← Book details Dattijon Arziki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 118

Sashe 62

Dattijon Arziki Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Abun da idanun Aishatu ne suka nuna mata taqi yarda ta kifawa kanta mari, tana mintsinin hannunta, ta ji eh ita ce ba mafarki take ba, amman taqi yarda da hakan.
Cikin 'barin jiki ta qaraso dab dasu idanunta na neman rufewa, haka ta daure ta tsaresu da ido, eh tabbas Ma'aruf mijinta shine saman Rabi'ah 'kawarta aminiyarta wacce ta aminta, ta kamasu tirmi da ta'barya.
Baya ta matsa da sauri tana toshe kunnuwanta, daman kuka sam bazata iya ba adaidai wannan lokacin.
Cikin fitar hayyaci ta ce“Me ya kamata nayi musu?â€
Kai ta girgiza ta ce“Babu tabbas ko ba mgna ka zuba ido ta ishi me hankali. Haqiqa na tafka kuskur me girma na auren Ma'aruf sai abu na biyu aminci da Rabi'ah duk da kuwa ana garga'dina akan mugayan halayanta naqi sbd bana shedar abinda idanuwana basu gani ba! Tih wai tin yaushe suke aikata masha'a?â€
Zaune tai dabas can nesa dasu ta basu baya, jin yadda Rabi'ah da Ma'aruf suke zuba sambatu ya saka ta gigice ta 'dimauce ta haukace ta fita daga sahun mutane dishi-dishi take gani, kunnuwanta sun 'dauke 'dif idanunta sun rufe ruf komai ya tsaya mata, take taji cikinta ya mur'da taji wani abu kamar lema na binta gefen cinyoyinta daga hakan bata sake sanin inda kanta yake ba.!
Sai da suka kwashe tsawon 50 minutes suna abu 'daya kafin su samu gamsuwa.
Ma'aruf ya mirgina gefe yana maida numfashi, Rabi'ah gabanta taji yana mata azabar zogi dakyar take motsawa sabida caccakar da ya mata bata wasa ba, tasan badan qarfin magugunan da ta shaba ta matsa tabbas da ta jima da sakin kukan wahala.
Miqewa yay tsaye yana dafe kansa zuciyarsa wani iri ba da'di, ya kwashi kayansa ya nufi bedroom.
Watsi yay da kayan sakammakon ganin Aishatu babu rai cikin jini ya 'kurma wani irin ihu yana fa'din.
“Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Aishatu! Me ya sameki don girman Allah karki min haka.â€
Ya 'karashe mgnar yana cicci'barta zai nufi waje, sam ya gigice ya manta ba kaya ajikinsa.
Rabi'ah wacce tai mutuwar tsaye tsabar tashin hankali ya sakata sakin fitsari har wani irin amai yake taso mata, ya akayi Aishatu ta dawo? Yanzu Aishatu ta kamata da mijinta suna aikata masha'a?
“Wayyo Allah na shiga uku na lalace son zuciya 'bacinta! Ma'aruf tsirara kake ka saka kaya don Allah.â€
Ta 'karashe mgnar tana saka kayanta tai waje aguje sbd batajin zata iya kwana agarin nan yau sbd abun kunyar da tai babba ne, sai dai toh ina zata?
Ma'aruf haka ya maida kayansa cikin najasa ya 'dauki Aishatu yana kuka kamar yaro 'karami ya fita.
Nura wanda ya gaji da zaman mota ya fito ya shigo suna zaune me gadi ganin Ma'aruf da Aishatu cikin jini ya 'daga musu hankali.
'Kofa suka bu'de masa Nura da gudu ya nufi motar ya bu'de masa ya shigar da ita shima ya shiga yaja suka nufi hospital.

*Tchad*
Ibtisam lokacin da ta shigo falon duk suna falon Jaddatu Hanan Rayyana Laraba, duk ana fira.
Sallama tai suka amsa, ta gaishesu ta zauna kusan mahaifiyarta.
