← Book details Dattijon Arziki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 117 OF 118

Sashe 117

Dattijon Arziki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yau 'diyan Rahma suka cika wata uku cif yau aka sallamesu daga hospital idan kaga murna wajan Rahma da Abie abin baya fad'uwa.
idan kunga yadda Abdulwahab wanda suke kiransa da Dady UmmulAymana kuwa da Mamy suke kiranta masha Allah idan ka kallesu sai ka kuma bazaka tab'a cewa bakwain ne ba sunyi wani irin girma da wayo gasu da dariya Dady kuwa akwai shan yatsa.

Ibtisma ma ayau suka iso Chad Ja'afar yaje ya kawosu, masha Allah ita da 'danta sunyi wani irin girma yaron tamkar yakai wata hud'u katone sosai ga shi baida kuka.

Tinda suka iso taba Ja'afar Rafael ya kaisa gidan Baba Tsalha ita kuma ta shiga gyaran gidanta kafin yamma tsaf ta gyara ko ina ta d'aura musu girki.

Ibtisam ta fito daga wanka d'aure da towel take jiyo kukan Rafael, murmushi tai ta ce“Ai kam yaron nan yayi qoqari ai kam da ya bari naje.â€

Qaran bud'e k'ofa taji ta waigo,tana goge jikinta da qaramin towel.
Idanu suka had'a da J'afar ya shigo d'akin yana rungume da Rafael, yana tsala kuka.
Dariya tai tana fad'in.
“Mon Amour haka ake reno? Ka wani matse yaro.â€
Wani irin kallo mai cike da so da sha'awa da k'auna yake aika mata.

Fari tai da idanu tana d'aga masa gira.
Da sassarfa ya qaraso wajanta ya had'asu da yaron ya manne aqirjinsa.
D'an qara tai tana kallonsa.
Gira ya d'ga mata ya ce“Kinci bashi zuwa dare, oya basa abincinsa.â€
Amsarsa tai tana zama gefen gado ta fara shayar da yaron ashagawab'e ta ce.
“Mon amour yaushe zamu je gaishe da da Baba Tsalha da Jaddatu daga can nagano auntie Rahma?â€
“Zuwa gobe insha Allahu, yau sai kin biya bashi.â€
Ya k'arashe mgnar yana sumbatar wuyanta yana shafa fuskarta.
Dariya kawai take masa ganin yadda ya wani sakata gaba yana matsata ita dai yaronta take shayarwa.

Rahma tinda sukazo gida tai wanka ta shirya cikin riga da skirt na material tayi wani irin kyau tamkar Dady da Mamy ba daga tsatsonta suka fito ba.
Zaune suke a babban falon tana kallon yadda aka sake canza komai na falon, Merrah na wasa da Many tana b'angala dariya, Dady kuwa na wajan Jaddatu ta Hana kowa d'aukanta yaron baya gundurata.

Abie ne ya shigo yana waya.
Idanu suka taurawa juna shi da Rahma.
Kai ta langwab'ar tana tutturo masa bakinta, da idanu tana take masa magana.
Murmushi mai taushi ya sakar mata, yana d'aga mata gira ya qaraso falon ya nufi wajan Mamy tana harba k'afafu ya sunkuya ya amsheta hannun Meerah yana murmushi ya sumabceta ya ce“Aymana wayo koh?â€
Meerah tai dariya ta ce.
“Masha Allah kamar sunyi wata hud'u ko biyar.â€
Murmushi yay ya nufi wajan Jaddatu ya zauna, yana kallon Dady yanajin tsananin k'aunar yaran har cikin jininsa.

“Ok Mustapah karka wani damu komai zaiyi daidai insha Allah, ngd ok bye zuwa jibi inada meeting a mexico da na dawo za'a San abunyi.â€
Jaddatu ta ce“Allah ya qara rufa maka asiri ya mama albarka.â€
Rungumeta yay ita da Dady ya amsa da.
“Ameen Ummina.â€
Ya k'arashe mgnar yana kallon Rahma wacce ta shagwab'e fuska tana kallon Mamy na harbe-harbenta, Meerah na mata wasa.
Miqewa Rahma tai irin tayi fushi Abie yaqi mata mgna ta haura sama.
Jaddatu ta ce.
“Takwara ina zaki? kije da Aymana ki bata Tasha, kinji doctor ya ce kar abarsu suna jin yunwa naga baki basu mono ba tinda mukazo madaran ma basu shaba sosai.â€
Rahma ta dawo ta zauna ta ce.
“Ummi da kwanciya zanyi kaina naji yana ciwo kad'an.â€
Abie danne dariyarsa yay yasan k'arya take fushi tai.
Jaddatu ta ce.
“Subahanallahi sannu to ki shayar dasu ki barsu sai kije ki kwanta, Abdul d'auko mata magani.â€
Rahma ta mashi Mamy ta fara shayar da ita.
Yarinyar tana Sha tana kallon Rahma k'urrr Rahma ahankali ta ce.
“Mamana kallo koh?â€
Karaf akunnen Abie.

