← Book details Dattijon Arziki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 118

Sashe 2

Dattijon Arziki Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Dattijo ne farin balarabe dogo mai matsagaicin jiki, d'an kimanin shekaru 50 cif aduniya, amman tsabar jin dad'i zaka d'auka bai fice shekaru 45 ba.
Kyakkyawan gaske ne ma'abucin fara'a, yana d'auke da doguwar fuska mai zagaye da k'asumba da saja da wani gemu mai tsayi kyau wanda yake shan gyara, yanada yalwa gashin jiki sosai,yanada dara-daran idanu masu haske wanda k'wayar idanunsa golden ne, idanunsa nada wata irin baiwa acikinsu, wanda da zaran kun had'a idanu sai kaji shakkarsa, dan ko Raiyana da ta gama masa tijara ba ido cikin ido take masa rashin kunya ba.
Yanada gashin idanu masu kyau haka girasa mai kyau labb'ansa jajadattakza Rahama irin labb'ansa ta d'auko, sai dai nata pinky ne nashi jajaye masu taushi da shek'in jin dad'i.
Yanada dogon hancin da doguwar hab'a hak'oransa farare ajere reras yanada wushirya ta k'asa yanada dimple d'aya mai lob'awa sosai ko mgna yake lob'awa yake bare yay murmushi dan bai fiye yawan dariya amman murmushi bayada ruwansa.
Tsaye yake a gaban wani tafkeken dressing mirror yana sanye da tsadaddun manyan kaya na alfarma na kece raini, yalwatacciyar suman kansa ta sha gyara sai shek'i take, yana fesa wani shu'umin tsadaddan turare mai azabar sanyin k'amshi.
Waya yake cike da nutsuwarsa da dattakunsa cikin harshen larabci, yana sakin murmushi tamkar ba yanzu aka gama gasa masa mgna ba, gefen fuskarshi dimple d'insa na lob'awa.
Daga bathroom ta fito, farace siririya ita ba gajeraba ita ba doguwaba, kana kallonta kasan shuwa Arab ce, sabida gashinta har gadon bayanta, zatakai shekaru 32 a haife.
Manyan Idanunta wanda suke cike da wutar sha'awarsa ta tsira masa tana jin kamar ta rungumeshi, amman kwarjininsa ya hanata.
“Malam ina mgna kaji.â€
Ta k'arashe mgnar tana rik'e k'ugunta Juyowa yay fuskar shi atsuke ba fara'a cikin zazzak'ar murya shi ya ce“Ok zan zagaya asibitoci ne idan na dawo zamuyi mgna karka damu yallab'ai Nga sosai bye.â€
Ya tsinke kiran ya jefa wayarsa irinta Rahma aljihun gaban rigarsa ya nunata da yatsa ya ce“Ni kika fad'ama mgna irin wannan mai d'aci? Kinci darajar masu daraja Raiyana, banawa mutum gori amman ya na aureki? Kema baki fi sauran matan ba, duk wacce bata cika sharud'ana ba ta kuma ci jarabawata ba zata tab'a samu naba, har abadan sabida kun farkar dani daga bacci kun d'and'anamin azaba, darajar mahaifiyata kawai ta saka nake zaune dake, ashe kema mage ce mai kwanciyar d'aukan rai. (Na Sajida niger) .
“Good bazan sake ki ba sabida inada kima da daraja Wa idanun al'ummah kici gaba da zama kici arzik'i iya cinki, amman ki kiyaye harshenki.
Fita ban waje jeki d'akinki.“
Ya k'arashe mgnar yana nunata da yatsarsa.
Raiyana ta kauda kanta daga kallomsa sabida wani irin sonsa da yake azalzalar zuciyarta, ta ce“Wallahi nima dab nake da fad'awa duniya tasan kai waye. Kuma wajan Rahma d'iyarka wacce kafi so,zanje na mata bayani...â€
Fincikota yay cikin wani irin zafin nama, abinka da k'aefafan namijj, duk da kuwa an kwana biyu, amman k'arfinsa na nan.
Ihu ta saki sabida azaba yadda k'asusuwanta suka amsa.
Ya d'aga hannunsa zai mareta ya fasa, ya hankad'ata gefe.
sabida ba halinsa bane dukkan mata, dan duk tarin matan da ya yi bai tab'a dukan kowaba.
Tsawa ya daka mata
“Barmin d'akina idan kika sake shigowa ba tare da izini na ba, kiyi kuka da kanki bani ba.â€
Ya k'arashe mgnar yana dafe kansa da yake barazanar tarwatsewa.
Cike da mugun shakkarsa taja k'afafunta ta fice tana rufo masa k'ofar da k'arfi, tana tsoron hukuncin da zai d'auka dan ba k'aramin so take masa ba, kawai tana masa barazana ne dan ya mata abinda take so, shi kuma kaifi d'ayane.
“Astagfirullah wa'atubu ilak!
Ummu Aymana kin tafi kin barmu da Chakwakiyar duniya ni da Baby Ummina. Ance na auri babbar mace ga tanan na aura ba hankali, ba wayo sai jaraba da son abin duniya, shin wai ta ina zan fara neman matar da zata fahimce ni ta zauna dani tsakani da Allah yadda nake so mu rayu inuwa d'aya cikin aminci? Oh! Ya Rabbi!â€
Ya k'arashe mgnar cikin harshen larabci yana k'arasa shirinsa, ya fesa turaren ya d'auki sauran wayoyinsa
biyun kasancewar waya uku yake anfani da ita, kowace da muhallinta.
