an siya, kekuma an sace taki, sai ta Malam...â€
Isowa yay yana fad'in.
“Yauwa ga iyayan naka zaune, anata lissafi, Delu amshi ki masa fatan alkhairi.â€
Deluwa ta amsa tana kara wayan akunnenta, tare da sallama.
Ja'afar ya gaisheta, ta amsa tana masa addu'a, ta bek'awa inna mai waina.
Inna bayan ya gaisheta ya fad'a mata suna hanya, ta shiga kwararo masa addu'a akan Allah ya had'asa da mutanan arzik'i inda shima zaiyi arzik'in.
Sai da ta idar da masa addu'ar arzik'i ta ce“Allah ya kaiku lafiya bak'in buzuna.â€
Ja'afar ya girgiza kai yana murmushi ya ce“Ameen innata Ngd ban Baaban.â€
Wayan ta ba Malam tana fad'in.
“Gaskiya Malam ka siyo min battery d'in waya domin Allah fa.â€
Deluwa ta ce“Ni kuma ko rakani Masai ce asiyo min.â€
Dariya ya musu yace“Insha Allahu zan siya muku Allah ya mana bud'i na alkhairi.â€
Ya k'arashe mgnar yana komawa d'akinsa.
Inna mai waina ta tab'e baki ta ce“Wai Deluwa meyasa kikeda bin gasane? Mufa ba yara bane.â€
Deluwa ta ce“Ameen Malam mun gode. Allah baki hkr ai gaskiya ce ke mai sana'a ma kin roqa bare ni mai zaman banza.â€
Inna ta ce“Akoyi Sana'a zama zaunewa deluwa, au kice saa'ar waina abaki take?â€
Deluwa dariya tai ta ce“A'a wlh ni kam sai dai na biki da fata alkhairi.â€

Unguwar geban zogi
Ibtisam tin jiya batada wani sukuni arayuwarta, yau tin safe zazzab'i ya rufeta, sai da Tanko ya kaita asibiti wajan 9 na safe aka mata allura gudun karta rikice musu, dan bata iya ciwo ba. Alhmdllh jikin ya yi sauqi.
Zaune take arumfar k'ofar d'akinsu,tana shan lemon zak'i, Aydah na ma Nadra tsifa sai zungurata take, Fu'ad na musu dariya, yayin da Taslim mai bin Ibtisam 'yar kimanin shekaru 14 tana famar qanqaran farce.
Ramadan ne kad'ai baya gidan, duk k'anen Ibtisam ne.
Sanye take da riga da siket na atamfa mai sauqin kud'i, amman d'inki ya mata kyau, fuskarta ta rame kamar ta tashi daga jinya.
Laraba ta kalleta ta ce“Don Allah Ibtisam ki ajiye hankalinki ki manta da waccan yaron ki tsaya ki saurari mazan kirki masu sonki da alkhairi.â€
Taslim ta ce“Haba Anna ki barta mana ai ba'asan abinda Allah ya shirya atsakanin su ba.â€
Laraba ta ce“Iyeee! Taslim duk nawa kike har kike shiga mgnar masoya? Wlh zanci ubanki.â€
“Toh Allah ya baki hkr Anna amman wlh banson ki matsa...â€
Wani guntin ice ta jefo mata ta mik'e aguje ta shige cikin d'akinsu.
Ibtisam batace komai ba ta mik'e kamar an tsikareta, tana zumb'uro baki gaba tana diddira k'afafunta.
Laraba ta ce“Zanga yadda za ki aure shin dan ubanki....â€
Tanko da yake shigowa mak'ale da waya akunnensa ya ce“Yauwa d'ana munata muku addu'a kaga ganima agida na shigo bari na baka k'anwar taka Ku gaisa, nasan kana son tambaya nauyi ya Hana. Ke Ibtisam taho amshi kuyi bankwana sun d'auki hanyar Tchad. â€
Ibtisam ta langwab'ar da kanta ta fara rau-rau da idanu ta ce“Wayyo Baba Wa?â€
Tanko ya ce “Amshi manaâ€
Ibtisam ta amsa ta kara akunnenta.
Jin murya Ja'afar ya saka ta nufi d'akinsu aguje.
Laraba ta ce“Ikon Allah! Yanzu abinda kake daidai ne?â€
Yaran suka mik'e duka suna masa sannu da zuwa.
Tanko ya ajiye mata bak'ar leda gabanta ya ce“Yau kasuwa ta yi kyau ga hanji ayimana farfesu musha da dare, yaran albarka kuji Allah ya albarkace Ku.â€
Suka amsa da “Ameen Baba.â€

