← Book details Dattijon Arziki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 118

Sashe 23

Dattijon Arziki Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Raiyana tsaye tana waya cikin shiga ta alfarma, fuskar nan tata cikin fara'a sai wani irin 'kayataccan murmushi take, ka ganinta kasan duniyar na mata da'di.
“Auntie Saro ki sha kuruminki duniya sabuwa, billahilazi la'ilah illah huwa! Bari zan fita zan biyo gida bye.â€
Bata jira auntie Saro tai mgna ba, ta katse kiran ta dannawa Wahida kira.
Bugu 'daya ta 'daga, ta bushe da dariya ta ce“Tabbas bakina yay ka'dan wajan gode miki, ki shirya yanzu zanzo mu tafi Malam ya ce muzo.â€
'Kitt ta katse kiran, tana murmushi ta sa'bi jakarta tana waqa.
Jaddatu zaune cikin falon, tana kallon tashar Aljazeera, Hanan na gefe tana waya, Iman nata wasanta.
Raiyana ta qaraso da sallama ta zu'be qasa dab da qafafun Jaddatu ta ce.
“Ummi zan 'dan leqo gida auntie Saro ba lfy.â€
Jaddatu ta ce“Subahanallahi! Allah ya bata lfy. Wai Rahma bata dawo daga gyaran gashin ba?â€
Raiyana ta kwantar da murya ta ce“Ummi ai bata jima ba zata dawo na tafi.â€
Hanan ta ce“Ba dan qiwuya ba da na biki.â€
Raiyana ta ce“Karki damu akwai gaba Hanan Ngd.â€
Sallama sukayi ta fita.
Jaddatu ta ce“Hanan inaga Rahma fa jinnu na damunta, sbd gaskiya ta canza sosai, abin ya tashi daga kanmu ya koma kan Abienta.â€
Hanan ta ce“Wlh nafi zargin wani abun yake damunta bari ta dawo zan mata tambaya a nutse.â€

Raiyana Yahaya direba ya fita da ita, sai da sukayi nisa sosai ta ce“Yahaya idan munje zaka saukeni sai ka dawo, idan na gama abinda nake zan kira ka.â€
Cikin ladabi ya amsa da “Toh hajiya.â€

Ibtisam zaune kusan Falmata, su na gyaran shinkafar da zasu girka da dare, yayin da Binta kusan warin Ibtisam take gyara kayan miya.
Ibtisam duk bata jin da'di gabanta sai matsanecin fa'duwa yake.
Falmata ta kalleta ta ce“Ibtisam yau lafiyarki kuwa?â€
Kanta 'kasa ta ce“Mamie gabana yake fa'duwa, amman inata addu'a.â€
“Yauwa kici gaba da addu'a.â€
“Toh mamie.â€
Ta amsa ta mi'ke ta 'dauki buta ta shiga bayi.
Wayarta ta ciro arigarta ta dannawa Ja'afar Kira.