Agaggauce ya fito ya murza k'ofar wacce take zallar glass mai duhun gaske key ya nufi wajan Rahma ya ganta dan yasan ba lallai ta tashi ba, kasancewar tazo hutun makaranta har tsawon wata 2 zatayi, kafin ta koma (Espagne). Tinda ta zo yau tsawon kwana 7 kullun cikin baccin hutu take, idan tai breakfast ta koma bacci sai azuhur ta yi sallah ta sauko ta yi lunch, ta zaga cikin gidansun, ko ta fita wajan shak'atawa.
Wani had'add'an falo ne ya tsaru an kashe masa mahaukatan kud'i, wajan had'asa yaji kayan alatu, wasu irin manya kujerune masu zubin na sarauta, sukama falon k'awanya.
Wata farar dattijuwa ce 'yar kima nin shekaru 67 kallo d'aya zaka mata kasan balarabiya ce, zaune take hakimce, cikin shiga mai kyau, sanye take da rigar sanyi doguwa irin ta 'yan saudiya, har k'asa irin mai kaurin nan, ta yane kanta da madedecin gyale mai kauri, falon k'amshin turaren wuta da wani irin d'umi mai dad'i da na'uran d'umama d'aki ta d'umama k'aton falon.
Idanunta akan tafkekiyar Tv plasma, tana kallon tashar Aljazeera, cup d'in shayine ahannunta tana kurb'a hannunta d'aya tana jan casbi.
K'aton agogon da yake manne jikin bangon ta d'aga kanta ta ga 11:00 am.
Cup d'in ta ajiye cikin harshen larabci ta Ce.
“Ya Rabbi! Yaron nan me yake har 11 ta yi bai fita zuwa abinda zai k'ara masa kusanci da mahaliccin sa ba!? Ga shi gobe zai wuce zuwa Gabon. Wannan shagwab'abb'iyar d'iyar tasa sai ta farka ta b'ata masa lokaci, tinda naga da safen shayi kawai ta Sha, Rahma bata iya bacci da yunwa.â€
Ta k'arashe mgnar tana kallon hanyar beni, tana kiran.
Latifah!“
Cikin rawar jiki ta k'araso tana zubewa gaban tsohuwar, cikin harshen larabci ta ce.
“Jaddatu Rahamu ga ni Allah yasa ba laifi na yi ba?â€
Idanu ta k'ura mata tana janyo sandarta. Wanda ganin hakan yasa Latifa matsawa can nesa.
“Wlh Latifa cikin harakokin ki akwai munafurci, idan ba haka ba, daga kiranki sai kice kinyi laifi? Kaji munafukar yarinya, kina zaro min jajayen idanu kamar gauta. Jeki d'auko min wayata ad'aki saura ki shiga duba abinda baki ajiye ba, banda Rahma ta nace tuntuni kinbar gidan nan.â€
Latifa tai k'asa da kanta kamar zata fad'in abin arzik'i, sai ta fara mgna da harshen hausa sanin batajin hausar, ta ceâ€Zama daram agidan nan bid'ar kud'i nazo Allah ya datar dani kyayi kya barni munafukar tsohuwa kawai, wlh darajar d'anki mai kirki kike ci, da ina neman kud'in zamu samu muhalinmu na kanmu, da na jima da lakad'a miki duka na gudu, daga baya na rok'i gafara.â€
Latifa ta k'arashe mgnar tana mik'ewa ta nufi hanyar da zata kaita d'akin Jaddatu Rahamu.
Jaddatu Rahamu ta ce“Ke!! Zo nan, me kika ce da hausan?â€
Latifa ta ce“Jaddatu addu'a nai miki.â€
“A'a k'arya kikeyi, jeki aikin na fasa naji ai me kika ce zakimin sata ko? Je ki
kira min Ummin Adnan.â€
Latifa ta rusuna ta ce“Tom an gama Jaddatu.â€
Ta k'arashe mgnar ta fice zuwa kiran Ummi Adnan.
Rahma tana shigowa bedroom d'inta saman wani tamfatsetsan Royal bed mai girman gaske, ta kwanta taja wani irin jibgegen bargo kalar pinky mai taushin gaske, yana fitar da wani irin mahaukacin k'amshi, ta rufe dukkan jikinta, yayin da dogon gashinta ya baje ya rufe mata fuska, ta rungume wata k'atuwar Teddy wacce girmanta ya kusa ita.
Sannu ahankali take kuka mara sauti, cikin shashek'ar kukan ta fara mgna da harshen larabci cikin sansanyar muryata mai dad'i kamar sarewa.
“Ammi Raiyana ashe a idanun duniya kike nunawa Abiena so? Me yasa kika furta masa wannan mgnar wacce nasan ta masa zafi...â€
Jin k'aran bud'e k'ofar ya sanya tai saurin.........!

*🔥FITATTU HUƊU🔥*

*DATTIJON ARZIK'I* N300 katin MTN ta wannan number *+22795805*

TSINTACCIYA
Nimcyluv

SULTAN
mss flower

BAK'AR FATA
AUTAR MANYA

Gaba É—aya 800
Via 68517335 Na'ima Shu'aibu Sulaiman Fidelity Bank, masu tura kati 08188934 ga ƴan uwa na Niger +227905 za ku tuntuɓa. To show evidence of payment 08142105218

*Real Ladingo+22715805* For more information😇

_*🤲ðŸ¼Ya Allah ka jiÆ™anmu kayi mana rahama badan halinmu baðŸ™ðŸ¼.*_
2/2/22, 09:18 - Buhainat: _*DATTIJON ARZIƘI*_

*BY*
_Rahma ladingo Ummu Fareesa😘_

_*🔥FITATTU HUƊU🔥*_

_*HOME OF QUALITIES WRITERS ASSOCIATION*_

*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*

_*cнapтer 3&4*_
Chapter 2 · 0% Book details