← Book details Dattijon Arziki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 118

Sashe 43

Dattijon Arziki Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Abie ya har'de hannayensa saman 'kirjinsa, ya kafeta da narkukkun idanunsa, cike da mugun mamakinta yadda ta dun'kule waje 'daya kamar me jin sanyi, ta dage tsakaninta da Allah tana gabzar kuka, tana rattabo masa bayani.
“Ni kam shi kenan don Allah Abiena kayi hkr na tuba, wlh ba dan naji mgnar ka bane, nazo corridor 'din nan dan na 'buya. daga wajanka nake zatona kana bathroom, lambune zanje ina tafe 'kamshin ka ya farmaki hancina, ina 'daga kaina na hango ka, ganin kamar waya kake mai mahimmanci shine na 'buya idan ka gama sai na zo gareka.â€
Ta kai 'karshen mgnar tana ha'de kai da guiwa tana 'kara sautin kukan.
Abie wani sihirtaccan murmushi yay, ya matso ya tsugunna gabanta, kamar zai shige jikinta sai ya 'dan matsa gefe.
Dab da kunnenta ya kai bakinsa, ahankali cikin wata sihirtacciyar muryasa mai taushin gaske, ya furta.
“Ok.. ok! Baby naji bar kukan, kin san ban jure kukan ki? Toh meye ma na kukan Baby ummina?â€
Ya 'karashe tambayar, yana bin dukkan jikinta da wani irin sihirtaccan kallo. “Wow! Babyna wanka ya yi kyau.â€
Sanya tattausan hannayensa yay ya 'dago kanta, dab da fuskarta yake fa'din “Shiru baby please, kinga yadda kikayi kyau kuwa? Kin zama kamar 'Yar 15 years ba 18 years ba baby ummina.â€
Ya 'karashe mgnar yana zama 'kasan ya shigar da ita cikin 'kirjinsa mai fa'din gaske, ya kwance 'dan kwalin kanta ya barbaje dogon gashin kanta wanda yasha gyara da maiyuka masu tsada yana wani irin fitinannan 'kamshi, ya shiga shafawa anutse yana sumbatar gashin, yana sakin murmushi, ha'di da buga bayanta alamar lallashi.
Rahma tai shiru ta daina kukan tana sauke ajiyar zuciya wata irin nutsuwa na shigarta, ga wani sanyi da yake ratsa zuciyarta, gefe dadda'dan turaren jikinsa mai masifar tsada, 'kamshinsa ya gama kashe mata jiki,tai luf abinta har sake 'kam'kameshi take, tana lumshe idanunta sbd da'din yadda yake sosa mata gashin kanta.
Bakinsa ya kai dab kunnenta, ya fara mata mgna cikin siriryar murya, wanda tsinin la'bbansa ya kasance yana gugar fatar kunnenta, tai saurin 'kam'kameshi tana 'yar dariya.
“No! Baby bar dariya mgnar gaskiya muke, zan miki tuni akaro na uku kinada miji, akwai igiyoyu guda uku akanki, tin kina 'yar 'yar shekara 12 aduniya, ki kiyaye kisan irin shigar da kikeyi, yanzu da hakan za ki fita lambu ki gilma 'kartin ma'aikatan gidan su na kallon ki?â€
Ya 'karashe tambayarta yana 'dago da fuskarta wadda take cikin tafin hannunsa, ya zuba mata rikitattun idanunsa, ya na ha'de fuskarshi tam! Alamun ba wasa.
Ya shiga tattara mata dogon gashinta irin na asalin larabawa.
Rahma 'kurr ta masa da idanu, tana nazarin mgnar Abie, sai ta kasa jure kallon nasa ta sadda kanta, ganin Abien ya birkice mata lokaci 'daya sai ya zame mata tamkar wani matashin saurayi 'dan shekaru 30, duk da daman bazaka ta'ba cewa ya kai shekaru 50 aduniya ba, sbd jin da'di ga hutu da ya gama ratsa shi.
Tunanin mgnarsa ta shiga wai tanada miji tin tana 'yar 12 years, ta kula wanda idan bazata manta ba, wannan shine karo na uku,amman yafi shekara bai mata mgnar ba sai yau sbd yasan ba wani mazan take kulawa ba, sannan bata shigar da za'aga ko fatar wuyanta bare bayanta.
Kanta ya fara 'daurewa shin da gaske yake ita 'din matar aure ce? Ta ya zai 'daura mata aure da wanda bata saniba? Kuma tin tana 'yar shabiyu, kenan yanzu shekarunta 6 tanada aure? Sannan ba shawarata? Duk da tai qarama lkcn batan meye aure ba.
Shin yaushe ne ma ashekaru 6 ya 'daura mata auren? Dan yanzu ta shiga wasi-wasi ganin mgnar yau ta banbanta da na shekarun baya, tin batada wayon kirki, yake yawan fa'da mata tanada aure, ta riqe martabarta mijinta yana tafe gareta sai ta kammala karatunta. amman tinda ta zama cikakkiyar budurwa sau 3 kawai ya mata mgnar.
Da sauri ta 'daga kanta kamar an tsikareta.
Idanunsu ya sarqe cikin juna.
Jurewa tai idanunta cikin nasa ta damqe hannunsa, sosai ta fara mgna.
“Abiena, idan ban manta ba, wannan shine karo na uku tin fara zamana cikakkiyar budurwa kana tunatar dani inda miji, amman sai bayan shekara kake fa'damin, wanda hakan yake sakawa na manta na shagala, duk da zuciyata na gayamin banida mijin kana gayamin hakane amatsayina na 'yarka domin na kare martabata da martabar gidanmu...â€
Dogon numfashi taja ta 'boye kanta cikin 'kirjinsa wanda jikinta ya 'dauki mugun 'bari sbd yadda ta ga Abien ya kafeta da idanu yana sakin 'kayataccan murmushi, sai kawai kasala ta saukar mata.
