← Book details Dattijon Arziki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 118

Sashe 21

Dattijon Arziki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jaddatu zaune tana Jan casbi. Latifa na zuba mata shayi.
“Latifa ya nakeji kamar cittta da kananfari ya yi yawa ne?â€.
Latifa ta ce“Jaddatu yadda naake sakawa kullun ne na saka kur'bi kiji.â€
Hanan tai dariya ta ce“Ummi na neman laifinki ne yi ki wuce abinki.â€
Jaddatu ta bugama Hanan casbi ta ce.
“Wlh za ki koma inda kika fito shegiya uwar tusar tsiya.â€
Latifa tai saurin ha'diye dariyata ta zubawa Hanan shayin ta bar falon cikin sauri gudun kar ace ta yi.
Rahma ta wucesu 'Kala bata ce ba.
Jaddatu ta ce“Rahma ni kikewa gaba bayan duk fitsara da kika min 'dazu?â€
Rahma ta dafe goshinta ta juyo ba tare da ta yi mgna ba ta ha'de mata hannuwaðŸ‘ta juya ta fice.
“Anya junnu basu shafi yarinyar nan ba kuwa? Ikon Allah! â€
Iman ta bi Rahma da gudu.
Abie ya sauko ya zauna kusan Jaddatu yana murmushi ya ce“Ummi keda Wa?â€
Hanan ta ce“ita da Ummi qarama, wai ta fice dan bata mata mgna ba wai shi kenan gaba take mata.â€
Abie yay dariya ya ce“Ba ruwana sunfi kusa.â€
Jaddatu ta ce.
“Dole ka fa'di hakan mana Abdul.â€
“Ummi bari naje mu gaisa da baqon naku...â€
“A'a wlh ban ciki can kai da 'yarka, iyayan kwashe².â€
Raiyana ta ce“Wlh fa ummi kwashe2.â€
Hanan tai dariya ta ce“Ummi ina sonki za ki mutu ki barni.â€
“Ai dole tinda ke tsaron duniya kikazo.â€
Abie ya sumbaci Jaddatu ya mi'ke ya kaima Hanan duka ya ce“Ban ta'ba ganin me maida Uwa kaka ba sai ke.â€
Ya 'karashe mgnar zai fita Raiyana ta ce“Abincin fa?â€
Bai kalleta ba ya ce“Sai na dare nayi ciye-ciye cikin jirgi.â€
Ya qarashe mgnar yana tafiya.
Da idanu ta rakasa, sosai take masifar sonsa ta sani idan batai wani abun ba ba zata ta'ba samunsa ba.

Rahma tana zaune kusan Abie 2 suna fira, sai ta ga kamar ya sauya mata.
Abienta ne ya shigo da sallama suka amsa.
Rahma taqi kallonsa tana ji ya zauna dab da ita, har tana jin hucinsa.
Abie2 ya ce“Ya gajiya?â€
Abie ya amsa“Alhmdllah! Ya zaman hkr har na samu lokaci zuwa gobe sai mu tattauna insha Allahu.â€
Abie 2 ya ce“Ina godiya Allah ya qara girma ya tsareku da dukkannin abin qi.â€
Rahma da Abie atare suka amsa da.
“Ameen.â€
Rahma na shirin kwantar da kanta akafa'dar Abie 2 Abienta yay azamar kamota ya mi'kar da ita tsaye ya mi'ke.
Kuka ta sanya masa ta fara fizgewa.
“Ya Rabb! Baby me na miki kuma? Oya muje naji.â€
Bai jira komai ba ya 'dauketa ca'dak kamar jaririya ya mannata 'kirjinsa ya fice daga falon.
Abie2 ya tintsire da dariya ya ce“Ikon Allah! Wannan 'diyar tamu akwai rigima.â€
Rahma shiru tai jinta 'kirjin Abienta tai luf harda tura fuskarta 'kasan wuyansa tana shaqu ni'imataccan 'kamshin jikinsa.
Lambu ya nufa da ita.
Tsakiyar wasu korayen ciyayi ya sauketa ya zaunar da ita shima ya sauna ya kamo hannayenta yana murzawa ya 'dago ha'barta.
Cikin taushin murya ya ce“Fa'damin laifina baby ummina sai na baki hkr ok. Amman kar na sake ganin ko kusa kin zauna kusan Abieni 2 duk rada na sake gani zan kore shi.â€
Kallonsa ta yi tai saurin runtse idanunta ta kwantar da kanta a'kirjinsa ta shiga sauke numfashi da Sauri Sauri, bugun zuciyarta na qara tsananta, ta shige jikinsa sosai ta kira shi.
“Abiena Rabin raina?â€
“Na'am Baby ummina mene um�
Kai ta girgiza masa ta shiga sauke ajiyar zuciya.
Tsakiyar kanta ya sumbata yana shafa kanta yay mata ra'da akunnenta.
“Babyn Abienta yay sauran sati 2 ki koma Espagne. â€
Kuka ta sanya masa.
“No! Karatu dolene babyna tare zamu zan tsaya har tsawon sati sai kin warware na dawo ok?â€
Kai ta jijina, tana sakin murmushi.
Haka ya samu cikin dubara har ta Saki jikinta ya Kama hannunta suka zagaya lumbun, ya tsinko mata lemu da ayba basu qarasa nuna ba, kiran magarib ne ya dawo dasu cikin gida.