Can kuwa 'bangaran Ja'afar da Rahma, tafiya kawai suke sunata hirar soyayya kamar wasu tsofaffun masoya, sbd shaukin da suke ciki sam Ja'afar baisan sun bar gari ba har sun fara riskar jeji.
Rahma ta kamo hannun Ja'afar 'dayan yana driving da 'daya ta jim'ke cikin nata ta marerece ta kirasa “Habiby na.â€
Kallonta yay “Qalbina mene ne?†ta shagwa'be fuska da larabci ta ce.
“Habiby na atini ma'ou sa ashrab.â€
“Ya Rabbi! Ban jin larabci Qalbina.â€
Ashagwa'be ta ce“Habiby na ka ban ruwa na sha.â€
“Ok kar kiyi kuka.â€
Cikin sa'a akwai robar faro guda uku ta Ma'aruf, ya gangara bakin titi yay parking ya bu'de mata murfin ya bata.
Ma'kale kafa'da tai ta ce“ban amsa kai zaka ban abaki ko nayi kuka.â€
Ja'afar ya lakaci hancinta ya tallafo fuskarta da tafin hannunsa 'daya.
Idanu suka 'kurawa juna kamar zasu cinye junansu zuciyoyinsu na wani irin bugu, dak-dak.
Ita ma tattausan tafin hannunta ta sanya ta riqe fuskarshi tana shafa sajansa.
Yatsunsa biyu ya zura cikin 'dan 'karamin Jan bakinta, ya kafa mata bottle 'din ruwan ta fara kwankwa'da, idanunsu manne waje 'daya.
Tana idar da shan ruwan ta marerece ta ce“Habiby na kana sona?â€
Hancinta ya lakata dai-dai zaiyi mgna kiran Ibtisam ya shigo.
Wayar ya zaro daga gaban aljihun rigarsa.
Ganin Ibtisam ce ya saka ya kalli Rahma wacce ta kwantar da kanta kafa'dar sa tana kallon ba'kar kyakkyawar fuskar shi.
Fuskarta ya shafa, yay picking call 'din ya manna wayar kunnensa yay mata sallama.
Ibtisam daga can ta sanya kuka ta ce“Mon amour kana lfy kuwa?â€
Ja'afar ya ce“Subahanallahi! Mon cÅ“ur! Mene ne na kuka wlh ina lfy, yi shiru kinji.â€
Ibtisam ta sauke ajiyar zuciya ta ce“Toh mon amour nayi sai ka dawo je t'aime. â€
“Moi aussi je t'aime bcp bye muahhhhh....â€
Wayar yaji Rahma ta fizge ta katse Kiran tai jifa da ita side 'din baya ta fashe da kuka jikinta na 'bari.
Ja'afar ya rikice hankalinsa yay mugun tashi ya tarairayota jikinsa ya mannata 'kirjinsa, ya shiga lallashinta shima hawaye yake ganin kukanta duniyar tai masa zafi, ga wani irin 'kunci da yake ji.
Jin 'dumin hawayen Ja'afar da ya sauka gefen wuyanta ya saka Rahma 'dago da kanta ta kalleshi.
Cikin rikita ta tallafo fuskarshi cikin tafin hannunta, ta ce“Kayi hkr habibyna na daina kukan amman don Allah karka min kishiya kaji¿â€
Ja'afar ya ce“Zanyi qoqarin miki duk abinda kikeso Qalbina amman ki daina kuka kinji?â€
Kai ta 'daga masa tana sakar masa sansanyan murmushi, ta goge masa hawayen fuskar shi, ta gyara zamanta ta basa sauran ruwan ya sha, ya ma motar key, yaci gaba da driving.