Cikin fizgo numfashinta wanda yake 'ko'karin barin gangar jikinta, ta ce.
“Abie nasan bazaka ta'ba cutar daniba, sai dai ta ya kasan inada miji ka bari nayi soyayya da wannan baqin yaron arashin sanin nayi? Sannan kasan inada mijin ranan ka isko ina bacci ka shiga kwararo min da addu'a Allah ya ban miji nagari mai tsoron Allah wanda zai riqe maka 'yarka bisa amana, toh me yasa kayi addu'ar nan um Abiena?â€
Abie ya numfasa cikin ra'da ya furta.
“Baby lokaci na tafe, wannan duk mai sauqine babyna randa na miqaki 'dakin mijinki, zan miki bayanin komai, na kuma miki alqawalin randa kika ha'da idanu da mijinki idan har bakya sonsa kinji bazaki iya zaman aure da shi ba zan saka ya sakeki ki kawomin za'bin ranki na aura miki Ok babyna?â€
Rahma ta 'dago cike da farin ciki ta ce“Allah da gaske Rabin raina Abie?â€
“Wallahi da gaske Rabin Raina ummina, nayi alqawalin sanyaki farin ciki na miki duk abinda kikeso daga nan har na bar numfashi.â€
Ya 'karashe mgnar yana 'daga mata gira 'daya ha'di da wani 'kayataccan murmushi wanda ya saka duk ta birkice tama kasa sanin da wa take tare.
Cikin diriricewar da tai ta maqale masa sosai ta manna masa kiss saman goshinsa muryata na rawa ta ce“Ngd Abiena ina sonka kaji.â€
'Yar dariya mai 'kayatarwa yay, wacce ta sake rikitata ta sakar masa kukan shagwa'ba.
Ganin kamar ta diririce ta shiga wani yanayi wanda shi yasan meye ya miqe da ita tana jikinsa yana fa'din “Na tuba ummina shiru please. â€
Shiru tai jinta kwance cikin 'kirjinsa ya nufi hanyar bedroom 'dinsa da ita.
Bai direta ko ina ba, sai tsakiyar makeken royal bed 'dinsa ya kwantar da ita ya lulu'beta da wani tafkeken lallausan bargon wanda yake fitar da dadda'dan 'kamshinsa, ya rankwafo ya mata kiss agoshinta, ya ga yadda take kallon lips 'dinsa tana matsar kwalla.
Waskewa yay ya ce“Oya Babyna bacci, bari na shirya zanje hospital 'dinki na dawo, ance wani bawan Allah yana nema na.â€
Ya shafi fuskarta, yana barin wajan.
Idanunta ta runtse bata iya furta komai ba, sbd bazata iya mgna ba, adaidai wannan lkcn nan, sam bazata iya ba, ayanayin da take ciki.
Kamar bayan 25 minutes cikin baccin da ya 'dauketa mai da'din gaske taji tattausan lips 'dinsa saman kumcinta ya manna mata kiss, 'kamshinsa mai azabar da'di ya mamaye dukkan 'kofofin hancinta, ta sauke numfashi mai wahala, asanyaye cikin baccin da yake cinta ta kirasa.
“Abiena! Pls.â€
“Na'am Babyna! Pls me um?â€
Kai ta girgiza dakyar ta iya fa'din.
“Jibi mukeda jarabawa ya kamata gobe na wuce.â€
Ta 'karashe mgnar tana bu'de shanyayyun 'kananun idanunta masu haske, ta kalleshi yadda ya rankwafo sai taga sosai ya cika mata gaba.
Hannunta ta 'dora saman fuskar shi tana ta'ba sajansa, zuwa gemunsa ta ja dogon hancinsa ta 'dora yatasarta saman jajayen lips 'dinsa wanda sak baida banbanci da nata.
Sosai take kallon tsantsar kamarsu da Abienta, ta ha'diye wani irin yawu ashagwa'be ta kira shi “Abiena bacci nakeji sosai.â€
Ra'da ya mata ya na sakin murmushi.
“Ok Baby oya bacci ko na kawo miki shayi me zafi? Idanunta ta rufe ruf, kai ta girgiza tana hamma, still idanunta rufe. Murmushi yay ya sake kissing 'din kumatunta ya ce “Ok bye ki tashi lfy Baby.â€
Ya 'karashe mgnar yana janye kansa dab da ita ya juya ya fara tafiya, hasken 'dakin ya rage mata, ya rage gudun Ac.
Sai lokacin ta bu'de kyawawan lumsassun 'kananun idanunta wanda suke cike da bacci, kallonsa take cikin 'danyar shaddah me suna (Annur) brown coffee, 'dinkin ya fito da dattakunsa sosai, wata irin tafiya yake mai cike da kamala.
Har sai da ya fice ya rufo mata 'kofar kafin ta janye idanunta daga 'kofar.
'Katuwar ajiyar zuciya ta sauke ta shige cikin bargon, tana shaqar 'kamshisa asakalce ta furta.
“Wlh daman ace mijina halaiyarsa da dattakunsa da kominsa irin na Abiena ne, amman gaskiya banjin zan wani sosa tinda Abie ya min alqawalin raba auren idan bana sonsa, Abiena Allah ya baka mace tagari, Allah sarki ummatah Allah ya jiqanki da rahamarsa.â€
Ta 'karashe mgnar tana goge hawayen da batasan yadda akayi suka zubo mata ba. Ahaka baccin ya sake saceta.
Chapter 43 · 0% Book details