Ja'afar fita yay yaje kasuwa ya siyoma Ibtisam dogayan riguna masu sauqin ku'di irin na shuwa arab guda biyar da hijabai uku takalma uku sai mai turare sabulu da soson wanka.
Tinda ya dawo ya zauna tsakar gida har lokacin da aka fara kiraye² magarib, ya mi'ke domain tashin Ibtisam.
Sosai take baccinta hankali kwance.
Tsugunawa yay dab da katifar ya du'ko kansa bakinsa dab da kunnenta cikin nutsuwa ya kirata.
“Mon cÅ“ur! Ta shi.â€
Yadda la'bbansa suke ta'ba fatar kunnenta sai taji kamar susa mata fatar kunnen ake cikin bacci.
Sake mi'kewa tai tana turo baki gaba.
“Oh! Bazaki tashi bâ?â€
Ya qarashe mgnr yana mur'da kunnenta.
Zabura tai tana fad'in .
“Wayyo Anna zafi....â€
Idanun hu'dun da sukayi da Ja'afar ya saka ta ha'diye sauran mgnar ta sadda kanta.
“Ta shi ga kaya nan na siyo miki anjima za ki koma wajan baba me taxi akwai budurwa dai dai ke ki jira nasan me zanyi, sauran kice gudowa kikayi zaice musu ke matata ce 'daki muke nema zan qaura nabar ma su Harisu nan.â€
Cikin murna ta mi'ke ta fice da gudu tana fa'din.
“Allah yasa“Na zama matarka.â€
Da kallo ya bita yana murmushinsa mai tsada ya motsa 'kasan labb'ansa ya ce.
“Ameen baby love.â€
Alwala yay ya tafi masallaci.
Itama alwala tai ta zari hijab 'daya cikin kayan da ya siyo mata ta saka, tai sallah.
Su Harisu koda suka isko Ibtisam abin bai basu mamaki sanin irin soyayya da sukewa juna, kuma ya kirasu ya musu bayani akan su rufa masa asiri har komai ya dedeta. Bayan sunyi abinci baba Tsalha yazo ya tafi da Ibtisam kewayansa. Da hannu biyu Falmata da yaranta suka kar'beta.

★★★★★★
Bayan sati 'daya.
Rainaya tana ta shirya tugunta cikin sirri wanda Ja'afar da Rahma basa tunanin ko a mafarki irin k'addara zata iya afka musu.
Haka Ma'aruf na Gabon bai dawo ba.
Duk wani motsin Ja'afar a Tchad ya sa ni, tsaf zuwan Ibtisam ne bai saniba sabida ba damuwarsa bace, yanadai bibbiyarsa idan yana masa aiki,shi mutunne idan kana masa aiki sbd sana'arsa mai ha'darin gaske toh bai yarda da kowa, ba ko waccan direban ya 'batar da shine har lahira sabida zai tona masa asiri.
Amman abu 'daya ya basa mamaki Ja'afar bai saka masa idanu ba, shi dai aikinsa yake na driving.

Ibtisam hankalinta kwance Ja'afar na kulawa da ita kullun da safe zai shiga su gaisa, haka zai kirata da sabon layin da siya mata suyi fira.
Baba tsalha ya ce su shirya kawai sai suje Cameron wajan yayar Baban Ibtisam karime sai suyi mgna ta fihimta sai 'dauro musu aure acan amman sai anyi mgna da Malam Adamu dan auren ya yi albarka.