Ibtisam jin Ja'afar lafiyarsa lau, taji da'di sosai ta saki jikinta sunata aikin 'dora girkin dare.
Yahaya gidan Wahida ya ajiyeta ya juyawarsa gida.
Bayan sun gaisa suka fito bakin titi suka tari me taxi sai gidan Malam daman Raiyana sanye take da niqab.
Kai tsaye unguwan *Amriguebé*
Aka kaisu.
Wani gidane can kan tudu.
Lokacin da sukazo sama da mutum 10 suna bin layi, su ka zauna har layi yazo kansu.
Wani siririn mutum ne zaune, yana Jan wani babban casbi, wanda ya cika masa gaba, mai dubu ne cass ajere .
wankan tarwa'da ne a'kalla zai kai shekaru 45 ahaife, sanye yake da manyan kaya harda rawani na buro uba, ya na'de akansa.
Wasu irin kayayyaki ne na tsubbu ajibge agabansa, kama tin daga wasu irin qore kwalaban turaren tsubbu faifai allon 'karfe, da sauran abubuwan da sam idan ba shine ya maka bayani ba bazaka ta'ba ganewa ba.
Zaune suke gabansa yayin da suka basa dukkan hankalinsu da nutsuwarsu, su na kallon wannan uban tulin casbi wanda yake famar jansa, bai tankasu ba har yanzu.
A saman wani 'katon faifa wanda yake cike da 'kasa fara tass mai kyawu, ya 'dora casbin.
Hannayensa duka ya kifa saman faifan yana sadda kansa qasa sosai yana wasu irin siddabaru.
Wanda kakejin wani irin kuka kuka dariya dariya na tashi ka'dan-ka'dan. Sai wasu manyan kwalabe guda biyu sunata motsi suna gwara kansu, wani irin sautin qara na tashi.
Raiyana ta firgice sosai matuqa sabida afarko bataga irin wannan abubuwan ba, sam baiyi abin ban tsoroba, hoton Ja'afar da Rahma da sunayensu kawai ya ce ta kawo masa, bayan kwana 3 uku ya ce ta dawo ta amshi sakammako, shine ya bata strawberry roba biyu ya ce tai qoqari kowa ya ci roba koda 'dayace an gama aiki, sai bayan kwana biyu ta dawo.
'Kasar faifan ta riki'de ta koma baqa qirin.
“Hajiya leqo kiga aiki yayi fa! Manyan aljanune miji da mata muka tura musu, bayan sunci wannan strawberry 'din sun shigesu, tsananin soyayyar da sukewa juna itace zata dinga gudana tsakanin Rahma da Ja'afar. Dan Rahma aduniya ayanzu bata 'kaunar kowa bata son zama da kowa idan ba Ja'afar ba, ba zata ta'ba iya rayuwa a wannan qarnin da ake ciki ba sai da Ja'afar. Haka shima, sai dai shi bai kamu irinta ba, sbd yawan addu'ar da yake, ga ta iyayansa, sbd son da yakewa budurwarsa na nan cikin ransa ba zai fita ba, sai dai ayanzu zaifi jin son Rahma, ku matso kuga *BARBARUNDA DA BARA'UNTA*
Sun sakasu fita daga gari, idan kinaso suje wata qasa ko wani gari wanda har abdan sun tafi zasu iya tafiya dasu....â€
Rainaya lokacin da ta ga Rahma da Ja'afar acikin faifa yana sharara uban gudu a mota, Rahma ta kwantar da kanta saman 'kirjinsa, suna hira harda dariya. Abin ya girgizata ya bata tsoro matuqa.
Cikin rawar jiki ta damqe Wahida ta ce.
“A'a Malam a maidosu don Allah karsu bar gari a maida su Rahma ta kaisa wajan Abienta ta ce shi take so a aure mata shi kuma karya musu, ya aura mata shi don Allah. â€
Malam damuna yay dariya ya ce.
“Wlh bazai ta'ba kamuwa ba yadda kikeso ba yadda banyi ba dattijon atsaye yake fiye da tunaninki, ga mahaifiyarsa bata baccin kirki ko wane lokaci addu'a take masa. Abu 'dayane dai zai yarda da auren sbd tsananin son da yake mata, shima sai yaga tana neman rasa ranta, sbd bai son ta auri ba'ki yafi son balarabe 'dan uwansa. Amman ki shirya akwai wata gagarumar matsalar bayan kin samu cikar burinki, dan zai saurareki ba dan sihirin zaiyi tasiri akansa ba, sai wani dalili daban wanda Allah bai ban ikon gano ko meye ba.â€
Raiyana ta dafe 'kirjinta ta ce“Na shiga ukuna! Matsala malan?â€
“Eh amman zan magance miki ita, yanzu dai abinda za ki kawo abawa ma'auratan jinnu shine ba'kar saniya qosassa, sai ba'kin sa, da ba'kin bunsuru sai jar akuya da zakara uku farare tass da ku'di jaka 'dari za ki ga me zai biyo baya cikin satin nan, bayan an saka aurensu zan fa'da miki sharu'da idan kin kuskure ki tabbata akwai matsala.â€
Raiyana ta ce“Ngd malan damuna za'a kawo duk abinda ka lissafa Wahida gobe sai ki kawo ku'din ya siya yanzu ga jaka 'darin.â€
Ta juye masa ku'din gabansa.
Wahida ta ce“Mun gode aikinka na yadda akeso.â€
Bayan sun fito bakin titi su ka tari taxi kai tsaye sai unguwar (Joumal)
Gidansu Raiyana.
Chapter 23 · 0% Book details