Sashe 27
Dattijon Arziki Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
aikin jinnu bai damuba da gaban iyayanta yake cikin zazzaqar muryasa ya ce“Oyoyo My Qalbi.†Zo zauna kusa dani gasu Abba nasan bazasu hanamu auren juna ba.†Abie 1 idanunsa sunyi masifar yin ja kansan yayi wani irin mugun sara masa atake jijiyoyin kansa suka fito sukayi ra'dau² wani irin jiri yaji yana 'dibarsa azaunen, bakinsa 'daci yaji maqoqwaronsa take ya bushe, hakan ya saka ya kwantar da bayansa akujeran ya runtse manyan fararen idanunsa da suka zama kamar gauta. Ahankali 'dan 'karamin jan bakinsa yake motsawa, ya shiga kiran sunan Allah. Rahma ta iso ta zauna kusa da shi tana sakin tattausan murmushi, suka qurama junansu idanu. Abie2 ya ce“Ikon Allah! Wannan wane mai 'daukan alhakin ne yay wannan abin mai ha'darin gaske?†Abie 1 ya bu'de idanunsa cikin dauriya ya ce“Pls Abdulmajid kayi wani abin tin ban rasa raina ba.†Ya miqe tsaye ya zuba hannayensa cikin aljihun wandonsa ya nufi hanyar fita. Rahma yaji ta rungumeshi ta baya tana kyalkyala dariya ta ce“Abie Ngd zaka auramin Ja'afar ko¿†Murmushin yaqe yay ya cireta ajikinsa ya lakaci hancinta ya ce“Eh jeki zauna Abie 2 ka kula da kasancewarsu har ya tafi.†Ya juya da sassarfa yabar falon. Cikin farin ciki ta dawo ta zauna suna firasu su uku, Abie 2 na qara musu 'kwarin guiwa sbd yasan idan Allah ya yarje masa matuqar daman ba 'kaddara aurensu bace ahaka toh tabbas zai rabasu da shai'danun aljannun nan. Abie yana fita ya shige wata narkekiyar mota qirar Jeep 2021 ba'ka shi 'daya ya fizgeta ya nufi gate yana zuba uban horn. Megadi sanye da uniform, ya wangame masa gate jikinsa na rawa, ya sulala motar aguje ya fice daga gidan. Security's 'dinsa na ganin haka suka shiga mota suka rufa masa baya. 'Bangaran Ibtisam ranta ya yi masifar 'baci atake taji matsanecin son da takema Ja'afar ya riki'de yana zama tsana mai zafin gaske dan ya gama yaudarata. Bayi ta shiga ta ci kukanta ta gode Allah ta fito ta shiga 'dakinsu kamar abin arzi'ki ta bu'de Jakarta ku'din da Ja'afar yake bata ya ce“Ta dinga siya abinda take so ta kwashesu dukkansu ta 'kirga ta ga tsaf zasu isheta komawa Niger. Hamdala tai ta 'kullesu jikin kallafinta ta 'daura a'kugunta ta sanya dogon hijab, ta goge lambobin da suke cikin wayarta baki 'daya ta ajiye wayan sama Jakarta dan tai al'kawalin bazata tafi da komai na Ja'afar ba. Fitowa tai Baba mai taxi na zaune Falmata na masa fifita yana con abinci, sbd zafin da aka fara. Bintu na zaune. Ibtisam ta rusuna cikin 'boye damuwarta ta ce“Baba zan amso magani nan kanti cikina na mur'dawa.†Baba me taxi ya ce“Subahanallahi ai kuwa tsamki ba da'di leqa ki gayama Ja'afar sai kizo muje asibiti zaifi akan wannan maganin katin ban sonsa.†Cikin murna da alamun nasara ta amsa da “Toh Baba.†Ta miqe ta fara tafiya Falmata na cewa. “Sannu Ibtisam tsamki ba da'di Allah baki lafiya.†“Ameen†ta amsa ta fita. Cikin sauri ta fice tana addu'ar karta gamu da Yahuza ko Harisu. Ganin ta karya kwanar gidan ta sanya gudu sosai take gudu na uban mamaki, har ta kawo bakin titi ta samu taxi ta shiga tana maida numfashi ta ce“Babbar Tasha zamuje.†Me taxi yaja suka tafi. Su na dab da isowa tashar motar, wanda Abie shi kuma yake zuba uban gudu ba qaqqautawa, sam baima san Inda zaije ya samu nutsuwaba, sam bai lura da mai taxi na gabansa ba, sai da ya qureshi ya furta “Ya Salam!†Ya na qoqarin taka baurki yana zuba horn dan mai taxi ya kauce,tinda burkisan yaqi taku sai ji kake Kauuuuuuuuuuu ya bige mai tasan ta baya, motar ta kife 'kasa tana gangarawa gefen titi, lokacin mai babbar mota kuma yana dab da isa wajan motar me taxi wanda jama'a suka kwashi salati ana ihuuuuuu. Abie tsabar firgita jikinsa rawa yake Idanunsa ya firfito waje yana fa'din. “Innalillahi wa'inna ilahir raji'un!!