Jaddatu ta ce“Har kin dawo?â€
Ibtisam bata san me ta ce ba kai kawai ta 'daga Rayyana ce ta fassara mata sbd tana jin hausa.
Ibtisam ta kalli hoton Abie wani tam'kememe yana sanye da wata farar shaddah 'dinkin tazarce ya yi masifar kyau, 'kayataccan murmushi akan fuskarshi.
Idanu ta lumshe ta sake bu'de ta sauke idanunta akan na shi da Rahma fara'ar fuskarta ta kau, tai saurin kauda kanta tana jin wani irin zafi aranta, sam aganinta basu daceba sbd kyawunsu ya yi yawa duk da ta ga suna Kama, amman dai ta kasa yarda 'diyarsa ce duk da kuwa tasan zai haifetan.
Rayyana ta ganeta sarai da gangan ta ce“Ibtisam ya dai? Ko hoton Ummi da Abie ya burgeki?â€
Murmushin yaqe tai ta ce“Eh sunyi kyau miji da matane ko?â€
Rayyana taji gabanta ya fa'di tai saurin cewa.
“A'a babanta ne.â€
Ibtisam ta sauke ajiyar zuciya a'boye ta ce“Uhmm! Sunyi kyau.â€
Laraba ta zubama 'yarta idanu sbd abin nata yanzu ya daina bata mamaki tsoro yake bata.
Jaddatu ta kalli Raiyana tana riqe baki ta ce“Ikon Allah Rayyana wani munafurcin kike son 'kullawa kika sauya harshe?“
Rayyana ta miqe ta ce“A'a Allah bada hkr Ummi ba wani munafurci da akayi wlh.â€
Ta sanya kai ta haye bene.
Ibtisam ji tai bazata iya zaman falon ba ta miqe ta nufi bedroom 'dinsu.
Laraba tabi bayanta.
Tana zuwa ta rufeta da fa'da.
“Ashe ke bakida hankali sakarace shin ke mayyace ne Ibtisam ko me? Kina kallon mutum har matarsa ta gane.â€
Ibtisam ta ruqo idanu ta ce“Oh! Matarsa ce wannan 'din? Humm! Yo dame ta fini idan ba fari da da gashi da shekaru ba, wlh bata fini da komai ba...â€
Baki Laraba ta buge mata.
Ibtisam ta saki kuka ta ce“Don Allah ki rabu dani Anna idan bazaki tausaya min ba wlh tallahi ba laifi na bane ina sonsa ne bansan ya zanyi ba.â€
Ta fa'da cikin kuka tana shafa zoben hannunta tana kuka.
Laraba tagumi tai ta sakata gaba dan ta ga so take ta kashe mata aure da qarfin tsiya.
Cikin fusata ta ce“Wlh Allah idan kika kashemin aure ta qarfi Ibtisam bazan yafe miki ba, ki dawo hayyacinki.â€
Ibtisam ta rungume Laraba ta ce“Ki tayani da addu'a.â€

*Espanol*
Su na zuwa gida Meerah ta ha'dama Rahma ruwan wanka ta sake wanka, ta sanya riga doguwa green colour marar nauyi me qaramin hannu, tana zuba 'kamshi jikinta ba 'kwari, haka tai sallah ta fito falon wanda Meerah ta gyara ta kunna turaren wuta sai uban 'kamshi yake, ga wani irin sanyi me da'di.
Saman sofa ta zube tana kiran Meerah.
Gabanta zube tana mata sannu da jikin.
Rahma cikin sanyinta ta ce“Ina wayana? Abie ya fitane tinda muka zo banjin motsinsa ba?â€
Meerah ta ce “A'a yaje dai masallaci ya dawo ina ga yana can sama bedroom 'dinsa.â€
Meerah bata rufe baki ba sukaji qaran takunsa yana nufo falon.
Rahma ta 'kurama corridor d'in idanu, tana fa'din.
“Meerah jeki aikin ki pls kawomin apple bakina 'daci wlh.â€
Ta 'karashe mgnar tana langwa'bar da kanta, daidai lokacin suka ha'da idanu, da Abienta.
