← Book details Dattijon Arziki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 88 OF 118

Sashe 88

Dattijon Arziki Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

Sai da sukayi kukan su suka gaji ba me rarrashin wani, kafin Abie ya yi jarumta ya miqe zaune, janye Rahma daga jikinsa, yay ya sakko daga saman bed 'din, ya ware mata hannayensa ya ce“Taho My Baby muyi hkr kinji?â€
Kai ta jinjina masa ta rarrafo ta miqe tsaye ta sakko ta shige 'kirjinsa.
Zagaye hannayensa yay bayanta, ya matseta sosai, itama haka tai suna sauke ajiyar zuciya, ajere-ajere.
Sun jima ahaka kafin Abie ya zareta ajikinsa, ya kunna 'kwan wutar 'dakin, ya zaunar da ita bakin bed, ya sumbaci kumatunta, ya shiga bathroom.
Bai jima sosai ya fito ya Kama hannunta yana qarema rigar baccinta kallo 'yar mintsina komai nata waje.
Cike da jin kunya ta sinne kanta ta runtse idanunta.
Murmushi yay ya miqar da ita tsaye yaja har qofar toilet ya ce“Oya kiyi alwala ki fito.â€
Kai ta 'daga ya bu'de mata 'kofar ta shige.
Ta 'dan jima ka'dan ta fito 'daure da towel, tana noqe², sanye da jallabiya ta iskoshi, yay 'yar dariya ya kamota ya sanya mata jallabiyar hannunsa, ta mata ya yane mata kanta da mayafi, ya shimfi'da musu dadduma.
Sallar nafila da yake duk daren duniya wadda gajiya bata hanashi yinta sai dai ko halin ciwo, yaja su raka hu'du, fiye da awa 'daya suna zaune yana kwararoma iyayansu addu'a itama tanayi.
Shafawa sukayi ya miqe ya kamata ya ciremata jallabiyar ya warware mata mayafin ya saka mata rigar bacci, ya 'dauketa ya kwantar saman bed. shima ya canza kaya zuwa na bacci ya rage hasken 'dakin ya hauro saman bed 'din ya 'dorata 'kirjinsa ya lullu'besu da bargo yana shafa bayanta, ya kirata cikin ra'da.
“My Baby ummina!â€
Rahma ta amsa cikin sanyin murya da “Na'am Abie.â€
Sbd tusayinsa take matuqa yanzu fiye da kanta, dan ita 'din tasan ba marainiya bace tinda tanada Abienta, sai dai taso ace iyayanta na raye tanajin 'duminsu, amman Allah baya barin wani dan wani yaji da'di.
“My baby bacci kikeji ko?â€
Hannunta ta tura cikin sumar kansa tana shafawa ta ce“A'a Abie qarasa min labarin pls.â€
Murmushi me ciwo ya yi ya ce“Ok Babyna.
Naja'atu tsabar firgici da tashin hankalin da ta shiga alokacin bakina ya yi ka'dan na zayyano miki su, sai dai na kwatanta, dan zaune tai kusan gawar riqe da wuqar ta kasa motsawa, na iso jikina na tusma ina ta'ba Abbu ina ya mutu, saman gawar na zube ina wani irin kuka ina kiran sunansa.
Can kuwa kafin sukai ga ta'ba megadi sojojin da suke tsaron lafiyata sun dam'kesu sun saka musu ankwa, ko mantawa tai akwai jami'an tsaro agidan masu kulawa da lafiyata, sannan gidan Abbun kansa akwai security.
Ashe ihun da nayi sunji wasu na tare da 'yan fashin.
Ahalin da suka iskomo ya gigitasu, Naja'atu jini ya 'dauketa ta shiga beqa musu wuqar tana fa'din.
“Nice na kashe Abbu ya aurama mijina yarinyar da na Rena ina mata kallon 'yarsa don Allah kuce ya yi hkr kar ya sakeni...â€
Wani soja ya kifa mata gigitaccan mari wanda yasa tai shiru sabida bataji ba gani.
Handkerchief wanda ya mareta ya sanya ya amshi wuqar hannunta, ya cema sauran sojojin.
“Ku kaita mota ko ha'data da sheguncan.â€
Kasa cewa komai nayi kallonta kawai nake ina mamakin abinda ta aikatama mahaifina.