Ibtisam ta zauna dabas atsakiyar katifarsu, cike da farin ciki ta kirasa“Mon amour! Rashinka ya dameni yau sai da aka min allura zazzab'i.“
Ta k'arashe mgnar muryata na rawa.
Ja'afar ya ce“Nasani daman Mon cÅ“ur hakan zata iya faruwa, kiyi hkr tinda Baba nada waya kafin na turo miki kud'i ki siya zamu dinga mgna da zaran mun isa lfy idan nasamu aiki zan siyi layi na kiraku kinji abar k'aunata?â€
Ibtisam ta ce“Toh Mon amour Allah ya kaiku lfy wane gari zaku?â€
Ja'afar ya ce“Tchad.â€
Ibtisam ta ce“Don Allah sahibina karka bawa shuwa Arab daman kusantowa kusanka bare suyi yunqurin amshemin kai, dan banga macan da aduniya zata sameka face bataso ba, qarya take, kasani rasaka daidai yake da rasa rayuwata.â€
“Ya ilahi! Haba! Yi shirunki banga macan da zata samu rabin rabin... Dogon numfashi yaja, dan jiyake ya yi mgna sosai dama kuma ita ce mai saka shi doguwar mgna.
Ashgwab'e ta ce“Sahibina qarasa pls kaji?â€
“No! Mon cÅ“ur bari na isa lfy je t'aime ki kularmin da kanki banda samari ki jira muradun ranki ina dawowa nan da wata 3 insha Allah domain ki ni nakine har abadan...â€
Yay saurin yanke kiran gudun karta sanya masa kuka. Dogon numfashi ya sauke yana yamutsa fuska ganin yadda mutane da dama na cikin motar suke kallonsa, ya had'e face dan ya tsani kallon k'urulla, kafad'a ya d'aga irin ko ajikinsa d'in nan..
Ai kuwa Ibtisam da kukan ta b'arke tana kiran Ja'afar, tai saurin toshe bakinta kar ajita.
Sai da tai kukan ta gaji ta fito ta bama Babanta wayarsa, Laraba nata masifa, idan Ibtisam ta lalace laifinsa ne.

Sosai motarsu Ja'afar ta nausa tsakiyar jeji sai fatan sauka k'asar Tchad lfy.