*Gabon*
Zaune yake a falonsa daga shi sai guntin wando, iya guiwa.
Waya yake yana 'kyal'kyala dariya ya ce. “Wallahi naso rama abinda ya min toh amman shegen yaron ina mugun anfanuwa da shi, duk wani abin 'karfin tasirin asirine wlh ko zaka kashesa bai San cewar shine ya satomin 'diyar governor ba a *Hermepolite*, sai da na tatsi 20 millions kafin na bayar da ita, har yau basu isa su kamani ba. Amman kasan shi nakeso ya 'kwamuso min Rahma Abdul Majeed Abdulwahab Marocco. Sbd yaron akwai sa'a atare da shi.â€
Daga can mutumin yay dariya ya ce“Au wai har yanzu an rasa hanyar bi asaceta? Ni kuma da zakabi shawarata idan an satota kar kanemi fansarta da ku'di kawota ayi safarata wlh yarinyar nan yadda Allah ya mata halitta mai kyau zaka samu millions ba adadi amaidata karuwa kawai.â€
Ma'arufa ya ce“No! Akwai abinda zan shirya na rama wulaqanci da ya min, inason na samu wacce yakeso na 'kwamushe... Kai nafasa ramuwar gayyar ma, Rahma Abdul Majeed bari kaga abinda zan saka Amata sai muga zai rayu ko mutuwa zaiyi uban nata...â€
Knocking 'din qofar akayi ya mik'e ya nifi qofar yana fa'din.
“Madam ta dawo gobe nake shigowa Tchad zamuyi waya.â€
'Kofar ya bu'de, Aishatu tsaye tana yamutsa fuska.
Gefenta Rabi'ah ce ta kafesa da idanauwa.
Gira ya 'daga mata, ya ce“Baquwa mukayi?â€
Aishatu ta fice tana fa'din.
“Rabi'a h ce baquwa? Ji sokana.â€
Dariya yay ya nufi bedroom 'dinsa Aishatu ta bi bayansa.
Rabi'ah ta zauna tana karka'da qafafunta, ta ce“Bazan barki kici arzi'kin nan ke 'daya wlh.â€
Saman gado ya kwanta Aishatu ta zauna tana shafa tumbinsa ta ce“Ni kaban ku'di zamuje shopping. â€
Baki ya ta'be ya ce sai kin ban na 'Dana marowaciya, dudu so nawa nayi tinda nazo zo naga babyna.â€
Zatayi mgna ya rufe mata baki da nasa ya shiga dagula mata lissafi da Rana tsaka ya 'barjeta son ransa Allah yasa qofar arufe da Rabi'ah ta jiyo ihunsu.
Da kansa ya shirya suka fita har Rabi'ah wacce ta dinga masa irin wasu abubuwa a 'boye na alamar tana sonsa da sun ha'da ido.

*Niger Tahoua*
Tanko tsaye tsakar gida yanaa kallon yadda Jamilu yke musu tijara ba kunya ba tsoron Allah.
“Wallahi na Baku sati idan Ibtisam bata dawoba daga yawon tamba'dar sai kun biyani kayana da ma'kuddan ku'da'den da na kashe muku har na gyaran gidan da na muku. 'Kilqmq da saninku ta gudu kunyi hakan dan kuci dukiyata....â€
Laraba da takaici y isheta ta warto muciya ta sauke masa adoron bayansa, sai da ya rankwafa.
Zata qara masa Tanko ya riqeta.
“Ai ka bari na qara masa fita ka barmana gidanmu bazamu bayar da ku'din ba kaji 'dibar albarka uban waye ya janyo mana 'yarmu ta 'bata idan ba kai ba?â€
Jamilu ya ce“Ni kika buga toh ki jira sakammako kuma auren ba fashi tinda kun bani.â€
Ya fice da Sauri ganin tana Neman zubar da Tanko qasa sai ya 'dauka ko aljanu gareta.
Tanko ya ce“Insha Allahu zamu baka ai ni inason auren.â€
Laraba ta ce“Ba wani nan qilama da saninka ta gudu wlh zataci ubanta duk randa ta dawo aure kuwa ba fashi, ai kawai na nuna masa rashin ta idon da ya nuna mana ne, yo Wa ya bamu ku'din biyansa.â€
Taslim ta ce“Yanzu Anna meye anfanin irin haka? Kunyi sanadin 'batan aunty Ibtisam, ammaan ba nadama sai ma jiran kike tazo ki azabtar da itaâ€.
Ta qarashe mgnar tana kuka.
Ta shige 'dakinsu.
Tanko ya zauna yay tagumi yama rasa dalilin da yake son dole 'yarsa mafi soyuwa aransa matsa mata har tabar gida.
Chapter 21 · 0% Book details