← Book details Dattijon Arziki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 118

Sashe 47

Dattijon Arziki Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Kallon Ibtisam yay yana riqe da ita jikinsa, bata iya ko 'daga 'Yar yatsarta sbd alluran da aka mata,shiyasa tai lamo jikinsa tana famar zaro idanunta cizonsa take so ta yi ta kasa sbd batada kuzari ko guntu atare da ita.
Hancinta yaja ta hararesa tana zaro masa idanu.
Guntin murmushi yay yana 'daga mata gira.
Karaf akan idon Laraba, wacce ta takure waje 'daya.
Ta ce“Lah ha ilah illallahu! Me zan gani Jafaru iskancin da yasa ka nace ka biyo mu kenan? Yarinyar ba lafiya keke neman koya mata iskanci? Toh meye idan ba iskanci ba 'daga ma mace gira....â€
Wawan bugo Tanko ya kaima bakin Laraba tai saurin kaucewa tana rufe bakin nata.
Abie kunya ta saka bai 'dago kansa ba yana mamakin matar matuqa.
Ja'afar ransa ya 'baci sosai amman yay shiru bai ce komai ba.
Tanko cikin kwantar da murya yaba Ja'afar hkr.
Ya kalli Abie ya ce“Don Allah Alhaji daga munje an bata 'daki idan zaka dawo zamu biyoka wlh MATAR nan bazata bari azauna lafiya ba acan shi ka'dai zai iya jinyar matarsa daman ai ba yarda take damu ba.â€
Abie ba tare dare da ya yi mgana ba ya jinjina kansa hakan ma ya yi.

Rahma ma tana can tana shirin tafiya Espagne gobe insha Allah.

Sai tsakiyar dare suka shigo 'kasar Australia.
Tinda airport Ja'afar yasan lallai wannan 'kasar babbar 'kasa cikin manyan 'kasashen duniya.
Laraba 'kauyanci 'kiri² ta dinga nunawa.
Wasu manyan motoci guda biyu akazo tarbarsu da ita.
Lallai Abie babban mutum ne wanda duniya ta san da zaman sa.
Ba hotel suka nufa ba, wani tamfatsetsan gidane wanda yake mallakin Abie 'din.
Tinda wajan gidan zakaji sha'awar ina ma ka kasance acikinsa.
Suna shiga falon wanda ya gaji da ha'du suka zazzauna.
Pa 'din Abie nan Australia ya shiga musu sannu da zuwa bayan ya jido kayansu.
Abie ya ce “Nadeer yanzu dare ya yi sosai zuwa gobe sai muje asibitin kaje kaima ka kwanta sai da safe.â€
Cikin girmamawa Pa Nadeer ya amsa “Allah ya huta gajiya Oga.â€
Babban kukan Abie wanda idan yana 'kasar shine ya shirya musu daddan girki nan falon saman carpet ya shimfi'da wata babbar lade mai kyau ya jera musu abincin.
Sai da sukaci suka nat Abie yama Tanko da Laraba jagora Inda zasu kwana.
Yazo yama su Ja'afar wanda Ibtisam 'din bacci take.
Abie ya ce“Kaje da abinci idan ta farka cikin dare sai ka lalla'ba ka bata, ka dinga kiyayewa kar ka ajiye duk abinda kasan idan ta gansa zata iya 'dauka ta buga maka.â€
Ja'afar yay godiya yana qara ganin kima da darajar Abie 'din.
Abie bayan ya rufe falon ya shige bedroom 'dinsa mai girman gaske ta tsaru. Wanka yay ya 'dauro alwala ya shirya yana baza 'kamshi ya Rama sallar magarib da isha, ya miqe ya fara nafila.
Ja'afar ma hakance bayan ya kwantar da Ibtisam yay wanka ya rama sallah ya shiga nafila dan tin rada ya dawo haicinsa bai sake cikakken baccin dare ba sosai.
Abie sai 'karfe uku ya gama bayan ya jima yana ma Allah kirari yama mahaifinsa da Ummu Aymana and Aliyu addu'a, ya miqe ya cire jallabiyar ya sanya kayan bacci kwaso wayoyinsa yana dubawa kasancewar layinsa na Australia har biyu.
Ganin kiran Rahma yay har miss calls 6 a'dayar layin miss calls 7 da message 2.
'Kwan filar 'dakin ya kashe ya bar na gefen gadon ya 'Kara gudun Ac kasancewarsa mutum mai son sanyi sosai. kwanciya yay yana dafe goshinsa Allah ka'dai yasan halin da take ciki.
Message 'din ya duba.
_😭“Abiena Allah yasa kana lfy ina kiranka ka qi ka 'dauka na kasa bacci ina son naji lafiyarka, ya gajiya? I miss you so much Abiena.😢_
Kansa ya dafe yana fa'din.“Oh! Babyna ina fa lfy gajiya ce kawai.

Bai kirata ba ya tura mata message.
_😔“Wayyo Babyna yi hkr Abienki ya gaji ne, sosai ina lfy, gobe zan kiraki nasan yanzu kinyi bacci, kina maqale cikin zuciyata ban manta dake ba, gajiya ta saka ban kira ki ba, miss you too baby ummina.😘_

Dr Moha ya kira sukayi mgna akan gobe suna shigo asibitin.
Har tsawon 5 minutes yana jiranta shiru yay murmushi daman yasan ta yi bacci.
Addu'ar kwanciya bacci ya karanta ya rufe rabin jikinsa da blanket, ba jimawa bacci yay awon gaba da shi.

Ja'afar uku bata qarasa ba, ya kammala ibadarsa ya miqe da jallabiyar ya kwanta yana rage hasken 'dakin.
Jikinsa ya jayota ya rungumeta tsam yana kallon kyakkyawar fuskarta, yana shafa gashin kanta wanda bai fiye yawa ba.
Addu'ar kwanciya bacci ya karanto musu.
Yaji Ibtisam ta fara motsi sai yaji ta shige cikin 'kirjinsa sosai ta 'kan'kame shi.
Ajiyar zuciya ya sauke ya sake matseta gam yana shafa bayanta alamar lallashi.
Cikin baccin gajiyar da ya 'daukei shi yaji wata irin iska mai 'karfi kamar guguwa.
Azabure ya bu'de idanunsa bakinsa 'dauke da addu'a.
Abienda idanunsa suka gane masa'ne ya yi masifar gigitashi.....!!

_💃ðŸ»'Yar Ajin Tubarkallah🥰_

_*🤲ðŸ¼Ya Allah ka jiÆ™anmu kayi mana rahama badan halinmu ba.ðŸ™ðŸ¼*_
3/2/22, 22:41 - Buhainat: ```D A```

```47&48``

_*My Sisters Don Allah Don Darajar Annabi Karki Karanta Idan Baki Biya Ba, Na Ku'dine Idan Kinga Yana Yawo Na Satane Ga Hanyar Da Za Ki Samu Naki Akan.😟👉ðŸ¼300N +22796515805*_
Chapter 47 · 0% Book details