Tana shayar dasu ta barsu ta haye sama bedroom d'insu wacce basa Iya rabawa ita da Abie ta shiga ta Mirza key tai kwanciyarta tanajinsa yazo taqi bud'ewa Abie abun dariya ya basa shi ssam baiga abinda ya mata ba Har dare Rahma fushi take da Abie,
Bayan yaran sunyi bacci Rahma kwantar da kowane saman gadonsa taje tai wanka ta shiyar cikin wasu irn kayan bacci masu masifar kyau, tana wani irin k'amshi.

Abie na falo zaune waya yake yana Danna laptop.
Wani irin qamshinta ya daki hancisa yay saurin d'ago da kansa ya kalleta.
Kai ta d'auke tana turo baki, sai wani irin taku takeyi jikinta ko ina motsawa yakeyi kayan jikinta na bacci basuda maraba da tsirara, gabansa tazo ta gifta tana qoqarin nufar hanyar fita.
Da sauri Abie ya miqe yana fad'in.
“Hamza! Wani uzuri ya taso min gobe insha Allahu zamuyi mgna.â€
Bai tsaya jin abinda Hamza zai ce ba ya katse kiran ya jefar da wayan kan sofa ya nufi wajanta da sassarfa ya damqo hannunta ya juyo da ita gabansa ya riqo k'ugunta ya mannata da k'irjinsa ya tura fuskarsa tsakanin k'irjinta yana shafa k'ugunta can k'asa² ya ce.

“My baby me nayi take fushi Dani haka? Haba my honey wata uku bama keb'ewa yau kuma kina fushi da Abienki abin sonki?â€
Kukan shagwab'a ta saka masa ta ce.
“Yo My Abieh ba kaibane ka wani shareni d'azu da yamma yaranka kawai ka kula, ni kuma inata kewarka inata missing d'inka inata sonka my Sweety darling. â€
Ta k'arashe mganr tana kallonsa tana turo baki.
Abie ya d'auketa sama yana juyi da ita tsakiyar falon ya ce“Wallahi nafi damuwa dake nafi sonki akan yaranmu ki Lura mana babyna Ummina na wajan ba daman na rungumeki na miki kiss yanzu dai yi hkr na amshi laifina OK? â€

Ashagwab'e ta ce “Ok naji toh goyani.â€
Bayansa ya sab'ata yana zagaya falon da ita tana b'angala dariya, kamar wata baby ya nufi bedroom d ita.

Kwantar da ita yay ya nufi wajan yaransu ya tofesu da addu'a ya dawo ya kashe wutan d'akin ya haye bed qamqame juna sukayi suna murmushi Abie ya fara cire kayan jikinta yanabi ko ina nata da kiss na fece sabida yau aikin babbane.

B'angaran Ja'afar ma da Ibtisam yau sun raya darwn ciki da dumbin tarihi sun gurji junansu.

Washegari Rahma jikinta ko ina ciwo yake mata sabida da asubaha ma bayan sallah sai da yay making love.
Misalin goma ta farka lokacin Abie ya shirya yaran yazo ya sanyasu gabanta ya basu abincinsu saida suka k'oshi ya kaisu wajan Jaddatu.

Breakfast tai ta sake shayar da yaran ta ta barsu ta tafi b'angaran Meerah.