Hanawa nayi akai Abbu hospital sbd yariga ya mutu, ita kuma amman Ana kai su Naja'atu police station dole 'yan sanda suka zo suka tafi damu da gawar hospital, sai bayan mun tafi na saka aka kawo Ummi wacce tashin hankali ya saka ta suma sai asubah ta farka a lokacin an gama bincike an gano Naja'atu ce ta kashe Abbu aka bamu gawar nida Ummi muka masa wanka zuwa 7 na safe gidanmu ya cika da jama'a ba masaqar haqqi, labari yaje kunnensu Haleesa da Hanan nace su bari sazo anutse tinda kin tafi can su zauna dan Allah idan zaki dawo kuzo tinda yanzu ba gawar zasu iske ba.
Humm mahaifin Naja'atu da kansa ya tsine mata albarka haka uwarta bayan kwana uku da rasuwar Abbu kotu ta yankewa Naja'atu hukuncin kisa sbd cikakken shedu.
Mutuwar Abbu bata 'karasa wata 'dayaba naji na tsani 'kasar da take mahaifata baki 'daya, na fara bincike 'kasar da take akwai larabawa amman wa'danda suke marasa arziqi dayawa, kuma wacce take cu'de da baqar fata.
Nan goggle nasamu sunan Chad na fara bincike.
Cikin lokaci 'kan'kani na tarkata kan dukiyata, wacce take mallakina wacce nake nema da zufana dan ina manyan Business ga aikina na soja, wanda ina samun albashi me yawon gaske.
Randa nace nabar aikin soja na mayar musu da komai nasu har manyana sai da sukayi kuka, ba ka'dan ba.
Na gayama Abby shawaran da na yanke akan barin 'kasar Sam bai hanani ba, sbd yasan naji zafin kisan gillar da Naja'atu tama mahaifina.
Ni na fara zuwa Chad kai tsaye gida na nema mai kyawu da tsari na siya, na kuma sayi 'katon fili wanda nakeson na za'bi kalar ginin da nakeso.
Ina dawowa na siyar da gidana na bar 'katon gidan mahaifinmu wanda nasan dole zamu dunga zuwa, dukiyar abbu kuwa duk abanki sbd nida Hanan ne 'ya'yansa, na 'dauki mahaifiyata muka koma Chad.
Cikin wata 'daya na fara haraka business 'dina, Haleesa da Hanan dake kuka zo Chad kina ta famar tambayata Naja'atu na dai ce miki mun rabu Abbu kuma ya rasu kikayi ta kuka.
Na nema miki makaranta me tsada kikaci gaba da karatunki, karatun Qur'ani kuwa da sauran litattafan addini malami na 'dauka yana koya miki agida. Cikin shekaru hu'du a Tchad da nayi, nayi suna sosai kamar wanda akace arziqina agarin yake abun har tsoro yake bani ashe da ba arziqi gareni ba, cikin shekarun nan nayi gidaje uku manyan amman wannan da muke ciki yafi girma, nayi companys biyu kowa kaji yana kiran sunana inada manyan abokan kasuwanci k'asashen duniya da dama wanda nake zuba hannun jari a companynsu.
Ni dake shaquwarmu tafi ta da, ina 'dan tuna miki an miki miji ki riqe kimar kanki kisan kinada aure, sai kiyi dariya ki rungumeni kice.
“Abienha wasa kake na Sani ai.â€
Ni kuma nayi murmushi na sumbaci kumatunki na ce“Iya gaskiyar na gaya miki Babyna.â€
Sanin ke d'in halalinace ban damuba da duk irin shigewar jikina da kike ban ta'ba sakawa araina ba, inajin wani abu game dake dan nasan akwai lokaci. alokacin ne kuma kika kammala secondary school, kika ce Espagne kikeson karatu sai da na fara siya miki gida a can tamfatsetsan sa na 'daukeki na kaiki alokacin ne kuma mata suka addabeni wlh ni kuma bana son ko mgnar so wata mace tamin, shiyasa duk nacinsu sukayinsuka barni, amman Rayyana ta addabi rayuwata duk da ganina na mata wahala amman tsabar naci irin Nata sai da ta samu ganawa da Ummi ta shiga jikinta wataran har wuni take zuwa nan ta yi ta mata hidima ta zamar kalar tausayi anfi shekara ahaka ban ta'ba ko amsa gaisuwarta ba, ummina tausayin Rayyana yasa ta sameni ta min mgna akan nayi hkr na aureta tinda karatunki da saura sosai, ba duka mata suka taru suka zama 'dayaba ta jaraba Rayyana ta ga tsakani da Allah take sona, kawai dai na bita da toh ne amman zuciyata San bata kwanta min da ita ba.