Tsura masa idanu tai yana sanye da jallabiya milk colour tai masa kyau gashin kansa sai sheqi yake, yana zuba wani irin fitinannan 'kamshi.
Laptop 'din hannunsa ya ajiye saman center table, ya zauna dab da Rahma ya kamo hannayenta ya sumbata, yana murza 'karamar yatsarta, ya hura mata iskar bakinsa saman idanunta.
Firgigit tai ta dawo hayyacinta.
Shagwa'be fuska tai tana turo 'dan qaramin bakinta gaba ta ce“Abienah kayi kyau wlh kamar saurayi Abie nah, kamar na qaroma 'yan mata uku ka cike hu'su har Ammi.â€
Ido 'daya ya kashe mata, yana gyara mata gashin da ya zube gefen fuskarta, ya sumbaci tsakiyar kanta mai fitar 'kamshi man da take anfani da shi.
Dab kunnenta ya ra'da mata “Ok kiyi ta kallon Abienki ai nakine ke 'daya Babyn Abinta Ummin Abienta, kul naji bana son wasu matan koda kuwa 'yan gold ne na yafe ruhina ta isheni.â€
Yadda yake mata mgnar bakinsa dab da kunnenta har fatar bakinsa na ta'bo fatar kumnenta kamar yana goga mata da gangan ya sanya Rahma ta 'kyal'kyale da dariya tana qamqame Abie tana saqalo hannayenta wuyansa ta tsira masa 'kananun kyawawan idanunta tana dariya.
Shima kallonta yake ya 'dora hannunsa saman kyakkyawar fuskarta yana shafawa yana Jan siririn hancinta, ya sumbaci idanunta, yana kallon fararen haqoranta casss.
Ahankali ya ra'da mata“Pls Baby dariyar ta isa kar ta 'kulle min cikin ki OK? â€
Kai ta 'daga masa tana sumbatar kumatunsa tana kallon bakinsa ya 'daga mata gira, ya ce“Babyna ce Meerah ta ha'domin coffee me da'di.â€
Ya qarashe mgnar yana janyo laptop ya kunna yana sake matseta cikin jikinsa. Sumar kansa ta shafa ta sumbata tana fa'din“'kamshi wlh me da'di Abienah.â€
Ta 'karashe mgnar tana sauka daga jikinsa.
Fizgota yay ta dawo jikinsa tana sakin dariya tana cewa“Abie Rabin raina ka karya min hannu wayyo zafi.â€
Dariya yay ya kamo hannun ya ce“Mugani Babyna sharri.â€
Rahma kallonsa take tana murmushi ta ce“Abie mgnar ammi wai me ta min ne wai nace karka rabu da ita?â€
Ido ya kashe mata ya ce“Babyna idan zan wuce bayan kin kammala shan maganinki dake zan wuce bana son karatunki ayanzu OK?â€
'Kananun kyawawan danunta ta zaro tana kallonsa, ta marerece fuska, ta tallafo fuskarshi tana kallonsa tana Jan dogon hancinsa ta ce“Am da gaske Abienah baka son nayi karatun gida zamuje?â€
Ra'da ya mata akunnen.
“Yes Babyna bana so ki hkr bayan bikin ki zan mayar dake wata 'kasar OK?â€
Goshinsa ta sumbata ta ce“Ok Rabin raina an gama nima wlh bana so daga yau kaje kawai ka amso takarduna ko?â€
Ta 'karashe mgnar tana kallonsa.
Gira ya 'daga mata ya ce“Allah ya miki albarka Babyn Abientah.â€
'Yar dariya tai ta janye tana fa'din “Abie bari akawo coffee me da'di.â€
Ta qarashe mgnar ta nufi hanyar kitchen, da 'dan gudunta, jikinta ko ina na motaswa yake.
Abie kai ya girgiza yana fa'din.
“Babyn Abienta yarinyar kirki.â€
Chapter 62 · 0% Book details