*Tchad*
Misalin 4:50
Jaddatu Rahamu na zaune cikin hamshak'in falon nasu casbi ahannunta tana ja, idanunuta akan k'atuwar Tv dan take manne abango, mutanen tamkar agabanka suke.
Tashar Al'jazeera take kallo daman ita kullun nan ne wajan kallonta.
“Latifa! Wai shin wane irin shayine kike dafawa kaman nace ki dafa min kan Kharuf? Wlh zan iskoki Mutubah mu kwashi 'yan kallo.â€.
Ummin Adnan da take fere dankalin turawa wanda Rahma tace a mata fatensa da hanta asaka dafafen k'wai, shi take son ci da dare.
Murmushi tai dan tana jiyo mgnar Jaddatu.
Fitowa tai daga kitchen ta nufo falon.
Da sallama ta iso ta duk'a ta gaishe da Jaddatu ta amsa fuska asake ta ce“Jaddatu kiyi hkr Latifa yau batajin dad'i cikinta ya tab'u zawo take da amai bari na juye miki shayin naga ta kashe gas tin d'azu ta tafi b'angaranmu.â€
Jaddatu ta ce“Allah na gode maka da ban kai ga sha ba,sabida Allah yarinya nan zawo take amman shine dan jaraba bazata fad'a ba akaita asibiti sai ta gogawa sauran ma'aikatan gidan kwalara?â€
Idanu ta zaro lokacin da ta hango Latifa da tray da flask d'in shayi da cups sai gwalo idanuwa wanda suka mata Ja take tana tafiya a d'an duk'e.
Jaddatu ta ce“Lah! Ha'ilaha ilallahu! Ke! Latifa dakata! Karki isomin da kwalara nan, koma jeki b'angaranku don Allah har ki warke yanzu na fad'awa Abdul Majeed kafin ya tafi ya saka akaiki asibiti wlh ciwon kwalara d'aukarsa ake.â€
Latifa tsabar haushi ya saka tak'i tsayawa, aranta take fad'in.
“Allah ban komawa bari kiga na sakata gudu mugani.
Ta k'arasa mgnar tana k'ara gwalo idanu ta nufi wajan Jaddatu tana fad'in.
“Don Allah Jaddatu kiyi hkr kinata jirana wlh cikina ne ya murd'a na tafi b'angaran mu, ga shayin wlh na yau yafi na kullun shan kayan had'i.â€
Jaddatu ta mik'e tana tokara sanda ta nufi hanyar bedroom d'inta dan tskaninta da Allah tsoron Latifa ta rab'eta takeyi.

*GABON*
Cikin garin (Libreville)
Wanda yake (Capital d'insu.)

Unguwan *Haut de gué gué*
Wani tsararran gidane mai kyau ya k'ayatu sosai an zuba ababan more rayuwa acikinsa.
Wani madedecin falo ne wanda yaji kayan alatu masha Allah, da manyan kujeru masu tudu ga laushi, k'amshi turare sai tashi yake.
Falon ba kowa, sai qaran Tv da ya kard'e falon, amman hakan baya hakana jiyo muryoyi ana hayaniya tin daga nesa kafin ka iso k'ofar bedroom d'in kakejin hayaniya cikin d'aga murya da ruwan masifa.
Da sauri na k'arasa k'ofar d'akin na lab'e na kasa kunne ina jin abinda ke faruwa. Wata kalma ce da na tsinto ita ce ta saka na lek'a ta 'yar k'ofar sabida ina son naga shin wai su wand'an nan mutane wasu irin mutane ne? Idanuwana na runtse da gaggawa sakammakon arab da nayi da........ “Innalillahi!😳🙆ðŸ»â€â™€ï¸ðŸƒðŸ»â€â™€ï¸

💃ðŸ»Yar Ajin Tubarkallah🥰

*DATTIJON ARZIK'I* N300 katin MTN ta wannan number *+22796515805*

SULTAN
mss flower

BAK'AR FATA
AUTAR MANYA

TSINTACCIYA
Nimcyluv

Gaba É—aya 800
Via 6850917335 Na'ima Shu'aibu Sulaiman Fidelity Bank, masu tura kati 08167888934 ga ƴan uwa na Niger +22796515805 za ku tuntuɓa. To show evidence of payment 08142105218

*Real Ladingo+22796515805* For more information😇

_*🤲ðŸ¼Ya Allah ka jiÆ™anmu kayi mana rahama badan halinmu ba.ðŸ™ðŸ¼*_
2/2/22, 09:19 - Buhainat: _*DATTIJON ARZIƘI*_

*BY*
_Rahma ladingo Ummu Fareesa😘_

*🔥FITATTU HUƊU🔥*

_*HOME OF QUALITIES WRITERS ASSOCIATION*_

_*BAKANDAMIYATA🥰* Tafiyar sannu-sannu ce👌ðŸ¼latsa nan hajiya kai tsaye ki sadu da marubuciyar_ _*dattijon arzik'i🥰 don girman ALLAH idan ba siya zakiyi ba, karki tab'oni.ðŸ‘ðŸ¼*_
👇ðŸ¼
*Http://wa.me/+22796515805*

*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*

_*cнapтer 11&12*_
Chapter 9 · 0% Book details