Bayan wata d'aya, Rahma yaranta tsotsa yanzuma tserewa tai b'angaran Abie2 ta barosu wajan Jaddatu.
Iskowa tai Meerah ba lafiya zazzab'i sun dawo daga asibitin ciki wata biyu.
Rahma tai ihu ta b'ire kan Abie2 tana fad'in.
Abie2 nah Ashe bayan kai zan sake ganin dangin Mamyna.?â€
Abie2 yay murmushi ya ce.
“Rahma bakya girma ai mu kam tinda munada Abie da Ummi sun ishemu sune komai namu ga kuma Meerah zata fara bamu sabuwar zuri'ah.â€
Meerah ta ce.
“Ni kun wareni kenan?â€
Rahma ta Saki Abie2 ta rungume Meerah ta ce“Ai kam kallon Abie nake miki har abadan mamyna.â€
Dariya sukayi nan sukaci gaba da hirasu sai da Abie2 ya kori Rahma dan batada niyar tafiya.

Kwance tashi ba wuya har Allah ya sauki Rayyana lafiya ta samu 'ya mace mai kyau wace ta d'auko baqin mahaifinta amman sosai tana Kama da Rayyana. An samu Asma'ulhusna, sosai take samun kulawa wajan mijinta yarinyarta kuwa ita kanta tasna tanada gata wajan yayunta.

Auntien saro ma ta samu wani dattijo na gari tayi aure suna zaune lafiya bata rufe wata shidda ba itama ciki ya b'ullo.

Aishatu Gabon itama tanada ciki haihuwa yau ko gobe sai muce Allah ya raba lafiya. Ma'aruf yanzu kam.kud'i Hamdan ba laifi sunfi qarfin abincinsu motar hawa sutura ga shi da bayar da sadaka Farook anyi wayo sosai masha Allah.

Meerah ma ciki ya tsufa taso zuwa gida haihuwa Rahma ta roqeta ta bari bayan haihuwarta zasuje tare itama tana son zuwa ganinsu Abby Morocco.
Ibtisam da Ja'afar anata zuba love suna renon Rafael sai wayo yake masha Allah yana tafiyarsa ko ina kamaninsa da Ja'afar na qara fitowa.

Masha Allah Ja'afar harakan kasuwancinsu na company na k'ara hab'aka, addu'a ba dare ba Rana duk wani me nemansu da sharri Allah ya tsaresu.
Harisu anyi bikinsa da Maimuna k'anwar Ja'afar, Taslim ta samu wani yaro mai shegen kud'i ga hankali bikinsu watan gobe su Ibtisam sai shirye² tafiya akeyi.

Inna yanzu masha Allah an FASA tuyar waina Ja'afar ya hana tin kafin auren Maimuna ya kashe gidansu an yimusu gini mai kyau na zamani abun sai Wanda yagani Mal Adamu ma ya hanasa siyar da ruwan duk da yaqi yana zuwa abinsa, ya ce baya son zaman gida hakan bai saba.
Mahmoud ma a samu aikinsa ba laifi shima bayan sallar azumi bikinsa da wata yarin nan bayan layinsu.

Jaddatu Alhmllah zamu sabida tana qoqarin kulawa da Rahma da Abien, jikin tsufa yau da lafiya gobe jiki ya tab'u haka lamarin yake amman masha allahu har yanzu da k'warinta.
Sosai Ibtisam da Rahma suke zumunci masha Allahu, Abie ya d'auki Ja'afar kamar d'an uwansa.

Rahma tsaye ta fito da wanka.

Idanu ta zaro ganin Dady da Mamy tsaye suna janyo kayan kwaliyarta suna watsarwa, sunyi baja-baja da kayan dressing mirror.
“Wayyo ni Rahama na shiga uku Yara wata goma Sha uku amman sun iya shegiyar b'arna haka sabida Allah, wlh sai na zaneku.â€
Ta k'arashe mganr tana nufar wajansu aguje suna ihu suka fita suka nufi falo ta biyosu.

Jikin Abie suka fad'a suna sakin kuka.
Turis ta tsaya tana hararensu.
Abie ya ce.
“Don Allah Baby kije Allah ya baki hkr zan biyaki abinda suka lalata kinji amman bar raza min su.â€

Baki ta zumb'uro ta ce.
“Ai wallahi daman nasan ni yanzu tawa ta qare baka sona sai Dady da Mamy.â€
Ta k'arashe mgnar tana juyawa bedroom.
Dariya Abie yay yana rungume yaran ya ce.
“Ku kam Allah ya shiryamin Ku kuna d'aukomin mgna wajan Manmmy yanzu dai cikin wata biyun nan ramuwa nawa kuka sakani wajanta?â€
Chapter 117 · 0% Book details