Kamar wasa Ummi ta tisoni gaba lokacine kuma na siyi gida a Australia me azabar kyau, na kuma siyi filinki anan Chad wanda zan Gina asibitin Yara babba da sunaki.
Ganin Ummi ta matsamin na samu Rayyana na gindaya mata sharu'dana akan bazan kusanceta ba sai naga yadda zamanmu ya bada, ban kuma San ranan ba, sannan karta dinga shiga sabgana idan bani ne na nemeta ba, na haramta mata zuwa sashena har sai idan nine na nemeta karta kuskura ta tambayeni na sauke mata haqqinta tinda na fa'damata gaskiya, banda takurama 'diyata idan tazo hutu,duk ta amsa da ta amince cikin 'dauki, nan na saka aka gyara musu gidansu ba laifi na siya musu kujero da kayan kallo da komai aka zuba agidan, sai lokacin nake fa'da miki kikayi murna sosai amman lokacin kuna jaraba ba damar zuwa.
Bayan magnar da wata 'daya aka 'daura aurenmu, Sam banyi wata gayyar jama'a ba sosai wajan 'daurin aure.
Farkon zuwanta sosai ta kwantar da kanta tana bin dukkan dokokin da na gindaya mata, tanama Jaddatu biyayya sosai komai ita kemata, amman hakan bai saka na yarda wani abu ya ha'damu ba,iya gaisuwa har ta cika wata biyar ko shidda ne na manta alokacin kuka samu hutu kikazo sai dai naga kamar babu ruwanki da ita sabgar gabanki kike duk da kuna mutunta juna, azuwanki ne bai fi satiba ta fara min qorafin sai na bata haqqinta wanda lokacin 'koshi ya gama ratsata ga jin da'din duniya wanda ni kaina nasan tana buqatar namiji, naso sallamarta amman ina ganin bai daceba.
Akuma zuwanki ne na fahimci tana masifar kishinki sosai sbd yadda take ganinmu dake komai nawa kece ashine ta 'kulla wannan tuggun da zuciyata takusa bugawa, wanda Allah ne kawai ya dubi zuciya sbd da shi ka'dai na dogara ya kuma ce mu dogara da shi zai yayema dukkan damuwarmu sai dai wani lokacin rashin ha'kurinmu yake sanya muga kamar mun roqi Allah bai amsa mana ba, amman da zamu tsarkake zuciyarmu idan munada buqata wajan Allah idan mun roqesa mubar wasiwasi tabbas zamuga sakammako mai kyau, kamar yadda na amshi jarabawata akanki da soyayyar Ja'afar da nayi gajan hkr ko amatsayina na mai ku'di nace na 'dauki mummunan mataki, akansa kafin na gano tuggun Rayyana ne toh da nine zanyi nadama ba Rayyana ba, amman ina sane na shareta na sakamata idanu ban fasa gayawa Allah Rana tsaka ta tonawa kanta asiri bayan Allah ya warware 'kullun da ta muku.
Ajiyar zuciya ya sauke ya ce“Tana sona amman tanada son zuciya abin duniya take so tabbas nan gaba idan ta samu waje zatayi abinda yafi na farko kina zaman 'diyata ta cutar dake bare matata, banida burin ha'daki da kowace mace ke 'daya kin isheni rayuwa, zaman da nayi da ita darajar mahaifiyata ce yasa na zauna da ita, amman tin bayan da asirinta ya toni ta matsa na saketa daman jira nake kisan matsayinki ta kuma sheda hakan agaban kowa kafin na saketa na bata jari ta qara gaba, idan kuma tazo da hauka sai na fasa ta qara gaba ina duba maricinta ne da yayarta tanada kirki ba wai dan halinta zanyi ba. Baby kinji dukkan abubuawan da suka faru arayuwarmu.â€
Ya 'karashe mgnar ya tallabo fuskarta yana kallonta, murmushi 'dauke akan fuskarta.
Itama kallonsa tai ta jinjina masa kai cikin sanyin mgna ta ce“Abie ashe ammi ce ta ha'dani da yaron nan? Taje na yafe mata amman Abie karka saketa sbd dani pls kaji?â€
Hararenta yay ya sanya bakinsa saman la'bbanta ya cijeta ka'dan, ta saki qara tana qamqameshi ashagwa'be ta ce“Abie Rabin raina zafi.â€
akunne ya ra'da mata, “Sorry my baby ko za ki ramane?â€
Ya tambayeta yana cizon fatar kunneta ahankali.
Qara ta saki tana fa'din“Wayyo Abie zafi fa!â€
Chapter 88 · 0% Book details